Showing 84001 words to 87000 words out of 304363 words
juya na kalla ko yana wurin saidai ban ganin kowa.
Sati biyu muna hakan har kowa ya gama fahintar komai ranan monday bayan mun fito daga daukan karatune hannatu ta tutsiyeni da tambayan dalilin rashin zuwana group discussion a yan kwanakin nan ?
Ba komai kawai na daina hakan ne don nima na koyi fahinta daga malami da kaina wani irin kallo tayi min ta sake murmushi tare da fadin.
Zahra kenan kina ganin a dan zaman mu tare a school din nan ba zan iya fahintar halinda kike ciki ba ke bake bafa har su manir da sauran su ina iya fahintar yanayin su suma maza.
Nasha zaki fada min don muga ko za a iya walwale matsalan a cikin sauki duk da daga ke har master din kuna kokarin boye muna cewa babu komai a tsakanin ku.
Umhumm hannatu ki bari kawai wanan zancen ya wuce nake gani don ina kokarin mantawa da komai kan wanan zancen.
Zahra kina ganin cewa ku bata tsakanin ki da master shine mafita a gareki ko me kifa sani irin su master tsada sukeyi yanzu a cikin maza.
Ko kin san yawan yan matan school din nan da suke son kasancewa dashi amma yaki bada daman hakan, ni wallahi dama ganin yanayin sa idan badon naga gidansu ba sai nace shi din dan gidan wasu manyan mutane ne sosai a garin nan.
To amma kuma nasan shi har irin sana,anshi sai hakan ya fara sani a kwankwanto a kanshi kuma yanzu dai ba wanan nan bama zahra meya kawo matsala a tsakanin ku ?
Kamar bansan tana magana ba don hankalina na mayar a wayana ina duba ban dago kai gareta ba naji tace to shike nan yanzun na fahinci irin zaman da mukeyi da juna dake duk da kece kika daukeni hakan.
Don ni tsakanina da Allah nake zaman arziki dake ba don wani abuba can zarah amma naga ke ba haka kika daukeni ba ke har yanzu.
Nan nake kawo maki korafin yayata dake tasheni ki bani shawara in kuma je inyi amfani da shawaran naki yai min amfani a karshe.
Kaina dago na kalleta a cikin yanayin tausayin kaina nace hannatu ba hakana bane matsala aka samu an fadawa Abbana cewa wai soyayya muke da Ahmed shine Abbana yai min iyakan tsayawa dashi.
Abba fa har wanan zancen yakai kunnen Abban ku kai mutane basu da kyau yanzu shiyasa wasu ke fadin anbar kiwon dabbobi a yanzu an koma kiwon mutane.
Ba wanan ba hannatu Abba har Ahmed din ya kira yai mashi iyaka dani ya kumaci zarafin shi a kaina da wani ido zan kalli Ahmed a yanzu kike gani.
Ke kanki Hannatu kinsa Ahmed kadai ke min bayani na fahinci abinda darasi ya kumsa na gane yanzun kuma Abba yaci mashi mutunci kan haka, har yana fadin cewa Ahmed baida asali .
What ta fada da dan karfi tana kallona kafin tace min kuma shi Ahmed din yasan da wanan zancen bansan koya fada mashi ba daya kirashi din.
Zahra ki bar wanan zancen don Allah mu bari sai mun samu lokaci mu zauna asan yadda za a bullowa lamarin sai dai ban zaton ya fadi hakan a gaban shi Ahmed din ai.
Nima shine tsorona don nasan halin Abba zai iya fadin komai ko a gabanshi idan ranshi ya baci tunda acewa Abban soyayya mukeyi nida Ahmed din ba karatu ba.
Amma ke baki ganin rashin kyautawan ki ga hakan aisai ya zata kema hakan da Abban yai mashi bai dameki bane kamata yayi mu sameshi mu bashi hakkuri .
Kinga a nan zamuji shin Abba ya fada mashi maganganu marasa dadin kamar yadda ya fada maki ni gaskiya kamar hanyar daya dace ke nan mubi nake gani.
Hannutu kunyanshi gaba daya nake ji a yanzu bazan boye maki ba kan wanan maganan wallahi nasa cewa ba karamin shakuwa ashe mukayi dashi ba.
Don tun wanan ranan wallahi Hannatu na nemi farincikina na rashi a tare dani kullun jin kaina a cikin kinci nake kuma Abba har zai tafi ya kara jadda min cewa duk aka fada mai cewa angani tare dashi zai dauki mumunan mataki a kaina ranan .
Wanan yasa nake matukar tsoron fita har mu hadu din dashi wani dan gulma yaje kuma ya fadawa Abba kinsan Abba ba zai raga min ba idan har yaji hakan.
Gaskiyane ki dai bari gobe idan nayi tunane kan yadds zamu bullowa zancen sai mu san abin yi don gaskiya ban baki shawaran barin wanan guy din ba zahra.
Murmushi nayi tare da fadin wai meyasa mutane ke yawan dauka muna soyayya da Ahmed ne, mutuncine fa kawai a tsakanin mu kema kin sani.
. Nikan ban yarda da wanan maganan ba ga kowan ku donko makaho ya laluba yasan gaskiya kedai kawai mubar zancen sai gobe in sha Allahu.
Ina hanya komawa gida wayana yayi ringing na mika hannu na dauka daga gefena ya musa ne a layin da murnana na dauki wayan ina gaidashi.
Zahran mama ke nan ya fada na lumshe idona don tunawa da wanan sunan da suke kirana dashi shida ya jafar yace yanzu kin zama busy ko neman mutane bakyayi ki gaidasu.
No wallahi yaya ba hakana bane yace to ya ne Allah karatune yanzu yai min yawa sam banda lokacin kaina ga komai yanzu.
Saina soyayya da yan uwanki dalibai ko Zahra Abba ya kawo min karanki yace kin fara soyayya da wani karamin yaro dan karamin gida a school din ku.
Wallahi ya ba hakana bane na fada ina samun wuri na parker motar na kwashe komai daya faru na fada mashi har mutuncin dake tsakanina da Ahmed din da dan sabon da nayi dashi fiye da kowa a school din.
Bayan ya gama saurarena yace min kin gane zahra ki janye duk wani alaka tsakanin ki da kowa yanzu kiyi facing din studies din ki kamar yadda Abba yake son kiyi.
Shawara sosai ya bani kafin mu kashe waya bayan munyi sallama na tayar da motar na karasa gida ina tunane don ni abubuwan ma sun min yawa a yanzu nake gani.
Ranan banyi barcin kirki ba ina faman tunanen maganganun ya musa dana hannatu a raina sai kullawa nake ina walwalewa ni kadai a dakin nawa .
Washegari na tashi sukuku dani nagama shirin da zanyi na fice a gidan tunda safe na samu malamin yazo bai shiga ajin ba don haka kusan tare dashi muka shiga.
Sai bayan gama lectures din ne hannatu taso muyi maganan jiya din sai ya kasance kaina yana dan sara min muna fita maimakon mu wuce zuwa mosque sai cewa nayi da hannatun kaina ke min ciwo zanje gida insha magani in kwanta.
Kallon mamaki take min din muna da lecte karfe biyu da rabi ganin da gaske nake yasa ta kyaleni in tafi din na nufi wurin motana nadan duka ina bude motan naji muryan shi abayana yana fadin
🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
2️⃣7️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Zahra lafiya kike kuwa meke damun kine yau zaki bar school da wuri haka don naga kin fito daga aji ana karatu zaki gida ?
Wani irin faduwan gaba naji ya ziyarceni lokaci guda ga kunya kuma haka yasa na dan dauki lokaci ban iya juyowa na fuskance shi ba lokaci guda.
Kafin na tattaro karfin halina na juyo tare da fadin ina wuni bana jin dadine yasa zanje gida yanzu nasha magani indan kwanta nagode sai anjima na fada da sauri na fada motana ina kokarin tayar da motan.
Hannuna dake rawa na kasa saka key din motar da kyau yasa shi matsowa zuwa window motan yana fadin kina ko cikin hankalin ki zaki iya tukin motan a haka.
Murmushin dole na zakulo a fuskana kamar makaryaciya nace meka gani zan iya mana a daidai lokacin motan ta tashi ban kalli inda yake ba sai horn nayi mai na barshi wurin yana bina da kallo har na bace mashi.
Ajiyan zuciya ya sauke ya juya a hankali ya koma wurin da yafi yawan zama wasu lokuta inda a nan ne kuma muke haduwa muyi karatun dashi.
Bai dade da zama wurin ba su munir suka sameshi gaisawa sukayi dashi manir ke fadin yau master da kanka karigamu isowa ajin ?
Dan murmushin gefen fuska ya sake ba tare da yai magana ba don inda sabo a yanzu sun saba da hakan nasa na rashin magana wanda kuma a hakan har muka shaku da juna dashi kowan mu ba mai son yawan magana ba cikin mu.
Sunyi karatun su na dan lokaci duk da sun gane karatun nasu yanzu akwai sauyi a cikinshi sosai don bai yawan nacewa wurin maimaita masu.
Bayan sun gama an fara watsewane a wurin tana batun wucewa ya hada kayanshi hannatu ce taki tashi tana zaune ya dago ya kalleta yana fadin .
Hannatu lafiya dai ko yana kallonta ta dan gyara zama tana kalllon shi tace Master magana nake son yi dakai akan zahra.
Zahra ya ambaci sunan a cikin mamaki kafin ya dan kada kai yana sauke murmushi tare da fadin wani abu ya farune sai hannatun tace a,a master.
Kasan dai zahra bata da sata abokiyar data fini school din nan kaf don haka ta fada min duk abinda ya faru a sallah break din nan da Daddysu yazo.
Muyi magana ta fahinta na bata shawara a jiya akan zamu ganka yau mu baka hakkuri kan hakan sai gashi yau din ta tashi bata da lafiya don haka ta tafi gida tun dazun.
Eh na ganta da zata tafi din nake tambayan ta ko lafiya zata koma gida wanan lokacin take fada min bata jin dadin jikintane.
Ok ka ganta ke nan nasan duk akan matsalan takune bata jin dadin jikinta amma master sai nake ganin kamar zakuyiwa kanku sakacin da zai dameku a baya.
Akan me fa ya tambaya yana kallonta a cikin mamaki murmushi ta sauke a fuskanta tace haba master na dauka ai in kun boyewa kowa hakan ni ba zaku boye min ba don nasan abinda ke tsakanin ku yanzu dai.
Meke tsakanin mu din banda abinda ke tsakanina dake shine karatu nan da mukeyi sun kuma ce ta daina yanzu shike nan kowa ya tsaya a matsayin shi ai.
Nasan ni din ba ajinta bane don bankai matsayin tsayawa da yarinya irin zahra ba kema kin sani abinda kowa ya sani ne kuma don haka kada yanzu kema ki shiga cikin masu ma alakata da zahra din wani fassara na daban.
Murmushi Hannatun ta sauke mekama da yake a fuskanta tace nawa akayi muka gani a garin nan matsala dai ko wani mahaifi da nasa kalan fahintane .
Shi mahaifin zahra a nawa fahintar an kai masa zancen nakune ta baibai yasa ya hau haka ba tare da bincike ba a kai har ya yanke hukunci irin hakan a tsakanin ku.
Hannatu na kula kina son jan zancen da nisa yanzu bayan an rigada an wuce wanan wurin ko nake gani yace na bar ko wani irin halaka da yarshi na kuma bari.
Itama din ta bar hakan ba sai kowa ya tsaya matsayin shi ba yanzu kuma ke kanki kinsan hakan ban kai matsayin da zan zauna da zahra ba gaskiya kema kin sanda hakan.
Ita zahran ai bata dauki haka ba idan ka duba irin rayuwan ta na saukin kai a cikin mu sam bata nuna cewa mu din ba ajinta bane take tare damu.
Ai akwai diyan attajirai irin ta masu jan aji cikin makarantan nan wasu ma basu ko kai matsayi irin nata ba amma suna ji da kansu cewa su din diyan wasu kusan garine su.
Ni a ganina gaskiya ya kamata ku tsaya ku fahinci juna kai da Zahra tunda kuna son junan ku a yanzu kowa kuma yasan da hakan gareku.
Haba hannutu ban zaci wannan zancen zaki zo min dashi ba a yanzu don da ban tsaya sauraren ki ba gaskiya mutumin nan yai min iyaka da yarshi fa tare da kakausan murya kan hakan.
Itama yar nasa da alaman tabi umurnin mahaifin don haka kibar wanan zancen don Allah ta tafi hakana don gujewa matsala nan gaba kan hakan.
Abu daya nasani shine idan naganta a cikin matsala zan iya taimaka mata final yana fadin hakan ya fara tafiya da niyar barin ta surin zaune yaji muryan ta na fadin.
Saika shirya karban mumunan labari game da zahra don kuna kiris da jin abinda bashi ba a kanta nan da yan kwanaki kada don hakan yanawa rayuwan zahra barazana a yanzu.
Juyowa yayi da sauri yana kallon ta kafin ya bude baki yace me hakan ke nufi ke nan tace abinda idon ka ya gano maka dazun game da ita.
Ban fahince ki ba hannatu kaje kayi tunane a kai ta bashi amsa ta mike ta bar wurin da sauri ya bita da kallon mamaki kafin shima yasamu ya daga kafanshi ya bar wurin cikin damuwa.
Tunda na dawo na fadawa ummah banda lafiya ta ban magani tare da zaton ko ciwon kainane yake son tashi min har hayaki da shakawa duk saida ummah ta tsareni nayi.
Kafin na shige dakina nayi sallah na kwanta sai barci mai nauyi ya daukeni ban falka ba sai karfe shidda da rabi da kyar na iya mikewa na shige ban daki na dauro alwala na fito.
Ban daga ba saida nayi magariba da isha,i lokacin har ummah ta leko ta gani kona tashi daga barcin da nakeyi saita samu ina sallah.
Abinci na fito naci tare da kannena na koma daki don jikina da ya danyi min nauyi a ranan wanka nayi nashirya kwanciya tareda karanto adduan kwanciya nakai kwance.
Kamar ana jiran in kwanta a lokacin wayana ya danyi tsuwa alaman kira ya shigo saidai flashing ne kiran nayi mamakin hakan amma sai na zaci hannatu ce ke min hakan don itace me dabi,an flashing a kira.
Bandaga inga mai mun kiran ba lokacin naci gaba da abinda nakeyi nakashe bedside lamp dina na lumshe idona a hankali.
Amadi dake tsaye a kofan gidan su wanda dawowan shi ke nan unguwan tasu wuri ujulanshi ya sake danna ma lambana kira karo na biyu gaban shi na faduwa sosai lokacin.
Saidai kwarin gwiwan shine zancen su da hannatu don ya karkare wunin ranan da wanan zancen arashin da hannatu tace idan baison ya rasani yai wani abu don ina gab da salwanta rayuwana.
Gashi basu samu tsayawa da ita yaji ma,anan fadin hakan ba tayi tafiyanta ta barshi da tunane a zuciyar shi wanan ya sakashi a cikin damuwa sosai a ranan .
Don haka yaga dacewan ya kirani yaji meke faruwa saidaya danna kiran farkone yaga mezaice dani din bayan warning din da mahaifina yayi mai a kaina cikin kakausan murya da cin zarafi.
Har ya juya zai shiga gidane wata zuciya tace dashi ya sake kirana ko zan dauka din zuciyan shi na bashi cewa anyi min kakausan warning a kanshi don yadda yagani a idona lokacin.
Don hakane ya daure ya danna kira a wayan nawa yagani ko zan dauka in sauraren shi sai yaji kiran ya shiga saidai wayan yana ringing ban daga ba ga zuciyar shi sai bal bal yakeyi yana tsaye a cikin duhun unguwan shi kadai.
Salamu Alaikum yaji daga bangarena cikin muryana mai sanyi ina mashi sallama hakan yasa ya gane banyi blocking din layin shi ba ashe kamar yadda ya zata.
Ya amsa da wa,alaikis salam zahra ya jikin naki da sauki ko ya fada don bai san me zaice dani ba a lokacin sai yaji nace.
Ohh master ne naji sauki wallahi nagode ya kake ya kaka a gaida ita kaka tana lafiya zataji ya fada a bangaren shi .
Sai kuma mukai shiru na dan lokaci shi baiyi magana ba ni kuma ban kashe wayan tasa ba lokacin lokacin ina sauraren shi don ina gudun kashewa ya dauka wullakancine hakan .
Saboda wanda ya kula da kai har yakira yaji lafiyan ka ya gama maka komai a rayuwa ai don hakane na jira naji har ya kashe ko kuma yana da abin fada min lokacin.
Zahra!!! Duk da mahaifin ki yai min iyaka dake yace ni din da sana,ata da komai bankai matsayin koda sabulun wankanki banyi darajan shi ba balle nace zanyi soyayya dake a rayuwana ba.
Duk da naso fadawa Alh cewa ni din ba wai soayya nake yi dake ba a lokacin zaman amana da mutunci mukeyi saidai daddy bai bani daman yin hakan ba gareshi.
Yace ni din banda asali da arziki da zance zanyi mu,amula dake don matsayina baikai ga hakan ba saboda haka in rabu mashi da yarshi ko kuma yasa a wullakantani da kowa nawa a garin nan.
Ido na runtse ina