Showing 288001 words to 291000 words out of 304363 words

Chapter 97 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33312

hakan inda dai zaluncine da yanzun sunsan dabaran da sukayi suka zalunce mu ai kome mutum yayi ai don kansa wallahi ta mike tana fadin haka.
Wai me kaya ya daure me cira ke wayyo Allah ke kuma masifa aka kara koyo maki a can kuma zuwan ki turai din don Allah ke ke Asmau you are very stupid na kara jin bakinki a cikin zancemsu sai na bata maki rai sha shan banza kawai mara ta ido.
But ta shige daki Dije tace aika kyaleta na dawo ke nan daidai nake dako wace dakariya a gidan nan idan kin dameni wallahi gidan ubanki zaki koma da zama tunda kuna da gidan kakanin ku a can.
Kada ki dauka kunci banza sai kun san kuyi wanan ta,asan a rayuwanku indai nina haifi Rashida da cikina sai kawai mukaji inna ta saka kuka ta dora hannu a kai tana kurma ihu.
Daukan yaranshi yayi ya juya harshe yana fadin ba zan tashi mu tafi bane shi baisan abinda yasa Dijema tayi wanan maganan ba yanzu.
Nikan na mike na kama hanya don duk na matsu mu tafi dama don a gajiye nake sosai lokacin ga wahalan ciki ga kuma gajiyan mota duk a jikina don na dade banyi tafiya irin haka ba lokacin.
Aisha ce ta shigo sai ihunta naji tayo kaina ta rugumeni tare da fadin ashe daku akazo yaya bai fada min ba ta sakeni ta kara kallona tana mamaki sai kuma ta sakeni tayi wurin yayansu da sauri tana kallon yaran.
Kafin taji muryan Dije na fadin kiyi kukan jini koki kaini ga alkali shi zansan kinyi zuciya ai da sauri kuma ta sake masa yaran da sukaki zuwa wurinta tac
Lah dije ta fada mata a jiki tana murnan ganin mu a lokacin taji yaya na fadin Dije mu tafi nakai yaran nan suci abinci yunwa suke ji lokacin cin abincinsu yayi.
Inna zaku kuma ta tambayi dijen tace a hasale inda akafi son mu da tatalin mu tana wuce Aishan tana fadin ai zan dawo gidan inga karyan mara kunyan yarki.
A ina kuka sauka kuma shine fa na dawo da wuri in gyarawa yaya daki nace ai ki barshi a gidansa daya gina sabo muka sauka dama jiyan da mukazo.
Kukan inna ta bari tana sauraran zancen mu da Aisha da tace lah yaya yayi gina a garin nan dama bamu sani ba yaya nayi maka murna sosai wallahi dama na dade ina tunane yadda zai sauka a nan yanzu.
Lallai dani ko za a wanan gidan yau babu inda zaki zauna gidan uwarki tunda nagane kasheshi kuke sonyi da ransa don Allah umma ki bar zancen nan hakana don Allah.
Inda nasan sayar dasu zai zama magana haka nima da ban taba masa kayansa ba ai har gashi saboda su umma kina kokarin yi min baki waime aka sayar kuma Aishace ke tambaya don bata san ba,asin maganan ba a lokacin.
Rufa min baki duk bakinku daya ai anga mun tafi an hade kai an kamawa yaro dabbobinsa an sayar a cika talle da miya ko ?
Hannu nayiwa Aisha tazo guna da sauri na riketa muka bi bayansa daga can nace tazo muje gidan namu don a gaskiya na hango rashin hannunta a cikin lamarin .
Daga can din kuwa muka shiga mota kafin ya koma ciki ya fito da Dije data tsaya fada a cikin gidan tana bata muna lokaci ya samu ya fito da ita da kyat yasata mota muka tafi.
Saida muka danyi nisa ya furzo da iska daga bakinshi yana fadin wai Dije meyasa kika tanka akan dabbobin nan tunda ba zaki gane komai a cikin zancen ba don ni na gane inna yanzu abinda yaranta sukace take bi.
Ba hakana bane yaya kace abinda Asmau ta fada dai, nikan ai sun bareni a gefe daya don ina fadin gaskiya ko lokacin da suka sayar da dabbobin nan saida na nuna hakan bai dace ba.
Amma inna ta nuna min kayan dantane ai don haka nafitar da bakina a ciki ko kuma ta saba min kuma idan nayi waya na fada maku zancen wallahi sai ta saba min ina ji ina gani Asma na zugata aka kira mai saye ya sayesu wullakance yanzu haka akwai uku da nake gani a gidan mani a nan unguwar mu .
Wani Mani dai mani da Aeka tace shi wanan mutumin mai sankon nan da katon ciki dake zama gidin darbejiyan gidansa kullun da dabbobi.
Ai kuwa kowa yayi mai tsaye a garin nan sai ya dawo min da akuyata don sammako zan masa a gida in tara masa mutane hakan ma yafi wallahi bakiga tayin wullakancin da yayi ba amma inna ta shige daki da Asma waisuyi shawara sai gasu sun fito suna fadin sun sallama masa akan ashirin ashirin kan ko wani dabba din ya kwashi banza ya tafi.
Kaji ko kaji cin amma wanan dabbobin da sukaci suka koshine za a sallama a hakan don rashin sanin ciwon kai Dije ai baki san rashin sanin ciwon kaiba sai kinga abinda yanzu Asmau take saka ina yi kamar wacce ta asirceta.
Don ina magana sai cewa inna tayi ina bakin cikin da yar uwata a yanzun don naga ci gaba ya sameta nake hassada da ita duk zancen da Aisha keyi bai juyo ba saida ta fadi wanan kalamin ya juyo yana fadin.
Cigaban meya sameta da har ake bakin ciki da ita na lalacewan da tabari tayi hakan a yanzu ko na batawa kanta lokaci shine nima nace ai yaya karshe dai dakin Dije na bude na share na koma ciki don ban iya ganin takaici.
Naji dadi sosai lokacin da yan gidan su Anty sukazo suka kwashe mata kayan ta don wallahi da yanzu anyi abin kunya don da ba a samun komai a dakin nan nata don zuwa lokacin har an bude taganku ashe ana shiga ta nan ana diban kayanta ban sani ba.
Salati me karfi dije ta saka tace wallahi ko dije abu daya ne bansan waye yake wanan aikin ba a lokacin tunda ban zama a gidani lokacin na fara karatu bani zama sosai dasu a gida.
Shigowan mu get din gidan yasa kowa yin shiru banda Dije dake faman sakin salati irin nasu na tsofi a lokacin muka fifito a motan zuwa cikin gidan inda muka samu mama mai aiki da yarinyar nan binta sun gyara gidan tsab yadda yake so sai kamshi ke tashi ciki.
Yaran ya aje ya nufi dakinshi ban tafi ba saida naba yarana abincin sukaci na samu na shiga dakina na kwabe kayan jikina don in huta saboda ina son komawa wurinsu ummah na kai masu abincin dare a asibitin.
Wanka nayi na fito na samu har lokacin yana dakin shi bai fito ba sai yaran dake manne da dije don sun saba da ita sosai binshi nayi in lekashi na sameshi yayi wanka ya saka jallabiya ya koma ya kwanta rigingine saman gado yana tunane.
Jin shigowana yasa ya dago ya kalleni nace aina dauka barci kakeyi bayan la,asar din nan yace No ina nan dai ina tunanen duniya wai zancen inna da Asma yace kwarai kuwa.
To ai kallo daya zakaiwa Asmau yanzu kasan cewa ta canza ga yadda muka barta a baya sosai don na hango tsaban rashin kunya yanzu a idanunta sosai yasa har na fara tunanen anya barinta da Dije ba matsala bane kuwa ?
Ashe kin fahinci abinda nakewa ke nan nima tunanen da nakeyi ke nan don ba zan barta da ita a gidan nan ba su kashe min ita idan kuma nace zan barta a nan karshe zakiga duk sun kwaso sun dawo nan din sun tare min a gida.
Zahra ba zan boye maki ba tun farko na tsani wanan yarinyar mara mutunci da rashin ta ido don bata da kunya ko kadan shiyasa nake daure masu lokacin kina ganin laifina kan hakan.
Ba laifin ka nake gani ance idan hannu ya rube baka yakeshi don sun zama hakan ai ba zaka iya rabasu da kai ba ni kuma tsakanina daku gyarane a tsakanin ku ba batawa ba.
Zan bata zabi biyu kafin a gama gyarawa Dije tsohon part din mu ta zauna ciki ita da Aisha kafinta gama karatun itama tayi aure idan taki ko daya sai dai ta koma gidan ubanta ta zauna.
Idan kayi tsauri da yawa kuma zakayi laifi a wurin inna gaskiya don haka ka bisu a sannu ba irin su inna ake bi a sannu ba zahra don ma ina haka din da itace yasa abubuwan suke dan min sauki.
Don da ban daure fuskana a kansu abinda yafi haka yawa ta mace zuwana na karshe a wurin su da nayiwa mijinta noman doya saida muka gama wahala an fara cire amfanin gona.
Rana daya haka kawai na dawo gidan na samu yana bala,i waina koma gida shiya gaji da ciyar da dan daba nasa ba har makwabta a lokacin saida suka shigo suna bashi hakkuri amma haka mutumin nan ya rufe ido yayi min tonon asiri nida ita a garin mutane.
Wani ya fada mai awurin cewa wani kasan yaron nan shine karfin aikinka bana don baka taba noma irin haka ba yace ai Allah ne ya bashi bani ba haka mutanen nan suka harharda min abin arziki.
Allah ya taimakeni kuma can mutum na dan aiyukansa yana samun kudi ina da dan kudin motana a aljihuna shina kulla washe gari na kamo hanya ni kadai na dawo gida tun lokacin ban kara komawa wurin su ba har suka dawo nan din.
Don me ni kuma a yanzu zan rike masa yaransa ba dole dani dasu don haka zan takawa kowa burki a tsanake zanyi komai kafin na bar kasan nan insha Allahu.
Ai don inna kayi komai badon shi ba haka kuma su din kannen kane kun hada nono dasu basu da wani wanda yafika yanzu a duniyan nan koda kuwa baka dashi ba zasu wuce zancenka ba don kaine dai nasu da zasuyi tunkaho dakai a fadin garin kaf don ka hada uwa dasu.
Shiru yayi zuwa lokacin idanunsa sun kade sunyi jawurin Amir ya shigo yana kuka hakan yasashi tashi ya fita don ya tambayi meya sameshi ya shigo da kuka lokacin na samu daman gyara masa dakinsa har bandakin na wanko na gyaro ko ina na dakin na fito.
Mamace zaune gaban mai magani tana hawaye tana fadin gaba daya yarana sin lalace min ban gane kansu ba mazan sun barkace haka matan masu aure duk nike dauke da laluransu yanzu.
Daga mai auren dangiya sai mai auren barawo don har gidan kaso an kaishi kan rikici dole hankalina ya tashi da wanan bala,in da aka sako min an barkata min kan dakina lokaci guda haka.
Yau kuma sai inga diyar abokiyar zamana tazo min da suran da nake mafalkin inga yayana sun kai itace ta zama tauraruwan gidan mu har tana iya daukan nauyin kowa a gidan yanzu.
Ki duba kiga yadda musa ya koma min dukiyan da mahaifinsu ya danka mai ya salwantar dashi ya koma yana rokon dari dari biyu don yasha sigari sai ta kara fashewa da kuka.
Hjy maimuna ki saurareni da kyau idan kin mantane in tuna maki tun farko na fada maki ki barta da yarta don wanan matar bata kallon kowa da sheri idan muyi mata a lokacin zai iya dawowa kanki.
Kikace abi ko wani hanyane a dai kuntata mata yanzu sakamakon ki kike girba hanya dayace shine ki gyara zuciyar ki da kowa kamar yadda har yanzu gata nan da zuciya daya take zaune dake da yayan ki.
Ban taba ganin takai ki ko danki wurin wani boka ko malam don ai maku sheri ba idan kuma baki yarda da zancena ba zaki iya zuwa gaba kiji.
Saidai idan kawai meshi yana son cin kudin ki to zai iya ce maki wani abu akasin hakan don kawai ya bambari kudi a hannun ku yanzu amma amsa dayace sherin kine yake bin ki a yanzu hjy.
A karshe ta bata wai abinda za a bawa yaran na tsari dana samun daukaka duk da abinda aka fada mata bata yarda da hakan ba saida ta karbo kayansu ta shigo mota suka dawo gida tana masu bayanin yadda zasuyi amfani dashi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA[7/15, 11:40 AM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣8️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Jikin Abba da saukin musulunci don ba a cewa ba sauki ga musulmi sai dai ace Alhamdullahu don tun zuwa a yadda muka sameshi yake kwance sai ruwa da ake faman kara masa ko wani lokaci.
A haka master ya shirya tafiyan su cikin kwana uku da zuwan mu garin inda zasu tafi dashi da ummah sai shehu da zai bisu a matsayin namijin da zasu dashi.
Nan mama ta dire ta hau masifa wai an kawo mata munafunci ai ansan itace zata fita dashi akace ummah a wanan karon yan uwa har da meeting hjy ta nemosu dashi a dakinta kan wai ba aiwa mama adalci ba da za a tsameta don haka saidai a fasa tafiyan a barshi nan ko ina ai Allah ke bada sauki ga mutum ba wani ba.
Nan baki ya kasu biyu ana kus kus sai baba harunane yayi kindunbalan fadin asha hjy asha ashe ba lafiyanshi muke nema ba ke nan tunda har za a tsaya zaben wanda zai tafi dashi.
Matan nan matarsace ta farko kuma uwar yayanshi itama haka kuma yar tane zata fita da mahaifinta waje sai muce mu bamu yarda da wanan gatan da zasuyi mashi din ba yanzu ko me ?
Hjy don Allah kibar shiga irin shirmen na mata don yanzu shekarun ki sun dara yin hakan a tsaya ayi zancen Allah a nan meye zamu tsaya muna wani kwana kwana a kai bayan saukine Allah ya kawo masa.
Saunawa ita hjy maimuna ake fita da ita duk fitan da yakeyi da maimunan yakeyi sai yanzu da Allah ya nuna mata nata lokacin zatace kuma zatayi bakin ciki da hakan har tasa ki tara munan kan wanan zance nata na son kai.
Abin nan bada kudin shi bane itama bada nata bane muma nan duka ba a cikin jikin mu bane din me zamu zauna muga dan uwan mu zai cutu mu kyaleshi muna kallo ?
Inda wani zaman lafiya tayi dasu a baya na kyautatawa juna nasan dole hjy salma ta daga kafa aje da ita yanzu don kara amma kiri kiri ana tauye mata yanzu Allah yaji kansu ya juya arzikin zuwa garesu sai kuma a nuna masu bakin ciki a fili.
Hakanane yayyun nasa suka kama fada haruna kayi maganan gaskiya a nan don gaskiya hjy idan muka marawa hakan baya sai a zagemu ma a gari.
Ita maimuna bata da kunya da tsoron Allah sam a zuciyar ta ina auren gaiya da wullakanci tasa akaiwa yarinyar nan tare da yayanta donta tozartasu a gidan kowa yasani ba abinda kowa bai sani ba a nan saidai in kun boye.
Izzalan naka ta motsa zakaciwa mutane mutunci a yanzu ka fadi ra,ayin ka kowa yabi ina shike nan suyi ta tafiya ita kuma sai tayi hakkuri nasan ma shima ba zai yarda ya zauna ba zai bisu ya samo lafiyan shi.
Kuma abinda yasa nace hakan ai kowa nan yasan maimuna itace wayayya mai ilimi ni shiyasa kaga ina mara mata baya ga komai yadda mijinta ya dauka din.
Hjy abar wanan zance wayewa wani irine hjy salma bata dashi wanan wani zancene kawai kuke son ku kawo yanzu a cikin zancen nan kuma amma inane hjy salma bata iya shiga ita kadai.
Sam baba haruna baiba da kafan da zancen mama zaiyi tasiri a garesu ba nan ya koge zancen kowa yaja bakin shi yayi shiru gwaggo shafa ita ke tsegunta muna yadda akayi daga baya a wurin ummah.
Tana kallo suka shirya da kyar mama ta iya fitowa kofan gida rakiyansu suka nufi Abuja dashi inda zasu shiga jirgi subar kasan tare da master dasu baba su biyu akai wanan tafiyan inda su zasu dawo gida bayan sunga tafiyan su din.
Mama ina wuta ta saka ummah a lokacin saidai mutane kar suke kallon ta don kowa yasan abinda ke faruwa banje rakiyan Abba ba har Abuja nan dai gida mukaje mukaga tashinsu don a lokacin gaskiya nayi nauyi cikina wata bakwai nea jikina.
Aisha tana gidan mu tare damu tun ranan bata koma can ba saidai taje ta dauko kaya kala uku don canzawa zuwanshi abujane ya rakiyan Abba ya samu mahaifinshi kan zancen dawo da mummy dakinta.
Murmushi mahaifin nasa yayi kafin yace a yanzu na gane ka saukin kanka yafi girman kaka babana kaida kanka kazo min da zancen wai na dawo da yabi cikin gidan nan kuma ?
Ai a zatona na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login