Showing 249001 words to 252000 words out of 304363 words

Chapter 84 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33366

zasu tafi gida a lokacin su hamza ne da mamah zasu kwana dashi saboda mamace da girki yamma a ranan ta fake ga hakan don alaman hakan data nuna har ummah din ta gane me take nufi.
Amma sai ji nayi master yace ummah don Allah zan samu a sauke min zahra a gida don zan tsaya har a sakawa Abba wanan ruwan daya rage kafin na koma gida.
Ikon Allah mu meye amfanin mu a nan din da har saika tsaya a nan din No ki barshi tunda hakan ya tsara ai ba a hana mutum aikata alheri ko banza yana debe min kewan su musa da basa nan a yanzu don yadda yake nunawan nan gareni.
Dadafa dama nasan za a rina tunda naga hakan yana gudana amma su musa da jafar kasan sunfi wanan din matsayi dai a hakan donshi surikine kawai yarka yake aure ko ?
Hjy Maimuna wanan maganan da kikeyi a gaban yaron nan bana jin dadinsa ko kadan don kawai ya nuna kulawanshi a matsayin yaya na uban matarsa shine laifinsa a yanzu ?
Donshi bai dauka a yadda kike zato ba da zuciya daya yake komai da yakeyi a nan din kuma iya kulawan da zai nuna ke nan asan yana da tarbiya ai da nuna kulawansa.
Gwaggo shaface take wanan maganan tana kokarin saka hijabinta a wuyanta jin abinda ta fada din ya sosawa mama da yaranta rai daga can baba haruna yakarbe da fadin nima hakan dai naso gani .
Don yaron gaskiya ba laifi yarone ko banza mai mutunci da sanin girman manya shi bawai yana hakan bane gaskiya don wani abuba shidai halinsa ne kawai hakana.
A wurin mama taso ta rufe idanu taci masu mutunci yadda ta saba yi amma sai Abba din ya dakatar da ita ga hakan yace a, a fa hjy maimuna.
Meye illan yaron nan yanzu ina ke kika karfafa aurenshi da maahmah lokacin dana hana nisai na dauka yanzu ai ashe kirkin nan nasa da kikagani yasa kika matsa na bata shi tunda ta nace akansa din lokacin.
Amma kuma yanzu kina kokarin fadin abinda ba daidai ba akan yaron don an fadi gaskiya meye laifin yaron nan yanzu kuma gareki.
Donni sai yanzu nakema alfahari dabawa zahra shi da kika saka nayi don yafi min wa yancan mazajen nasu Rukkaiya mutunci don shi ko wani zuwa nayi zai shigo ya gaishe balle mijin Aisha dako ganinsa ban ma taba yiba ni har wanan lokacin .
Ai hakan abin alfaharine a gareki don kece kika bada goyon bayan na aurawa ita zahra shi ga kuma auren yayi amfani tunda ba a jin tsakanin su ai hakan abin alfaharine.
Dakin yayi tsit lokacin da Abba ke wanan bayanin idon mama ya kara rufe lokaci daya taji wani bakin ciki ya tokare mata makoshi ta bude baki a zafafe ta fara fadin.
Yanzun kuma zakace mijin zahra yafi na su Aisha kirki ko me don wanan shishigin daya fara yima a yanzu shine kirkin dayafi sauran ?
Har ni zaka dorawa wanan alhakin kace nice nace ka daurawa zahra aure dashi saukin abin mara asaline daishi sai kabi a sannu don tsuntttaciyar mage bata taba zama magen kwarai.
Har idon ka ya soma rufewa da dan wanan halaiyan da ake nunama dama nasan an kulla wani abin ne tundazun danaga yana wanan rawan kan na munafuci gareka ai.
Su wa yan nan da kake kokarin ganin laifinsu a yanzu sune dai din sarakan naka na asali wanda kasan uwarsu da ubansu gari kuma ansani koda yakema tsayawa fadan hakan yanzu ai bata bakine don ita gaskiya gudace.
Murmushi Abban yayi yace wai meke damunkine haka maimuna kan yar cikin ki yaya balle yaron nan ba shege bane da uban sa kilama kaida kake Abuja zaka iya sanin mahaifinsa ai.
Wanan Alh Abubakar dangaske mai company oil and gas da kakeji shine mahaifinsa shine dana farko a wajensa wanan matsalan dai da suka samu da iyayyen ita mahaifin yaron shine kawai ya jawo matsala a garesu nakin yarda tabishi a lokacin da zai koma gida.
Ummahce take fadan hakan cikin kunan rai ita da gwaggo shafa don cin fuskan da mama din keson tayiwa Ahmed din a wajen saboda in indon mama ya rufe kowa tana iyaciwa mutunci lokaci daya ita haka halinta yake saboda irin izzanta.
Dakata Salma wai kina nufin dangaske mai kanfunan nan na Abuja dama shine mahaifin yaron nan tace kwarai kuwa Alh don yaron shine na farko daya haifa a nan.
Nayi mamakin wanan bayanin da ummah take yin don ban taba tsayawa na fada mata komai daya shafi Ahmed din ba irin wanan saboda wauta irin nawa a lokacin.
Shiru dakin yayi kafin mama tace wata sabuwa ke nan dansa ko dan dan uwansa ba balle wanan tazo mujitane kawai akeyi don gyaran zance kila dan dan uwasa nema ake fadan hakan.
Kai Abba ya daga yana kallon Ahmed din da alokacin yana tsaye bakin kofa ba wanda ya farga da shigowanshi dakin sai Abban da fuskanshi yake kallon kofan dakin shi zaiga mai shigowa a lokacin.
Hannu yayi alaman ya karaso yasa kowa ya juya yana kallon kofan a daidai lokacin wasu hawayen bakin ciki suka fara zubo min a idanuna.
Kai din ashe dan babban mutum ne irin Alh Abubakar ka tsaya a haka ana barna maka suna a nan don me baka koma gun mahaifinka ba don asalinka ya gyaru.
Tsayuwa ya gyara kafin yace hakan ra,ayinane Abba amma kwanan nan zamu koma can don zan bar nan din saboda na samu aiki a karkashin UNICEF don haka ba zan bar zahra a nan in koma kasan waje ba sai idan ta kammala karatunta zan dauketa mu tafi tare.
Allahu akbar Allahu akbar dama haka yake a wurin Allah baba Ado ya fada daga inda yake tsaye din yana sauraron cin mutuncin mama da takewa surikin nasa a lokacin.
Kafin ya juyo yana fadin to maimuna kinji kinji yanzu da kanki akan yarmu duk yake wanan batda sau din don irin ku masu mumunan fassara da akidan banza yanzu kinji gaskiyan koshi waye a bakinsa ko ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/25, 3:09 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣5️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Dakin yayi tsit baka jin motsin kowa a lokacin don ko haraban asibitin yayi tsit sosai a lokacin Abbane ya kallo inda mama take zaune yace.
Mamakin zancen wanan yaron ya hanani barci don indai dan gaske dana sani wanan mai arzikin mutumin dake da motoci da gidajen haya a Abuja shine mahaifin yaron nan da gaske abin nasu akwai daure kai ke nan a cikinsa.
Abinda nake nazari daya tsaya min a raina maimuna shine ke nan ita salma da yarta sunsan da hakan suka boye muna kome hakan yake nufi yanzu ?
Sai lokacin mama tayi magana tace Alh makircin Salmane kuma baka sani ba wanan matar mai tsaban jinin makirci kaga har yar nata ta koyawa wanan halin ke nan zurfin ciki da iya shiri ga salma kamar matan farko take a wurin iya tako.
Kai anya ban tsanmani sunsan da hakan suma gaskiya don da salman ta fada min kota fadawasu musa a lokacin suma dai ina tsammanin daga bayane suka sanda hakan kila.
Au baka yarda ba ke nan da shirin salma ko ai salma zata iya aikata fiyema da hakan nidai ina tunanen bandan cikinsa bane kila dan wani dan uwasa daine na kusa yake son yayi amfani da sunansa yanzu din.
Wanan mutumin yadda naji kana kwatantawa ina zai auri mace irin wanan don da gani arzikin nasa kamar na gadone don haka inama zai hadu da wanan matar anan ya aura.
Abba din bai kara magana ba bayan hakan daya fada yaci gaba da nazarin da yakeyi a cikin zuciyarshi na shi kadai don yana son ya natsu yayi tunane a kai alokacin.
Mama bata iya barci ba a ranan don wanan maganan da taji yazo mata a bazata sai sakawa take tana walwala da kullawa a kasan zuciyarta a daren ranan gashi a asibiti suke tayi data sanin kwanan da tayi asibitin a ranan .
Garina wayewa tace gida zata tafi gashi duk iya kokarin ta na son ta boye bacin ranta takasa hakan saida aka fahinci halinda take ciki lokacin.
Har Abba ke fadin ke kuma meya faru dake haka naga kin fita cikin hankalinki ko kwanan asibitin ne ya taba maki zuciyarki kika koma hakan.
Tsuki taja tana fadin wanan wuri aiba wurin da mutum zai zauna bane har ya saki jikinsa gida zan koma nadan yi wanka in huta kafin rana in fito da haka tabar asibitin ranta na mata suya tun a cikin mota ta fara kiran yaranta da su hadu gida gata hanyan gida din yanzu itama.
Tambaya suke hankali tashe don sanin mahaifinsu na asibiti kwance a lokacin sun dauka wani abune ya sameshi don kiran safe yana nunawa mutum ba lafiyaba a lokacin saboda mafiyan kiran safe tashin hankaline.
Karfe daya saura ya dawo gida tun daga bakin layin nasu babu kowa a lokacin don dare ya soma rabawa a lokacin kowa ya samu wuri ya natsu sai me lalura irin nsa daya hadu dasu mutum biyu bai kara haduwa da kowa ba kuma.
Saidai abin mamaki yana tura kofan gidan su ya shiga yayi tozali da uwargarke a kwance kofan mu kamar tana gadin wurin duk da yadda yake jin zuciyan shi ba dadi hakan bai hana ya fadi cikin mamaki ikon Allah uwar garke kece nan kin tsukene yau kika dawo nan kina gadin mu kuma.
Kamar taji meya fada sai kai ta dago ta kalleshi ta mayar ta kwanta shi kuma yana kokarin rufe kofan gidan dake bude kodaya gama ya juyo sai ya samu ta daga daga wajen ta nufi hanyar bandakin da ake dauresu.
Hakan bai bashi mamaki ba ya dai shige ciki ya rufo namu part din don yasan babu inda zata koda ba a daure taba a cikin daren nan tunda gidan rufe yake.
Ya samu na rufe kofan amma turawa kawai nayi don ban zaci zai kai wanan lokacin haka a can ba bai dawo ba don haka na kwanta sai gajiya yasa barci ya daukeni a nan falo inda nake dakon dawowanshi.
Baya ya rufe kofan ya shige ciki ya gama abinda zaiyi sannan ya dawo falon ya tayar dani muka shiga ciki kowa nada gajiya don haka bai matsawa kansa da nemana ba a ranan.
Washe tunda safe na dora girkin da zai tafi dashi asibitin karfe takwasa na safe duk na gama ya dauka ya nufi asibitin don ya kai masu.
Bai samu kowa a wurin Abban namu ba a lokacin don hamzan da mama ta barshi dashi ya dan fita waje ya busa taba yabar Abba din a dakin shi kadai a lokacin Ahmed din ya shigo.
Suka gaisa ya tambayi lafiyan jikin yace yaji sauki sosai don ya samu barci a daren jiya sosai ba kamar kwanakin da suka shude ba.
Nan ya zuba masa shayi yana sha suna dan hira jefi jefi dashi a zuciyarshi kuma yana mamaki mutum kamar Abba za a bari shi kadai a dakin asibiti ina iyalinsa suke don yasan ya bar mama asibitin dare jiya kafin ya tafi.
Aka turo kofa ummah ce da yaran data hana zuwa school ranan don su samu zuwa gaida Abba din nan suka shiga gaisawa da juna tanawa Ahmed din ba,a da fadin.
Kai wanan matar taka da rawan kai take wai ita har ta gamawa Abban naku abin kari ta rigamu kawo masa ke nan ato su sukasan zafina fiye daku bagashi har yazo dubana ba ku kuna gida.
Wallahi bansan hjy maimuna ta koma gida ba ai ni duk daukana ai tana nan ga masu nacin dana tsaya shiryawa nan su sai sunzo sungaida Abbansu tana nuna yaran dake gaban Abban suna magana.
Malam Ahmed ina kuma zuwa Abba ya tambayi Ahmed din dake shirin fita daga dakin nan ya juyo cikin ladabi yace ruwa zan karbo nan bakin get na dawo Abba.
Kagani ko an manta da ruwan yana nan nasa Tani ta fito dashi tun jiya da dare da muka koma har safen nan ina zuci zuci na fito dashi fili na manta wurin sauri.
Ahmed din ya fice yaja kanina babba suka fita tare ruwan ya sayo ya wurin bag biyar ya rabawa sauran dakunan shi kuma ya nufo dakin da Abban yake kwance dana goran swan ya kawo masu.
A yadda ya samu Abban da ummah zaune ya tabbatar mashi suna wani muhinmin maganan daya shafi rayuwansune a lokacin don yanayinsu kawai ya kalla ya gane hakan zanje gida na daukota ya fada.
Yauma ba zata shiga school din bane tunda jikin Abban naku da sauki sai ya danyi kasa da kai yana dan murzan hannayeshi yace damawai tazo din dai ta dubashi hankalinta zaifi kwanciya.
Kai amma Ahmed kana da wani zance don me zaka biyewa shirmenta bayan tana shirin zana jerabawa nan da yan kwanaki masu zuwa idan Allah ya kaimu.
Kinga kyalesu yakawota daga nan sai ta wuce ai sunsan abinda sukeyi amma kafin ka tafi idan ba matsala ka dubo likitan yazo ya dubani.
Don naji sauki ina son sallama yau nagaji da zaman asibitin nan to barin duba Abba ya fada ya samu likitan bai karaso ba don haka ya dawo ya fada masu lokacin hankalin ummah yana gun yaranta don haka bata bi ta kansu ba kuma.
Har ya fita yana tunanen rayuwan irin na gidan mu a yadda yadan kulla a dan zaman asibitin nan ba karamin kokari Abba keyi da iyalishin ba aje iyali irin wanan sai mai dauriya dayasan kan duniya.
Ba zai iya jure zama a tsakanin su ba don haka ya mike ya fita dan dama dama Abba din ya kan iya dan sakewa dashi a wanan zaman asibitinne kuma har dan fara ganin sakewan fuska ga Abba din.
Falon ta fado hankali tashe sukai ido biyu da uwar dake zaune ita kadai tana dan dukan kafanta a kasa tare da bubuga hannunta saman kujeran da take zaune a kai.
Babu ko sallam tana shigowa sukai arba da mahaifiyarsu din ta fara fadin mama lafiya ni wallahi har kin ban tsoro na dauka Abbane wani abu ya sama ai tana maganan tana kokarin cire gyalen dake kafadanta a lokacin.
Amma ai jiya kan ku tafi ya samu sauki aiko ni dan Allah zauna ki tayani tinane ko zancen nan danaji gaskiyane da sauri Aishan ta kallo uwar a cikkn son tasan meya faru lokacin yar uwan nata Rukkaiya ta shigo da yarta gida.
Mama wallahi har gabana ya fadi saida nazo banga kowa a kofan gidaba hankalina ya kwanta na dauka Abbane yayi margaye wallahi.
Ke sakarece Abban naku kike son ya mutu to mama akwai wanda ba zai mutu bane duniyan nan kowa ai tunda yazo saiya koma don babu mai tsayawa gadin ta.
Ni dan Allah ki zauna kun isheni da shirme wai ashe mijin zahra dan wani babban maikudine a Abuja mutanen nan dasu suka munafuncemu suka rufe zancen.
Dan me kudi kuma ta ina mama kodai dan dangin mai kudin kinfasan mutane da karya mama sai a shirya karya yanzu ki dauka gaskiyace.
Akwai kamshin gaskiya a cikin zancen nan don haka nake ganin ba karya bace wai shine dan farin mutumin ke yanzu hakafa waje zasu koma da zama wai ashe saboda zahran ya zauna nan har lokacin nan.
Mama ke ina kikaji wanan zancen don Allah kuma har in gaskiyane mu meye ruwan mu cikin zancen su suka sani da wanan ai bamuba.
Wallahi A bakin Shafa shafa makirace tasan komai amma ta iya rufe muna haka kuma salma da kanta ta fada da Alh ke mamaki ya tsure yaron shine yake fada mai gaskiya.
Kasan Niger ko, ko mali don suma kasan wajene ai, ji sauniya ana maki zancen US yana aiki under UNICEF nefa ashe kingako dole hankalina ya tashi ai don ko yannan ku maza basu iya samun wurin nan balle mazajen ku da basuyi wani karatun kirki ba.
Jikin Aishace ya fara sanyu don ta fahinci me uwar ke nufi itako Rukkaiya cewa tayi ko ma me yake ai baikai mazan namu wayewa ba tunda har yanzu a babur yake yawo a gari.
Rukkaiya kin kuwa san me mama ta hango a nan dan kwanaki kadan zakiji cewa zahra da mijin ta sun faso gari wata kilama har yafi kowa.
In ma zancen nan gaskiyace ko a yanzu yafi kowa don mahaifinshi shahararen mai kudine da yake zaune abuja ashe duk bat da sawu yakeyi a nan din.
Haba mama wallahi biri yayi kama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login