Showing 60001 words to 63000 words out of 304363 words
kija kannen ki kuka taho ana fadin ku tsaya gwaggo abinda hjy ke muna dinne ba dasi wallahi laifine don muje gaida ita kuma , .
Fitowan su ummah da gwaggo daga dakin ne ya katse mu ummah na fadin baku sanarda mutum ba sai kawai muji wai ga Amarya nan zuwa gaidani ku dai baku dauki cin amana bakin komai ba wallahi suna ta cacan baki mukaji muryan Abba na sallama zasu shigo ashe shine tare da sabuwar matar nasa .
Da murna kanne suka nufi Abba suna mashi oyoyo da zuwa kamar yadda suka saba yana shafan kansu zuwa wurin kujera matar tana biye dashi a baya.
Yes farace bata kai ummah na fari ba saidai tafisu tsayi da jiki ma,ana tana da nata irin kiran itam mama wankan tarwadace ita don ita ba baka bace kuma ba fara ba.
Daga inda nake zaune na mike na nufi wurinsu na dan rage tsawo ina fadin sannu da zuwa Abbah a a mamana kece nan yau ba school ke nan ya tambayeni yana riko hannuna.
Na dan juya wurin matar dake bina da kallo nace sannu da zuwa tace yauwa sannu ko idonta tar a kaina daga cikin glass din idon ta tana karemun kallo.
Hannuna rike dana Abba din ya nufi kujera ya zauna ni kuma na zauna a makarin kujeran sai kuma na daga ina fadin ga wuri ina nuna mata dayan kujeran dake kusa da wanda Abba din ya zauna.
Tace na gode takai zaune tana gyara lafayan jikinta data lalaye saman wani rantsatsen lace dake jikinta daga can inda ummah take zaune take fadin sannuku da zuwa.
Yauwa Abbah ya fada ya juya wurin sabuwar matarshi yana fadin hjy karima ga salma nan uwargidana itace matana ta farko ga yaranta nan kuma kina ganisu.
Iya makirci sai ta dan zamo daga yadda take zaune da farko tana fadin mun sameku lafiya ummah ta amsa daga can da fadin Alhamdullahi ya hanya ya akabar mutanen gida kuma ?
Lafiya kalau ta fada tana dan murza hannun ta tare da fadin akwai nisa kan nan da Abuja gaskiya na dauka tafiyan ai ba wani mai nisa bane sosai yadda yake fadi.
Da akwai nisa sosai gaskiya aiku isa ku huta sai a kawo maku abinci daga can gwaggo shafa ke fadin ai akwai abinci da aka kawo daga gidan hjy ma.
Au to ai shike nan har ina zancen a shirya wani a nan din akai masu tunda mungama tun dazun Abba ya juyo yana fadin daga gida hjy kuma nan din ba akwai abinci ba tace sunyi wai dama don zuwan kune ai aka hada din acan tunda su nan basu sanda zuwan kuba.
Ba,a fada masu cewa yau zamu zo ba nika ina jin haka na mike tsam na bar falon bansan ya suka karasa ba a wajen don ban sake fitowa ba sai da dare da zanci abincin dare din na fito.
Amadi azzumin nan duk da ya samemu a cikin walwala in sha Allahu amma sai naga kamar bamu fara mai tanadi da wuri ba don gaskiya irin gab da azumin nan komai kara kudi yakeyi farashi na hau hawa sosai na kayan masarufi.
Kukan uwargarke ya dakatar da Dije ga fadin abin da tayi niya fada lokacin me kuma uwar garke kewa kuka yanzu kuma , ?
Allah ya gani kukan uwar garke a yanzu tsoro yake ban don yanzun haka wani alaman take nufi da hakan....
ZAINAB IDRIS MAKAWA
HAYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃👠👜💍👡👛 🥿👘👗🧤
INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION.
ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M A C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝
TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI.
YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
1️⃣9️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Fitowana ke nan daga dakina zuwa falo muryan ummace ke fadin ki dauki kayan abincin nan ki kaiwa su Abban ku a falon shi daga nan ki tambayeshi idan suna bukatan wani abin ki kai masi.
Ja nayi na tsaya a wuri daya ina kallon ummah din dake magana dani lokacin kafin nace da ita ummah wani abincin kuka girka masu a nan kuma ?
Ina su gwaggo sunce an girka masu a gidan hjy ai to Abbah ku yace kada a kawo a nan zamu girka ai kinga ni yaune kawai zan basu abinci daga gobe hjy maimunace zata basu har su bar garin nan don dole nasan dai ya koma zuwa Monday ai.
Badon naso ba na dauki abincin dake a shirye nida Tani muka nufi part din Abba din Tani ta tsaya daga kofa nice na fara shiga da kayan abincin ciki da sallama a bakina.
Suna zaune saman kujera daya zaune a hade jin sallamana yasa Abba ya dan gyara ga yadda suke zaune din na nufi wajen dinning dinshi yace kawo muna nan zaifi.
Na juyo nazo gabansu a kasa na aje saida na aje abinci kafin na dago ina gaida Abba da ina wuni Abba mama kuna lafiya ina ita umman nakune nace tana side dinta na juya wurin matar data kafeni da idanu nace mommy ina wuni ?
Lafiya kalau yan mata wanan mamatace itace na sakawa sunan hjyn mu Abba ya fada na mike nafito na karbi na hannun Tani ta juya ta koma ita.
Na kai gabansu na aje ina jin Abba na mata bayani take fadin wanan na ganta dazun a part dinsu su wa yancan ne ban samu ganin su ba.
A nan na gane sunki yarda data gansu ke nan son nasan suna gidan dai weekend bamu fita zuwa ko ina ki turo min umman taku Abba ya fada.
Na koma na isarwa Ummah da sakon Abba na dibi abinci na koma saman doguwar kujera na zauna na fara ci ina kallo ummah tace kina da dabi,an son zama a nan kici abinci ga wurin cin abinci can ki bari.
Hakan baisa na daga ba naci gaba da kallon da nakeyi din tare da kannena naji ummah tace min dazun da kukaje gidan hjy abinda takewa ke nan ashe ta nuna maku jan ido ga zuwan ku.
Bansan meya yasa hjy take wanan halin ba haka ko kudin da ku nazo daga gidan mu oho barta kawai na iya fada ai dole tunda tasan gaskiya take takewa duk abinda mutum yayi don kansa ai.
Can naga ummah tamike ta fita ni dai har muka gama kallon mu muka shige ban fito wajen ba ban kuma san lokacin data dawo part din ba don na kai kannena daki na rufo kofan daga ciki data shigone ta rufe kofan.
Washegari misalin tara na safe wayana ya dauki kara ina kwance lokacin ban tashi daga barcin safen da nakeyi ba na lalubo wayan na kara a kunnena bayan na dauka.
Muryan Ahmed naji yana min sallama na karba mai muka gaisa yake fadin badai baki tashi ba har yanzun daga barci ba zarah ?
Murmushi nayi ina fadin yanzu dai aikatashe ni brother yace manya ke nan har wana lokacin mutum yana kwance yana barci ?
Nayi murmushi yake fadin zahar don Allah idan ba damuwa zanzo gidan kune na karbi kudin nan dake hannun ki zamu shiga kauye ne mu sayo wake da gero don azumi daya kawo jiki.
Nayi shawara na sayo su da kudin tunda lokacin sayan su ke nan yanzu nabi wanan riban da zan samu OK na fada kudin suna nan yadda ka bani su ban taba ba ai.
Na sani yace min nazo ba matsala na karba kazo mana idan kazo saika kirani nafito na fada yayi min godiya ya kashe wayanshi a lokacin nima na mike na daga gado inda na boyesu sunan yadda na barsu na dauko tare da bude wardrobe din na na ciro wani envelop na ciro kudi a ciki na hada dasu na mayar da sauran a ciki.
Bandaki na shiga na kewaya na fito na daura gyale akaina lokacin wayana ya dauki kara wata kila dama yana kusa da unguwar tamuce dama.
Na dauka ina fadin gani fitowa ina daga wajen get ya fada nace ka shigo kawai ciki zan fito yadda nake dagani sai dogon riga da gyalen dana daura a kaina na fito.
Na hangoshi a cikin shiga irin na kauyawa da suke shiga daji da wani hula aja akanshi saidai yana hangoni ya fara cire hulan a kanshi ya nufoni fuskanshi dauke da dan murmushi.
Muka hade muka kara gausawa na mika mai kudin zakace wani takardane yadda ledan suke don yadda na shiryasu a ciki.
A daidai lokacin su Aisha tare da Rukkaiya suka fito daga cikin gidan namu ko su san sunga mutane a wurin basu nuna muna hakan ba.
Daga inda muke yake fadin ina kwanan ku Rukkaiya ta wani kalloshi tasa kai ta wuce mu yace toh ga manya gaisuwan ma sai angadama ake karbawa a gidan ku.
Murmushi nayi nace yanzun kauyen zaka ke nan yace dana bar nan mota nacan mun fara taruwa sai mu daga Allah ya tsare na fada naji karan bude kofan fitowa again.
Mamace ta fito naji gabana ya fadi ras na juya ina gaida ita tayi dan jim kafin ta amsa tana wucewa zuwa wurin motar dasu Aisha suke shiga ko ta shiga baya sukaja suka fice a daidai fitan su naga duk sun kallo mu suna magana.
Yai min sallama shima ya tafi na juya na koma ciki a falo na samu ummah tsaye suna hada abin karyawa ita da Tani nasan sun makara ko kuma aiki yayi masu yawa lokacin.
Ummah ta juyo tana fadin yaushe kika fita daga nan nace yanzu wani ne yazo amsan takarda a wurina nakai mashi .
Amma kinsan Abban ku yana gari kika fita haka ko ai yanzun na fita na bata amsa kizo ki kai kayan nan falo nasan kila sun tashi suna jira yanzu.
Nace to na fara daukan kayan zuwa falon Abban mu nayi sa,a babu kowa a falon har na gama jerawa na juya zan fito naji an bude kofan matar ce ta fito na juya ina gaida ita tace.
Aa kece ashe ina jin mitsine ina ciki na leko nace eh da kara fadin ina kwana ta amsa min cikin murmushi tare da fadin sannu da kokari ki gaida ummah taki kafin na shigo gaida su.
Wanka na fito duk da ina jin zuciyana a wani irin don ba dadi ko farin ciki a zuciyana mai na zauna ina shafawa naji wayata ta dauki ringing na duba Ahmad din ne ya kirani na dauka.
Yayi sallama na amsa ya fara fadin nazo na bude kudin naga sunfi wanda na baki a jiya yawa eh na sani nima bansan me zanyi dasu ba na baka ka kara don naga kana bukata .
Amma zarah hakan zai iya hadani dake don kudi ba ayi mai haka Allah dai ya bada sa,a na fada yace amin yanzu kim aramin dai na kara ke nan nace eh aro din na baka.
Amma kuma ban faye son kudin wani a cikin sana,ata ba abin dan uwa aibana aani bane na bashi amsan na kashe wayata naci gaba da shirina rana shigar atampa nayi dinkin riga da buje.
Har na kwanta na mike na nufo waje kitchen na wuce na dauko goran ruwa na fito ido muka hada da amaryan Abba dake zaune a falon ummah tana fitowa daga bedroom din ta.
Matar yar kwalisace sosai don shigarta kawai zai nuna hakan kamar na shareta saidao na daure na sake gaida ita ta amsa itama a cikin fara,a tare da fadin hjy ki bani yar nan taki mu zauna tare da ita Abuja .
Ayi hakan tana karatu a nan ai Dear ya fada min ai a can kuke kuka dawo nan yanzu wallahi ummh ta fada mun dawo gida saboda yara su saba da yan uwa da al,adun mu na nan din ta fada kamar yadda Abba da mama suka tsarata a lokacin.
Abinda ummah ba ta sani bashi don mama dake son dawowa gida da yaranta a lokacin yasa muma tasa aka dawo damu kusa da ita don kada mu zauna birni suna gida su.
Don dama Abujan tace zata dawo Abban yace bai yarda da hakan ba shine tayi makarkashiya wurin hjy inno kakarmu Abba yasa kowa dawowa gida.
Murmushi matar tayi kafin tace nayi mamaki keda kike da yara kanana haka kika yarda kika dawo nan ba tare da yaranki sun samu wadatattacen ilimi ba kamar yadda yan uwansu suka samu a can su.
Nan ma ai sunayi ba laifi bawa duk baya wuce kadaranshi ai in Allah ya nufa zasu zama wani abu a rayuwa zasu zama din aiko mahaifinsu a nan din yai karatu har ya zama wani abu yau a rayuwan shi.
Hakane Allah ya raya munasu ummah ta amsa da amin sai sukai shiru gaba dayan su don matar ta kula da ummah bata da yawan surutu yasa taja bakinta itama tayi shiru .
Waya Abba ya bugo mata zata gaisa da wasu abokan shi yasa ta mike zuwa falon na Abba tavarwa ummah part dinta duk ina dakina ban fito ba yinin ranan.
Mama ko tana can a family house din suna kwasa dasu gwaggo don takai karan gun hjy saita samu da sanin tsohuwar da aka toshe wa baki da abin arziki akai auren ashe.
Wana yasa suka hargirse a wurin ta fara fadan bakaken maganganu garesu suma suka shiga ramawa tafito hasale ta juyo zuwa gida.
Dije ce ta leko daga daki sukai arba da akuyanta datayiwa suna da uwargarke da yau uwargarken ta juye ta komawa dije wani abu na daban da Dije ta kasa fassarawa lokacin.
Yauma tun fitan Amadi gidan suke takon saka a tsakanin su dalili kuwa shine ruwan kasarin da ya kwana Dije ta gyara masu don Amadi yau sakkon fita yayi bai samu tsayawa yadda ya saba gyara masu ba.
Ita kuma ganin ai ruwan baiyi komai ba yasa ta gyara masu shi ta aje tana kokarin juyawa ta bar wurin taji kamar an bangajeta ra dauka wani a bayanta mai karfi yayi mata wanan bangazan .
Allah ya gyara bata kai kasa ba ta juyo taga uwargarke a tsaya tana ture ruwan cikin jarkan da kai hakan bai mata ba tasa kafa kamar mutum ta ture ruwan ya zube a wurin.
Da sauri Dije taja baya a firgice don sai taga kamar ba akuya bace mutum ne ai gabanta don yadda uwar garken ta nuna hasala a fil sai hakan ya ba Dije tsoro ya koma dakinta ta shige sai lekowa takeyi daga cikin dakin tun safe ta kasa fitowa ta dan rage aiyukanta na gida kamar yadda tasaba yi.
Gashi kamar hadin baki yau ba wanda yayi sallama a gidan ita kadaoce a cikin gidan sai dabbobin ta dake kiwonsu inka debe uwar garke dake tsaye tun lokacin bata kwanta ba ta kurawa kofan dakin Dije din ido babu kiftawa.
A daidai lokacin da Dije din ke lekawan ne a yanzu uwargarke din ke kwantawa a makwancinta komawa Dije din tayi baya ta dafe kirjinta tana sauke ajiyan zuciya.
Sai kuma raji shigowan mutum gidan yana sallama da mamaki a fuskanshi yake bin gidan da kallon ganin a yadda ya fita yabar gidan haka ya dawo ya samu gida kamar tun safe Dijen bata leko wajen ba.
Dijeh ya fada da karfi kuma a razane yana sauri zuwa kofan dakinta sai gata ta leko a tsorace don ta sheda shi din ta gani ko wani sukai arba da juna a hakan.
Amadi kaine ashe ta fada kamar a tsorace tana kokarin yunkurawa ta mike tsaye lokacin yace wai lafiya kike kuwa Dije ? Tace balau ba kan , kadai huta a san nayi a gidan don ga baki daya duk a firgice nake yau