Showing 246001 words to 249000 words out of 304363 words

Chapter 83 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33284

dan matsa ina tambayan ya jikin nasa sai anty Aishace tace min da sauki yanzu kike tafe ?
Eh na tsaya na karasa girki nazo dashine keko da tambaya kikekin sani ko an tsaya neman na mashin ne ko ana can ana dabara tunda ba abin hawa ke garesu ba hjy ta fada.
Koma meke garemu aidai nazo na wuce zuwa wurin Abba inda mama da ummah suke saman gadon suma zaune nabi Abba din da kallo duk ya rame ya fada sosai ga farin gashi ya cika masa fuska sai ya koma min kamar ba Abba ba.
Halan me kika dafo zahra zara hjy ta tambayeni nace dawisu da jimina na bata amsa ta mere bakinta tace da wanan mijin naki fakirin ai ko a makwabta baki jin kamshin su a wanan unguwar naku mai kazantar tsiya din nan.
A lokacin yake sallama ya shigo da kayan abincin cikin daki yana sallama duk abinda ta fada kuma a kunnensa amma ya wayen ce yana gaidasu tare da tambayan mai jiki.
A, a dama tare kuke ashe waiku ga irin masoyan birnin nan ko anyo tafiyan mata da miji din nan to yaya son ran naki ai nafiki tunda zamanin ki ko kofan gida mijinki bai yarda ya fita dake gwadawa tsara.
Mai karatu kowa yasan dan hausa da fadin magana kai tsaye ta fada min na fada mata wai ashe hakan kuma laifine a wurin ta sai ta fara fadin .
Ke ki fita a idona zahra don ke haka kike fadawa mutun duk kalman dayazo bakinki kai tsaye niko danayi aure ba macen da zata nuna min yatsa ban gwada mata ba.
Ke har wani auren kikayi haka a jeme kike ganin kinkai kowa Allah ya gani ya hanawa jaki kaho da bamusan iya tafiyanshi ba.
Maahmah kama min bakinki a wurin nan kada ki tayar da mahaifinku ummah ta fada don ganin zancen zai baci a lokacin hjy tace ki barta mara kunya ina daidai da ita ai.
Yarinyar nan ina kula duk muka hadu sai wani dage kai takewa mutane kamar wani yasata zaman gidan mijinta haka ke kika mayarda kanki baya a cikin dangi ai ba wani ba.
Idan na mayar ai bada wani na mayar din bako kaina na mayar hakan bake ba wai ba nace kiyi shiru ba ke baki da kunya ko maahmah ?
Muryan Abba naji yana fadin wai meye hakane kafin wani yai magana Rukkaiya tayi saurin fadin Zahra ce da hjy suke musayan yawu daga zuwanta.
Kingani kuntayar dashi kuma likita yace a barshi ya samu barci wai wama ya bari ana shigowane saida nacewa Uwa kada ta bar kowa ya shigo dakin nan fa.
Harda ita maahmaah din naji ummah ta tambaya sai mama din tace ita daban ne da saura kodon su Rukkaiya na ciki zaune dole ke nan sai itama din ta shigo kike nufi.
Wai meye hakan ne kukeyi a gaban surukin ku kuma kai kuzo nan Abba din ya fada jin hakan yasa muka taka zuwa gareshi muna gaidashi.
Ya kalli Ahmed yace tare kuke tafe kana gari ke nan yace eh nazo sai kuma nayi dan rashin lafiya shine ban koma ba yace jam aiko kaganta bata bugo muna ba ya jikin naka yanzu kuma ?
Yace da sauki sai kuma tari ya kama Abban hankalin kowa ya daga a dakin da kyar ya samu ya lafa yana son cigaba da magana da Ahmed din sai tarin ya hana.
Mama tace wai maganan dole baka bari har ya fadama sai kajawa kanka matsala kuma tunda likita yace ka samu hutu.
Ke haka nake fama dashi fa yanzuma ai naji saukinsa sosai ya fada kamar bai gane me mama din take nufi ba a lokacin.
Suyi fira da Ahmed din yana bashi labarin ciwon nasa a lokacin ne ummah ta bude abincin tana fadin ga Abinci nan sukazo ma dashi ko a zubo makane ?
A bari a kawo daga gida mana wanan din wasu suci mama tayi saurin fadin hakan shi kuma Abba din yace don me zan bar wanan din ba yata ta dafo min ba zuba min inci jin hakan yasa kowa ya fuske a dakin nan ummah ta dan zuba masa ta dora masa gaban kazan ya karba yana zolayan mu yana ci.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/23, 7:27 AM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣4️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Ruwane daure a hannunshi ake kara mashi yayin da mu kuma muke zaune gaba dayan mu a dakin muke kallon yadda ruwan ke tafiya.
Ranan yadda Abba ya kulla master ya nuna yana da muhinmanci a gareshi zakice ko yasan da zancen samun aikin master din ne a lokacin yake hakan.
Don ya mayar dashi kamar dan cikinsa ko wani makusancinsa haka a wajen duk da mama da wasu irin su hjy kakarmu suna kokarin kushe zancen Ahmed din idan yace a kirasa yaje yayi wani abin .
Yanzun ma neman sa yakeyi don bazance Abba yama san sunan Ahmed din ba don cewa yayi ina shi wanan yaron yaje ya kira likitan ruwan ya kusa karewa.
Mama da ranta yake bace ta zubawa diyanta da suke cin abincina ido don ba a kawo wanda tace a girkawa Abba din ba duk da ummah ce da alhakin hakan amma a gaban kowa mama tabada umurni a waya a girkowa Abba abincin a kawo masa.
Sai gashi mai aikin nata tayi sanyin akin ba a gama da wuri ba wai nikan wakene basu samu ba ansha wahala kafin asamo nikan saboda ba wutan nepa kwana biyu garin.
Har yakai Aisha ta jawo kullan ta debi abincin itama Rukkaiya din ba kunya ta zuba taci hjy kuma tace su miko mata kataran kaza guda kada in shammaceta da halina don da ta dauki fushi dani nima tun kallon warning din da ummah tayi min yasa na kama kaina a dagin.
Wai me zaimane kuma mama ta tambayi Abba din a dan hasale tana nuna bacin rai ga hakan gareshi yace yazo yaje gun likitan mana ya fada a dan wahalce alaman yana jin wani wuri a jikinshi lokacin.
Saishi zai tafine ga su hamza a waje a kira wani mana yaje saiga Ahmed din ya turo kofa ya shigo Abban baibi ta nata ba yace kana inane nake neman ka ka duba likitan nan tun dazun zafi nake ji sosai.
Subbahanallahi naje na danyi sallahne dama ya fada yana aje kayan sanyin drink's daya kwaso a cikin leda mai yawa ya kawowa su ummah.
Bari naje na nemoshi ya fada da sauri zai fita sai kuma ya juyo yana fadin Princess ki rabawa kowa drinks din asha ga saura nan yaro zai kawo ya fita.
Lokacin kuma yaron yazo da katon biyu na kananan gora masu sanyi ko ina ya samoshi oho shi kuma ya fita na mike na bude ledan naga wanan na cikin ledan daban yake da sauran nagane nufinsa yan gidan mu su sha wanan din me tsadan .
Wanan kuma na rabawa dangi dake waje hakan kuma nayi suna godiya inka debe mama da yaranta da karba kawai sukayi suka aje a gabansu amma kuma bai dadeba yaran suka bude suna sha suna yaba sanyin drinks din.
Can hjy ta mika hannu ta dauko nata tana fadin bari musha indai ba dan jarinsa ya kwashe yayi wanan bajinta ba garemu don a yaba masa.
A to mama ai kema kin sani mama ta fada tana hararan kwalin lemon na gabanta sai Rukkaiya tace mukan ina ruwan mu sha zamuyi tunda ba a roka ba.
Dani da ummah yu mukayi kamar bamu jisu ba don lokacin ma ina magana da ummah nake fadin ummah a bude maki kishane tace barshi har likitan yazo muji sai gasu sun shigo tare da likitan.
Kallon dakin likitan yayi yana fadin kai kunyi yawa mana cikin dakin nan at list dan hutu sosai muke son ya samu don Allah a rage a bar mutum daya ko biyu su zauna dashi shima din banda hayaniya please.
Kallon kallo aka fara a dakin nice ta dayan mikewa don kallon da ummah tayi min na tattara kaya zuwa waje nan nafito naga yan uwa sun cika asibitin wasuma idan ace ba a shiga sai subar sako su wuce.
Wanda bamu gaisaba muna gaisawa dasu can naga su Aisha sun fito tare da hjy suma ana wani rawan jikin masu shimfida suka fito wajen don su zauna.
Gurin gwaggo shafa na nufa na dan duka a gabanta tare da dafa cinyoyinta ina fadin gwaggo ki gafarce ni wallahi kwanan nan bana samun kaina kinsan ina gab da gama karatuna yanzu.
Tace ni yanzu me nace bandaiyi magana ba ko wai tsaya ta fara kai hannunta saman marata tana shafa ina dariya tace wai tsaya zahra injin dai ba planing kukeyi ba don Allah ?
Yan uwan auren kifa zahra dana bayan ku har wasu na batun kara na biyu na dan marairaice ina langabe kai nace to gwaggo Allah ne bai kawo ba ai da ansamu din.
Ke fadi gaskiya kada dai kurciya ya debeku kuje yin wani planing can tun baku fara samu ba wallahi gwaggo ba hakana bane ina dariya ta jawo kaina ta rada min a kunnena kodai surukin nawa raggone zahra ?
Muka kwashe da dariya tare hankan ya kara jawo hankalin mutane a garemu daga can naji muryan hjy na fadin ke Shafa ke da nufin tazo tana kiranta.
Duk da zato zunubine amma nasan don ta dauke malta hankaline ta barni yasa take mata wanan kiran haka ni kuma saina koma na zauna inda ta tashi din kusa da matan su baba Ado.
Dasune ma muke dan fira jefi jefi kafin naga fitowan master daga cikin dakin ya nufi wurin mashin dinshi ya hau nan matar baba haruna ke ce min ke maahmah ga mijinki can fa zai tafi.
Nace kila ba nisa zai tafi ba mama suna jin dadin yadda nake basu girman masu na matsayinsu na matan ubannena dukkansu muna gaisawa lafiya dasu fiye da gwaggonena da suke nuna jin tsoron hurda damu kada mama ta gani ta daure masu fuska su rasa samun abin duniyan da suke samu a wurin Abban mu din kai duniya akwai cakwakiya a cikinta musanmanna namu nahiyar ta sokoto.
Don sai kiga idan kina hurda da uwargida ko amaryan gida wani lokaci ko gaisawa ba ayi tsakani sai kiga an dauki kishin duniya a dagwarawa kai.
Wanda zance irin wanan rayuwan mun saba don mun taso a cikinsa don mafi yawan yan uwa suna bangaren mamane suna tsoron hurda da ummah kada ran mama ya baci tunda itace me power agidan na mu.
Binshi nayi da kallo har lokacin daya hau mashin din ya fita daga cikin asibitin ina nan zaune wata tobashiyan mu tazo duban Abba din take tambayan hjy da.
Hjy tsohuwa ina nawa abinshan da aka raba zoki kwata hjy ta fada tana kallonta kafin tace kinsan dama ai isan baka isa bane akayi dama inba karya ba ina za a iya bamu kayan sanyin da zai wadatace mu wurin nan dama ?
Daga can cikin matan su baba Ado daya tace kinsan hannun daya saba bada alheri baya gajiya da umhumm don haka a sannu zai bayar kowa ya wadata wata rana.
Gaba daya wurin sukayi tsit ana sauraron su tare da mamakin to ke yar buga waya saka bakinki cikin zancen jika da kaka har kina sharbe magana daga zuwan ki haka.
To nikan ina nissani amsa dai na fada masu daga nan inda nake zaune don nasan manya na fadin duk wanda yabaka kadan wata rana shinaka baka babba ai.
Sai lokacin na gano me hjy ke nufi da zancenta gashi Allah da ikonshi na samu wandata bata amsa a take daidai da maganan da tayi din don da darko sam ban gane me suke nufi ba.
Saida naji wanan matar baban namu na fadin gulmoddiya,i nika wallah na fada dama tunda zahra tattaho ta raba muna kowa guda guda naga wadda suka binta da harara shiyasa na gane maganan da sukai ai.
To inbanda tsiya asibiti har wurin zuwa cin dadine wanda ya taho gaida mara lafiya ina ruwanai da wani abu kamar wanda ya taho gidan buki.
Tsam na mike na nufi wani wuri dana hango mata suna alwala nayi alwala na dawo na tayar da sallah bayan nagama na dawo inda muke zaune na hango dawowan Ahmed din tare da wani ya goyoshi mutumin ya dauko wani abu a bayan mashin din.
Saida na duba da kyau nagane ashe wani yarom makwabtan mu ne ya goyo ya dauko generator da fanka don kawai a kunnawa Abba din tunda yace zafi yake ji sosai likita kuma ya bada daman hakan garesu.
Nan suka hada mai iska ya kuma samu barci sosai karfe hudu ummah ta fito don tayi sallah nan take cewa na koma gida don mijina yaje ya huta shima tunda shima ba lafiyan ce dashi ba.
Saida na shiga na kara duba Abba har lokacin yana barci yan uwansa maza na samu a dakin zaune tare dashi nayi masu sai an jima na tafi.
Ahmed din ne ya kaini gida a lokacin muka samu inna da kawayenta suna shirin zuwa duba Abbana sai gashi mun dawo suke tambaya akace da sauki na dawo nayi girkine in koma Ahmed ya fada.
Sai inna din tace gasu tambai dasu inno sunzo zamu tafi asibitin mu dubashi eh yana nan har yanzu barci dai yakeyi ana masa karin ruwa.
Yayi masu kwatance yace sai sunzo zai dauki dije yaje da ita akai sa,a sun samu Abba ya falka yana zaune suka shigo dakin tare da Dije ya gabatar mai da ita cewa kakanshine wace ta tayar dashi.
Suna dakin su inna suka shigo su hudu sun samu ummah na tsaye gaban shi tana gyara mai baki da aka bashi abinci nan ummah kawai ta sansu don haka ta gabatar da inna ga kowa ta hanyar fadin ga mahaifiyar mijin Maahmah da yan uwanta.
A,a, a ikon Allah itace mahaifiyarshi dama baba Ado ya fada a cikin mamaki basu dade ba sukayi masu sallama suka fito daga dakin nan kuma gulma ya tashi sun kasa hakkuri su fice daga asibitin har yakai suna gulma a gaban matan baba Ado din ido ya rufe a lokacin don gulma.
Sai bayan sun wucene suka gane ai yan uwanane ashe suka tsaya a gabansu suna gulma don su basuga alaman gaskiyan abinda suke ji a wurin mutane ba.
Tunda gashi sun samu ummah tsaye tana kula da mijinta haka kuma babu wani abin nakasa a jikkn ummah da zasu zaga asalima yau sun gane cewa itace na kwaso a kammani.
Har suka fito suna zance akan yanayin gidan mu duk da sun gani a idon su hakan bai hana su aibanta uwata ba wanda innace keta zuba akai har suka hau mashin suka dawo gida wanda anan ma dai saida suka dan taba gulma kuma kan mama don yadda take watsa masu kallon banza a lokacin yaciwa abokan na inna rai sosai inda wasu ke fadin mu dai aiko yama uwar sarakuwarki take a gidan mu tafi muna wanan nakasassan matar uban nata dake wani jiji da kanta ga mutane.
Don gaskiya ummah ta nuna su natane don ta basu kullawa sosai a dakin wando ko kallon arziki mama taki tai masu sai kallon su da ta dingayi a wullakance karshe ma kamar ta matso da su fice daga dakin don ta fara fadin anyi yawa a dakin lokacin yasa suka mike suna Allah ya sauwaka suka fito.
Hakan ne mafarin fadin maganganun su har dayan ta tsaya tana fadin abinda idonta ya gano mata a cikin ahalin namu .
Bai dawo gidaba sai bayan magariba inda yazo ya daukeni da abincin da nayi muka koma asibitin don duba jikin na Abban mu da a yanzu yaji sauki sosai saidai karfine da baidashi har yanzu din.
Don a gaskiya matsalan shi da hjy karimace duk ya haifar masa da wanan matsalan don ba karamin barna hjy karima din tayiwa Abban sanadinsa ba a lokacin.
Wanda har hakan a yanzu yake barazana a cikin arzikin Abba din saidai bai fadawa kowa hakan ba amma ita ummah ta riga data samu labarin komai ta hanyar aminiyarta dake can Abujan.
Wanda itama tajine a wurin mijinta har take sanar da ummah din halinda mijin nata yake ciki ita kuma taja bakinta tayi shiru bata yarda ta fadawa kowa ba balle ace a bakinta akaji.
Sai gashi hakan ya tabbata don yadda Abba din ya dawowa iyalan nasa abin yabawa kowa tsoro a lokacin amma sai suka dauka cewa ciwone ya kaishi ga hakan daya zama a yanzu din.
Bamu dade a wurinsu ba don ummah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login