Showing 303001 words to 304363 words out of 304363 words
don aikina nan kada ya tsaya ga kuma ginan gidan ki Dije naso ace angama kafin nayi tafiya ki koma ina nan .
Washe gari bai tafi ba saida yaje yayi sallama da Abba dasu ummah yayi masu alheri mai yawa ta bajinta ya tafi hannatu kuma a ranan ta bugo min waya zata shigo garin don jos suke zama da mijinta inda yake aikin koyarwa a can jami,an jos din.
Zuwanta yai min dadi sosai don ta debe min kewan wucewan master kwanata biyu a gidana bata fita ko ina ba saiga na ukune ta shirya ta tafi gidan yan uwanta.
Ta kwana biyu kafin kuma ta wuce kauyen mijinta can ma tayi masu kwana biyar ta dawo kamar dawowanta nake jira a daren nakuda ya kamani mukaje asibiti da ita da dije banfi min goma sha ba Allah ya saukeni lafiya.
Na haifo dana mai kama da ubansa sak kamarsu daya da Amir da gani kaga jinin fulanin usuli mun kwana can saboda dare yayi da safe aka sallamoni muka dawo gida.
Sai bayan mun dawone muka bugawa ummah waya ina sanar dasu mamaki tayi don koda dare munyi waya lokacin na dan fara jin nakudan.
Na samu barci a lokacin ya bugo min waya ganin shine hannatu ta tayar dani tana miko min wayan na karba shine yake kirana da vedio call.
Na dauka abinda na fara nuna mashi fuskan yaron dake barci yana nade a cikin showel fari da karfi yace what zahra kin haihu ke nan ashe gaskiyan dije datace idan na wuto daku zaku wahala har nake ganin laifinta ta hana min matata.
Kafin can yace me muka samu nace baby boy nima na samu babana yanzu yace Allah ya raya muna baba a cikin sunna na amsa da amin kafin ya koma tambayata bana jin komai ko a jikina ?
Lafiya kalau nake gaskiya kuma ina shan magani ok a debo ganyen tumfafiya a dinga dan gawa yaron jikinshi dashi da mankadanya kindai san yadda mukewa yarashi a nan na amsa da eh Allah ya raya muna baba Ali custom akan tafarkin addinin islama na sake fadin amin.
Washegari yan uwa da abokan arziki suka cika gida suna zuwa barka wanda hakan ya zamo min bakon abu don can bai mutum biyu ko uku dake shigo min ba idan na haihu.
Sai nan na gane dadin haihuwa a gida din yadda yan uwa suke cika gida suna kuma aikawa jariri adduan fatan shiruwa da more rayuwa a gareshi.
Sati ya kewayo aka rada wa yaro suna tare da yanka anci ansha yadda ake gudanarda shagalin suna bisa al,adan malam bahaushe inda yan uwan haihuwan master sukazo don halartan bukin sunan yaron nan da yawa suka sansu suka kuma san a yanzu master ya wuce raini a wurin kowa.
Idan nace dake su Anty Aisha da Rukkaiya sai gwaggo shafa dake uwar buki sune a tsaye a sha anin kada kiyi mamaki balle iri didiman da sukaga anyi tun suna diba suna boyewa duk da ana fada min nace su kyale kowa na dan lokacine ai abin.
Da zasu tafi kuma nabi kowan su da abin arziki aka kaisu gida duk immani ya kashesu don sunsan in sune ba zasu iya daure in shige masu gaba ba yadda su na barsu suna min komai a lokacin kuma yadda sukaga dama.
Duk yadda master yayi kada a samu matsala da inna a lokacin sha,anin hakan bai yuyuba don saida inna ta aiko nan gidan wai a basu nasu naman da aka soya.
Nasan yadda ya tsara abin don saida ya fada min komai ga yadda za ayi hakan dayace din kuma nasa akayi komai ankai gida mu ankai gidan inna amma saiga Asmau a cikin dare wai inna ta aikota ta karba.
Nace bamu kasa komai da ita ba a nan don ankai maku naku a can ai so ba ruwan ku dana nan nagani amma dai bari a dan debo maku wanda ya saura don ni ban ajeba a nan din duk yan buki sunci abinsu.
Bansa metaje ta fada ba sai ga inna din ta dako muna sammako a gida fitinanta ya tayar damu da cin mutunci harda zagin iyayyena tana kiran yan uwana da mayuwanta .
Hakan ya fito dasu Salima daga dakunan su har hjy murja aka taru ana kallonta ganin bakin fuska baisa ta fasa ba saida Dije tace ke kan yar da wanan halin naki Rashida.
A gaban yan uwan haihuwan danki kike tonawa kanki asiri kin dauka wani kike tozartawa a hakan suna maki kallon mahaukaciya a hakan.
Lokacin ta fara bin yan fararen yan matan uku da kallo kafin ta juyo kan ita hjy murja din sai taga ta muzanta a gaban su lokacin hjy murja ta fara magana tana fadin.
Wanan gaskiya baidace ba ace ana fadan nama a gidan dan alhaji dake da dukiya shanu kamar ya kashesu wanan gaskiya abin kunyane a wurin mu fulani idan sunji.
Kame kame ta farayi tana fadin na fada maku fadan nama nazo nazone don wanan yar rainin wayau data algaje min da tana kokarin maidashi danta don samu wurin.
Guntun tsoki Salima taja ta juya zuwa ciki haka suka barta nan da guda guda niko ko lekowa banyi ba don nasan suna gidan a lokacin .
Kwanan su uku damu suka juya abinsu zuwa Abuja suka barmu nan gusau din nima dana kwana biyu yace mu shirya mu koma Abuja da yara don gidan na can yagi girman biyun wanan da muke ciki.
Nasan dai bai wuce umurni Abbansa ne hakan don abinda inna tayi a gaban iyalinshi suka gani zaisa yai masa magana a kaina da zamu tafi na roki Abba da har ya koma nema Abuja din kan zanzo dasu ummah tunda yara suna hutu.
Hakan ya bani daman komawa da Ummah Abuja daga lokacin don master yace a nan su kannena zasu tsaya suyi karatunsu shi zai dauki dawainityar komai yanzu.
Wanan ya jawo fitina a gidan mu sosai don mama tayi fitina tayi korafi amma Abba ya nuna shi ba ruwansa in itama zata dawo nan din ne ta zauna aisai ta dawo.
Taga ba zata iya barin yaranta dake aure a zamfara ba ta koma Abuja da zama zasu sha wahala idan bata kusa dole mama ta hakkura ta zauna a nan zamfara don kawai duniya ta juya mata a yazun .
Ta haka rami ya fada da ita a lokacin tayi data sanin dawowa arewa datasa Abba yayi damu dasu gaba daya ta manta cewa haka kaddaran yake muna a rubuce.
Inna ko wanan rashin mutuncin da tayi a gaban iyalin Abba ya zama mata data sani a yanzu don dan abinda take samu yanzu da kyat na iya shawo kan master ga kuma Asmau din mijin yaki.
Aishane zuwan mu Abujan nan ta hadu da wani suka shirya akai masu aure kafin mu dawo din nan bayan auren ta da wata uku muka bar Nigeria da yaran mu uku muka dawo nan inda master sai ci gaba na alheri ke samunshi a yanzu.
Wanan shine labarin tumfafiya uwar kwankwamai don na yarda master lamarin shi a tumfafiya sirin nasa yake mu daraja duk wani abin alheri da muke ganin yana bibiyan rayuwan mu wani lokacin alherine a garemu ma,assalam nagode daga zahra US yar , , , , , , , state.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YA ALLAH KABA BABY ZAHRA LAFIYA YASA AIKIN NAN DA ZA AI MATA GOBE NA KODA YAZAMA SILLAR SAMUN SAUKINTA YASA YAR TA MORIYACE AMIN NA ALLAH SU TAYAMU DA ADDU,A GOBE NE ZA A SHIGA DA ITA AIKIN ALLAH UBANGIJI YASA AYI CIKIN NASARA AMIN MUN GODE .
SAI MUN HADU LITTAFIN MAI ZUWA MAI SUNA (KARAN DAFI)