Showing 147001 words to 150000 words out of 304363 words
miji kuyi hakkuri dashi hakana gaba dayansu suka juya suna kallon kayan da aketa shigowa dashi part din.
Daga nan naji mommy ta dagoni muka mike zuwa nawa part din mommy kamar tana jurane mu shige naji tana fadin.
Zahra sai kin jajirce a wanan gidan kada ki kuskura ki koyi wanan halin nasu ko kusa gida da kazanta haka kamar ba mata a cikinsa harda yaran mata amma kaya haka gajal ko ina.,
Ai ba zata koyi wanan halin nasu ba tunda bata taso a cikinshi saidai idan taso amma yaro na tashi wurin sallama bai koyi tsabta ba.
Wace saboda tsabatanta har muna tsamanin shiya hanata samun haihuwa da wuri maman Zahra akwai tsabta kan gaskiya don komai nata tsab yake.
Mommy ta amsawa mama Geshuwa din data fadi hakan kafin su dawo kuma kaina suna fadin yanzu idan mun tafi ki tashi ki dora girki ga kawarki nan ta kama maki ku hada abinda zakuci.
Hannatu ta amsa da fadlin dama zamu dora ke nan kuka shigo hakan nada kyau gaskiya kada ki yarda kiso jikinkin ki ki jajirce sosai kinji Allah yaiwa auren ki albarka aka amsa da amin
Na kuma ji wanan uwar mijin naki na wani zance kan yayanta kada ki yarda ki basu fuska da zasu raina ki ki tsara girman ki bawai sai kin sake masu yadda raini zai shiga ba don su din kinga kamar jahilai suke.
Don in raini ya shiga tsakanin ku daga baya ko kinso gyara hakan ba zai yuyu ba shi kuma mijinki ba zaiki yan uwanshu ba ya goyi bayan ki don haka kisan yadda zaki zauna da kowansu.
Sun kai wani lokaci kafin suyi min sallama su tafi muka mike muka gyara gidan nida hannatu muka dora girki kamar yadda sukace nayi din .
Sai yamma lis hannatu ta tafi nima nayi wanka na canza kayan jikina zuwa wani dogon riga mai laushi a jikina na saka kamshi a jikina da dakin na zauna ina jiran a tayar da sallah.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Zaune suke sun tasa kayan dasu mama suka kawo masu sai guda da shewa akeyi anawa uwar kirarin cewa tayi sa,an haihuwa wanan irin abin arzikin haka ai kowa nason ya haifi haka a gidansa ya kumaga hakan.
Ahmed din ne ya shigo da abincin dabbobi niki niki a hannun shi zuwa wurin da aka kebe dabbobin a bayan dakunan nasu na kwana.
Sai ya samesu baje baje da kaya a gaban su suna rabo yayi mamakin ganin hakan daga ina wanan kayan ya fito hakane shiya fara gaidasu sukayi mai sannu da zuwa ya wuce.
Uwargarke ya hango kwance tun daga nisa tana tuka da bakinta tausayi dabbobin suka bashi yasan hankalin shi ya dauke bai yawan basu abinci a cikin yan kwanakin nan daya fara sha,anin bukinshi sosai.
Gashi biyu harda ciki akuya daya da tunkiya daya suna dauke da ciki a jikin su sai suka kara bashi tausayi mikewa sukayi lokaci guda saidai banda uwargarke din don tana kwamce har lokacin tana tuka.
Abincin ya diba ya zuba masu mai yawa ya dauki sauran yasa saman rumfar su ya debo masu ruwan sha bayan ya gyara wurin ya aje masu a gaban su.
Jada baya ya danyi yana kallon dabbobin kafin ya tako zuwa wurin uwar garke din yazo ya tsuguna a gabanta ya fara dan shafa bayanta a hankali kafin yace.
Uwata wai fushi kikeyi danine haka ko abincin baki kalla ba yau kuyi hakkuri bawai na manta daku bane abubuwane sukai min yawa a kaina wallahi.
Nasan kina jin me nake fadi kiyi hakkuri ki tashi kici abinci kafin su raga maki jagwalgwalen su subar maki sudi ya fada yana mikewa .
Kallo ta bishi dashi ya juya da niyar tafiya lokacin ta mike tana girgiza jikinta nan kasusuwanta suka shiga sake sauti har yana ji daga inda yake zakace ko wani abune ke wanan karan haka.
Ita kuma sai yaga ta dona kai ta dan sun suna abincin ta fitar da kanta ta nufi ruwan da ya aje masu tana kwankwada a lokacin ya tako yabar wurin.
Yazo daidai kofan Dije ya sake samun su a yadda ya barsu da farko ana zaune ana ta kasafi abubuwa daga can yaji muryan Dije na fadin kai Amadi yaka.
Jin hakan yasa yaja ya tsaya wuri daya tare da dan kallonta kai yaka nice ta fada a dan hasale tare da yafutoshi da hannu alaman yazo.
Gani hakan ya tako zuwa inda suke harkokin su din yaja ya tsaya tace wanga kaya dakagani daga gidan su amaryan ka yafito suna sunka kawo muna shi a matsayin gara.
Wanan uban kayan haka Dije kamar abubuwan sunyi yawa aina gani ya fada yana sake bin kayan da kallo tare da mamakin karara a fuskanshi.
To uban zuga ko gidan irin mu tallakawana haka akeyi al,adana da kowa yasan anayin shi tun dacan mahaifiyarshi ta fada kekan baki da dabi,a ke dai san mutanen nan suna cikin gidan nan kike batun sake layi.
Jin hakn yasa ya dan juya kamar a tsorace yace suna gidan nan dama Dije tace wallahi kaidai tun dazun sunkazo suka kawo muna amarya nan muka gaisa .
Yarinya haka tubarkallah masha Allah Allah dai yabamu hakkurin zama da juna sauran mutane suka amsa da amin shikuma ya juya da niyar barin wurin.
Ina zaka so nake ka tsaya a cire maka naka kason da zaka dauka da wanda zakaba abokan ka da sunka tsaya ma harka buki.
Shi zai cire masu Innan mu kibar yin haka ba sai abinda anka basu zai dauka ba amma ina na taba jin ance wai yaro ya kwashi duk abinda yakaso.
Rashida mika damun rayuwan kina haka wanga abu don danga anka kawoshi so kike ku zauna ku rabawa kanku a tsakanin daga baya kuma azo a tuna da wani aji kunya ?
Dije ke fadin wanan maganan a hasale ga yayan nata dake faman rabon kayan cikin shagala da rudewa abin yana ba tsohuwar haushi yadda sukeyi yasa ta tsare jikan nata tana fada mai abinda ke faruwa.
Don tasan tare suka sha wahalan rayuwan su dashi yanzu samu yazo sun yi baja baja suna daukan abinda suke so a tsakanin su ba tare da tunawa dashi ba.
Shiko yana ganin hakan ya juya ya tafi ba tare daya sake juyowa ya waigosu ba don kawai yaji cewa iyayyen zahra amaryanshi suna gidan lokacin.
Don hakane ita inna harta samu daman yin yadda takeso da kayan ta raba yadda take ganin ya dace kowa na wurin har da Dije suka saka masu ido ita kanwarta.
Shine daya fita daga gidan don ganin iyayyena a gidan sai bai dawo gidan ba a lolacin shine dalilin daya fita tun safe baishigo ba sai wayan daya kira ya sheda min ya dawo ya samu ina da baki ya tafi.
Sai bai sameni ba sai Hannatu data dauki wayan tana fada mai ina ciki tare dasu mama yace ta sheda min hakan.
Bakin ummah gaba daya a ranan suka kama hanya suka koma garuruwan su da suka fito akabarsu da wasu yan gari da take hurda dasu a nan suka tayata gyaran gida.
Da yamma kowa ya watse ya koma gidajen su hakan yasa tana kammala sallah bayan tafiyan Tani mai aikin mu ta rufe part din ta don haka bata san wainar da ake toyawa a gidan ba a lokacin
Ta daisan cewa Aisha tana gida har lokacin don ba a kaita gidanta ba ana rikici tsakanin su da mijinta da danginshi.
Wanan yasa fita ya auku a tsakanin Abban mu da mama a daren wanda ba karamin fitana sukayi ba a tsakanin su don Abba yace sun jawo mashi zubewan mutuncin shi a idon mutane.
Ai garama auren zahra din da kuke ganin bata dace ba yafi min wanan zuban mutumcin naku maimuna yadda baki ba yarki tarbiya ba haka ta dauko min miji mara tarbiya mashayi yana muna iskancin dayaga dama.
Hakan daya fada ya batawa mama rai sosai tace koshi ai baka san ko wani irin miji bane da har ka fara yabon shi da wanan auren na zahar ai gara yarka ta zaunama a gida.
Case dai yakai har yan uwa suka shigo gidan da daren don da sauran yaran sukaga case din yana kara zafi shine suka bugawa Hjyn su Abba sai gasu sunzo da yan uwan Abba din.
Yake fadin gaskiyane bata son a fada mata wallahi sai in rabu dake maimuna hakan ba wani Abu bane gareni ita kuma ta bude baki tace dashi.
Yo kasaka mana idan ka sakeni shine me a yanzu Alh kana ganin zan mutune ko wani abu haka kawai zan zauna kana zuba mim bakar magana kan laifin daban aikata ba.
Niba irin matarka bace da zaka zauna ka takata yadda kakeso tana nan lake dakai don jaraban tsiya na kada ka saketa ta barka ko wani abu.
Tana nufin wai ummah a maganan ta shi kuma yace tafimin ke ai duk irin cin kashin da kuka zuga nayiwa salma da yarta kada kice ban sani bane ko wani abu ina sane da abinda kike nufi da hakan sarai wallahi.
Da kyat dai aka samu aka raba fadan nan kowa ya warse a kan da safe za a san abinyi akan auren Aisha din aji inda aka tsaya ga zancen wurin mijin nata.
Kowa ya watse cike da bacin rai a zuciyar shi amma na mama yafi don ji tayi kamar ta mutu a ranan don bacin rai.
Ledojin pure water ya sayo masu yawa zasu kai kwara ashirin ya loda a firdge din da suke a corridor dina kafin ya kunna suka dauki aiki lokaci guda.
Saida ya tabbatar dasun dauka ya juya ya sake fita ya koma baya ya duba dabbobi kafin ya dawo ya shige dakin namu bani falon ina ciki ina sallah lokCin ban daki ya nufa ya watsa ruwa a jikinahi ya fito ya dauki dogon rigar jallabiyan shi ya saka a jikinshi.
Kana ya juya ya fita zuwa masallaci din a lokacin su suka tayar da sallahsu a unguwar duk da ina zaune ina addua bai hana ya fada min cewa ya fita zuwa sallah ba.
Bai shigo ba sai bayan sallah isha,i ya dawo a lokacin na hada mai abinci na aje mai a dining din mu dan karami da aka kafa min gefe daya a falon don cin abinci.
Ga kamshin turaren sandal na wuta dake tashi a dakin ko ina saidai dan duhun da falon ya dauka don ban kunna wutan ba a lokacin.
Ya kunna wutan ya shigo dakin na ina tsaye na idar ina nade sallayan danayi sallahn akai na dan juyo ina amsa mashi sallaman shi.
Ya amsa yana fadin na barki ke daya ashe hannatu din ta tafi ban sani ba nace eh da yamman nan ta tafi wai akwai abinda zatayi a gida tace.
Tayi kokari sosai wallahi samun amini haka a yanzu sai an tona na nade hijab dina ba tare dana bashi amsa ba na nufi inda wayana yake aje na dauka kana nakai zaune saman gadon.
Abinci yana falo na fada ina zama saman gadon idan kin idar sai ki tashi muje muci don nasan yanzu hutu kike son kiyi tunda da gajiya a jikinnki yanzu.
No ni ba zan sake cin abinci ba don munci da hannatu kafin ta tafi dazun shine baki jirani nazo munci tare na ciyar dake da hannayena ba koda yake kuma gara da kikaci da ita din don zakifi sake jiki da ita kici sosai.
Nidai ina zaune a inda nake ina jinshi sai dan murmushi danayi kadan lokacin a fuskana sai naga ya kai dan kwance yayi rigingine yana fadin.
Na saka ruwa a cikkn freezers din nan na waje don nasan idan mutane sun gane zasu dinga zuwa suna tambaya a basu hakan yana da kyau ai na fada.
Can kuma sai dakin ya dauki shiru na dan lokaci don kowa da irin tunanen da yakeyi a zuciyarshi lokacin don nidai tunane nakeyi akan zancen fridge din yayi yanzu din shi kuma yana tunane akan yadda rayuwa zai kasance a garemu.
Mun dan kai wani lokaci na zata yayi barci ne a hakan sai na kawar da shirun da fadin kada kai barci a hakan bakaci abinci ba fa.
Idona biyu ina dai tunanen duniya ina jiran ki tashi ki bani abincin ya fada cikin basarwa dan jin nayi kafin can na mike ina fadin muje din na zubama sai naga ya miko min hannayen shi.
Alaman na kamashi ya mike ai sai na kalle ina zan iya daga karfafa irin ka haka Master nine ma mai karfin zahra zaki iya ai ki gwada ki gani mana na dan make kafadana alaman naki.
Ban kuma wuce ba na tsaya a kanshi tsaye yace to ki zauna kada ki gaji yana nuna min wuri a gefen shi kusa da inda yake kwance din.
Kallon wurin nayi sai na dan juya da niyar komawa inda na bar wayana in zauna naji ya koma hannuna yajani zuwa jikin shi na fada mai lokaci guda ba shiri a jikin nasa ya mayar da hannayen shi ya rufmu a tare.
Idanuwana na runtse lokaci guda don jin jikin mu daya hade a wuri daya lokaci guda Zahra banda abinda zance dake sai in kara gode maki.
Ban taba yin tunane ko tsamanin saka rai da samun ki a matsayin mata a gareni ba sai gashi Allah ya mallaka min ke yau a matsayin matar sunna ta aure a gareni.
Kokarin nake na kwanci kaina daga yadda muken don a sabon abu naga abin yana faruwa dani lokacin wai nice a jikin wani namiji hakan nan ?
Yana kokarin wasa da sassan jikina kuma kwance wuri daya dashi a lokacin duk da ina kokarin janye jikin nawa baisa inji alaman yana da niyar sakeni ba shi a lokacin.
Ganin hakan yasa nayi karfin halin fadin don girman Allah Master ka bari ka barni in samu natsuwa a jikina please na fada a cikin karfin hali.
Lokaci daya da fadin hakan tsam naji ya sakeni ya koma gefe daya yana numfashi a hankali kafin naga ya mirgina ya tashi zuwa falo ba tare da yin magana ba.
Abinci ya zauna yaci kafin ya gama yajewa iyayyen shi saida safe a nan ne dije ke nuna mashi kayan da aka deba muna cikin na garan da aka kawo muna din a gidan.
Inda take mashi bayanin komai bai tsaya saurarenta ba ya mike yana fadin da safe zai shigo ya kwashe don dare yayi a lokacin.
Y nufi kofan gidan ya rufo masu gida ya juyo ya shige part din namu shima ya rufe saboda tsaro ya tsaya ya duba ko ina kafin ya juya ya shige dakin ya rufo.
Koda ya shigo dakin ya hangoni na sunkule a wuri daya saidai kafafuwana suna kasa hakan yasashi tsayawa ya dauki kafan ya dora min su saman gado tare da daukan wayana dake hannuna ya aje a gefen gado kafin ya fada bandaki ya dan jima yayi broshe ya fito.
Ya dan dade a tsaye yana kare min kallo yadda na kwanta da a laman a firgice na kwanta ko kuma damuwa yasa na kwanta a hakan da nake kwance din.
A hankali ya tako zuwa bakin gadon ya hau gefen gadon shima a hankaki don kada motsin shi ya tayar dani barcin dana samu din ina yi a lokacin.
Haka ya kwanta yana dan juyi a hankali yana faman yan sake saken maganganu a zuciyar shi kafin ya mirgino zuwa inda nake yana jin nimshina na sauka a kunnuwan shi.
A daidai lokacinne ya sake ajiyan zuciya yakai hannunshi saman jikina ya rungume ni yana mai jin wani iri a zuciyar shi lokaci guda.
A haka barci ya dan fara satan shi a hankali ya fara runtse idanuwan shi a hankali ya kara manna jikin shi danawa ya fara barci.
Can wajen asuba ya falka a lokacin na kara dunkulewa sosai cikin jikin shi barcin ya gagareshi komawa baisan sanda ya dauki hannayen shi ya fara dan wasa da sassan jikina ba a hankali.
Jin hakan kamar a mafalki yasa na bude idanuwa a cikkn magagin barci ga idanuwana da nauyin barci lokaci guda nake fadin wai hannatu meye hakane ?
Murmushi yayi ya ci gaba da abinda yakeyi a lokacin matsawan da yayi da yin hakan yasa na bude idona da kyau ina dahintar abinda