Showing 159001 words to 162000 words out of 304363 words

Chapter 54 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33299

zata iya kula dashi ba tayi auren ko an fada mata yar aikina haifa matane tunda sun saba kwanciya ana girka masu suna ci ko ?
Ke Aisha fito ki koma cikin gida ki daina zuwa kama mata aiki tunda tana iyawa inma bata iyawa ai gani saiki fada min abinda zan kama maki kiyi ba sai anje ga haka ba.
Daga dan tsakar wurin mu ya tsaya yanawa kanwar tashi magana a fakaice ta aje abin kubewan ta juya ta fita sai naji uwar tayi kwaba tana binshi da kallo ta juya ta tafi.
Jikinane yayi sanyi saiga hawaye na silalo min a fuskana ya karaso ciki bayan fitan ta yana fadin kema princess meyasa zaki basu aiki bayan kinsan halin inna ?
Dago kai nayi da niyar in fada mai yadda zancen yake sai na kasa sai hawayen dake bin fuskana ya dauki roban ya daga yaga saura kwara uku a ciki wanda bata goge ba yace aima ta gama ashe akwai wani abinda zan kama makine dashi ?
Na girgiza kai na samu na bude baki da kyar nace komai na hada sai wanan din ya rage min dama kuma Aisha din ta gyara min shi ai.
Ya danyi shiru yana kallon yanayina kafin ya juya zuwa ciki ya koma ya kwanta yana duban laptop din shi da yanzu yake aiki a cikinsa har na gama girki ana gab da magariba na wuce shi na fada bandaki nayi wanka tare da dauro alwala.


ZAINAB IDRIS MAKAWA[22/04 3:41 PM] +234 806 730 5151: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣5️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Kamar yadda jikina yayi sanyi haka shima na kulla jikinshi yayi sanyi sosai tun lokacin da abin ya faru har zuwa bayan isha,i bamuyi magana dashi ba.
Ya dawo baya ya shigo ya dauki abu ya sake fita ya dan jima a wajen ya dawo ya sameni zaune ina waya da Hannatu a lokacin ya samu wuri gefena ya zauna yana sauraren mu don a zaton shi muna magana ne kan abinda ya faru tsakanin mu da mahaifiyar nasa yadda wasu mata sukeyi idan matsala ya faru dasu.
Sai yaji magana mukeyi kan test din mu har dai zuwa lokacin da muka gama wayan na kashe ina gyara zama tare da lumshe idona naji muryan shi yana fadin.
Zahra na yanke shawara zan nemi wuri mu koma can nidake don irin wanan matsalan da inna take yawan maki koda yaushe.
Bana jin dadin ganin yadda akan sister dina inna take rufe ido tana fada maki maganan duk daya zo mata a ranta kandan matsala kadan tsakanin ku raina yana baci da hakan sosai wallahi.
Jin abinda yake fada din yasa na dan sakw runtse idanuwa don na kasa fahintar ko ya fara ganin laifinane kan matsalan mahaifiyar nasa yanzu dani.
Da kyat na daure na iya fadan magana daya da cewa yin hakan kuma shi zai kara haifar da babban matsala a tsakanin mu dasu.
Don zasu dauka nice na baka shawaran ka barsu ka tafi can nisa dasu mu zauna mu kadai ba tare dasu ba din don nayi yadda raina keso ke nan yadda take zato ina yi a yanzu.
Koma me zat fada ta dade bata fada ba don ba zan yarda da irin hakan yana faruwa ba ko yaushe tsakanin ku.
Gaskiya niba zan tafi ba ni dai takewa hakan a kanka kuma zan daure duk wani kiyayyan da take nuna min a yanzu har zuwa lokacin da zata gane cewa ni din ba haka nake ba a yadda ta daukeni din.
Shiru yayi ba tare daya fadi komai ba sai zuwa can naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin don Allah ki kara hakkuri bisa wanda kikeyi a yanzu nasan ba a kyauta maki ga hakan kiyi hakkuri don ni naja maki hakan.
Ba zakaci abinci bane sai yayi sanyi na tambayeshi don mu kawar da wanan zancen ya nisa tare da fadin zanci amma tare dake don nasa baki ciba har yanzu.
Bana jin cin komai ne yanzu amma muje in zuba zanci na fada ina mikewa ya jawoni nayo baya zuwa jikin shi na fada ba shiri.
Rufoni yayi da hannayensa yana neman fuskana ya hada da nasa yake fadin princess nasan kina daure komai ne a kaina don kada naga kasawan ki.
Kiyi hakkuri don Allah zahra hakan yana min ciwo matuka a rayuwana ba komai don Allah wata kila nidin ce nakeyin abu ba daidai ba wani lokacin .
Ji nayi yace hmmm kin dai fadi hakan ne yanzu amma nasan abin kema yana damun ki nace toko ya dameni yaya zanyi tunda matsayin uwancikina take a gareni nasan zata bari wata rana insha Allahu.
Sai naji ya kara rungumeni yana sauke ajiyan zuciya kamar wani zai kwanceni gareshi a lolacin yadda yake min din.
Da kyat na samu nayi mai dabara ya daga mukaje cin abinci ba laifi na dan daure na danci don hankalinshi ya kara kwanci don hakan ya kwantar mai da hankalin shi .
Zaune yake yana tunanen irin mafalkin dayayi a daren yana son tunawa amma kuma ya kasa gano komai a kwakwalwan shi.
Yana yawan ganin matashin a yan kwanakin a mafalkin shi bai masa magana amma yana ganin matashin kamar yana cikin damuwa sosai game da wani abu saidai ya kasa fahintar damuwan matashin me zuwa mai da siffan danshi yasir daya haifa.
Da farko ya zata yasir din ne yake cikin wani hali amma yana kiran wayan matashin dan nasa yaji yanayinshi yana cikin kwanciyan hankali sosai lokaci.
Don haka suka dan taba hira kafin suyi sallama ya kashe wayan nasa din a lokacin yaci gaba da nazarin mafalkin da karo na uku ke nan yana yinsa a dan lokaci nan da yake ciki.
Gyara zama ya danyi yana fadi a zuciyar shi shin kodai wanine daga cikin danginshi yake cikin wani damuwa irin haka alakar jini yake bibiyan shi a yanzu.
Yasan a yanzu yana da rauni da sakaci zuwa ga yan uwan nasa da bai kulasu yadda ya dace din saidai shima yasan cewa haka kawai yaji baya son kula kowa nasa a yanzu.
Dan daman shi daya shine alherin sa ga mutanen unguwa da mutanen gari bai kaiga ya fasa dan basu ihisanin daya kan dan raba garesu ba idan yazo garin duk da yasan bai masu komai ba a cikin irin tarin arzikin da Allah ya nufeshi dasu a rayuwa.
Duk da yasan maidakin shi ma,ana uwargidan shi Yabi da yanzu kusan itace ke juya komai a yadda takeson ya kasance a rayuwan ta.
Duk da hjy tayi kwatance da kokarin rabashi da kowa kamar yadda tayi nasaran rabashi da yan uwanshi ta hanyar kakabesu kaf a rayuwansu .
Sai ita da nata yan uwan da irin mutanen data yarda su zauna a kusa dasu lokacin amma kuma duk da hakan batayi nasaran rabashi da aminan saba na kurciya da hakkurin su kan irin wullakanci da suke fuskanta baisa sun gaji sun bar mijin nata da ita ba.
Wanan abin yana matukar konawa hjy rai don ta tsanesu kamar yadda ta tsani mutuwarta a lokacin haka ta tsani ta bude ido ko kunnuwanta yaji mata yana ambatan sunayennsu ko zai masu wani alheri a rayuwan su.
Hakama yanzu da zancen wanan matashin mai kama dashi daya fito yasa hankalin hjy din ya kara tashi sosai duk da bata sancewa shi wanan matashin wayeba gareshi.
Tayi kokarin acikin siri nasa mutanen ta su binciko mata wayeshi amma anyi rashin sa,a har rana ita yau basu ma ji wani duriya daga gareshi ba balle ganin shi.
Har tellansu isah da shima yaga matashin ta bincika a waya amma ya nuna mata shima ganin shi yayi kawai kuma yaga kaman nasu kamar yadda wasu da dama dake wurin ranan suka sheda hakan.
Tun abin yana damunta a rai har ta dan fara sakewa don ba wani labarin da zai gamsar da ita akan matashin ta bar abin ga kamace kawai irin na dan Adam wani lokaci.
Da wanan tunanen ta manta da zancen saidai bata bar wani kafa don daure mijin nata da takeyi a ko yaushe na ya zauna under control din ta kada ya tsalake duk wani abinda tace dashi a rayuwa.
Ta kumaga nasaran yin hakan don ko banza shidin ya kasance ba mai hayaniya bane ga kuma asirin dake aiki sosai a kanshi ko yaushe cikin barbade yake a jefa a filon kwanan shi.
A shafa a takalman sakawan shi a zuba mai inda zaibi duk akan duniya da zai iya bari itama zata iya barin shi ko wani lokaci amma ta manta da hakan duniya kawai aka saka a gaba lokacin da nema daga ita sai diyanta kwara hudu data haifa dashi biyu maza biyu mata.
Saidai iya binciken ta ita da bokayen nata da malamai Allah ya batar masu da basiran cewa dan nashi yana raye ko yaushe sukayi mata duba sai suga ai baida wani da a duniya sai diyan ta.
Don kamanin danta suke bata sak da wanda suke gani a duban nasu don hakane hankalinta ke kara kwanciya don tasan sungama da wanan babin a rayuwanshi ko.
Bata san Allah ya riga daya tsago wanan hallitan a cikin jikinshi ba yana rayuwa a wani bangare na daban a cikin kasa kamar yadda suma suke nasu rayuwan cikin jin dadi a daulan mijin nata da Allah ya azurta shi dashi ba.
Ba wani abu takewa hakan ba tun farko ita da kakanta data bar duniya a yanzu tareda yan uwanta dake taimaka mata wurin irin wanan halin nason su mallaki duk wani abin hannasushi tun farko.
Don irin hakane yasa tun farko suka nisantashi da kowa nasa bayan sun gano barshin gida a lokacin bashine solution a garesu ba.
Yasa suka karya asirin ya dawo gida saboda sunsan dukiyan ba zata ciyu garesu ba su kadai tunda ga yan uwanshi da suke uba daya sun mamaye komai bayan batan nasa.
Yau gidan yana da jama,a sosai don mijin nasu dake gari don hakane duk wace ke girki bata da hutu idan mijin nasu yana gari.
Irin hakane ya kasance ga ummah da girkin ya fado kanta a washegarin ranan da Abba yazo garin ke nan zata karbi girki hannun mama wace ita iya abincin dare dana rana zata girka dashi din.
Suna kitchen suna aiki da Tani mai aikinta don tun karfe biyu suka dora girki a gidan suna tsaka ga aikine yan uwan Abban mu mata suka shigo don ganin Abba din a lokacin don ya kwana biyu bai leko garin ba.
Tun bayan auren shi da hjy karima yanzu Abba din sai ya kwashe kwanaki mai tsawo bai leko Gusau ba suna can Abuja tare da amaryan shi .
Ganin tana aikine basu tsaya a part din ba suka shiga wurin mama sun dan dade tare da mama din kadin Abban ya sallami wasu bakin da yake ganawa dasu lokacin yace su shigo gashi kafin wasu su shigo mashi ya tsayar dasu wurin son ganin su din.
A wanan lokacin ummah ta shiga lokacin girkinta na ranan don haka ta shigo falon suna ciki da yan uwan nasa don ta dan rage wasu aiyukan daya shafi rayuwan Abba din da suke masa da kanau basai sun saka yan aikinsu ba sunyi.
Gwaggo uwace ke fadin hjy salma naga fa sai wani sharning kike yi yanzu meye sirin hakanne yanzu sai gwaggo rabi tace meya dameta yanzu tunda ta aurar da yar mu ai dole hankali ya kwanta kafin wa yan nan su taso kuma don Amira kan ba yanzu ba kusa auren ta sai me rabon ganin hakan.
Gwaggo uwale din ta kara fadin aiko naga mama da mijinta a mashin zasu makaranta wanan yaron akwai kokari wallahi haka zai daukota saman yar mashin dinshi ya kawota gaida mu har gidajen mu.
Mashin kuma zahra dince ke yawo a gari saman mashi ina motar nata koya lalace ne kuma Abban ya tambaya acikin mamakin jin hakan ?
Daga inda gwaggo shafa take zaune tace wace mota kuma yaya motar daka sa a karbe a hannunta tun lokacin auren su kake rambayan mota kuma yanzu ?
Ni din nan nasa a karbe mata mota akan wani dalili ya tambayi su gwaggo din sai gwaggo uwa tace ikon Allah wanan ai tsohon zancene mota kan an karbe munyi korafin hakan har mun gaji ai.
Allah zai bata insha Allah da yake yaran daga ita har mijin nata ai ba masu rawan kai bane kaga basu damu da hakan ba gwaggo shafa ta fada .
Idan yana gari ya kaita da yar mashin dinshi in baya gari kuma tace mai mashin ya nema mata da yake kaita ya dauko ta har lokacin da zai dawo daga wurin nasa karatun.
Ni din nan na saka a karbi mota ya kara fada cikin zafin rai da jin hakan ya dora da fadin towama na aiko ya karbi motan a hannunta wai ?
Yaya gambo mana tazo ta karba tace hjy maimuna ta turata kace a karbi key a hannun zahra din gwaggo shafa ta fada.
Salma salma ya kwadawa ummah data shige kira a hasale saiga ummah din ta fito yace kinsan da wanan zancen cewa Mamah bata da mota a hannun ta dama tunda tayi aure ?
Dan murmushi tayi kafin tace na sani mana bani na karbi key din na bayar a kawo maka ba a daudai lokacin mama tayi masu sallama falom itama ta shigo.
Dana aikowa a karbi key din motan ko zahra ta auri yaron nan a cikin fushina tunda ta nace sai shi aidai zahra diya tace har yau kamar dukkan diyana a garin nan.
Ke maimuna ya akayi har Gambo ta karbi key din motar zahra akan wani dalili waya turata ta karbo key din yanzu kuma ina motar nata ?
Wanan kuma saidai idan ka manta don munyi maganan hakan da kai kace baka ga ranan bata mota ba ai don in ya bace ba zaka gyara ba ko mjjin nata ba zai samu kudin gyaran wana motan nata ba.
Ok da mukai hakan sai nace a karba a hannunta ko me don ban gane kan wanan zancen ba dama kin fada min hakane don kisa a karbi motan a hannun yarinyar a tozarta ni a gari ko me ?
Wanan wani zance ne kuma haka kake min ni zanda a tozarta ka ko yar ka data auri fakiri a cikin garin nan ita bata tozarta kaba sai ni zan saka a tozarta ka ?
Na yaushe kuma tunda girma ya gama zubewa a idon jama,a yanzu kowa yasan haka ai tunda hakan baifi karfin ka ba ummah ta fada tana kokarin wucewa cikin dakin kwanan Abba din.
Tare da dorawa da fadin ni dai nasan kaddaran mutum baya ketare shi mamah kuma yarkace koka saka ai maka haka abinda na sani dayane shi mahakurci mawadacine idan yayi hakuri ga komai fatana dai ta zauna lafiya a dakinta.
Wanda bakiwa fatan zaman lafiyan bama sun zauna lafiya dakunan su ai dama nasan duk wani shege da ficen da kikeyi salma akan yarana ba yau ba na sani.
Saidai ki sani haka zaku kare dake da yar naki a wahalce gidajen auren ku yanzu kin fadane don nayi bayanin hakan kome wai ?
Allah sarki ni da kika gani nan ban taba bin dan kowa da mugun nufi ba balle diyan ki ga Allah na dogara da komai nawa ba wani ba nasan kuma Allah bai manta da muba ga hakan.
Zancen mota kuma a inda akayi ta dagani har mamah din a nan muka bar zancen don haka ki nemi wanda ya tayar da zancen a yanzu gareshi.
Tana fadin hakan tayi shigewanta ciki ta barsu a nan Abba din ya bisu da kallo kafin ya hade wasu yawun takaici yana fadin ji nan maimuna kada ki mayar dani karamin yaro don Allah ?
Nafa san abinda nakeyi bawai ban sani bane ta ya zan sakaki ki karbi mota a hannun yata bayan bansa kin karbi na sauran yan uwanta ba ?
Kedai kawai kinyi hakan ne dan wani manufa taki can na daban sanan abinda ya ban mamaki cikin zancen nan da ba wanda ya fada min komai kan hakan sai yanzu nake jin hakan daga bakin ku wai ?
Manufar me kana son ka dora laifin hakan yanzu a kaina kana denarying cewa baka sani ba ya kallota yace maimuna halinki yanzu wanene ban sani ba ?
Kedai kinyi hakan dawani manufa taki kuma ki kawo min motar na gani kafin na wuce inda gyaran da za aiwa motar ayi kafin akai mata abinta.
Yana fadin haka ya mike ba tare da sunyi zancen daya kawo yan uwan nasa ba wurin shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login