Showing 21001 words to 24000 words out of 304363 words
a hankali lokacin shi yanawa ummah bayanin halinda ya sameni ciki hankalin umma ya tashi sosai lokaci guda ga zancen data sama nata anayi dakin mama ga kuma wanan matsalana a yanzu.
Nan tayi mai godiya suka kamani bayan ummah tace don Allah ya jira ai masa sako yace shi don Allah ya taimakeni ai badon wani abu ba.
Bawan Allah mun gode don Allah ka taimaka muna da wanan maganin da kace shi ka shaka mata ta dawo daidai din kaga sai a dinga mata amfani dashi Tani ku shiga ki dauko leda ko kuma barin shigo dai ummah ta fada.
Ta biyo bayan mu duk da yace bai karban kudi haka bai hana ummah bayar da dubu biyar akai mashi ba da leda amma yaki karban kudin ya dai raba maganin biyu yayi alkwarin zai karo aimun amfani dashi.
Ikon Allah ashe har yanzu akwai irin yaran nan karamin yaro haka da halin manya ummah ta fada ta maida kallonta gareni kuma kafin ta nisa don abubuwan sun daure mata kai a lokaci guda haka gashi kuma bata ko karbi lamban matashin ba har ya tafi.
Tsuki taja sai tani ke fadin hjy wani abin ne wallahi ya kamata ace mun amshi layin yaron nan amma rudewa yasa mun barshi ya tafi bamu karba ba.
Hjy ni ai har gidan su yayi min kwantace na kuma gane layin nasu kai amma kin kyauta min Tani don in maganin yana da kyau ai dole mu nema mu aje a wurin mu don bacin rana irin haka.
Barci nayi sosai ranan saidai ina tashi naji wasai ba wanan ciwon kan ko gani dishi dishi gashi na koma ina jina normal dani kamar ba abinda ya faru dani.
Saidai da idan na tuna da abinda ya faru dani sai naji nauyi da kunyar hakan amma idan kuma natuno da abinda wanan matashin ya fada sai naji somehow amma aiba kowane yasan haka ba na fada ni daya a daki ina jan tsoki
Itako ummah kantane ya kara daurewa sosai da lamarin mama don data fito har kofa ummah suke yarta tana sallama ummah din saiki rantse babu wani abinda ya taba hadasu ko suke shiryawa a kasa daya shafi kisantaka irin na matan da basu da hakkuri da tawakkali ga ubangiji.
Shin ko sun dade suna mata wanan bata gano bane sai yanzu da ubangiji ya haska mata har taji da kunnuwanta ba wani ya fada mata ba amma sai gashi taji komai a saukake.
Har da shigowa dakin suna gaida maamah da jiki sukai Allah ya sauwaka kamar da gaske sun damu bayan fitan su ta lekasu sai gashi suna dariya kamar wasu yara dasu irin nuna sam basu damu ba su.
Ranan haka ummah ta kwana cikin damuwa da tashin hankali har gari ya waye tun kan tayi sallah saida ta leka dakina ta tasheni da barci na tashi nayi sallah.
Sam ummah bata zata zan samu zuwa makaranta ba a ranan sai gashi na fito da shirina ina sallaman ummah din bata yarda na fita gida ba saida ta tabbatar da cewa na karya kafin na fita.
Dkn Tani bata riga da ta iso ba a lokacin don haka ummah ta hada min shayi da ruwan flask din dake dakinta ruwan tea din kawai nasha ban hada da komai ba nasha na fita.
Tani don damuwan data kwana dashi bata zo gidan mu ba direct data fito sai ta wuce gidan wanan matashin don ta karbo maganin tayi sa,a ta sameshi ya fito zai tafi school.
Saida ta tuna mai ko ita wacece tare da fada mai sakon hjy yasa ya dubi lokaci yace su shiga daga ciki tabi bayan shi zuwa cikin gidan tana bin ko ina na gidan da kallon mamakin iri rayuwan talaucin da bayin Allah nan keyi a cikin gidan nasu.
Ke nan duk yadda kake ganin kanka kafi wani don wani na can bai kaika ba don nasa irin talaucin sudake cikin gida har da siminti a tsakar gidan tana ganin talaucinta ga wa yanan su dan dakunane kamar madafi suke rayuwa a ciki.
Nan yaiwa Dije dan bayani a gurguje ya barta da Tani su karasa maganan tunda shima itace ta karbo mashi don haka ita tasan yadda zasuyi bashi ba.
Nan ne hira ya barke a tsakanin su har take labartawa Dije komai har kudin dayaki karba hannun ummah din duk a cikin dadin hira Tani taba dije labarin komai.
Tare sukaje aka karbo malam Tanimu yayi masu bayanin komai yadda za,ayi amfani dashi har dana tsarin jiki da sauransu duk ya bada ta bashi dubu daya ya amsa yana ta godiya.
Hakan yasata makara da zuwa aiki koda tazo ta samu ummah tayi nisa ga aikin hada breakfast ummah taso tayi fada sai ga leda ta fito dashi tana fadin aida zancen ku na kwana a raina hjy.
Shiyasa na makara ga wanan na karbo dana uwar dakina wanka zakiyi har yaran kuyi hayaki wanan kuma yace kusha tun da asuba na neman sa,an makiyane da makarun su.
Kallonta ummah keyi kamar da tuhuma a zuciyar ta sai Tani din tace hjy ko baki aikeni ba ni mai zuwa na karbo maki wanan din don koba ki fada ba mai hankali yasan zaman da akeyi a wanan gida.
Ba wani abin muni na karbo maki ba kariyane da tsari ance ko kana da kyau kara da wanka don ni gaskiya ciwon nan da uwar dakina keyi kwanan nan da ayar tambaya a cikinsa.
Ciwo bai tashi sai lokacin da yarinya zata je daukan darasi kan abinda zai amfaneta a rayuwa kinga wanan alaman wani sherine dake faruwa a wani kulli dake faruwa a wani wurin.
Kome ke faruwa da ita da sanin Allah nasan ina iya addua na kan zuri,ata koda yaushe ina neman kariya gun ubangijina da ya tsare mu kan abinda bamu sani ba mai cutarwa zuwa garemu.
Kwarai kuwa hjy nidin shedace kan hakan nasan baki wasa wurin ibadan ki don shine ma har yau ba a ci galaba a gareki ba amma kuma ki sani.
Yaran nan zaki duba idan ana harin ka ba a sameka ba za a iya samun yaran ka ko wani abin ka shine dadin kiwon dabba da kikaga mutanen kauye sunayi.
Sun san ma,anan hakan shiyasa ba kauye bai rabuwa da kiwo koda ta kazace kuwa don sai ya fadawa dabban naka don ansan naka dinne.
Kiga ko dole a tallafawa rayuwan yaran nan don maganan gaskiya hjy maimuna bata kaunan yaran nan ta yadda har bata iya boye hakan a gaban kowa saboda kishin ki daya shafesu.
Nisawa ummah tayi kafin ta kai kallonta ga kullin maganin da Tani din ta karbo mata tace bawai ban sanda hakan bane na dade da sanin akwai kiyayya har ya shafi yarana saidai bana son na raja,a gun irin wa yan nan abubuwan ne har ya bata maka imanin ka.
Amma na gode in sha Allahu zan gwada zanyi muna amfani dashi da yardan Allah musanman kan ita maamah din don wanan matsalan nata ya fara damuna gaskiya.
Ciwo haka daga sama Allah na tuba ni wanan matsalan haka ta ina zan soma taron shi hjy haka na faruwa kana zaune da yaron lafiya da rana tsaka ya sauya ma .
In sha Allahu maamah tafi karfin duk wani shedani da shedanci ki dai dage kiyi masu amfani da wanan maganin koba komai ba a san inda kizo ke saka ba ai shiyasa akewa yara tsari da adduoi a yanzu sosai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[27/12/2022 11:39 AM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
1️8️⃣
AL AZIZ,,,,,,,,,,
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Allah ya taimakeni ba a wani taru sosai ba a makaranta amma haka nake ganin kamar idon kowa na kaina lokacin suna kallona haka na fito na rufo motana a hankali na tako yadda na saba tafiya a nutse zuwa department din mu.
Akwai mutane saidai ba sosai ba don safiyane sosai lokacin kamar yadda na saba shiga da siriryar sallama haka na shigo na dan gaisa da na kusa da ida na zauna daga haka na zaro takarduna na fara karatu.
Can na tuno da lecture din da ban samu attendedi ba jiyan da rana lokacin da abin ya sameni don dolene na koma gida saboda bana cikin hayacina lokacin.
Dago kai nayi na kalli ta gefena ina fadin don Allah yar uwa jiya an dauki attendaces ne na rana wani iri tayi far da idanu tana fadin ke baki ajine lokacin da aka dauka din.
Kaina girgiza tare da fadin banda lafiya na tafi gida ban samu daukan darasin rana ba jiya din kaita jijiga min tana fadin jandi kina da aiki ga wanan malamin da baijin Allah tana fadan haka ta juya ta barni cikin damuwa.
Har muka fito daga lectures din ina tunanen rashin yin attendance da ban samu yiba don nasan halin lectural din da zafin kai sosai da a hankalina nake ba abinda zaisa na yarda naje gida a lokacin.
Tun daga nisa na hango mutum yana bin motan da kallon mamaki saidai baiyi kama da dan makaranta ba shi don kayan jikinshi da suke kode duba ga yadda yan makaranta ke shigowa cikin kure adaka ko wani lokaci ba mazanba ba mata ba.
A hankali nake takowa cikin mamakin me yake nema a wurin motan daga bayan shi na tsaya ina mai sallama ya juyo yana amsa min tare da fadin ashe kin samu shigowa yau din ?
To yaya jikin naki banda waya naso na karbi layin mahaifiyar ki naji yadda kika kara ji sai rashin waya ya hana hakan saidai ki kula tunda kina da lalura koda kinji wani abu zaki iya nemana ina Science department UG four.
Sake kallon shi nayi ina mamaki a raina dan makarantane wai wanan din dama ashe ga yadda yake nunawa shine wanda ya kaini gida jiya ke nan nan na fara kokarin tuno da abinda ya faru jiya din tabas shine wanda ya tsaya ya kare min mutuncina a jiyan don ummah ta danyi min bayani kamar yadda yai mata shima.
Saida na nunashi da yatsa nace Kaine kaine dama ka taimaka min jiya nagode gida zaki tafine ya fada yana kawar da fuska gefe daya kamar baison kallona.
No mosque zan tafi nayi sallah daga nan saina tafi wurin malamin mu ya shigo jiya bana nan ya dauki attendance kuma baida sauki mutumin.
Wani department kike ya tambaya wanan karon yana kallona apply chemistry nake karantawa na bashi amsa kai tsaye.
Ok department din mu daya ke nan dake idan kina da matsala zaki iya nemana duk da ba wani sani nayi sosai ba kan haka.
Ki dai kula da addua kafin ki fito gida da kuma lokacin da zaki shiga school din don yanzu mutane sun baci sosai.
Saboda haka don Allah idan kinji alama ciwo zai taso ki samu wuri ki dinga natsuwa don jiya badon Allah ya gyara ba zaki iya halaka kanki a motan nan.
Don a yanzu taimako yayi karanci sai gulma dasa ido ga al,umma ana yadawa a duniya don mutane yanzu suna tsoron taimako saboda shiga fitinan jami,an tsaro.
Ki kula sosai saboda kasancewar ki mace don mutane basu da gaskiya yanzu yana kaiwa nan ya dago yace na barki lafiya dama motan nan da na gani nayi mamakin ganin kin shigo kuma school yau duba ga yadda na kaiki gida jiya a wani yanayi can.
Duk wanan bayanin da yakeyi sai kallon fuskanshi nakeyi ina son intuna inda nasan fuskan nasa saidai na kasa tuna hakan saida ya juya zai tafine na tuno ai shine wanan guy din na shagon abinci dana ga anaciwa mutunci har naji haushi matar a raina na taimakeshi.
Kayan jikinshi na kalla duk sun kode saboda tsufa ga takalman kafan shi duk sun kode sunyi wani baki dasu da ganin shi zagaka gane shi din fakirine na gaske tun daga duba ga yanayin shi kuma a haka yake rayuwa cikin diyan mayan da masu hali bai damu ba.
Wani irin tausayin shi naji ya shigeni lokaci guda sai naji matukar sanyin jiki gashi dai da halin kirki irin wanda ake son samun dan musulmi dashi .
Amma rashin gata yasa ya koma kamar mahaukaci a ciki mutane har wasu na tafiya suna kallo inda muke ganin na tsaya dashi ina magana ashe sam baya shiga harkan kowane a makarantar.
Shine da aka ganmu tare suke mamakin hakan don bai kula kowa shi kadai yake rayuwan shi gashi dai kamar shiya halittawa kanshi kwakwalwan shi don hakane malamai suke ji dashi sosai.
Naje sallah na dade a masallacin zaune kafin na kalli lokaci na fito saidai na kasa zuwa kai korafina wurin wanan malamin don ko naje ance baya duban mutane.
Don hakane na ba kaina shawaran na kyaleshi kawai zaifi min rufin asiri danaje ya tozartani don mutum ne shi mai ji da kanshi da zamani yana amfani da daman da Allah ya bashi yana wullakanta mutane ta hakan.
Ummah tayi kokarin buyewa kowa halinda yarta ke ciki a lokacin ba don komai sai don rsshin yarda da kowa a yanzu tunda ba yan uwane gareta ba a nan sai abokan arziki da dangin miji.
Suma din kuma wasune suke hurdan arziki da ita don sunfi bada karfi a bangaren mama dama haka yake a al,adan yanzu duk inda miji yafi karfi can mutane ke dosa don neman abin duniya da gulma.
Ko wanan maganin da Tani ta karbo mata saita koma tana tsoron amfani dashi don yanzu mutum ba abin saurin yarda bane tsakaninka dashi haka kai tsaye.
Wanan yasa take wasi wasin ko ta mayarwa Tani din da kayantane ta fallafawa ubangiji lamarin su don Allah shine mai yin yadda yaso da bawansa haka kuma bawa baya kaucewa kaddaransa tun rangini ranan zane.
To amma kuma zaman ta da Tani na amana ne don hjy tasha kullace tani din yadda tani tabata gaskiya da amana duk yadda hjy taso taja ra,ayinta.
Amma Tani din taki yarda da hakan har saida hjy ta kulafuci tani din taso ta tasa a kori tani din daga gidan saida ummah ta fahinci me mama ke nufi ta nuna jajircewan ta kan hakan.
Tun lokacin sai gaisuwane da sannu ke hadasu da hjy ddin tana taka tsatsan da lamarin mama din a gidan harta shigo ta fita da yamma tana part din ummah zaune.
Wanan gaskiyan da amana na Tani din yasa ummah kara yarda da lamarinta da har yanzun din ma hankalin ummah din ya kwanta da maganin data kawo wanda ita tsakani da Allah ta amsawa ummah din shi.
Dauka tayi ta kara dubawa kafin ta mike ta fito zuwa kitchen dashi a hannun ta Tani din tana tsame shikafan data wanke a ruwa taji shigowan ummah din yasata juyowa lokaci guda.
Ummah ce kofa rike da ledan maganin data kawo mata a hannun ta idon tani ya sauka kan ledan gabantane ya fadi take fadin hjy lafiya dai ko ?
Lafiya Tani ummah ta dan sake murmushi tana takowa cikin kitchen din tana fadin kinga Tani ba zan boye maki ba da farko ban dauki wana maganin da kika kawo min dazun ba.
Amma yanzun nayi tunane na aminta dake Tani duba da yadda mukai sabo da amana kuma a tsakanin mu dake nasan kinyi wanan ne da niyar taimakona nida diyana.
Don sanin halin rayuwan da muke ciki a gidan nan daba kowa yasan da hakan ba sai yan tsiraru suka sanda hakan a garemu.
Allah sarki hjy yadda kika rikeni nida diyana da yan uwana meye ba zan iya maki ba a rayuwa wallahi Allah jiya na kwana da tunanen uwar dakina a raina don kiri kiri ake son a illanta maki zurian ki nan a gidan nan.
Wanan yasa nayi asubancin zuwa gidan yaron nan na jiya da yai min kwatance shine nayi asubancin zuwa unguwar na kuma gane gidan nasu.
Saidai a lokacin nayi rashin sa, a don shi ya fito zai tafi makaranta a lokacin shine ya hadani da kakarshi ta kaini wurin wani dattiju a nan unguwar tasu.
Ni kuma sai ban boye mai komai na irin matsalan da kuke fuskanta a gidan nan shine yaba da wanan yace a kawo maku kuyi amfani dashi mugu na fili dana boye saidai aniyar shi ta koma mai .
Watau aniya makomiya ke nan yadaice kuyi amfani dashi kamar yadda yace ayi in sha Allah ya wadatar daku saida hjy naga kamar baki yarda dani ba kan hakan ?
Saidai banga laifin hakan ba tunda