Showing 204001 words to 207000 words out of 304363 words

Chapter 69 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33340

tas bayan fitanta din don wanan maganan data sake a gabansu shine kuma a karshe ya zamo silar shirin mu sosai da mutanen gidan da muke makwabtaka dasu din.
A gidan mu kuma mama taso ta dauki zancen da zafi saidai ummah bata kulata ba sam don haka bata samu wurin yadda mata maganan dake cinta ba a lokacin.
Haka kuma koda Abba shima ya bugo yana tambaya ko tana ina da dare bayan ta dawo take fada mai tana gida.
Hakama da safe ya sake tambaya duk tana fada mai tana gida yake tambaya bata koma asibitin ba tace tunda ga mutanen gidan mu da abokaina a gidan me zata komayi kuma ?
Jin hakan yasa tasan da wata a kasa akwai abinda ake shirin kulla mata yasa ta share zancen gaba daya shima Abba din yayi shiru ya daina tambayanta tana inane saidai idan sunyi waya a yinin ranan ya tambayi ya taji jikin nawa.
Sai tace bata kira ba don suce na samu barci mai nauyi inayi sun danyi hiran matsalan kafin ya kashe wayan tun wanan lokacin bai sake kiranta ba ya tambaya yasa ta share ta zauna gida ba don bata damu ba.
Yabi taji muryanshi yana fada abinda rabon ta da jin hakan bata san tsawon shekarun da aka dauka ba sai gashi ranan ya kirata da haka kuma a cikon kakausar murya dake nuna bacin rai karara ga meshi.
Ta dago itama ta kafeshi da idanuwanta tana sauke nata bacin ranta cikin nasa saidai ganin shi haka yasa nata ya kawu a cikkn dan kankanin lokaci.
Fada min dalilin ki na yin almubazaranci da abinci a gidan nan don bansan me hakan ke nufi ba saboda hakan ya nuna rashin tarbiya da rashin tsoro Allah kwata kwatama badai tarbiya ko sanin ciwon kai.
Ke nan nice din yau banda tarbiya banda tsoron Allah saboda nace mai aikina ba zata girka abinci a gidan nan ba duk mai sonci ya fito ya girka da kansa aiban daukowa kowa yar aikiba.
Ok ashe ita Asabe din yar aikin kice bata gidana dana dauka yar aikin gidanace ita amma yanzu barin kirata mu raba gardama sai asan hukuncin da za a yanke karshe .
Daga nan inda yake ya dannawa Asabe din kararawan kira da sauri sai gata dakin hjy yabi din a na ta samesu tsatsaye cirko cirko ba wanda kewa wani kallon arziki a cikinsu.
Ganinsu hakan yasa tayi niyar juyawa saiji tayi yace dakata shigo ta tako zuwa ciki ta tsuguna a kasa yace dama na kirakine naji zaman wa kikeyi a gidan nan ne ?
Yo Alh ai duk a karkashin innuwar ka muke zaune gidan nan yace ke kika san hakan don hjy tace ke yar aikintane yasa na kiraki naji daga bakinki yanzu idan zaman ta kike a cikin gidan nan da hukunin da zan yanke a yanzu kanku dama.
Jin haka yasa da sauri tace dagani har hjy din ai a innuwarka muke zaune ayi hakkuri Alh munyi kuskure dani da uwar dakin nawa hakan ba zai sake faruwa ba Insha Allahu.
Asabe yaushe har kika samu daman yin irin wanan maganan da maigidan nan haka sai taja bakinta tayi shiru tace na fadama Asabe a karkashina take na sake maimaitawa ko a yanzun din kuma.
Idan kayi hakane don ka tozartani dama to yanzunma na sake fada Asabe yar aikinace da diyana ba da wata ba ok idan yar aikin ce sai ki hada da ita yanzun ku bar min gidana bana bukatan bude ido in ganku a gidan nan kuma.
Alh ayi hakkuri ni din zan tafi ku sasanta kanku abin bakaina tafiya tare da hjy ba sai ya daga hannu yana fadin dama abinda nake son naji ke nan kuma najishi a yanzu don haka awa biyu na baku kubar min gidana.
Wani kallon mamaki take watsa mai lokaci guda kafin tace lalai namiji ba dan goyo bane yau Alh ni kake bude baki kace ka umurceni danabar maka gidanka akan wata mace ?
Eh ba dan goyo din nake ba kema ba yar mutunci kike ba tunda har kikaso tozartani a idon jama,a don kina ganin ban iya daukan mataki a kanki ko me ?
Ni kake fadawa na barma gidanka ido rufe haka yace kwarai na fada idan kika matsa gidan zaki barshi a yau ga baki daya don ina nadamar hada zuria dake da wanan hali naki na rashin imani ga kowa.
Baki ta bude cikin mamaki tana kallinshi kafin ita Asabe din dake tsugune gefen su ta mike tana kara bashi hakkuri da fadin Allah adaiyi hakkuri a faki gaba anyi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba don Allah.
Juyawa yayi ya fice daga dakin ya barsu a cikin tashin hankali don har lokacin hjy yabi bata samu rufe bakinta dake budeba a lokacin don mamaki dayasa ta dauke dip a lokaci guda.
Sam bata taba tunanen irin haka zaizo mataba a gidan don yadda da amanna da tayi da irin aiyukan mallaka da ake mata akan Alh wanda sai yadda tayi dashi a rayuwa.
Ga wayanta yana kara amma ta kasa dauka don yanayin tashin hankalin da take ciki a lokacin dole maishi ta hakkura da kiran da take mata lokaci.
Shiko na manzo yana fita malam sale na kiranshi ya dawo don haka yace ya kai kitchen yaba Asabe takaiwa bakin gidan suci amma kadata bari a gane ba a gidan aka girka abincin ba.
Zakice bani bace yadda na koma kwana biyu kamar wace ta dade tana jinya a hankali na bude idona ina bin dakin da kallo kafin in juyo ina kallon mutanen dake cikin dakin a lokacin.
Daga can naji muryan gwaggona Shafa wace autace a dakin su Abba tana fadin kin tashi mahmah ya jikin naki jin hakan yasa kowa ya kallo inda nake kwance suna min sannu da jiki.
A daidai wanan lokacin akai sallama a kofan suka shigo su ukune tafe mamace tare da yaranta Aisha da Rukkaiya dake dauke da ciki tsoho.
Nan aka fara gaisuwa tsakaninsu da wa yanda suka sama a dakin sai jan kamshi da mere baki mama din take faman yi kafin tace to ya mai jikin da sauki ko , ?
Yanzun nan falkawanta ke nan daga barci ance tun safe take barci sai yanzu ta tashi saita juya tana kallon inda nake kwancen tace Zahra ya jikin naki ?
Kokarin bude baki na nayi in amsa sai na kasa na dai gyada mata kai alaman amsawa a lokacin gareta wanan karamin asibitin za a kawota haka yaushe mutum zai samu sauki a nan ?
Aiko nan din ma suna kokari gaskiya gwaggo taba Aisha da tayi maganan amsa ballema ina ruwanta aida sanin uwarta aka kawota nan din kece mai bakin magana yanzu.
Kowa yai shiru kafin can ta fara fadin yaya za ayi in ta fada ace ankawota wanan wurin haka amma sai a dinga yin wasu abubuwa a boye kamar ba a son ka sani.
Ku daiyi hakkuri mu ko hakan ma munga sauki sosai wallahi ciwone inyazo sai hankalin na tare dakai ya gushe duk dabara saita bacewa mutane.
Dije dake zaune gefe ta fada cikin wani yanayi na fahintar abindake faruwa a dakin Rukaiya data fara tafiya tana toshe hanci alaman warin dakin ya isheta lokacin.
Mu zamu tafi mama din ta fada Allah ya sauwaka wasu suka amsa da amin suka fice ba tare da ko mutum dayansu ya karaso zuwa inda nake kwancen ba a lokacin.
Ganin hakan yasa na lumshe idanuna cikin takaici dajin zafin irin cin zarafin da suke min din yanzu don na fahinci suna kokarin nuna niba kowa bace a yanzu din cikin gidan mu.
Muryan mama din na jiyo tana fadin shafa mun biya mu dauko hjy muzo tace ita bata zuwa taga takaici tsuntsunda yaja ruwa shitaka doka suka fice.
Sai naji wata daga cikin matan da muke makwabtaka tace wanan fa wacece ita kuma matar babantane gwaggo shafa ta basu amsa taci gaba da fadin kinsan su yan gayu komai nasu na nuna haline asibitin ne bai masu ba wai yayi karami da kawo zahra nan da akayi.
Duk hiransu idona yana rufe har lokacin jin sallamanshi yana gaisawa da Dije yasa na bude idon don lokacin an rage yawa a dakin naji yana fadin gwaggo ashe kina nan har yanzu na zata zan dawo in samu kin tafi ai.
Tace haba dai na tafi kuma ai dole wanin mu ya zauna nan din a watse gaba daya kuma aiba komai kinyi kokari Dije ta karba don tana son labarta mashi zuwan su mama cikin hikima.
Wasu aiko zama sin kasayi a dakin sunce dakin yana wari yau aini naga abin mamaki dakin nan ko naga komu muna faman tsabatanshi ai don ko yar nan hannatu yanzu data shigo tana shareshi har ban dakin.
Baidai iskanci bane su nunawa mutane isa da gadara sufa haka suke duk inda sukaje sai sun rainawa mutum suna shiba kowa bane garesu.
Cikin kaguwa da tambaya yake fadin su waye sukazo dije din tace dashi hjyn gidasuce tazo da yaranta shine yar take fadan an kawo zahra asibitin yaku bayi.
Murmushin bakin ciki ya sauke a fuskanshi kadan yace lafiyan ta muke nema ba kyawon wuri ba ai dije ta tashi kuwa ya fada don kawar da zancen nata.
Eh ta tashi amma bata dadeba ta koma barcin ai idonta biyu koda suka shigo din ya tako zuwa inda nake yana fadin sannu zahra ya jikin naki.
Lokacin nayi kokarin bude idona na sauke akanshi ya kara matsowa kusa dani yace zakici wani abu da hannu na nuna mai ruwa nakeson sha.
Yace ruwa na gyada masa kai alaman eh yace da sauri ya dauko goran ruwa ya miko min yana kokarjn tayar dani gwaggo ta taso ta kama mashi goran ya gyara min kai ya ban nasha kadan na cire bakina .
Na koma saman filo gwaggo na kalla nan na hango tausayina zallah a idanunta take fadin ko zaki watsa ruwa ko zakiji dadin jikin naki ?
Na gyada mata kai alaman eh tace to bari a hada ai akwai ruwa a flask sai a juye kiyi wankan dashi inta fito taci abinci hakan akayi naji dadin wanan wankan don jikin nawa na danji ya kara sakewa ba kamar yadda na falka ina jin nauyinsa ba.
Washegari na samu sauki sosai a haka kuma yake fakan idon mutane yana shaka min magani sauki na kara shigata likita dayazo round yace zasu sallameni tunda naji sauki ke nan nayi kwana uku kwance asibitin.
Muka dawo gida ko nan bai bar min maganin ba saidai ban yawan magana sai abin ya kara damunshi dama can ba mai yawan surutu bace ni.
Ganin hakan yasa ya fara tambaya sosai a can wurin tambayan ne ake fada mai abubuwan shege dana tsohon kakana na Funtuwa da yaje.
Maganan dai dayace shine shafata akayi akwai makiya a tare dani mata biyu sune kebina da sheri amma iskan dake kaina basu yarda sun tabani ba.
Kaddaran mu daya dashi ba abinda zai cutar dani sai wani ikon Allah don muna da mabiya masu karfi a tare damu.
Yakanyi tunane wanan wani irin kaddarane haka maigirma da kowa ke fada ma har dai yakai ga tambayan mutumin daya tafi wurinshi a karshe yake fada mai cewa .
Ita kaddara basai ta wani abu ba ai kwai ya barwa Allah sanin sa amma gaskiya tsurarin mu iri dayane a tare suke tafiya daidai.
Tun Daga wanan lokacin ya natsu gida yana jinyata bai koma wurin kowa ba kuma na samu sauki sosai har ina zancen komawa school inci gaba da karatuna don ma Allah ya gyara ba a fara test din exam ba a lokacin.
Kwatsam kira yazo min na bisi cewa goma ga sabon watane tafiyan su zuwa interview don haka ya shirya dama da mukaji shiru an dan dake program din ne zuwa wani lokaci.
Nayi mai godiya tare da fada mai cewa nima nayi ciwone amma naji sauki na zata ai har anyi interview din ko ban sani ba ya tsusaya min tare da tambayan idan banji sauki ba mu shirya tafiyan dani muzo nan a dubani nace na samu lafiya.
Duniya ke nan wanda ban hada komai dashi ba ya nuna min kauna ta gaskiya har yana kokarin fita dani waje a duba lafiyata ga wa yanda muke uba guda suna nuna min kyama a yanzu don kawai ina matar fakiri.
Da yaya musane ya nuna kamar zai tausayawa lamarina amma yanzu har na manta dako yaushe rabon da muyi waya dashi don da farko muna waya amma daga baya kona kirama baya dauka hakan yasa na daina kiranshi.
Ashe abinda ban sani ba shine kamar yadda Abban mu yayi warning din kowa a kaina mama ma ta kara warning din diyan nata sosai kaina da ummah yanzu .
Shiyasa suka fita zancem mu ga baki daya ko ummah din sun daina waya da ita balle dan aiko mata da aike irin yadda sukeyi a baya.
Tun takwas ga wata ya bar Gusau zuwa Lagos abinka da dan tallaka tafiyan mota yayi bata jirgi ba hakan yasa ya wahala a hanya kafin yakai yana zuwa ya samu wanda aka hadashi dashi a cikin daren nan baiko gama hutu ba suka bar kasa zuwa us din.

Don Allah ayi hakkuri abubuwane sukayi yawa dole na dakatar da rubutun na kwana biyu yasa bakwa samuna kamar yadda muka saba kuyi min afuwa hakan ba yin kaina bane yan uwa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Abinda ya baka tsoro wata rana sai ya baka tausayi don kuwa wanan karon kuwa ta juyewa hjy Yabi matuka a gidan fafir Alh ya kafe akan sai ta bar masa gida tunda ya furta hakan .
Gashi sai faman kiran duk wanda tasan abaya yana jin nauyinsu tana roko da a bashi hakkuri amma amsa dayane don Allah wani ka gafarceni .
Banaki bin zancen ka bane amma dole sai yabi tabar gidan na na wata daya ko hakan zaisa ta koyi hankali nan gaba ire iren bayanan dake yawan zuwa mata ke na a bakunan mutanen data tura su bashi hakkuri.
Don sam bata taba tsammani da cewa akwai wani ranan da irin haka zai zo mata a rayuwa ba sanin cewa tsaye take kyam a gidan da kuma kan al,amarin mijin nata ba irin jinin da bata bayar ba akan sha,anin mijin nata.
Yau sai gashi tun bata kaiga ganin cikar burinta ba abubuwa suna son juya mata baya a cikin dan kankani lokaci haka gaba daya abubuwa sun rikicewa rayuwanta.
Bata da zabi dole ta sauke komai da takeji ta zubar da makaman yakinta ta kwatawa makiyanta ta samu tayi amfani dasu duk da cewa suna cikin lissafin mutanen da bata kauna a duniya ta gansu kusa da mijjnta kuwa.
Alh jabbo dole su zata kira don sune mutane na karshe daya rage ta jeraba sa,anta garesu ta gani ko za ai sa,a yaji maganan su a matsayinsu na abokan,nan sa kuma aminansa tunna zamanin kurciya da har yanzu suna dan biyewa junansu din.
Duk da ita din a yanzu tayi wani kokari da zatayi na ganin cewa ta raba alakan dake tsakanin shi dasu don ganin cewa a yanzu shi din ba ajinsu bane .
Abin kunyane a gareta dashi mijin nata a dinga ganinsu tare dashi a matsayin da a yanzu Allah ya kaishi din nan na zama fitacen dan kasuwa mai fada aji a cikin gwaunatin zamanin.
Don haka tayi duk wani kokarin ganin cewa ta raba tsakaninsu din su hudun ta fitar dashi daban a cikin su tayi kuma nasaran yin hakan yanzu sam ya daina ko zancen su arayuwan shi a yanzu.
Sai gashi yau ita da kantace mai bukatan taimako a garesu don gaba daya duk wani dabara nata ya kare don barin ta gidan kamar yadda ya umurceta dayi wani gazawane a gareta yanzu duniya zasu gane halinda take ciki dashi a lokacin.
Dole uwar naki tabi shawaran yar uwanta data samo mata layin wayan shi Jabbo ya dauka tare da tambayan waye don jin muryan mace da yayi a lokacin.
Da kyar ta iya amsawa cikin isa da takama da izza tana fadin kana magana da Yabice daga Abuja sunan ya fara maimaitawa a bakim shi kafin yace bai san wata mai wanan sunan ba gaskiya.
Ta fahinci iya gaskiyan shi kuma yana kokarin kashe waya yana fadin wrong number tace daga gidan dan gaske nake magana dakai ta juya harshe cikin filatanci yadda zai fahince ta.
Yace yabi dai yabi matar dan gaske ko watace dai take kwaikwayon ta a yanzu tace ita dince sai taji yace dewa,ya, i.
To hjy yabi badai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login