Showing 51001 words to 54000 words out of 304363 words
ka tambaya zaifi yace zaiyi hakan kasan mutane yanzu ba abin yarda bane yace hakane Dije ya fita.
Na san na gama makara saboda rikicin su mana dana tsayawa don ko kannina saida ga baya aka kaisu makaranta don kawai gudun zuciyar zama tare da ummah keyiwa yaja muna makaran.
Na iso makaranta sai dalibai kadan ne a wurin suke shawagi a nan zama nayi cikin mota ina kallo abinda ke wakana a wajen.
Sam ban san da zuwan mutum ba don hankalina daya dauku ga tunanen su mama why mama zata dinga yiwa ummah irin wanan halaiyan hakane ?
Nocking din window motan akayi wanda hakan yasani dan firgita kadan ina kallon wanda ke wajen tsaye.
Manir ne na gani yana dariya tare da fadin let coma yau ma kin makara ke nan don gaki a waje dan murmushin yake na sake a fuskana lokaci guda ina fadin wallahi yanzu na shigo nasan na makara na tsaya nan ina jiran har su fito.
Ashe mun zama daya don nima minti daya na kara na samu har ya shiga ko kinga mutumin ki can tafe ya fada hakan yasani dagowa ina kallon inda yake kallo.
Watau gaskiya MAYANA dan uwanan naki ina son rayuwan shi donshi haka yake da simple life bai dauki karyan duniya ya dorawa kansaba .
Yanzu fa kayan gwanjon sayarwane ya dauko haka abinshi ba tare da damuwa ba wallahi gayen na bala,in ban tausayi sosai idan na ganshi.
Wai me zamuyi mai kan karatun dayake karamune naso mu hadu a hada mai wani abu ina ganin hakan zaifi don kada mu takura ma rayuwa shi wana ba matsala bane idan kun shirya saina bada nawa dana Hannatu ai.
Ah Master salamu alaikum ya fada lokacin daya dan karaso inda muke tsaye din yana washe baki kamar yaga mastern gaskiya a gaban shi.
Bai amsa ba sai cewa da yayi lafiya dai na ganku ana ana class yanzu lokacin nake kokarin fitowa daga motar sai cewa da Munir yayi wallahi master mun makarane.
Kasan halin malami nan da rashin nasiha gara kawai mu tsaya waje har sai ya fito mu shiga sai kuma hankalinshi ya dauke ga wasu daya sani ya nufi wajen su ya barmu tare da master din a wurin .
Meyasa kike son makarane hakan zai iya jawo maki matsala ga karatunki fa naji ya fada nasan dani yakeyi yasa nace yau mun tashi babu dadine a gidan mu wasu baki mukayi sai dayan ya bata ana neman shi hakan yasani zuwa yanzu.
Allah ya baiyana muna shi na amsa da amin ya juya kamar zai tafi kuma sai yaja ya tsaya nadago na dubeshi muka hada ido yace dama son Allah wani zance siri nake son yi dake ko zaki fahince ni ban sani ba.
A take naji gabana ya fadi girman shi na batun barewa a idona a cikin daurewa nace ina jin ka sai naga yana tura hannu a aljihunshi ya ciro wani dan wallet a ciki na fata ya bude ya zaro dollars din Europe ya miko min yana fadin don Allah ko kinsa wanan kudin wace kasane ?
Jiya baya na zaro kayana na tsunceshi a ciki har guda goma gasu nan harda address din mai shi a ciki na karbi kudin daga hannun shi na duba Allah ya taimake mu nasan kan kudin don rana mun zauna da yaya musa muna hira falon mama yai muna bayanin yadda suke.
Nace ai wanan kudin ketarene kudine masu daraja da kima a idon duniya kudine wanda sunfi kowani kudi daukaka a nan duniya naga alama ya fada .
Kinga wanan katin kuma ina ganin na mai wanan kudine ya mata ya sako kayan a cikin gwajo ko wata kila ansace mai sune suka shigo nan din.
Kallon mamaki nayi mai yaci gaba da fadi cikin muryan damuwa da ace da hanyar da zanturawa mai kudin nan da kudinsa su koma wushi danayi hakan na sauke nayin hakkin shi a kaina.
Haba dai kaiko wana ai kamar kyautane ubangiji ya bakasu don a matsayin rabo sukazo hannun ka duba nisan tafiyan da suka sha a cikin duniyan amma ba wanda yasan da kudin nan saika.
Eh to nasan da hakan amma kuma shi maishi kamar bada sanin shi ya bar kudin a ciki ba ai nidai da zan samu a kira min layin naji saina fadawa mai shi cewa kudin yana hannuna zaifi.
Wai wanan ai long process ne idan har kudin basu kwantama a raiba zaka iya yin sadaka dasu ka huta ai wanan kuma kin kawp shawara babba zan kara bincika inji ya matsayin su suke a wajena.
Ban katin mugani ko za a samu lanban maishi a ciki sai kayi magana dashi to kina ganin hakan ba zai ja muna matsala ba ko babu wani matsala indai zai fahinci abinda kake fada.
Katin ya sake miko min nabi katin da kallo na dan lokaci kafin na gane lamban da aka rubuta na waya a ciki nasa na danna kira yana tsaye yana kallona.
Turancin da ake min yafi karfina na mika mashi wayan tawa kiran iPhone ya karba yana saurare sai kawai naji ya buge da turanci kamar wani wanda ya tashi a kasan waje.
Turanci sosai yake bugawa da mutumin saida yai mai bayani dala dala baturen ya gane sukai magana ta fahinta dashi yayi maigodiya suka kashe wayan ya miko min wayana yana godiya.
Mai karatu wanan abin ya kara jawo shakuwa da yarda a tsakanin mu don a tare mukai shawara har na binciko mai inda zaikai a canza mai cikin mutunci ta hanyar bashi lamban ya musa sukai magana dashi.
Na karbi kudin muka tura mai Abuja ya canzo mashi su in naira sai gashi ya tashi da wurin dubu dari hudu da dan kai wanan ba karamin tsoron hakan yaji ba.
Kallona yayi da mamaki yace kanwata kin san me ki rike wanan kudin a hannunki ki ban dari na fara juyashi ta wani hanya zan dan dinga zuwa kauye ranan sati in sayo kayan masarufi na kawo cikin unguwar mu in kasa.
Don wanan da kika ban da wanda na sayar da uwar garken Dije sune yanzu nake harkan gwanjona dasu muna samun rufin asiri a ciki kuma sosai.
Idan ban fadi karya ba ke alherice don haduwana dake dana rabe ki na samu alheri sosai a rayuwana ba zan boye maki ba.
Kai haba brother kawai dai nazo a daidai lokacin abine kawai yace ba zaki gane hakan bane kawai abar zancen nace shike nan.
Sam yanzu banda matsalan kan karatuna don muma haduwan mu dashi ya zama muna alheri a karatun mu sosai sai gashi ana hada babban group yana kara muna darasi saidai ba kulun hakan ke faruwa ba don hankalinshi ya kara daukuwa ga sana,an shi yanzu sosai.
Kusan sati daya bamu sashi a ido ba gashi karatu ya dau zafi sosai muna yawan test lokaci lokaci sai hakan ya tayarwa yan uwan karatuna da hankali.
Suka yanke shawaran cewa mu hada kafa muje har gidansu a dubashi ko lafiya da bama ganin shi dole yasa ba bisu don bani zuwa ko ina daga makaranta.
Munir ne ya binciko muna sunan unguwarsu din da kwatancen gidan nasu a inda zamu samu isa a saukake ga sayayan da muka hada kudi akayi za a kai gidan nasu.
A motana muka shiga saita munir din da maza suka shiga sune a gaba muna biye dasu a bayan su zuwa gida da dan nisa sosai da school din mu.
Dije ne kadai a gidan ban daki ta zagaya ta fito ta tsaya tana wanke hannayen ta idon ta ya sauka kan tsiron daya fito daga gefen dan gatangan kasan daya zagaye gidan nasu .
Ido ta kurawa wurin kafin ta taka zuwa gaban dan tsiron ta kara kura mai ido sosai hannu takai zata cire don kada haki ya jawo masu sauro don hakane gidan ko yaushe fes yake a garesu.
Wani kuka uwargarke tayi wanda yasa Dije firgita tana fadin ke yanzu nasan kukan ki da ma,ana yake watau kina nufin na nabarshi kada in cire ko ?
To Allah ya sauwaka ta fada tana barin wurin da sauri don lamarin uwargarken ya fara bata tsoro yanzu sosai yasa ta kara rike addua da karban magani a wurin malam tanimu da har saida ya shigo da kanshi kallo uwargarke.
Inda ya kara tsora Dije da fadin indai ba sun shigeta ba to tana da shafansu a jikinta gaskiya don alamu sun nuna hakan sosai ga dabban.
Haikan dije ta tsani uwargarke yanzu saidai tana tsoron nuna hakan afili don gudun wani abu yazo ya sameta wanda ya shafi iskokai.
Da tambaya Allah ya kaimu gidan nasu a kofa muka tsaya inda ba iya gidan ba kusan unguwan nake karewa kallon mamakin ashe akwai irin wanan unguwar tallakawan a cikon gari haka har yanzu.
Kofan gidan da naga munir din ya tsaya sai mamakina yakaru lokacin layin shiru sai motsin daka da mukeji a wasu gidan unguwan.
Fitowa yayi daga motanshi kiran honda ya nufo inda muka tsaya yana fadin to ai saiku fito ku mata ku shiga kuyi muna sallama ciki muji dole muka fito na tako da kyar ina bin bayan su zuwa cikin gida .
Hannatu ce a gaba muna biye da ita kusan nice fa karshe don haka akaji sallamana daga bayan su .
Wani kuka mai ban tsoro mukaji saida kowan mu ya kadu saboda sautin kukan nata har zamu juya muryan tsohuwar daga ciko tana fadin sannun ku da zuwa su waye ?
Nikan tsakiyansu na shige don ga bakidaya tsoro nakeji mama Ahmed muke nema mama Hannatu ta fada Ahmed a gidan nakuwa eh mama nan akai muna kwatancen gidansu.
Wanda ke karatu a jami,a babba kamar yadda yan gari ke fada kodai Amadi tsohuwar ta fada kai tsaye sai hannatun tace shi mama Amadi kuke ce masa ko ?
Ai saiki yawace unguwan nan kaf kuna neman shi da sunan nan ba a gane ba amma dakunce Amadi kowa yasan nan ne .
Yanzun nan ya dawo daga kauye kwana biyun nan duk bai fita don ciwon kafana daya tashi yana gidan nan yana kula dani.
Yaune dana danji sauki ya tafi kauye dauko hatsi kuma har sun dawo don naga an fara shigo da kayan su daga bayan mu mukaji suna shigowa yana fadin tunda kunzo aisai kun shigo kunga kakata Dije.
Turus yayi don ganin mu gaba dayan mune ashe mukazo don bai farga da motana dake can gefe dana parker ba a unguwar don samun saukin fita idan zamu koma.
ZAINAB IDRIS MAKAWAHAYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃👠👜💍👡👛 🥿👘👗🧤
INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION.
ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M A C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝
TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI.
YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
..🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
1️⃣7️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Duk juyawa mukayi muna kallon su don wa yanda ke shigowa da kayan da muka sayo masu a lokacin wanda munir ne ya bada shawara haka gare mu aka hada kudin aka sayo.
Master munji shiru ne muka biyo bayan ka don mu diba ko lafiya kasan ance ka kula wanda ya kulaka munir ke wanan maganan daga inda uwargarke take tsaye sai kuka takeyi har lokacin tana bubuga kafa a kasa.
Jinin jikina nasha don haka kawai naji tsikan jikina yana tashi duk lokacin da wana akuyan tayi kuka, magana yake damu amma hankalinshi na gun akuyan nan.
Tabarma tsohuwar ta dauko muna dakinta mu matan tace mu zauna Dije zasu iya zama kuwa ya fada mezai hana mu zauna mu da indan mun mutu akasa za a samu hannatu ta fada.
A gurfane nake a can karshe kusa da tsohuwar yayin da take zuba muna godiya da fatan alheri bamuyi aune ba aga wanan akuyar ta balle daurinta ta nufo wajen mu da gudu.
Muryan malam tanimu ne ke fadin kai kai kai kada ki soma karki fara wanan ga yayan mutane kaji mun akuya ke baki son bakine a gidan.
Amadi din ya mike ya kamata yana fadin aiko na baku abinci da zan fita dazun mana uwargarke ya dago yana fadin abinci ta gani yasa harta ballo a madaurin ta.
Kukan nan nata takeyi tana turjewa a wuri daya ya samu da kyar yajata yaje ya daure ta tare da zuba masu abinci saidai takici sai kuka takeyi sosai kamar taga wani abu.
Amma ba wanda ya farga da kukan da takeyi sai malam tanimu da akai mai bayanin dalilin zuaan mu yake sa muna albarka da fatan alheri
Nikan mikewa nayi daga inda nake tsugunne a cikin tsawala bayan na dan tabo hannatu nayi mata alaman da mu tafi.
Sauran suka mike sai anjima mukaiwa tsohuwar wani kuka sosai akuyan keyi da kamar guda na fice gidan ko kafin mazan su fito har na shiga motana ina kokarin tattara natsuwana waje daya.
Don harna shiga motar ina ganin kamar wanan dabban zata biyoni ta yakusheni har cikin motar sai waigen kofan gidan nakeyi ina kokarin tayar da motar na kasa saka key din motar da kyau.
Wai lafiya kike kuwa Mayana naga kamar a tsorace kike mana hannatu ke fada daga gefena don yanzu itace babban aminiyata ta kut a school din duk inda nake muna tare duk da halin mu yasha bambamda ita sosai.
Na samu na tayar da motar ban jira su karasa fitowa ba na fara yin kwana don barin wajen duk suka bini da kallon mamaki a hanya na saukesu nace gida zan tafi nabasu kudin taxis.
Na isa gida a firgice dakina na nufa da kyar na samu saita kaina nayi sallah la,asar na koma saman gado na dunkule wuri daya sai ga zazzabi yana neman kamani lokaci guda.
Jikin ummah ya bata cewa na dawo sai ta leka dakin ta hangoni kwance hardasu jan bargo na rufa kafana yasa ta gane cewa nice a dakin dai kwance.
A,a ke yaushe kika dawo har kika shigo banji shigowan ki ba ummah ta fada saida na yaye abin rufan nace dazun nan na dawo ummah babu kowa a falon lokacin.
Lafiya kuka dawo haka da wuri ta tambaya tana kafeni da idanu nace umma sanyi nake ji na dawo subbahanallahi ta fada to kinsha magani nace bansha ba ummah yanzun ne na fara jin hakan.
Waike yaushe zakiyi wayaune wai maamah ki tashi kici abinci kisha magani ina zuwa tana fadin hakan ta juya ta fita daga dakin binta nayi da kallo na koma na kwanta.
A haka ta dawo ta sameni kwance fada ta fara min dole na tashi nadan tsakuri abincin na hade magani na koma na dunkule sai barci yaso ya daukeni sai naji kukan akuyan nan a kunnena in zabura na bude idona.
Yanzun kai Amadi banda abinka ai kowa yasan mu tallakawane a garin nan ko meye abin jin haushi don sun kawo maka wanan kayan haka har gida.
Haba Dije ai wanan ya zama zubar da mutunci a gareni yaushe don ina koya masu karatu kawai zasu kwaso wana uban kayan haka su kawo min har gida watau gani mabukaci ko suke ganina .
Amma dai akwaika da wani zance Amadi ina kayan nan na dubiya suka kawoma don sun dauka kaine bakaji dadin jikin kaba yasa sukai haka a matsayinsu na aminan ka ?
Shiru yayi ya barta tana magana kafin ya mike zuwa ban daki saida ya kewaya ya fitone idon shi ya sauka kan dan tsiron daya fito a wurin katangan nasu.
Takawa yayi zuwa wajen tsiron ya kura mai ido na dan lokaci kafin ya juya yana fadin Dije tumfafiyace ta fito a wurin nan haka ?
Tumfafiya uwar kwankwanmai baki fita a wurin banza, sirinki sai Allah,