Showing 81001 words to 84000 words out of 304363 words
hankalin ki sosai abinda baki dashi ki kirani ko ki fadawa Hjy salma ta fada min.
Nagode Abba na fada yace wa kannena suzo suka taho yake binsu yana sallama haka muka rako shi har kofan part din mu don ya nufi part din mama yasa muka tsaya a nan muna masa Allah ya tsare.
Koda muka juyo zuwa ciki ummah ta fito falo a lokacin nan yaran suka rufeta da fadin Abba ya bamu kudi ummah tace kun gode ai na muka fara mika mata kudin an kawo kaina tace ki rike naki a hannun ki tunda ba tambayana kudi kikeyi ba.
Sallaman mommy ce hjy karima ta shigo da fara,a a fuskanta tasha kwaliya sosai a jikinta tana fadin to uwargida rangida mu zamuyi maku ta baki fa don Allah a gafarce mu.
Tare suka shigo da wanan matar suna sallama ummah din kafin ummah ta kakaro murmushi a fuskanta tana fadin muma ai ku gafarce mu zaku juya ke nan yau ashe ?
To ba dole ba tunda kun hana mu zama lafiya a nan din kunce bamuyi daidai ba ai dole mu juya kada azo rayuka suna baci a banza ni wanan matar da ace garin nan nake zaune tare da ita da mun kwashi yan kallo a tsakanin mu kullun.
Mace haka ba tsoron Allah sam a zuciyarta sai son kai da son zuciya kamar kowa ba mutane bane sai ita ai bata cika yar sheri ba tunda harta kasa hanashi kara aure takuma zauna da kishiyoyi aishe bata isa ba ke nan ?
Murmushi ummah ta kara sakewa tare da kallon matar da suke tare tana fadin baabba zaku koma ke nan ashe yaune tafiyan naku ?
Gashi dan tsaraba ba a hada maki ba zaki tafi hannu sake babu komai wallahi ko wanan fuskan da muka samu ai kin bamu komai sai kuma wani lokacin idan Allah ya kaimu.
Aita hakkuri kiji yar nan me hakkuri shike da riba wata rana in sha Allahu wata rana sai labari haka rayuwa take wani lokaci ga bawa mai tawakkali da Allah.
Nagode baabba ummah ta fada ta mika hannu ta dauko wani leda da tun shigowan mu yake aje a gefenta tana fadin hjy karima ga wanan a rikawa baabba ba yawa bamu sanda tafiyan ku ba yau ban hada mata komai ba.
Kai haba dai ba zamu karbi komai naki ba gaskiya haba dai bafa ke nabawa ba baabban mu nabawa don haka ki bar zancen nan don Allah.
Gaskiya ni banda bakin magana don ko hakan ai mun gode da karamcin ki garemu Allah ya kara bamu hakkurin zama tsohuwar ta amsa da amin.
Hjy kariman tace to ni ina skn naje nayiwa wanan sallama bansan da wani ido kuma zata tarbeni ba a yau don idan tayi min ba kyaleta zanyi ba.
A,a a rabu a gana alherine kada ki biyewa wanan aikin zama tare ne hakan don wanan zance ai ba kyaki zuwa kuyi sallama ba musanman ma ba da zata tafi.
Ke ke nan kika san wanan din bari dai din muje sai munyi waya in sha Allahu kuma suka fara tafiya don barin falon kafin ta juyo tana fadin daughter sai na aiko ke nan ko nidai nayi murmushi kawai na mike na dan rakasu zuwa fita part din mu dagani har ummah muka juyo muka dawo.
Hankalina na mayar ga tv da ake wani film din yara a cikin sa tani ce ta shigo tana fadin ashe yau zasu koma shike nan har sun tafi ?
To meye a ciki yanzu bagashi sun juya sun tafi tare ba kuma ba a isa a hana hakan ba don kwanan ni wallahi suyi ta kwana bashine a gabana ba.
Mazan nan da zaka mutu a kansu su kasa suma maka su wanan hauka hjy maimuna keyi tace wai bata yarda don sunzo nan din tare ta amshi girki ba tunda a can tare suke dashi.
Yanzu kinga ya barta da kunya kuma girma ya zube kan abinda baikai bai kawo ba an tafi an barta da bacin rai da takaici ga banza.
Ta dauka irin kine ai data saba takawa tana hawa yadda takeso a kullun tani ta fada yoni ina ruwana da wanan bakin haukan ?
Hjy ke wake daka ta taki keda ke barin mutum da wutar shi ta konashi ai zama da irin ku yana da wuyan sha,ani sosai idan mutum bai gama ganeku ba.
Ina zaune ina jin abinda suke fada gaba daya dana tattara sai na gane cewa abinda mama take son fada min ke nan da safe dana shiga wurinta yaranta suka hanata fada min komai.
Koma meye matsalansu ce ta manya hakan don su hakan ya shafa ba zancen mu bane mu yara wanan maganan tasu.
Mikewa nayi da niyar barin falon Tani ta kalleni tace dani uwar dakina komai ya wuce ke nan da alaman haka ?
In ma bai wuce ba ai itabta sani yanzu da muka kyaleta da shirinta ba gashi abin ya koma a kanta ba an watse a baram baram tsakanin su sheri ai dan aikene dama.
Nayi mamaki matuka da wanan zancen har yazamo hakan wani irin abune yaran nan basayi a garin nan amma saina wanan kawai aka gani a gidan nan har ya zamo min abin fade.
Yanzun dai ai intana da hankali tagani ke nan sai ta shiga hankalinta idan zata shiga don abin kulin sheri yanzu baida kadan ta dai rabu da yaron nan shima tunda har Alh ya iya kiranshi yayi mai warning nasan zai rabu da itane .
Haba hjy ki rabu da aikin so yana da wuya ace an rabasu haka farat daya yadda kuke nufi din nan sai dai ku bisu da addua shine mafita don uwardakina tana da saukin kai sosai don gashi dan maganan da nayi mata dazun yasa ta sake harta fito yau din waje.
Kuma fitowan ai ya zama mata alheri tunda uban ya shigo ya samu ra sake naga aisun shirya kafin su tafi hakan itama bai mata dadi ba yanzu ?
Darene gabanin asubahi lokacin sanyi ya sauko kowa najin dadin sanyin masu ibada a lokacin suna jin dadin yanayin dije dake kwance tana barci a cikin yanayin da kowa keji ta fara mafalki.
Sai dan juyi takeyi tana dan mutsutsuka kamar yarinya kafin ta mike zubur daga kwancen tana sakin salati lokaci guda tare da fadin Amadi ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
2️⃣6️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Ina uwargida da Amaren gida dama sarakan gida da kowa na gida muna maiba da hakkuri ga kowa dake jin ana fadan halin matsayin da yake a gida.
Uwargida sunce an soki matsayin su an rage masu GP amaren ma sukace ana fa yawan aza masu laifi hakama uwayen gida sarakan gida sun fadi korafin su.
To yar uwa rigace ta zamani abin yayi idan ke hakan ba halinki bane hslin waccan ce ko halin wanan don abinda yafi yawa a yanzu ne muke fada a fili.
Uwargida za a karo kishiya tace shigo zaki sameni ciki ai haka amaryan zamani da danmara a kwankwason ta take shigowa uwargida yanzu saidai kowa dabaran shi da rikon Allah ya fitar dashi.
Bana bayan kowa don kowa nawane a cikin don haka muyi nishadi mu karu da juna ta wani fannin don ace zomu zauna zo mu saba Allah yasa mufi karfin zukatan mu muyi kishi daidai da imanin mu amin nagode nagoda da bin novel dina ko wani lokaci.
Zufa take karyawa daga zaunen kafin ta tattaro zuciyan ta wuri daya ta samu natsuwa ta dauki hakan da sherin mafalkine ba wai zai faru a gaske ba.
Jin budan kofan jikan nata har shigan shi dan makewayin su ya fito duk a kunnen Dije da jinsa ya fito dags bandakin yasata bude kofan ta a lokacin da yai daidai da muryan Amadin dake fadin waye a wurin nan ne wai tsugune ?
Dije dake fitowa ta amsa da ina kuma yace daga barin katangan can kamar mutum yana zaune a wurin da sauri ta koma dakinta ta dauko toci tana kokarin kunnawa zuwa lokacin har Amadin ya mike ya kusa kai saitin wurin da lalube don ganin ko waye ?
A lokacin Dije ta hasko tocilanta a wurin ja yayi ya tsaya wuri daya yana jan tsuki tare da fadin ashe dan icen nan nefa yayi girma haka har nake ganin innuwanshi kamar na mutum a wurin.
Ya juyo ya koma inda yake duke da farko da shirin alwala Dije da ta shige bandakin ta fito ta samu zai fice zuwa masallaci tayi mai a dawo lafiya.
Ya amsa a gurguje ya fice daga gidan har cikin lokacin akwai sauran asubahi don haka akwai sauran duhu sosai gari bai gama washewa ba a lokacin.
Kai ta dago daga inda take zaunen ta kalli wurin da Amadin ya kalla abinda yagani ta ganowa idonta itama don mutum sak ta gani a wajen duke.
Gaban Dije ne ya fadi dam lokaci guda don abinda idonta ya gano mata din a lokacin sauri Dije tayi ta mike a daidai lokacin uwargarke ta saka kuka acikin muryan data kwana biyu batayishi ba a gidan.
Tun wanan lokacin wanan akuyan bata sauta kukanta ba haka take tsaye tana wani irin kuka sauran dabbobin kuma suna tsaye suna kallon ta yayin da kunnuwan su yake wani irin dage da alaman wani abin tsoro suka gani lokacin ya gitta.
Har Amadi ya dawo daga sallah suna a hakan wurin su ya nufa ya zagaya su ya dan duduba ko maciji suka gani don suna hakan idan dabbobi sunga wani abin cutarwa garesu.
Zasu dauki kuka sosai suna nuna alaman hakan saidai hakan yana da wuya a iya gane hakan idan ba mutum ya kwarai a kiyo yayi sabo da dabban zai iya fahinta idan ta shiga cikin bakon yanayi.
Share wurin yayi ya debo masu abinci ya canza ruwan shansu ya dan juya zaibar wurin a lokacin uwargarken ta dona kanta tsakankanin shi zakace tana susan kantane ajikin nasa a lokacin.
Kiyi hakkuri uwargarke kuci wanan dusa yau in sha Allahu zan sayo maku abinci idan zan dawo kuci wanan din ku koshi kafin na dawo yana dan ture kanta daga jikinshi.
Buta ya dauka ya cika da ruwa ya nufi bandaki ya watso ruwa don haka al,adanshi yake bai tsaya yayi wanka yadda ya kamata sai ranan jumma,a zai tsaya yayi wankan arziki ya gyara jikinshi ya fito mutum sak sai ko sallah bana da yayi kokari ya dinka kala biyu koshi da dalilin yin hakan a zuciyarshi.
Kananan kaya ya saka a jikin shi ya dauki dan jakkar da yake saka takardun shi ya fito bai tsaya wani duban ko shigar tasa tayi ba ya fito daga dakin.
Dakin Dije ya nufa tun kan ya karaso ya fara kwalawa Dijen kira yana fadin Dije ni zan shiga school kin san yau zamu koma makaranta .
Yaka Amadi muyi magana dije ta fada cikin tausasa murya yace wallahi Dije na makara yau din nan kinsan yau aka koma daga hutun sallah gani a gida har wanan lokacin zam iya zuwa na samu har an zauna.
Saina dawo Dije muyi maganan koma meye ya fada ya fara tafiya don barin wurin binshi tayi da kallo dama tasan kota fada mai abinda ke zuciyata din ba lalai bane ya yarda da ita don kasancewar shi dan boko yaro kuma.
Hakan ya tafi ya barta da mamakin shi na rashin tsayawan shi suyi zancen da take son yi dashi din gaba daya ta kasa gane kanshi cikin kwanakin nan.
Abubuwa yakeyi kamar wani abu yana damun rayuwan shi yana boye hakan gareta dkn duk da bai da hayaniya dama sai miskilanci amma yana dan sakin jiki ya fada mata damuwan shi a baya.
Amma yanzu sam baida lokacin tsayawa yin hakan sai ya nuna ko yaushe kamar a uzurce yake a yanzu din.
Har nayi sallama da ummah na kama hanyar fita daga part din mu muryan ummah ya tsayar dani lokaci guda na juyo ina fuskantan ummah din.
Maamah kin dai san abinda mahaifinku ya fada maki don haka ki kula ki kama kanki a duk inda kikaje don kimarki itace darajan ki ki kama kanki na fada maki.
Kwalkwal nayi da idona don ina jin dacin wanan kalman a zuciya nasan kuma mahaifiyata tafini jin hakan sosai a ranta dannewa kawai takeyi kada a gane hakan.
Na iya bude bakina da kyar nace ummah zan kula in sha Allah nasa kai na fita wurin motana na nufa saida na tsaya na dan duba motan don hango scratch a jikin motan danayi tun daga nisa wanda ni bansan dashi ba a lokacin.
Ban koma ciki ba na daure na fice hakana zuciya ba dadi har lokacin ga tunanen zancen iyayyena yanzu kuma na rasa wanda ya gogar min motana.
To waye yai min haka da motar nawa don tunda akai sallah ban fito ba lafiya kalau na aje motana kuma yanzu na samu hakan a jikinta.
Na shiga school a kan lokaci don haka na fito ina dan waige waigen satan kallon inda na saba tarardashi muke haduwa saidai a fakaice nake satan kallon wurin don kada na gashi kamar yadda muka saba din.
Nayi mamakin ganin hakan har na shiga building din mu na zauna a tsarge kowa ka gani aranan yasha kwalliya a cikin tufafi masu kyau don adon sallah.
Kaina dukar saman table din dake gabana ina tuno abubuwa da dama naji an dafa min kafadana na dago da sauri ina kallon maishi Hannatu ce a tsaye take min murmushi kafin ta zagayo ta dauke jakkar dana aje a wurin.
Ta zauna take fadin wai zahra idon ki ke nan dama wallahi zahra baki da kirki ace wai ayi sallah bakijini ba kuma baki nemeni ba kinji ko lafiya nake ba.
Kaina dago ina murmushi a gajarce nace haba Hannatu ko kallona kikayi ai zaki fahinci bana cikin dadin rai a tare dani yanzu don jikina na bani cewa har karamin rama nayi.
Kallon tsab tayi min kafin tace gaskine hakan kuma to meke faruwa na kalleta ina hade bakin ciki a cikina nace sallah nan ciwo nayi saidai bai kaini kwance bane.
Lectura ne ya shigo ya katse muna hira mu kowa ya samu wuri ya natsu aka fara lecture bamu samu kan mu ba sai karfe daya muka fito don break da za aje na sallah.
Hanya na canza hannatu ta kalloni tana mamaki bata da zabi sai bina da tayi muka isa wurin sallah baya mun idar ne wayana ya dauki karan kira lokaci guda.
Ban dauka ba don ganin wanda ke kiran nawa manir ne nasan kuma zancen karatu zai min don ko na dauka ban san amsan da zan iya bashi ba lokacin don haka naki daukan wayan karshema daukan wayan nayi na sashi a silent.
Ganin hakan yasa ya kira layin hannatu ta dauka tambayanta yayi idan muna tarene tace dashi gamu cikin mosque.
Ba zaku fito muje lesson bane yau ko baku gama hutun sallah bane ku har yanzu don shi dama sarkin barkwancine ko yaushe.
Kashe wayan tayi tana kallona tare da fadin Mayana mufa ake jira akace wurin lesson kada mu bata masu lokaci.
Ba zan samu zuwa lesson ba na bata amsa kai tsaye har yanzu jikin ke damun kine ta tambayeni nace eh kije kawai zan dan kwanta a nan cikin mosque kafin ku karasa.
Bataso zuwa ba don ganin banje ba amma na nuna mata ba komai ga zuwan nata don kada mutaru duka bamu je sai ta tashi ta mike ta fita sai dai da gani tana a cikin kwankwanto a lokacin.
Fitan ta nakai kwance kasan kafet din dake malale cikin mosqu din ina lumshe idanuna zaka dauka ko barci nakeyi a lokacin.
Tan isa kafin ta karaso manir yace ina ita kuma yar mulkin ko tana tafe ne mu cigaba ?
Fuskata ta dan bata kafin tace ina ganin zahra bata da lafiya don ko a class kusan haka na sameta a kwance dana shigo let start don nasan dama ba zata zo ba ya fada cikin wani yanayi.
Ok master yana da masaniyar rashin zuwan ta ke nan baidai bashi amsa ba ya fara gaidasu da dawowa daga sallah kafin su fara darasin.
Har suka kai lokacin da muke tashi yayi masu sallama ya tafi a karshe muka koma aji aka tashi na nufi gida haka muka dinga yi har sati ya shige suka fara fahintar cewa akwai matsala a tsakanin mune.
Gashi kuma har ranan bamu hadu dashi ba kuma ban fasa satab kallon wurin ba duk na iso zanyi kokari na