Showing 273001 words to 276000 words out of 304363 words

Chapter 92 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33321

Gashi da sanin ya kama ina zaune ranan bai fita ba yana zaune a gida falo yake kwance da yarshi suna kwasan rikici irin na yara yana biye mata.
Na taso na zauna ba tare da nayi magana ba ido kawai na kura masu daga inda nake zaunen ya dan dago kai ya kalleni yana fadin madam ya akayine na dan kallesu na gyara zama ina dan kwanciya tare da bata fuska don gaba daya banjin dadin jikina duk kwanakin.
Ganin banyi magana ba yake fadin ko jikin ne har yanzu muje asibiti naji sauki kawai dai jikin ne banajin karfin shi yanzu.
Kuma ga dai azumi ya gaba to Dije kuma ta nuna min gida take son zuwa yanzu don ta nuna ta gaji da nan din don zama wuri dayan ne nasan ya isheta.
A hankali nace haka dinne gaskiya ta gaji da zama kasan nan tana dai daurewane kawai bata nunawa jiya ai muna waya da inna take fadin wai Asmau ta samu miji ttace aure zatayi ita bata karatu.
Asmau da batako kare secondary school dinta bane take zancen aure a yanzu yace waya sanar mata ita ta sani don na kula inna ta daure mata.
Aisha dai munyi magana da ita tace wai FCE zataje kuma ban hanata ba tayi kokari ai idan ta tsaya tayi karatun don nam gaba zai mata amfani.
Muma gashi mun gama amma yanzu muna zaman gida shine ummah ke tambayana ranan tana min sheri wai ni dana tsaya nayi karatu yanzu kuma ban batun aiki .
Idanu ya lumshe kafin can naji yace gaskiya zahra bana bukatan kiyi aiki a rayuwana indai ba kinga gazawa na bane a gareki gaskiya tunda Allah ya hore min ya kamata ke ki zauna ki huta a gida kiji da dawainiyar gida kuma.
Amma idan kina ra,ayi ba zan hanaki aikin ki ba tunda ra,ayinkine dana iyayyen ki don da karatun ki na sameki don haka ba zan tauyeki ba a yamzu.
Gaba dayan mu shiru mukayi lokaci guda dagani harshi din da yake maganan a lokacina na dan wani lokaci kafin yace ina ma son kin mun list na wanda zamu turawa kayan sallah da abin azumi.
Saidai kada ki sa Abba da su inna dasu ummah da gwaggo shafa har da baba Ado dawa kuma can dai Mambila zan aikawa baba jauro da komai a can.
Duk kana da kudin da zakai wanan dawainiyar duk yadda ka lissafa murmishi naga yayi tare da fadin zahra ke nan kefa yanzu ba matar fakiri bane kamar yadda hjy tsohuwa take fada maki.
Wani kallo nayi mashi yace yes na sani zahra duk da baki taba fada min ba kina shanye bacin rai a zuciyar ki ke kadai ki sani bake kadai ke hadewa ba har dani abin yana taba min zuciyana .
Kada kice duk bansan halin da kike ciki ba na bakin ciki ga yan uwanki a kaina zahra nasan komai dake faruwa a lokacin kawai dai naga baki damu da hakan bane yasa nake sharewa nima.
Raina bata kafin nace ai ba don ka suke wanan maganan ba don ni da ummah ce kawai don su musguna muna suga mama taji dadi a rayuwanta shine kawai.
A ganin ki ke nan zahra lokaci yayi insha Allahu da zan nuna masu kuskuren su na fadin wanan zancen ni din dan halas ne zahra ba shege nake ba yadda suke daukana.
Shiyasa kikaga bana raina lamarin ummah da Abba don sun min komai a rayuwata don Abba yai min wani magana a lokacin daya tsaya min arai bayan ya gama min jawabi.
Wanda har yau dashi nake kallon Abba din don wanan kalamin na ba a wani a banza saika jajirce zuciyan ka kazama jarumi ka wanke kanka daga fadin mutane a kanka.
A lokacin nayi ta juya wanan kalamin a raina ina neman fassaranshi sai a yanzu nake kara gane me wanan zancen yake nufi a kaina zahra.
Abba yayi amfani da hikimarshi a lokacin ya aura min kene don yana da hope akaina kanki yasan zan rike mashi ke amana zan jajirce na zama abin kwatance dije gata nan itace ta fara fassara min me yake nufi a lokacin.
Nima dai nakanyi tunane meyasa Abba din ya yarda a lokacin haka kai tsaye ba tare da yaja ba kamar yadda ya nuna fushinshi a fili gareni ?
A yanzu din nakance what god has join together no one should put asunder on it dama Allah ya yomu a tarene kawai amma su mama dasu hjy tsohuwa sun nuna min zuciyarsu a fili a kaina.
Do master nida ummah munga abu a lokacin auren mu ummah tayi kuka kamar ranta zai fita amma kuma haka take ban karfin gwiwa kada in yarda wani ya fahinci abinda nake ciki har a kare bukin mu.
Ranan dai munyi ta hira a kan lokacin auren mu kafin Dije ta fito mu canza zance bayan kwana biyu yake tambayana ko nayi masa list din sai lokacin na tuna.
Na zauna na rubuta shi kuma ya karba ya copy a wayan shi Shehu ya turawa kudi aka sai komai yazo dasu nan part din ummah aka ta aikawa gida gadan yan uwana.
Har gun Aisha da Rukky akai gana gidan su hjy tsohuwa abinka da babban gida take kowa ke fadin albarkacin bakinsa lokacin hjy ko sai faman mere baki takeyi ta juya kayan shayin da turmin zani gami da kudin dinki da aka dora sama.
Shi wanan dan har yai kudin rabon kaya hakane dan tafiyan nan nasu hjy tsohuwa take tambayan gwaggo uwa dake dakin zaune lokacin.
Hjy tunda kikaga hakan ai kema kinsan arziki ya budu ke nan dama haka abin Allah yake ai ga bawa duk mai rai ba agama halittansa ba sai idan ya mutu.
Ni yadda naji ance babane shi yanzu a can turai din kuma wai wanan rikicin da mai sunan baba tela yayi shida mahaifinshine suka fito dashi don ance sun kashe kudi sosai ga maganan.
Ke rabani da karyansu na banza shi yayan ku baida kudin anso dansa ne sai wani ya saka mashi hannu yanzu da sauri ta dago tana kallon tsohuwar tace.
Wai hjy baki san halinda yaya yake ciki bane yanzu halan yayafa yanzu baida komai sheria suke tayi da wanan matar daya saka wai ta kwashe takardun kaddarorinshi tace natane .
Uwa a ina kikaji wanan zancen wallahi hjy a na dai boye maki maganan ne kada ki tayar da hankalinki ni yadda najima ance wai yanzu mijin ita zahra din aike rike da gidan nasu.
Baki kula ko hjy maimuna yanzu in zatazo da motar haya take shigowa ba ko inta samu wani yaje ya dauko ta duk motocinsu babusu yanzu.
Shiru tsohuwar tayi tana tunane kafin tace nikan nayi wanan tunanen don ko dan kudin da yake turo min yanzu ya daina sai in yazone ya hadani da dan dubu biyu ko ukku yace inyi hakkuri.
To wallahi kan hjy yayan mu ya samu kariyan arziki akan wanan auren kowa kuma ya sani ke daice ake boyewa akai sallama a dakin suka dakatar da zancen.
Matan su babane sukayo gungiya sukazo yin godiya gun hjy din don a dalilinta ai aka sameni don haka itama taci ai mata godiya a lokacin don hakane sukazo part dinta din.
Hjy munga abin arziki da zahra ta aiko muna wallahi mun gode ace a haifi da arzikin shi yafi a mutu abarmai gado inji uwargidan baba Ado.
Sai matan baba haruna tace aike baki sani ba yaya ance zakaran da Allah ya nufa da cara ana mazuru ana shaho sai yayi caran to shine nan.
Ana cewa mijjnta fakiri shegene baida asali yau gashi Allah ya azurta ta shiyasa ankace mai hakkuri yakan dafa dutse yaci.
Wane irin abune zahra bata gani ba ga wanga aure nata sai gashi yau Allah ya nufa sune masu bayarwa ana godiya.
Donshine Alh babba har hawaye yayi yau don ya rasa bakin da zaiyi godiya ga azumi tafe mazan mu suna cikin wani hali saiga wanga kyauta haka da rana tsaka ai dole kai hawayen godiya ga Allah.
Kowa na fadin albarkacin bakinsa hjy kan shiru tayi tana tunane kafin kowa ya koma part dinsa su barta da yaranta a dakin abin duniyane ya dameta jin halin da danta ke ciki.
Shiyasama bata iya tankawa kowa ba a lokacin don hakane kuma aka boye mata sai gashi gwaggo uwa yau ta fada mata kuma hakan ya tayar mata da hankali.
Azumi da kwana uku aka kwatar da hjy asibiti sakamakon jin halinda danta ke ciki yanzun da tayi shine akaga zata mutu a gida aka kwasheta zuwa asibitin.
Anyi sa,a Abba na gari yazo likita ya karbeta ga Abba nata kukan baida kudi lokacin duk master ya turo mashi da kudi masu yawa ummah ta kirani ta fada min halinda ake ciki don jikin nata sosaine lokacin .
Muna zaune tarene muna buda baki a nan wajen master ya kira mahaifinshi ya sanar dashi yace azo da ita nan abuja ta jirgi.
Abinka da hali nan danan aka shirya komai aka dauki hjy sai Abuja da yake tana da sauran kwana ta dai dan sha wahala ta mike.
Tare da mama sukai tafiyan ta karamci a wurin Abban Master don wani lokaci da kansa yake zuwa ya dubasu kuma duk iyalinsa sunzo.
Shi da kansa yake fada masu cewa Ahmed shine dana na farko dana fara haifa a duniya kaddarace ta rabamu a wani lokaci dashi.
Duk da hakan baku dubi yanayinsaba kuka dauki yarku kuka bashi don haka nake kaunan ahalinku ga baki daya don kun min komai a rayuwata.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/8, 6:44 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣3️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,


A cikin wanan watan azumin ya gane ina da ciki na biyu a jikina shine ke sakani wanan shirun da kuma yawan zazzabi kida yaushe da zaran ansha ruwa ko ace dare yayi ban kara lafiya sai zuwa goman safe zan dan ji karfin jikina in dan samu inyi wanka in fito falon mu duk da dai ba bacin komai amma zami gaisa da dije mu danyi hira sama sama da ira..
Don mafi yawan hira ita da Bahnan yata suke abinsu dije na koya mata hausa shi kuma ubban yana koya mata turanci haka yar ta taso da yare biyu a bakinta duk tana jinsu kuma..
Wata rana bau fita aiki ba dukkan mune a falin nasu zaune yana fira da Dije hannu daya kuma yanawa yarinyarshi wasa ta gudu daga wurin shi ta fada min a jikina.
Daje tace kai kai kai kada ki jin masu ciwo yar nan uwarki na fama da dan uwanki ko yar uwarki a jikinta katse abinda yake fadi yayi ya kallo Dije din da sauri.
Yana fadin dan uwa kuma Dije tace kai baka kula da cikin jikin matarka bane kome ko kana nufin asibitin da kuke zuwa basu fadama ciki bane da ita ?
Dan kallon Dije nayi na kawar da fuskana gefe daya ina ci gaba da dunkulewa yadda nake shima ido ya zuba min yana min kallon mamaki.
Baki na turo gaba na kawar da kaina gefe daya tsam ya mike tsaye ya nufo inda nake ya tsuguna daidai saitin kunnuwana yana fadin abinda Dije ta fada gaskiyane princess ?
Ban sani ba ka tambayeta tunda ta zama likita yanzu daga inda Dije din take tace kasan halin kan matar ka nima dai naga yawan ciwon yayi yawane yasa har na kula da ashe cikine da ita.
Wancan karon muna gida haka suka hanna a gane cewa cikine a jikinta wanan karon sai basu kayar da ita sosai ba amma suna bata wahala yadda ba a ganewa.
Nima ba wai na dade da fahitar hakan bane a dai yan kwanakin nan na fahinci hakan kasan dole in fahinta tunda ba yau ake ba ai.
Zama yayi kasa a wurin dirsha ya kura min idanu na yan mintuna kafin yace Alhamdullahi bini i,mati Alhamdullahi al kulli halin ya ar,rahman rahimin.
Allah ka bamu mai albarka daga inda dije take ta amsa da amin ni dai a zuciyana na amsa masu don nima kamar yadda dijen ta fada ban dade da gane cewa ina da cikin ba.
Gashi yace da an sallace zai fara shirin tafiyan mu gida mu kai dije data matsu ita gida zata koma don nan din gaskiya ya isheta.
Yanzun kuma ga zancen ciki ina zai kaimu gida haka a yadda nake cikina a wahalce gara dai ai ina nan kusa da bakin magani din.
Shine wata safiya zai fita wurin aiki yana tsaye bakin mirro ya daura tie a wuyanshi daga cikin mirror ya kalloni yace gaskiya zancen tafiyan nan na dije nayi cancel dinshi ba yanzu ba kuma sai bayan kin haihu zamu tafi gaba dayan mu.
Anya kana ganin dije zata yarda da hakan wace kullun zancen tafiyane a bakinta to ta tafi mana hakan zance mata idan ta matsa min mu gani idan zata tafi din ai.
Au sheri zakai mata kuma dijece fa kaidai idan ta matsa ka barta ta tafi din shike nan ai yanzu zan iya kula da kaina tunda naga yadda akeyi da farko.
No ta bari kawai idan kin haihu daga baya ma shirya mu tafi dukan mu gaba daya mu mu dan kwana biyu kowa ya ganku sai mu dawo ina ganin haka zaifi ai ko ita nasan halin dije idan na fada zata yardane nace idan ta yarda badon taso ba ka kuntata mata.
Ya gama shirinsa ya tako zuwa inda nake ya kai mun kiss agoshi tare da shafo marata a lokacin ne dan dake cikina yayi wani motsi yana canza makwancinsa.
Allah da ikonsa sai ga Dijen na fadi da kanta cewa ai yanzun kuma ba zancen tafiya gida gara a tsaya har in na haihu daga baya sai mu tafi din zaifi.
Tun nan na kara yadda da irin soyayyan dake tsakaninsu mai karfi ko dai ita ta kawoahi duniya ya tsaya a nan don kiri kiri ranan mun samu dan sabani dashi ta goya mai baya.
Amma daya fita ta dawo tana lakashi haba matar Amadi ba fushi akeyi ba ai kinsa na goyi bayansane kawai kada abin yai maku nisa amma ai nasan yaro saida kwabo.
Idan kuna gabanshi ki daina yiwa yarinyar nan tsanani yadda yake so sai a zauna lafiya amma ai nasan uwa ke bawa danta tarbiya kiyi hakkuri don Allah.
Amma kuma Dije ai ya kamata shima ki nuna mai tarbiyan yaro da wuri ake farawa ba sai yaro ya girma kace zaka tankwasashi ya lankwasu.
Ni yadda yake son mu bar yarinyar nan ba tarbiya gaskiya tsarinshi bai mun ba ki daiyi hakkuri yanzu ina yake ya fita sai kuma yamma ya dawo.
Keko kina gida da abinki wanan lokacin zaki samu ki sakawa yarki tsoron ki a ranta harta fahinci me kike nufi ko zatayi shegantaka a gaban shi saita kalli isanun ki don wanan kulawan da kike bata ai.
Shakuwa tsakanin da da uwa yafi karfi bisa na da mahaifi don ita uwa ko yaushe tana gida tare da abinta tana kuma kiwata abinta yadda takeson ya taso mata.
Mm a kashe rigimanne don kada shegen zuciyar nan nasa na fulanin ya motsa ya dauki fushi ba gaira ba dalili damu duka a gidan nan kin dai san halinsa ai.
Dije idan yayi ya bari ni ina ruwana da zuciyarshi tunda nima ina da zuciyar nawa tace a,a ke dai ba gashi zancen ya wuce ba yanzu.
Mafi yawan lokota a yanzu sakacin ubbanne yana cikin abinda ya bata tarbiyan yaran mu na yanzu don babu uwa da zata haifi da taki dorashi kan hanya mai kyau sai sakariya.
Wace bata da lokacin yayanta kamar namiji wai tana fita aiki ta bar yaranta da yan aiki a gida suna gurbata mata tarbiyan yaranta shiyasa a yazu din.
Mafi yawan yara so ya batasu sun lalace ta sanadiyar rashin kwabo zakiga a gaban kowa uwa taiwa danta tsawa a cikin mutane yaro ya kunyatata don bai saba da hakan ba.
A wurin buki zakiso nunawa mutane kece uwa saboda rashin tarbiya da zai kunyata uwarshi kuma kiga uwar na dariya tana wani fadi cikin zaro idanu ai zamu hadu kasan halina baka bari ko.
Yaron da wane shi uwa ko uba ya fada sau biyu bai daina ba duk har yanzu akwai irin iyayyen nan amma ba sosai ba masu jajircewa suba da tarbiya bisa al,ada da addini.
Kamar yadda kike sonyi a yarki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login