Showing 69001 words to 72000 words out of 304363 words

Chapter 24 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33332

Bayan shan ruwane da yamma suna zaune tare da Dije a kofan dakin Dije din da suka shimfida tabarma su biyu a gida ya dauki waya ya danna kira a layina.
Na dauka naga sunan shi na danna dauka yayi sallama na amsa yake fadin Allah yasa nine mutum na farko dana fara maki barka da shanruwa kada wani ya rigani samun ladan dake cikin hakan ?
A gaban ummah nake hakan bai hanani yin murmushi ba nace ai kuwa kayi sa,a kaina na farkon kirana amma ga hannatu nan yanzun tana kirana kuma.
To ki gaidasu mama ina masu barka da shan ruwa Allah ya bamu ladan dake cikin sa ya yafe muna kura kuran mu yasa muna cikin yan tattatun bayinsa na amsa da amin mukayi sai anjima dashi.
Na dauki wayan hanne nan ta hauni da fadin ke mutumiyar ina ta kira kina busy haka ko kiyi sabon kamune banda labarin hakan .
Mikewa nayi nabar falon ina fadin ke dai hannatu haka zaki kare da sheri har da watan nan mai albarka sai kinyiwa mutum sheri.
Brother ne fa ya kirani yau yana min barka da shan ruwa muke magana zakice wani sabon kamu kai kice master da kanshi ya kawo gaisuwan girma ashe shima muka taba hira sosai kan lecture din ranan kafin mu kashe wayan nikan na kwanta ban sake fitowa ba saida asuba da muka tashi yin sahur.
Yana aje wayan ya kalli inda Djje take tana cin abinci yace wasu mutanen akwasu da kirki tun suna kanana yarinyar nan fa dije yar gidan mai kudine da garin nan ake ji dashi amma bata dauki duniya da girma haka ba.
Idan kin ganmu da ita saiki dauka ba yar kowa bace ita din don sam bata nuna hakan hakama yanayin shiganta kulun na mutunci ne.
Ai wasu sun san ya kama ko a cikkn yara sai ka samu masu hali irin na dattako garesu yace hakane ko kudin nan ban fada maki bane natane ta ban na kara nake jan wanan jarin dashi .
Ranan da naje kauyen nan buhun gero hamsim na sayo maiwa ashirin sai masara moto guda na dauko ni kadai aka sauke min kaya kuma duk sun shige washe gari mai kudi kuda ya sayesu ya bani kudina kasa wallahi.
Amadi kace arziki ya budu muna har kana iya dauko abin dubu dubbai haka ka sayar yanzu a garin nan wallahi Dije haduwana da zarah ya zamo min alheri sosai a rayuwana Allah ke nan.
Kaga ubanka yayi watsi dakai a duniya ya manta da zancen ka a cikin duniyan nan gashi Allah yana taimakon rayuwan ka ta hanyar da ba a zata ba.
Shiru yayi don ya tsani Dije ta dauko mai zancen iyayyen shi idan suna magana idan ba don Allah da ita Dijen ba sai yace ai shikan baiyi dacen iyayye ba don ko ita mahaifiyar nasa daya sani ya bude ido da ita mijin da take aure ya yanke alakanshi da ita yanzu.
Don kuwa ta zabi bin mijin ta can dajin Niger state inda yake noma suke zaune har suka hayayyafa dashi yanzu bata zuwa gida kai da kai saita dibi shekaru take leko su tayi kamar wata daya ta koma garin sai kuma bayan wasu shekaru masu tsayi take dawowa garesu don haka ba zaice shi yasan dadin mahaifa ba saidai kakan shi mace itace Dije.
Kawar da zance yayi da fadin waiko yau uwargarke lafiya ta kalau kuwa duk shigowa nayi sai in sameta kwance tana barci ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
2️⃣2️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Don Allah kada ka/ki gangancin juya novel din nan ya koma audiovisual na saurare don riga da na sayarwa wasu dashi already yin hakan zai iya jawo shari,a a tsakin ni dake dasu don Allah a kaucewa hakan nagode.
Zan iyacewa wanan watan mai alfarma da muka shiga shi yajawo shakuwa da yarda da amincewa kana da amana gami da sabo a tsakani na Ahmed sosai fiye da tsamani.
Wanda a waya zamu tsaya muyi hira sosai kona sana,arshi ko abinda ya shafi karatuna haka wanda idan a filine ba zamu iya tsayawa da juna muyi magaba mai tsayi haka ba a tsakanin mu saidai a waya din.
Saiya kasance shakuwa mai tsanani ya fara shigar kowan mu tsakanin shi da dan uwa koda kuwa yana gun sana,ashi zai kirani yana fada min halin da ake ciki.
Wanda nima hakane ko zaune nake ni kadai zan iya kirashi kawai naji muryan shi mu danyi magana sai in kashe wayata haka kuma lokaci lokaci idan yaje kauyen zai yo muna tsaraban irin su kwan zabbi wataran ma zabbin da ransu kamar uku ki biyu yace a gyarawa kanwarmu autan mu tasha ruwa dashi.
Hakama kayan lambu irin na shan ruwa zai sayo ya tsaya a waje yaba maigadi yace a kawowa Amira tasha ruwa dashi itako yarinyar ta fara fada da duk wanda ya taba tana fadin nawane mijinane ya sayo min.
Da farko daya fara hakan ummah ta titsiyeni wata rana a dakina tana tambayana meye tsakanina da Ahmed da har yake min wanan sayayyan haka ?
Kallon ummah din nayi cikin ladabi a tsigar mamaki nace ummah Ahmed fa ba komai wallahi tsakanina dashi illa daukan kanwarshi da yake min shine kawai a tsakanin mu dashi nan nake fada mata kamar yadda ya fada min shi cewa.
Da yake zumunci damu yana jin cewa mu din kamar yan uwanshi na jinine sosai don a duniya ba wanda ya taba daukan shi da muhinmanci har yasan shi di mutum ne kamar kowa bayan haka ba komai wallahi tsakanina dashi ummah.
Saida tayi min wani irin kallo tace ki daibi sannu ummah din ta fada dan ke yarinyace karama har yanzu kisan kuma yadda ake son ganin bayan mu a cikin mutanen nan don haka ki natsu ki kama kanki.
Toh umma na fada ta juya ta fice daga dakin na sauke ajiyan zuciya tare da dan tunane a kan maganganun da ummah din tayi dani lokacin.
Ko ya akayi mama ta sanda wanan zancen har labarin Ahmed din yakai kunnen ta oho sai gashi tana sakewa ummah habaici da fadin kwadan mutum ya kaishi ga halaka.
Mudai mun godewa Allah diyan mu suna da farin jini daga mai jeep sai masu benz ke sallama muna ba fakirai yan ya Allah kuci ku bamu ba kazo ka sayar da akuya ta dawo tana cima danga a gida kuma.
Nan ummah ta dago da zancen da mamakiyi din a lokacin ta gane metake nufi da hakan abinka da uwa take ran ummah din ya baci da hakan.
Ita kuma tace da fakiri da mai kudi duka Allah yayi su yasan da zaman kowa zaman lafiya da kwanciyan hankali akajawa ba sunan auren mai kudi ba kwanciyan hankali ba.
Mama din tace kuma wai ummah da ita takeyi tayiwa diyan ta mugun fata to wallahi ta Allah bata mutum ba sanan ba hakan akaso ba wai kanin miji yafi miji kyau an dauka yar zinaroce zatayi sa,an maza don fari da kyau sai gashi Allah bai bada mai abin hannunsa ba sai wani fakiri ya kawo kanshi don kwadayi.
Wanan abin bai kawo kallo ba tsakani ku gwaggo habiba dake biwa Abba wurin haihuwa ta fada don a gidan hjyn su Abba abin ya faru sunje gaida ita da sallah.
Kuma amaryan su duk tana wurin itama don Abba ya tsaya sai su fito su tafi tare su hudu shi yana waje lokacin da wanan fitinan ya faru din baisan anyi ba.
Mafari kuwa wata tobashiyar mu ce ta kawo maganan tana fadin mama ina yan matan kine suwai basu fitane suna gida ko yaushe kumshe kodai basuyi kasuwa bane a hada su dasu Ali dacewa yayanta namiji shima abokin wasan mune.
Shine aka fara ba a har mama takaiga fadawa umma wanan maganan a bainan jama,a sai ran ummah din ya baci ta kasa hakkuri ta bata amsa.
Harda dorawa wai ba aso dai hakan ba din ba haka akai zato ba gareni an shiga boka an shiga malam ai farin jini abu taki ummah tace indai wanan ne kanki kikewa terere a fili don ansan mai mu,amula da shirka .
Haka suka kwasa suka dawo gida ran kowa a bace shi Abba ya dauka don fitan da yasasu yi dolene a tare lokacin yasa kowan su shan toka sai daga bayane amaryan shi ta fada mai abinda ya faru a can din.
Ranshi ya baci sosai da jin hakan ya tarasu a falonshi yana tambayan ba,asin abinda ya kawo hakan har suke mai cin mutumci a kan diyan shi.
Ni dai naga sun dawo inawa ummah sannu da zuwa da kyar ta amsa min ta shige dakinta ta rufo sai kuma can naga ta fito zuwa sashen Abban mu can ma ta dade bata dawo ba.
Bayan sun zaunane Abba ya kalli mama yace maimuna meya jawo fitina tsakanin ki da salma gidan hjy kuka tonawa kan ku asiri hakane ?
Daga inda hjy karima ke zaune tace uhumm tana gyara zama Abba din din ya kallota ya gane me hakan ke nufi datayi sai kuma ya juya da fadin ke salma yaya akayi hakan ya faru ?
Ba ita ka tambaya ba ta fada maka don ni bansan da zancen da take fada ba sai ji nayu a bakinta kawai na kuma bata amsa a lokacin don tasan koda tallakane ma dashi da mai kudi duk daya suke a wurin Allah.
Meye na wani kwanaye kwanaye a nan in ma wani ya kawoma gulman haka na fada don abune a zahiri dana fada kuma ita salma gata nan nace da zarah nakeyi ko me ?
Zarah zarah fa kika fada maimuna a gabana yau ita mamana din kike fadin sunan ta haka gatsau a gaban nawa ?
Zarah din ba sunan ta bane ko itace hjy da dole zan dinga sakaya sunan nata ko wani lokaci, yace yayi kyau yana gyara babban rigar daya dora saman fatan jikin shi.
Yanzu dai barin fada maku kuji idan kuna tsiyatakun ku kubar hada min da diyana don nina haifesu dukkan su kuma ba wani da dana haifa a gidan nan da ban nuna mai so ba a cikin diyana.
Don haka tsiyan ku ya tsaya iya kanku kuji sanan zancen maza har yaushe aka fara yi min haka a gidan nan ban sani ba yaushe suka zancen wasu samari can har hakan ya faru ?
Ke salma wani yaro ne ake magana a kan shi da yake son zarah sin ina zarah karatu takeyi yanzu yaushe har ta fara kula maza haka kika barta har wani na zuwa gidan nan wurin ta.
Shiru ummah tayi don takaicin da yake cin zuciyanta sosai a lokacin ba zata iya yin magana ba don zata iya fashewa da kuka lolacin don bakin ciki.
Ya juya wurin mama yace wani yarone wanan din nace ai gata nan ni ina zan sani nadai san na taba ganin su a waje suna hira ni zan fita ya tsuguna ya gaidani haka kuma na samu labarin yana yawan zuwa nan get din gidan nan ya kawo abu yace abawa Amera wai .
A gidan nawa har wani zai kawo abu yace abawa yata salma ni ban sani ba me kuka rasa a gidan nan yanzu ko a wani fanni na rage ku dashi wurin kula da iyalina ?
A,a Alh kowa yasan hakan ba gazawa bane duk da banso saka bakina cikin zancen ku ba amma ya kama dole saina saka yanzu shi alheri ki kyautatawa gun mace ba duban wanan a cikin shi.
Sanan idan zakayi adalci ba wanan yar kadai ake kawowa alheri ba a gidan nan ga nawa fahintar zancen da sukayi kamar kowa saurayi na zuwa wurin shi saidai wani yafi wani shine zancen nasu.
In ma magana ne ai zance zakayi akan su waye suke neman yayan naka kasani idan da gyara sai a gyara a zauna lafiya ina ganin shi zaifi ai .
Gara dai da tun farko kikace zancen bai shafeki ba don haka banga abinda zaisa ki tsoma bakin ki a cikin wanan zancen ba saiki jira idan kin haifa sun girma sai ki tsoma baki a zancen diya tukun.
Duk da dai ba lsifin ki bane hakan shiyaja muna shidake kokarin nuna cewa bamu da muhinmanci ya kiramu nan gaban ki don kikai mashi gulma ya zaunar damu yana muna wanan tambayan haka a gaban ki.
Dakata maimuna koda yanzu tazo cikin mu ya zama dole maganan gidan nan a zauna da ita ayishi tare a agama don itama yanzu zancen ya shafe ta.
Mikewa mama tayi tana fadin badai dani maimuna ba don bata kai mun can ba wallahi ita din nan saidai ta gigitaka amma ba dani ba kallon ku kawai nakeyi wallahi.
Au haka zancen yake idan baki kallemu ba yaya zakiyi yanzu maimuna barin fada maki duk abinda kike ji ina jin shi ina daga maki kafane don Alh amma ke din nan kinyi mun kadan wallahi.
Ai dole kice hakan ba dole ki daga kafa don Alh ba tunda ke kikasan shige da ficen da kikayi har kika kamoshi saidai saukin abin iyashi kika tsaya badai da maimuna ba ko ?
Fada sosai sukayi tsakanin mama da karima karshe tashi ummah tayi ta barsu a falon ta koma part din ta ta shige daki duk ina dakina ina barci don dan hutun da muka samu na sallah muna gida bamu fita.
Duk abinda yake faruwa nikan ban sani ba amma su Aisha sun sani don suma sun dauki zafi sosai a kan hjy karima har ma da ummah da akace tayi masu mugun bakin a gidan aurensu don haka suka dauki zafi sosai da ummah din suma.
Fahintar ummah bata cikin yanayi mai dadi yasa na bita dakinta bayan sallah magariba na sameta zaune a kasa saman sallaya ta hade jikinta da gado tana jan tasbaha a hannun ta.
Sallama nayi na shiga ta dago kai ta kalleni gaida ita nayi ina zama nace wai ummah anyi wani abune dazun da ku fitan.
Don tun dawowan ku naga yanayin ki ba dadi haka na kura mata ido ina son jin amsan da zata bani lokacin don na gama fahintar cewa akwai matsala.
Maamah na fada maki kada ki fada tarkon soyayya a yanzu kada ki biyewa su Aisha don ba daya kike dasu ba yanzu gashi zancen yaron nan da ake ganin ku tare har yakai gaban Alh ko .
Wani yaro ummah na tambaya cikin rudewa dama kuma fahintar cewa bakin cikin da ummah ke ciki ashe ta dalilina ne hakan ya faru.
Kasa na sauko inda take don dama a saman godo na zauna sai gani na zube kasa gaban ummah sallaman da akayine yasa batace dani komai ba nima din ban samu fadin komai ga ummah din ba.
Ummah ta mike ta fito zuwa falo wasu makwabtan mune da take abin arziki dasu suka shigo lokacin gaida ita da Sallah.
Sun dade tare hakan yasa na koma dakina na kwanta jiki a mace don abinda ummah ta fada min na shiga tashin hankali.
Abinka ga wauta irin nawa wai Ahmed din nayi niyar kira in fada mai ko zan samu shawara a wurin shi don sam ban yarda in magana gidan mu da Hannatu kawata ba.
Saidana danna kiran nakuma ga rashin dacewa hakan na kashe saidai kiran ya shiga sai gashi ya kirani dole na dauka yake fadin zarah yau lafiya kuwa naga flashing din ki a wayana ?
Sorry bakai naje kira ba saina danna sunan ka na samu kaina da fadin hakan gareshi murmushi naji yayi kafin tace duk dadin naman sallah da kike cine yakai ki ga hakan ina mama ina kannen mu.
Duk suna lafiya na fada a kasalance lokacin yace a gaida min su saina kawo masu goron sallah su da sauri na tare shi da fadin no ka barshi don Allah.
Cikin mamakin jin hakan yace lafiya kuwa kikace min hakan ina mungama wanan maganan dake ko raina abinda zan basu kikayi ?
No ba hakana bane akwai abinda yasa nace hakan kasan Abban mu na gari ba fita mukeyi ba koda kazo din koda nazo ai ba tsayawa zanyi ba don ina son zuwa in gaida mama da sallah .
Na sake fadin don Allah kayi hakkuri kada kazo don yanzu haka case akeyi da ummah din mu saboda wani abu so kada kazo gidan mu don Allah.
Abinda ya fada ya daure min kai don cewa yayi saboda nine ko zarah an fadawa mahaifin ku kina kulani dama nasan da wana ranan yana tafe komai dadewa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login