Showing 33001 words to 36000 words out of 304363 words

Chapter 12 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33294

na tambaya ina kallonta wanan ki bari har Abbah ku ya dawo saiya fadi hukuncin sa a kanta.
Su fito mu tafi to na fada kin dauki key din motar ne a, a ban dauka ba kije gun drower mirro yana nan sama sai ki aje min wanan sin wurin.
Na juya din na nufi dakin kwanan ummah na dauko na kuma aje mata wanan din na fito naci karo da kannena suna sauri kada in fita in barsu a gida.
Tare muka tafi yiwa ummah dake hada miya a kitchen sallama tayi muna Allah ya tsare da fatan alheri a garemu ta kara da fadin in dinga kula Allah ya tsare ya kare na amsa da amin.
Hayaniyar da yaran keyi na karadin shiga sabuwar mota yasa Aisha daga window dakin su tana kallon mu taga mun nufi wuri sabuwar motar kai tsaye mun bude mun shiga lokacin ta sake labulen ta juya da sauri zuwa fadawa mama abinda idonta ya gane mata din lokacin.
Mama da sauri ta taso tana fadin yau ga yar iska yar banzan yarinya kawai wai ni zarah zata rainawa hankali watau nayi abinda zanyi suke nufi ita da uwarta ko ?
Tana fita muna fita daga get din gidan namu sai kwalawa maigadi kira takeyi kada ya bude saboda dan tazaran dake akwai a wurin yasa maigadin baiji me take fadi ba sai kara wagale kofan dayayi muna na sauka na halba kan titi muka bacewa ganin su .
Tsuki taja ta nufo shi da fada shima wurin ta yazo yana faduwa yake fadin ina kwana hjy baka da hankali ne ina kada ka bude kofan nan su fita ka bude mata au ya fada yana kallon kofan tare da fadin walle banji hakan ba hjy kimun afuwa don Allah.
Tsuki taja ta nufi cikin gida da sauri part din mu ta nufa duk da Tani bata riga da tazo ba amma ko ina a gyare yake kamar ba yara a part din haka sai kamshi turaren wuta dake tashi a ciki.
Tun daga kofa take kwalawa ummah kira tana fadin ina Salman take wai maimuna lafiya ummah ta fada kamar yadda ta kira sunan ta babu hjy itama lokacin haka ta kirata dashi gatsau.
Maimuna mama ta fada cikin mamaki eh koba sunan ki ke nan ba ummah ta fada tana kallonta tana tsame hannunta da ruwa ya taba a kitchen da kyale.
Lafiya kike min wanan kiran tsshin hankalin haka meke faruwane wai Rukkaiya bata zo nan ba jiya tace nace ki ban key din motan nan da aka kawo jiya.
Wani kallo ummah tayi mata tana murmushi tace key din motan na maamah za,a baki idan zata fita sai ta tambayeki ke nan ko ko mulkin naki har yakai ki muna mulkin kama karya haka ?
Salma ni kike fadawa hakan yau ke wacece da ba zan fadawa haka ba ke uwatace ko kanwar ubata da ina girmamaki don wasu dalilai amma sai ga hakan ke kin dauka fin karfine hakan ko ?
Dana dauka kinsan mutunci yasa nake baki girma da kyaleki a matsayin wace ta girmeni a shekaru sai kuma sanin girman zumunci da nayi nasan ke yar uwan maigidanane daga baya kuma ina girmamaki kan yaran ki.
Amma yanzu tunda na fahinci manufarki dakyau a kan mu duk wani girma da kima daraja da nake gani naki na daina bakishi maimuna har abada idan bakin gyara ba.
Tana kawowa nan taja tsuki ta juya zuwa kitchen ta karasa aikin da takeyi ta bar mama a tsaye tana yankan sababi a falon mu har ta juya ta fita tana fadin.
Zan hadu dashi a waya shida ya baki zaizo ya karba ya kawo min ke har zama bariki kika koya da zaki nuna min kan mage ya waye a yanzu ?
Mu zuba dake da munafukan yarki data sameshi da munafuncin an bata motar Aisha tafi karfin shi ita ai ban san tafi karfin shiga wanan motar ba sai data nuna hakan yanzu.
Idanuwan mutane aka motana suna duban suga waye ya shigota haka ya haska kowa saidai na dan jima a ciki ina hada kayana kafin na bude na fito .
MAYANA wata ta fada wanan ai yar gidan mayana ce wace ke 200 level din nan yanzu maganganu irin na kus kus da jama,a keyi musanman yan makaranta da saka ido shike tashi a wurin har na shige science bluding na shiga department din mu.
Kowa na harkan gaban shi don malamin bai shigo ajiba lokacin ba wuri na samu nakai zaune inawa wace na sama sallama muka gaisa a musulunce da ita.
Wai naji suna fadin yau malam bai samun shigowa son baida lafiya sai lokacin na kallota ina fadin ayyah Allah ya bashi lafiya gaskiya naga ajin yau a haka.
Na dauko wayana a cikin jakkata don in kara tyring din layin ya musa don tun dare nake gwadawa wayan shi a kashe yasa yanzun ma na kara trying.
Saidai ban sameshi ba yasani jan tsuki ta kara fadin lafiya nace ba komai yi hakkuri na dameki ko ?
Yauwa dama ke nake duba tun dazun banga shugowan ki ba ya kika tashi fuskana na tsuke lokaci guda don ganin mai maganan dani danayi.
Ba kowa bane sai wanan guy din da nake ganin yana skn ya matsa min da surutu ko samu kan wanan da bansan komai a kanshi bama.
Nace don Allah ko kunyi maganan dashi ya yarda sai mu fara yau wallahi ni nasan zamu samu karuwa sosai a wurin shi wa ke nan wanan dana sama take tambayanshi ?
Kinga ga wata member mun samu gaki ga abokina sai mu tafi yanzun tunda muna free ko yaya kuka gani dakata malam don Allah.
Kai idan kayi mai magana laifine kaje ka sameshi mana amma ni ba inda zanje na fada ma ya wani kalleni yace but idan nayi masa magana har ya yarda zakiyi joining din mu dai don abin yai armashi ?
Jeka kayi na fada a dan fusace yace nikan nasan ba wanda yaki karuwa sai in bai samu ba dai barin dubashi ko yana free yanzu muyi maganan amma fa ki sani da sunan ki zanje in sameshi.
Yana fadin haka ya juya ya tafi naja tsuki ina fadin tunda kowa irin kane kada ka tsaya kai karatu ka kwaci kanka ka dogara ga wani.
Ganin yadda class din ke surutu rashin malami yasa na mike na fice daga ajin naji muryan wanan tana fadin jirani mu fita tare don Allah dole na tsaya muka fita tare da ita.
Wata sister ya tambaya cikin mamaki a,a MAYANA ta class din mu mana wace ka fadawa malam sister dinkace har malam din ya yafe muna mu shiga saboda ita.
Ok wallahi so muke mu hadu dakai ka taimaka muna kadan bamu group discussion tace wallahi kunyar ka takeji ba zata iya zuwa da kanta ba.
Ina take yau ai bata shigo ba nake gani don banga motar taba a park da sauri munir yace a, a tana nan class zaune ai tazo tun dazun.
Ka bari zan ganta muyi magana ya fada a cikin gadara da izza irin nasa na dan tallaka da gadara din nan don haka yake magana kamar dan basarake dashi .
To shike nan Done zamu saurareka amma ka taimaka ko don saboda ita please na barka lafiya sai mun jika please.
Baidai masa magana ba sai mikewan da shima yayi lokacin don tunawa da kaya gwajonshi dake ajiye a bayan ajinsu ya duba ba abinda ya samu kayan ya kara gyarasu ya dago zai koma lokacin ya hangoni tafe tare da wata muna tafiya a jere muna magana da ita.
Tun daga nisa na danna key motar tayi kara daya jawo hankalin mutanen wurin au motarki ke nan ta tambaya na kada mata kai take fadin wai dankari ashe dai ke din yar masu garice shiyasa tun zuwan ki baki kula kowa dama ?
Idan nace bata isheni ba farawa da iyawa nayi karya don na kula tana da surutu ita sosai sabanin nida zan iya zama magana saita kama nayi da mutu na bashi amsa daya haka ummah ke shan fama dani a gida.
Motar na bude na dauko goran ruwa guda biyu zan dago naji muryan shi yana fadin ashe kinshigo school din yau na juyo da sauri ina dagowa.
Yana tsaye a dan nesa kadan damu nace eh wallahi ina ciki tundazun na mikawa wace muke tare roban ruwa daya ta karba tana min godiya tare da jingina jikinta a bayan motan .
Dayan Goran ruwa dake hannuna na mika mashi sai ya girgiza kanshi yana fadin Alhamdullahi nagode amma ke baki iya zuwa ki fada min saiki turo min wani.
Banina turoshi ba shiyazo da kansa nasan dai da zancen wani kallo yai min kafin yace koda yake nasan kinfi karfin yin hakan da kanki saidai ki turo wani yazo.
OK wanan shine dama ake magana me surutu ta tambayeni na gyada mata kai tace malam ka taimaka muna mu dan samu sauki wallahi abubuwa suna da rikita kai yanzu sosai.
Idan nace zan dinga tsayawa na koya maku kullun zaiyi wuya hakan saidai lokaci lokaci insha Allah sai mu fara Monday idan Allah ya kaimu don yanzu na riga da na saro kaya ina son in shigar dasu ko Allah zai taimaka min.
Kace kai dan kasuwane ashe kana karatu kake da wanan lokacin to yaya za a ayi ya fada ya juya da sauri ya wuce ya nufi cikin department din.
Abba dake kwance da kyar ya mika hannu ya dauki wayan irin yadda yaji muryan mama din yasan wani abu ya faru ke nan a gidan ko yana shirin faruwa.
Meke faruwane hjy maimuna najiki a hasale dole in hasala Alh tunda yaron nan yana son ya fara jamin magana a wurin ka yanzu.
Wani yaro kuma ke nan kike magana ya tambayeta, tace wane yaro kuwa banda baba wai shine harda sayawa Zarah mota mai tsada haka tunda ya isa yanzun yake gani shi.
Na aika a karbo key din motar a hannun uwarta don hauka ita kuma ta hana naje da kaina tana son fada min maganan banza wallahi idan salma batai hankali ba zakaji nayi mata abinda ba,a zata ba.
Yace ita salma din kwarai kuwa wai yau ni salma ke kallo tana fada min in na isa na shiga dakinta key na ciki koko haihuwanta nayi da zan dinga kawo mata raini irin haka ?
Ai gaskiya ta fada wanan ya zama wullakanci da raini wayau a gareta wai ko kin manta salma ma matatace itama kuma tana gaba dake idan ma har wani abune baki kirana kiji yadda akayi.
Saiki je mata kai tsaye wai ta baki key koda karba ne aini dana ajeku yakamata na karba a hannunta bake ba don raini saikije mata kai tsaye haka kimkam.
Sai zancen motan da kikeyi wai baba ya dauki kudina ya saiwa maamah mota toh ba dauka yayi ba nida kaina na bada kudi ya sayo mata wanan motan kamar yadda na sayawa kowa lokacin fara karatun shi.
Ke kika tambaya na bada kudin motan kisaiwa maamah din moto a baya ashe baki sayaba sai kika gyara mata na Aisha tana shiga .
Maimuna ina zaki da wanan alhakin haka a rayuwan ki koso kike duniya ta zagemu don uwarta nada hakkuri da zama damu sai mu dinga takasu yadda ran mu keso ?
To ki tuna da baba da ita maamah din duk nina haifi abina kuma ina son kowa don haka ki kula don ba zan dauki wanan ba ya kashe wayan.
Tabi wayan da kallo ta dafa gado tana zama don da a tsaye take tana shirin zazaga mai bala,i a lokacin sai taji wani abu na daban daga gareshi wanda bata zata ba a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[02/01 10:56 AM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
1️⃣2️⃣
AL BARI,,,,,,,,,,

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Safara da marwa ta fara yi a cikin daki lokaci guda abu ya taru ya zama biyu a kanta lokaci daya ga mamakin hjy Salma ga kuma na Abba da yanzu ya barta dashi.
Meke shirin faruwa danine a yanzu mama ta tambayi kanta kafin ta wani juyo tana fadin wallahi karyan ki salma ko zan tafi ba komai a gidan nan kinyi karya ki hau kaina a gidan nan kun tabbata a bayan mu har abada keda zurian ki a gidan nan.
Mama kinga har an fara min magana wai anga zarah ta faso gari yau kowa sai zancen motar ta yakeyi garin nan Aisha yar kwalisan gidan mu ta fada daga kofa.
Jin hakan yasa uwar juyowa tana fuskantar diyar nata don jin abinda take fadi din ta faso gari tafi wa a cikkn ku don wanan motar data shiga shine finku da tayi ko me ?
To mama su mutane suna iya ganewane sai su dauka ita wata abuce a cikin gidan nan tunda gashi har su samira na fadi a group wai da motar da ita sun zama celibirty a garin nan ko ina sai zancen ta akeyi yau.
Ana tura photunan ta da motar haba dai mama saida nace kada ki bari ta shiga motar nan yanzu ga abinda hakan yaja muna kaskanci a idon jama,a da komawa baya.
Aisha zaki barni naji da abinda nakeji yanzu ko sai kin kara bata min rai zaki fice yanzun nan da kika ganni nan mun gama waya da baban kune yake fada min wai shi yabada kudi aka saya mata motar ashe ba baba ya sayaba shine ya saya nasan dai baban yaje mashi da zancen .
Shine tunda saida ya fara zancen dake anan kafin ya tafi shine dayaje gun abba yayi zancen da Abba din Aisha ke fadin hakan a hasale.
Rukkaiyace ta turo kofan ta shigo lokacin tana fadin wai kinji yan iskan nan har kirana sukayi suna min sheri wai sun san idan zamu fasso gari tamu tafi wanan ke nan.
Ina ruwan su yan sa ido da gulma ni mutane na ban mamaki ga sa ido kan abinda bai shafesu ba wanan ai tsaban gulmane da munafunci dama ai haka ake son gani a wurin mu ko yaushe.
To mama meyasa Abba zai yi muna haka yasaiwa zarah din ita kadai muya ware mu bai saya muna ba gaskiya ki tambaya muna muji dalilin shi nayin hakan ?
Ke Aisha ki fita min ido ki barni inji da abinda ke damuna a yanzu ko kin fini sanin abinda ya dace inyi ne kan hakan yanzu ?
Ganin ta dauki waya ta fara magana da yar uwarta yasa suka fice a dakin ransu bace har lokacin suna ci gaba da zancen wai ashe Abbane ya saya ma zarah mota bama ya musa ba yadda suke zato .
Don haka dolene suma Abban ya canza masu mota wanan lokacin wace tafi nawa idan yazo zasu sameshi da zancen hakan tunda basu gane kan mama ba lokacin.
Bai koma gida ba sai bayan sallah isha,i lokacin hankalin Dije ya tashi don bai saba yin haka ba ya kai wani lokaci yana waje duk ritsi magariba a gida take mashi.
Sai gashi yau din har yakai karfe tara saura yana waje yana shigo sukayi kicibis da Dije data yafa zani a kai zata fita neman shi suka hade da ita a kofan su mai dan guntun katanga a wurin.
A,a Amadi yau lafiya haka ka tayar min da hankalina kaida uwar garke dataki ci abinci ko ruwan gidan nan taki ci tunda ta dawo gidan nan.
Wai ina kashiga haka tun sallah asuba da kafita kabar gidan nan baka dawo ba har wanan lokacin haba Dije kin manta dani na mijine ?
Ban fita ba saidana fada maki cewa yau asubanci zanyi naje kasuwa daga can kuma na wuce zuwa school muna fitow na bazama cikin gari ina tallata kayana gashi kuma har Allah ya taimaka an kwashe don haka wana somawa akayi indai kaiwa darene ai yanzu.
Meya samu uwar garke din kuma wai ana nufin har yanzu mutumin nan bai biyo bayanta bane ko me abin ya fara daure min kai wallahi gashi kuma ban san gidan shi ba balle nabi sawun shi na mayar mashi da ita ai.
Yana magana yake kaiwa duke gaban uwar garke dake kwance tana tuka kamar wace tayi kiwo mai tsayi tana hadiyewa a cikinta.
Hannu ya kai ya shafa bayan ta a hankali yana magana da ita kamar da mutum dan uwanshi yake zance yace haba uwar garke ko fushi kike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login