Showing 36001 words to 39000 words out of 304363 words

Chapter 13 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33304

mune wai ?
Kiyi hakkuri muma dole yasa muka badake ga wani gashi kuma da rabon mu sake zama dake Allah ya nufa kin dawo garemu kuma kiyi hakkuri kici abinci ko ruwane kada kisamu illa a jikin ki.
Kici don Allah ko kisha ruwan yana kokarin mika mata ruwa a bakinta tare da shafan bayanta a hankali tayi dan kuka lokaci guda tana mikewa tsaye ta wani girgiza jikinta lokaci guda.
Zagayen shi ta farayi kamar tana sunsunan jikin shi kafin ta dan tura kafanta na gaba ta kada kwanon ruwan da ake zuba masu ruwan shansu ciki sai kuma ta dona kai a ruwan tana sha har lokacin hannun shi na saman bayanta yana shafanta a hankali.
Ikon Allah yanzu uwar garke haka zaki mani kiyi fushi dani kike karban abincin hannuna saina Amadi, kinyi fushi ke nan dani ko me ?
Dan murmushi Amadin yayi yana dagowa daga duken da yake yana fadin tayi fushi mana Dije tunda ke kikaba da shawaran sayar da ita.
Dana bada shawaran wa yakaita kasuwa ya sayar kawai dai har dabbobi sun san kitihi yanzu baiyi magana ba ya dan tara yayin kara yaje murhun dije ya debo rushin wuta tazo ya saka masu ya dan gyara wurin .
Hannayen shi ya dauraye yayin da Dije ta juya zuwa cikin dakinta bai shigo dakin kai tsaye ba saida ya kai kayan gwajon shi ya aje dakinshi kafin ya nufo wurin dije din yayi sallama ya shiga.
Tana gaban fitilan kwai donsu har lokacin basu da wuta a gidan su sai hasken na makwata dake dan shigo masu kasancewan ginan su yayi kasa sosai a cikin shiya.
Yayi sallama ya shiga yana fadin Dije yaya gidan ta amsa da gida lafiya Amadi ya kasuwan kace ka taba ciniki a yau din ya amsa da wallahi Dije ni har abin ya bani mamaki sosai wallahi.
Na dauka ai ba zasu shiga ba sai gashi mutane na yaba min wurin zaben kaya haka masu kyau ashe sana,a dadi gareshi Dije yau din nan da farawa kinga abinda na samu yana fito mata da kudin tare da fadin ba wani riba sosai na dora sama ba.
Don maishi yace min har in ina son naci riban abin kada na cika kudi da yawa a sana,a na zanfi gane kan abin da sauri gashi ko nabi shawaran shi naga alheri a cikin harkan.
Ya baka shawaran kwarai sosai gara daka bi shawaran nasa Allah ya umfana muna abin baki daya, kudin ya jawo gaban shi ya kirga ya ware wasu yana fadin.
Wanan Dije a sai abinci mu dinga girka abinci muma a gidan nan kamar gidan kowa sau uku yanzu a rana don Allah kada ki matse kanki da yunwa kuma Dije.
Yaro ke nan banda abinka Amadi farawa da iyawa saimu zauna mu kurmushe uwar kudin a cikin mu kuma tun yanzu.
A, a Dije ba zamu kurmushesu ba da yardan ubangiji Allah ne fa yai muna mafita ga hakan dama tuntuni nabi shawaran ki da ban tsaya aiki da madam kan dan kudin da take ban bai ko isa biyan kudin karatu na balle kuma muci daga ciki.
Datuntuni wanan sana,an nakeyi mu huta zama a cikin kunci irin hakan ki dauka ki sayo kayan abinci ko nan cikin unguwane kafin naje kasuwa idan na samu lokaci nasayo muna .
Amadi kudin nan yayi yawa ka rage don bakin mu mu kadai ko dari uku na saya muna abinda zamuci ba tare da riya ba in sha Allahu.
To Dije yadda kikace din ya mayar da sauran kudin nasa cikin aljihun shi yayi shiru na dan lokaci zancen karatun yaran nan ne ya fado mai a rai lokaci guda yaja tsuki don yana ganin zasu ja mashi cikas a cikin sana,anshi kan wanan karatun nasu .
Shiya rasa yadda akayi ma har ya bari sabo da shakuwa ya shiga tsakanjn shi da wani wani ma macen kuma yar mai kudi irin haka da zasu moreshi a banza.
Taimakone ai taimako taimako kuma baka san inda za a rama makashi ba gashi dai shine mai taimakon nasu har yanzu dai.
Washe gari kamar jiya ya fita amma bai yarda ya bar gida ba saida ya duba uwar gareke ya gyara masu wuri ya aje abinci ya dan shafa bayanta yana fadin kiyi kiwo ki koshi kinji uwar garke don Allah.
Yana fita masalaci yaje yabi jam,i daga nan ya fito kasuwa ya nufa ya samu babu mutane sosai ya zabi irin kayan daya kula ana so da ake tambayan shi.
Ya baro kasuwa zuwa school ya kasance jumma,a don haka daga masallaci ya shiga yawata kayan shi a cikin gari ya samu ya taba ciniki sosai a rana .
Yana ganin abubuwan amfani irin su kayan miya yana dan tsunta a gari har su alaihu da shinkafa don yasan Dije ba zata sayo ba tunda ba wasu kudi masu yawa a hannunta .
Wanan sayayyan da yayi sashi shawaran komawa gida da wuri ya sake biyawa kasuwa ya kara zaban kaya gredi daya samu an bude a lokacin.
Daga nan yayo gida ya samu Dije a bakin murhu tana hada miya don har ta kwashe tuwon garin masara data sayo a cikin unguwa miya ya rage ta hada.
Sallaman shi yasata juyawa tana amsa mashi sallaman tare da fadin yau an dawo da wuri ke nan yace to kinyi fadan dare jiya Dije.
Kayan da ya dauko niki niki ya aje a gefen ta bau tsaya ba ya nufi garke ya duba yar amanan shi uwargarke tana tsaye tana kiwo ya kara mata abinci ya kara gyaran wurin.
Dije data gama duban ledan tace kai dan nan har shinkafa ka sayo muna yau gidan tana mamaki Allah ne ya bamu sa, a ya nufemu da cinta a yau.
Nikan na riga dana tuka tuwon masara ga miyan yakuwa dana tsunko gidan malam Tanimu nan ina muna miya dashi yanzu muci.
Dan guntun murmushi ya sake a fuskanshi yana fadin ai bai baci ba Dije Allah ya kaimu gobe lafiya sai a girka a ci naman daine sai an gyara shi yau kada ya lalace.
Har nama ka sayo kace yau take sallah a wurin mu ke nan yau din nan nama kan dole a gyarashi kada ya lalace kafin gobe.
Tana magana tare da jawo ledan zuwa gabanta kaikai Amadi wanan ai kudi ya wahala a nan Allah yasa albarka sai ayi a hankali kada mu murkushe kudin mu koma zaune kuma.
Dan murmushin gefen baki yayi daga inda yake zaune dirsha a kasa yana kallonta kafin ya mika hannunshi zuwa wajen butan dake gefenshi ruwa ya gunda a baki ya kurkure bakin kafin ya zauna da kyau ya fara alwala..
Na dawo a gajiye Rukkaiya muka fara haduwa da ita daga irin kallon data watsa min na gane akwai wata a kasa ke nan don ko dan tsayawa ko mu gaisa irin yadda muka saba a ranan bamu yishi ba a tsakanin mu.
Sai ta wuce na wuce kowa yaja iska a tsakanin mu ya wuce dan uwa naga karfin halina ga yin hakan na shige part din ranan kanne na basu da lesson sun dawo gida da wuri duk suna falo.
Na yaye gyalen dana yafa a kaina nan suka shiga gaidani da dawowa ina amsa masu na nufi bedroom din mahaifiyar mu don in gaida ita .
Tana zaune bakin gado tana waya da hjy maryam kawar ta dake Abuja har yanzun da zama ita da mijinta da yaranta.
Zan iya cewa hjy maryam ce makwaciyar da tun zuwan ummah Abuja suke tare sun koma kamar yan uwa a yadda naji suna maganan zuciyana ya bani wani abu mai muhinmanci ya faru tsakanin mama da ummah ko Abbah.
Ganin hankalita naga wayan yasa nayi mata sannu ummah ya gida ta gyada min kai na juya na tafi na barta yadda na sameta zaune din hankalin ta a kan wayan.
Kamar yaddana saba ina shiga na wurgar da jakkana saman gado ban daki na shiga na gyaro jikina tsab ta hanyar rage wanke matse matsina da sabulu mai kamshi tare da dan tsane jikina na da tawul na fito na kwabe kayan jikina na saka na zaman gida.
Yunwa nake ji don haka na nufi falo don in samu abinda naciwa cikina lokacin abincina yana ajiye kamar kullun.
Zama karamin kanin mu ya taso shima zaici nan sauran suka nufo suma macen na tura ta dauko masu spoon muka zauna tare dasu munaci a haka ummah ta fito ta samemu.
Salati ta saka kafin ta nufo su tana masu fada don me ba zasu barni naci hankali kwance ba suka zauna min ga abinci ?
Ummah idan inaci dasu nafi cin abincin da yawa wani kallona ke kika sani ta watsa min nayi murmushi har takai kofan fita zuwa kitchen ta juyo tana fadin.
Ina kika aje key din motar taki tana tambaya take kallona taji amsan da zan bata na gyarawa kanina dake saman jikina zama nake fadin yana cikin jakata na aje.
Ki kula kada wani ya dauko ko idan kin dawo ki rika ajeshi a dakina don mutanen nan sherinsu yawa gareshi tunda ban bata key din da girma da arziki ba yadda taso.
Don haka ki kula sosai da tuki da kuma kanki a yanzu komai da kikeyi idon mutane yana kanki yanzu don komai ya canza yadda kuka sanshi a baya gidan nan.
Abban kuma yace naje maki kunne da kikula kada samun motan nan ya canza maki rayuwan ki a yanzu kici gaba da dabi,un daya sanki dasu abaya kinayi.
In sha Allahu ummah na fada a sanyaye tare da dukar da kaina kasa kafin na dago tashige ciki ta barni da kannena surutu suke min amma ban fahintar me suke fadi a lokacin.
Tunda na shige dakin kwanana ban sake fitowa falon ba na kwanta iya tunane nayishi a lokacin narasa gano dalilin sauyawan gidan mu yanzu cikin dan kankanin lokacin komai ya dagule a tsakanin iyayyen kuma.
Wace ta haifi mahaifin mu tana raye a duniya gidan mu baida nisa sosai da inda take don inda iyayyen mu suka fara zama da farko yanzu itace ciki zaune don kamar a family house din mu suke.
Don haka ganin ba school da safe na na kwashi yan kannena mukaje gida mu gaida ita kusan duk sati haka muke zuwa gidan duk da har na fahinci ba wani sin mu takeyi sosai kamar yadda take son su Aisha ba amma ban bari wanan yayi tasiri a zuciyana ba game da ita.
Da sabon motan muka fita zuwa gidan muna zuwa naga motan mama pack a kofan gidan kafin mu fito muka hangosu suna fitowa daga cikin gida ina kallon suna nuna mata motan namu.
Kafin su karaso sun tsaya magana muka nufi wurin iyayyen mu maza muka fara gaidasu don suna kofan gida suna shan hantsi a lokacin.
Har suka wuce bamu shiga wurin kakan tamu ba muna can muna gaisawa da mutanen arziki lokacin a cikkn gida don gidan namua babban gidane sosai.
Mun fito mun samu sun tafi kai tsaye wurin kaka tamu muka nufa sallama nakeyi amma muryan tsohuwa yana tashi a cikin hausan mutanen zamfara tana fadin .
Ni za a kawowa iya shege da raina ka fara nuna bambanci a tsakanin diyan ka dame ita takwaran nawa tafi yan uwanta da zai saya mata mota ya kyale sauran.
Sallama na karayi cikin daga murya sai lokacin aka amsa muna muka shiga tana fadin watace mune hjy na bude labule na shiga don tun ban shiga ba na fahinci a taikace kara mama da yaranta suka kawo wurin hjy ke nan .
Au jikokin gal ne haba mama wata gwaggon dake zaune tare da ita ta fada cikin bacin rai kafin ta dora da fadin haba hjy bai kamata ba hakan nan don Allah.
Kamar ban fahinci me suke zancen ba na aje mata ledan da muka saba zo mata dashi a gefe nakai zaune gefenta ina fadin tsohuwa mai ran karfe kin tashi lafiya ?
Har lokacin akwai sauran bacin rai a fuskanta ta amsa min kadaran kada ham tana fadin kema kin tashi lafiya yaya uwar taku ?
Tana lafiya tace mu gaida dake ga wanan tace a kawo maku nan muka gaida gwaggon namu muna dan hira sama sama tsohuwar ta fuske damu.
Can nace hjy akwai fura a fridge din ki ban sayaba uban naki bai aiko min da kudin saya ba tunda yanzu ya fara mikawa yara kanana kaddarorin miliyoyi suyi yadda ransu keso dashi.
A, a hjy badai Abbamu ba kan idan bashi ba wane zai dinga wullakanta kudi haka ke wanan motar da kike shige yanzu bai isheki ba sai kun tursasashi ya sayo maki wani ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[04/01 4:34 PM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , ,
1️⃣3️⃣
AL MUSAWWIR,,,,,,,,,,
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Don Allah kada kiyi ko kayi gangancin karata wana novel din a audoo don na sayar dashi already ga wasu yin hakan shari,ace tsakanin mu.
Zaman dai ba dadi amma hakan baisa mun bar gidan ba muna dakin ta sai shabiyu muka fito zuwa gida don zamu shiga islamiya lokacin.
Sai dare na samu zama da ummah mu a falo naji ta tambayeni wai meya hadaku da hjy yau ibrahim ke fada min tayi ta maku fada tana zagina da baban ku ?
Ummah zancen motar nan daine aka kai mata don mun samu su mama gidan wurinta nasan kara suka kai wai ashe Abbane ya saya min sai gwaggo uwanice ke dan tsawata mata har ta daina zancen amma taki sakin fuska damu.
Sai cewa take ai Abban zaizo zataji dalilinshi nayin fifiko a tsakanin diyan shi don ita ba zata lamunci hakan ba tun tana raye ya fara yin haka ina ga ta kawu bata duniya saidai idan ansa abinda akai mai a karkashin kasa.
Murmushi naga ummah ta sauke a fuskanta tana fadin Allah sarki yanzun ne zanwa Alh asiri kuma dacan baya ashe suma asirin sukai mashi ke nan ko ?
Little sister dinace ke min nuni da abinci na diba na bata wanan ya dauke min hankali ga maganan da mukeyi da ummah din.
Monday mun shiga school sam na mance da zancen karatu dan break din da muka samu sai ga mutum uku da mace daya sai wanan kawar dana samu tunda ita ke aje min wurin zama kafin nazo dana shigo zata daga min hannu nazo na zauna.
Oya muje muga guy din nan don muji ya za ayi tunda yau yace damu za,afara wa ke nan na tambayeshi cikin mamaki au har kin manta da zancen ke nan ?
Keko zancen karatun mana da zamu fara ta fada haka suka sani gaba dole na tashi mukaje muka sameshi yana gyara kayan gwanjon shi a bayan aji.
Gaisuwa suka fara mai muna tsaye daga baya kafin ya dago yana fadin yanzun ya kuke son ayi don gaskiya zaku takura min ga sana,ata kunsan tallaka baiga zama ba naso fita in zaga da kayan nan nawa cikin hostel ku kuma gaku.
Hakkuri zakayi master don kyau alkawari cikawa manir ya fada ok ya fada yana dan kalle kalle kafin yace mu karasa daga can zaifi wurin ba yawan gittaya sosai don haka sai yai muna dadin zama.
Bayani ya soma muna tun daga farkon yadda zamu gane kan topic din da Munir ya gabatar mai zaka rantse shi din wani baturene ko babban lectura ke bayani.
Abinda ya dakatar damu yan class din nasu ne sukazo mai da wata tambaya hakan yasa muka barshi a lokacin muka koma namu building din.
Tallan gwanjo na maimaita a fili why ga karatu ga kuma sana,a lokaci guda haka au kina mamakin guy din nan ne ko nima a gaskiya naji mamaki sosai wallahi.
Gashi Allah ya bashi amma baiyi girman kai da hakan ba ke da ganin shima kin san yana bukatan taimako sosai a rayuwanshi ko suturan jikin shi ka kalla.
Kune yayan manya irin su ya kamata ku dinga taimako inda halin hakan tunda muma yana taimakon mu da nasa baiwan da Allah yai masa ai yanzu.
Ba wanan ba ai da alaman wahala sosai z tare dashi idan kin dubs ya fada muna zamu takurawa rayuwan shi amma yanzu kina nufin da wanan sana,an zai rike rayuwan shi ?
Wata kilama hardana wasu a karkashin shi yanzu haka idan kin bincika ko yana da aurema a kansa ai kinsan yadda yake a kasan nan tamu yiwa yara auren wuri su dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login