Showing 258001 words to 261000 words out of 304363 words

Chapter 87 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33341

kallo titi saidai a can kasan zuciyarshi yana tunanen me yasa mahaifin nasa ya gigice game da zancen wanan hardo din Dala.
Sama sama yaci abincin kafin ya mike da zuman su tafi koshi don mahaifiyar Nabil dince data matsa akan sai yaci abinci zai tafi Nabil din yace bari a kira momi kuyi sallama.
Duk yana ganin nawan da Nabil din ke masa don yasha alwashin bai kara kwana a garin duk da karfe hudu har ya buga gashi biyar akace mota yana tashi zuwa zamfara na yamma.
Shigowan mahaifin Nabil dine da sauri ya dakatar dasu yace badai tafiya zakayi ba Ahmed yace baba na gama cika komai yanzu nake son in tafi nagode da irin dawainiyar da kukai mani.
Dakata Ahmed ina yabon kirki da hali irin na dattako da kake dashi kuma zaka bata rawanka da tsale yanzu gaba daya suka kalloshi cikin mamakin jin abinda ya fada daga shi Ahmed din har Nabil da mahaifiyanshi dake tsaye daga kofan fitowa.
Yace kwarai ina kunyi da mahaifin ka ya baka umurnin cewa ba zaka tafi ba yau din nan yanzu ina office aka kirani da bakon lamba na dauka ashe mahaifinkane ya kirani.
Duk da bai fada min komai ba amma ya rokeni da kada in barka ka tafi hakan yasa na dawo yanzu a gagauce don in cika masa alkawarin dana dauka kan hakan kayi hakkuri don Allah badon ni ba ka tsaya ka saurari mahaifin naka.
A hankali ya dago kai yace ba komai daddy zan tsaya zuwa goben insha Allahu ya fada nan daddy din ya shiga saka mashi albarka ashe abinda basu sani ba Abban nasu yasaka anbiyoshi anga gidan da sunan maigidan har nombanshi shine ya kirashi.
Dakin Nabil din ya koma ya aje kayanshi ya ciro wayanshi ya bugo min ina tsaka da gyaran kitchen din in dora girki tunda zai dawo ranan komai dare yace saiga kiran wayanshi ya shigo.
Na san shine saboda ringing din dana sakawa sunan na Assalamu alaikum ya bahbah dake tashe a lokacin na dauka da sallama ina fadin zaka taso ke nan ko ?
Yace wallahi na fasa saidai in Allah ya dawo dani lafiya zakiji ko menene ki fadawa Dije don kada ta damu kanta da leken kofa bazan dawo ba yau nace Allah ya kaimu a sanyayye.
Allah ya tsare hanya amma baka samu zuwa gidan Abba din ba da cewa Abban mu yace wani Abban wai nace Abban mu mana mahaifina yace Zahra kinsan na fada maki gaskiya ba zan iya zuwa ba ina jin nauyin hakan wallahi amma tunda ina shigowa yanzu watarana zanje ai insha Allahu.
Amma kasan yasan da zancen zuwanka ai koya sani zahra nayi mai alkawarin zuwa wurin shine ya tambayeni ina jin hakan nasan ranshi a bace yake nace Allah ya kaimu gobe lafiya na kashe wayana.
Girkin da banyi ba ke nan na koma daki na kwanta ina charting hakan ya dauke min hankalina ga komai saidai banji dadin rashin zuwa gidan Abban mu din da baiyi ba gaskiya ko banza zai duba muna jikin nasa ai a nawa tunanen.
Karfe biyar daidai Nabil ya sameshi a dakin yace ana masa sallama a waje haka ya taso ya fito yadda yake inda ya samu mahaifin Nabil ya fito masu da fararen kujeru a haraban gidan.
Ya iso yana masu sallama suka amsa nan Dady nabil din ya shiga yabon kirkinshi yana fadawa mahaifin nasa shiko sai murmushin yake yake masa.
Ya mike ya barsu a wajen nan ya kara gaisawa da mahaifin nasa da yanzun yanayinsa ya canza sosai ba kamar dazun da rana daya sameshi a massalacin ba.
Dan shirune ya biyo baya kafin yaji muryan mahaifin nasa yana fadin nagode daka yarda ka tsaya don ni na dauka ba zakai min wanan alfarman dana nema ba ai.
Sai alokacin yaji kunyar kansa yadda mahaifin nasa yake masa godiya akan abinda shi yakamata ace yayi mai a lokacin watau biyayya a gareshi ke nan aa zuciya ya kasa hanashi ya tsaya yai masa hakan.
Watau a game da zancen Dala kuma da kaimun gaskiya har yanzu zuciyana ta kasa gaskanta hakan don wanan bawan Allah akalla zaikai shekara arbain zuwa hamsin yanzu rabonshi damu.
Dukiyar mahaifitace a wurin shi masu yawa daya gudu dasu tun lokacin kuma ba a kara jin duriyanshi ba sai yau din nan da kazo min da labarinsa da bakinka.
Da ace wanine ya fada min da zan karyatashi don ba inda hardo mai sunanka baisa anyi mai cigiyarsa ba har kira anyi mai na asiri akan ya dawo amma hakan ya gagara.
Ba zai dawo ba Abba don kun kirashi don shima hatsabibin kansane sosai a kewayen kaf yana da girma da kima a idon mutane bai dogara da kiwo ba a yanzu da aikin gona ya dagora nake gani.
Don amfanin gonan da nake sayowa na sayar ya kaini wanan kasan arnakun har na hadu dashi saidai yaba kowa mamaki yadda yai min a wurin donshi ya nuna yasan ni yasan kuma koni waye.
Nan dai ya fada mashi komai daya faru dasu a garin har zuwa maganin daya bashi bayan ya gaiyace shi gidanshi din duk ya sanarwa mahaifin nasa.
Kafin dattijun mahaifin nasa ya danyi murmushi yace dama shi masanine don suna da gadon hakan amma sunan magajiya daya fada shine ya daure min kai a yanzu.
Shin kasan ko wacece wanan magajiyan da yake nufi sai Ahmed din ya girgiza kansa alaman a, a koda yake zaka sani nan gaba idan ka kawo kanka gidan amma koda kazo din kayi hankali da kowansu don zasu nunama a fuska sunfi kowa kaunan ka a cikin zurian mu saidai abin ba haka yake ba a zuciyarsu.
Sun danyi magana ta fahinta kafin suyi sallama mahaifin nasa yayi mamaki lokacin daya taya mai mota da zaisa a kaishi gida amma bai nasa mussun hakan ba kamar yadda yai tsamani zaiki hakan.
Shima ya rasa dalilin hakan din don haka kawai yaji tun lokacin zuciyarshi ta karaya akan mahaifin nasa tsusayinsa ya koma ji maimakin tsanar dayake ji nasa a baya wanan zaman ya kawo sauyawan komai a rayuwan su kuma.
Washegari da wuri ya karya don sammakon da zaiyi sai kuma yawan godiyan da mahaifin nabil da mahaifiyan shi suke masa yayi yawa don shi ya kamata ace ya gode masu kan dawainiyar da sukai masa na zama a gidansu sai gasu suke faman gode mai.
Mota har gida malam Bala driver mahaifinshi ya kawo shi tunda suka dauki hanya labarin hjy yabi da yaranta yake ba Ahmed din da zaman hjy murja yanzu a cikinsu.
Wanan yasa ya dansan wani abu a game dasu kafin su hadu din don ba dadi kashiga mutane baka san irin halaiyansu ba don hakan ake son bincike saboda hakan Ahmed ya ke shiryawa haduwansu din.
Yau tunda gari ya waye ina gida ban fita ba sam banyi tsamanin ganinshi a wanan lokacin ba sai jin sallaman shi nayi Dije na masa sannu da zuwa.
Thank god don a gaskiya ba ai mun girshi indai a wurin gyaran muhallinane don komai tsab a lokacin ba ga kuma abinci nayi na gama na aje don Warmer's dina masu kyau da tsadane suna aje zafi har wani lokaci.
Nayi mamaki kwarai ganin irin tsaraban daya dawo muna dashi wanan karon ga muryan inna har makwabta dama irin hakan take son gani ga dan nata ta dafa yadda take so ta faki idon dije tayi kyauta ta kuma sayar idan kudi ya kakare mata na kashi.
Yayiwa driver nan bazata don yayi mai goma shatara da zai tafi shima yanata godiya sukai sallama ya tafi har lokacin ba wanda yasan waya kawoshi gida sai bayan tafiyansune yake fadawa Dije ai driver mahaifinshi ne ya kawo shi har gida.
Amadi kaga Bukar din ne a can yace eh dije muna tare dashi jiya shine ya bayar da mota wai a kawoni gida iko sai Allah sanyin hali irin na mutumin nan gaskiya sai shi.
Ya kamata dai kaiwa kanka fada hakana ku shirya ko uwarkama kuji saukin zama don gani takeyi laifin duk nakane yanzu nasani Dije haka inna take tunane bata tunanen irin abinda zan sama a can.
Allah dai ya kyauta tsohuwar ta fada har takai kofa ta juyo tana fadin ai na manta in fada maka uwar garke bata gidan nan tun jiya da rana mun nemeta mun rasa kaf shiyan nan .
Kafin yai magana nina farayi don da karfi na furta bata gidan nan ta bata ko yau ina bude kofa na ganta a nan kofan kwance har ina mamakin yadda aka saketa tana yawo ba a daure ta ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/30, 7:21 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣8️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,


Tun wanan tafiyan uwar garke bata dawo gidan ba ta bata amma ina jin Ahmed kafin ya tafi yana fadin nasan uwargarke sarai zata dawo garemu komai dadewa don haka Dije ki kwantar da hankalinki don Allah.
Nakanyi mamaki haka tayaya akuya ta bata tsowon haka kuma ace ta dawo wanan kan ai karyane shirmensa kawai yake fadi don ta kwantar da hankalinta saboda tsohuwar ta damu ainun akan batar akuyan har yar rama tayi.
Bani kadai ba ko innan shi da kannensa idan yace zata dawo mukan masu dariyane mu nuna ai ta tafi ke nan don ba wanda zaibar akuya kamar wanan idan ya gani.
Har dai lokacin tafiyan master yayi wanan akuyan bata dawo ba muma sai zancenta ya fita a kanmu saidai idan mun tuna mukanyi hiranta wani lokaci.
Mai karatu na bar maki zance baya akan yadda muka kwashe da mama da yaranta a gidan mu don na kwana biyu banje gida ba saboda bin umurnin ummah da nakeyi da tace bata son yawan zuwa gida gareni.
Bamu hadu dasu irin haka ba sai wata rana da muka hade a family house din mu da akai rasuwa wata diyar baba harun ta rasu a wurin haihuwa sai akai sa,a koda naje gaisuwa suma alokacin sukazo nan muka hadu dasu.
Bayan mun gaisa ne na shiga da mutane na dawo dakin hjy inda suke muka gaisa na danyi wa kaina mazauni daga gefen su zakace ba asalin mu daya dasu ba yadda suke jan kamshi a lokacin.
Suna ta hiran su kamar ba mutuwa akayi ba a gidan akazo gaisuwa ba waike har yanzu dai shiru bamu ga gaskiya ba Rukkaiya ta fada tana kallona nace gaskiyar me kuma Rukky ?
Mijim ki mana da akace ya samu aiki a kasan waje kuma mahaifinshi mashahurin mai kudine Abuja duk ashe zukece don aji dadin bakine tunda ba alaman komai ga zahiri.
Na rasa meyasa mutane basu kunyan karya ko in kayi karya ka zamawa oho ji yadda aka zauna aka shirya karya a lokacin babu ko kunya ba tsoron Allah sai kace kowa dolone da zai yarda Aishace ta fadi hakan.
Kai yaran nan da shirme kuke kun taba jin an canzawa tuwo suna ta yaya mai hankali zai yarda da wanan karyan idan an fadi hakan ba an dauka mutane zasu raja,a suce gaskiyane a fara masu wani sabon kallo babba ma yayi karya ina ga yara mamata fada.
Fadin hakan da mama tayi yasa na gane abinda suke nufi watau ummah sunyi karya ke nan a kan mu don su gyara master a wurin mutane don kawai a dauka gaskiyace yana da asali.
Wai wa ake zancene haka hjy tsohuwa ta tsoma baki a lokacin sai Rukkaiya tace a,a mijin Zahra dai da akace wai ya samu aiki kasan waje nake tambaya munji shiru har yanzu bai tafi ba ?
Ke nifa ba wanan karya ya dameni ba sai cewa da akayi wai dan shararen mai kudineshi magana ba ko kunyar fada sai yanzune ake neman uban lakaka mashi daga sama kuma don gyaran zance.
Ai bansan lokacin dana bude baki nabawa mama amsan hakan data fada ba saboda bacin rai tana kokari tace ummah ce munafuka tayi wanan babatun don ta gyara surukin ta yasa idona ya rufe nace dasu.
Saukin abin dai duk garin nan kowa yasan Ahmed yana da ubansa dama shidin ba shege bane da ubansa nisa ne ya rabasu yake nan don haka babu abin mamaki don ace yau ga uban nasa yazo gareshi.
Ra,ayine kawai irin na Ahmed yake zaune a nan saboda kakansa amma idan karyane lokaci shi zai nuna kansa karya kuma ai ba kaina aka fara ba don wasu sunyi fiye da hakan bai zama komai ba har yau kuma suna zaune a cikin gari ba wanda yai masu maganan rashin bin mijin da akace zasuyi idan anyi aure zuwa wani gari.
Ina wuta su sakani su hudun har hjy sukayo kaina lokaci guda nan gidan makokin ya koma gidan fada wuri ya kicime ni kadai su da makaraban su a lokacin.
Kai kai kai wanan abin kunya har ina ko wani haduwa sai ku takali boyar Allah nan ita tana lamarinta bata sakaku ba amma ku kun sakata da laluranta gaban ta.
Shekaran Jiyan nan fa mijinta yazo ya sallami Alh cewa zai wuce kasan waje amma zai bar zahra garin nan har ta karasa karatun ta idan ta gama zasu koma Abuja gidan mahaifinshi gaba dayan su shine yazo ya fadawa Alh.
Inko haka ba gaskiya bane zaizo har wurin Alh ya fada mashi haka a matsayin shi na ubanta da yake dauka tunda shine madauri aurenta ku rika magana kuna taunawa don Allah wanan matar baba Ado din In kin tuna ta ranan data basu amsa asibiti itake wanan jawabin.
Aikin banza ya tafi din mu gani mana don an fadi shi zaisa mu yarda sau nawa ake irin karyan nan karya dai aiba kan mu bane farau na kara fadawa mama aiko su Aisha suka taso min kamar zasu cinyeni danya saida su gwaggo suka fita dani ina kuka don takaici.
Um,humm ke meyasa zaki biye masu ku zubar da hali ummah ta fada dana gama mayar mata da yadda akayi in su basu san me sukeyi ba kema baki sani ba ke nan.
Kuda kukaje wurin gaisuwa zaku tsaya kuna zubar da hali a bainar jama,a ana maku dariyan ga marasa hadin kai da wauta don Allah niki rufa min baki ta fada tana kawar da kai.
Nima dai kuka nake saboda abin ya bata min rai sosai a lokacin yasa nake kukan bacin rai haka gaban mahaifiyata din sai kuma can naji tace cikin murya mai taushi.
Ke mahmaah baki ganesu bane har yanzu dan hassadansu su a fili yake ala dole dai kada mu kai inda suka kai har ace zamu fisu wanan kuma yana hannun Allah ba mutum ba.
Uba dai basu isa su sake mai ubaba shi din dai wanda basu son ya zama uban nasa shine dai uban nasa haka kuma daukaka yana hannun Allah ke kinsan da a hannun mutum yake daba haka ba.
Kwarai kuwa tani dake aje kayan abinci ta fada basu da hankaline na a matsayin mahaukaciya nake daukan hjy yanzu a gidan nan inba hauka ba wanan maganan abin fitarwane har duniya tasan manufarki akan yar kishiyarki wanan ai gazawa ne da abin kunya kice na fada watarana sai kinji wani can yana saka mata magana kan hakan.
Nifa ba wanan ba wai ace hjy tsohuwa duk zance ya taso sai ta nuna min kamar ni barece ba jikanta nake ba dariya naga ummah tayi lokaci guda dana fadi hakan.
Ke barece mana tunda mahaifiyar ki barece a cikin su ai haka hjy take kowa garin nan ya sani tashi don Allah ki shiga ki gyara fuskan ki kada su dawo su sameki haka su dauka sunyu galaba akankine sake jiki ki nuna bai dameki ba tani ta fada.
Yau sai gashi master yaje yayi masu sallama har dakin mama yake ya sallameta ya bata dubu hamsin ya fito abinda ya gigita mama ke nan wanan kudin daya bata din don haka ta rude tana maganganu bayan fitanshi gashi anyi sa,a duk yaran nata suna gidan a lokacin.
Master ya tafi ya barni gusau tare da iyayyenshi duk da a lokacin ba walwala amma ba laifi don ya bar muna abincin da zai kaimu tsawon wani lokaci.
Ga kuma karamin ciki a jikina dake wahal dani wanda duk bamu san ciki bane a lokacin mun dai dauka mutanenane suke damuna ashe cikine a jikina Allah ya kawoshi lokacin ba a sani ba.
Ina faman laulayi ga kuma jerabawan da nakeyi Allah ya taimaka har na gama ciwo yakici yaki karewa ba barci sai hamma da hawaye kawai nake aikin yi.
A wani asuba da ciwo ya isheni ne na dauko wanan maganin daya kawo min na shaka a hancina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login