Showing 231001 words to 234000 words out of 304363 words

Chapter 78 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33326

fadin.
Wai zahra meyasa yanzu kike son mayar da kanki yar kauye ne ji wanan shigar da kikayo zuwa wanan wajen kin kyautawa kanki ke nan duk kin koma wata bagidajiya yanzu dake.
Kai Anty Aisha me shigana yayi mijinane fa ya dinka min su don haka dole in saka ji don Allah ke wakikafi miji idan ana magana saikiyi kokarin jefowa mutane zancen miji mikin ki bakauye da bai san komai ba don Allah ja can kina zubarwa mutane da aji kawai.
Rukkaiyace ke fadin hakan a hasale mutum ma ai sai yaji kunyan nuna ta yanzu hjy dake tsakiyansu ta fada dama jira nake tasa baki in fada masu magana don nakai wuya.
Ba sai nayi wani shiga ko nuna hali za a san cewa niyar Abba bace don jini ya rigada ya gaurayu da anta yanzu ko anki ko anso dole a lissafani a cikin yayan abba dai kuma ace ni din jikanki ce.
Wa zaki fadawa magana Rukkaiya ta fada a hasale don ma ita anty Aishan ce data tsaya wani maki magana indonni ki fito fiye da hakan bai dameni ba wallahi.
Nace koni hakan don na tsaya a iya inda Allah ya ajeni banje roko a wurin kowan ku ba kudin kuma ba fina kukayi da komai ko kunfini kuma bani bakin cikin da hakan saidai na kara godewa Allah na.
Wanan ya jawo hankakin mutane a wajen don har su gwaggo shafa suka jani ita Rukkaiya bata bar zancen ba sai fada min bakar magana mai cin zuciya takeyi.
Haka aka tashi baram baram da akazo gida ana magana kuma mama ta dinga daga murya sama tana fadin maganganu munana akan mu jin hakan yasa ummah tace dani bukin ya isa kada ki dawo jibi tunda abin hakane.
Jin hakan Tani da hannatu sukace wa ummah idan anyi min hakan ba ai min daidai ba ai Allah bai raba daya ba dama ke in gajarce maki naga abubuwa ba ga yan gida ba baga yan waje ba saboda ana min kallon matar tallaka ko yaushe.
Bandashi balle nabawa wani yaci a karkashina hakan kuma bai hana inbi yan uwan nawa ba haka kuma na dawo gida cike da bacin rai yaushe ne zanyi farin ciki a rayuwanane wai.
Ba kowa yaja min haka ba sai mahaifin mu daya nuna nida uwata bamu da muhinmanci a gareshi a gaban kowa zai nuna ra,ayinshi na wariya don abin ba a iya boyeshi ma.
Balle yanzu daya kafa min doka da Allah ya isa ga duk wanda yabani wani abinshi don kawai bacin rai dayayi dani kan wai na nace Ahmed nakeso da akai min kazafi kuma na hakkura na zauna dashi hakana.
Duk kuwa da gallazawan da mahaifiyan shi ke min a fakaice amma naba kaina hakkuri bantaba kai karan hakan a gida ba ina zaune ina hakkuri da duniya da abinda ke cikinta.
Wanan fitinan yasa ranan ina kwantawa nayi mafalki wai ina zaune gidin iccen tumfafiyan nan na gidan nayi tagumi sai kawai naga Ahmed a gabana ya baiyana.
Hannu ya miko min na dago kai na kalleshi ganin hawayen dake bin fuskana yasashi kada kai ya mikar dani tsaye maimakon inga munbi hanya shiga gida sai naga ya nufi cikin tumfafiyan nan dani saiga wani haske fau ya baiyana ya kashe min ido a daidai wanan lokacin na falka ina salati.
Yana gefena ya zabura yana kiran sunana tare da fadin ke zahra lafiya ko mafalki kikayine wai yana lalubo torchlight din shi ya haska min hawayene fam a fuskana ke nan hawayen da nakeyi a cikin mafalki har a fili ke nan.
Ga kukan uwargarke nan mai ban tsoro dake tayar min da tsikan jikina tanayi a lokacin hakan yasa na dan koma gefen shi na kara lafewa ina sauke ajiyan zuciya.
Wani lokaci mafarki yakan zamo gaskiya saidai mutum ya kula akan abinda yake zama kamar bushara agareshi idan yai mafalkin dashi don akwai wasu dake gane cewa wani abu zai faru dasu idan sunyi mafalkin dashi dolene sai wani abu ya faru da mutum a lokacin.
To nima dai hakan nayi tunane don in baki manta ba lokacin da nayi mafalki da uwar garke da wanan tumfafiyan saida nayi ciwo sosai a baya yanzu kuma gashi na sakeyi wanan ne ya daga min hankalina tundai da naji kukan wanan dabban mai firgitarwa a lokacin sai na kara shan jinin jikina.
Yayi min tambayan duniya ban bashi amsa ba yasa ya kyaleni saida safe ya kara tayar da zancen gareni ya tambaya wai me kikai mafalkine ya daga maki hankali jiya ?
Shiru na sakeyi yace oh yanzu na gane kinyi mafalki ke nan dani cewa na mutu ko shine baki son ki fada ya zama gaskiya.
Jin hakan yasa nayi magana nace a,a wallahi nidai kawai mafalki da wanan akuyan da kuma dan iccen tumfafiyan nan na gidan nan shine banso don yana zama min matsala idan nayi.
Au kema kina mafalki dasu ke nan ashe na dauka ni kadaine nake mafalki dasu ai a gidan nan don in fada maki gaskiya duk abinda kikaga inayi wanan abin yasa naki yarda mu hadu da mahaifina har yanzu don abinda akai masa a kaina har yanzu bai fita a jikinshi ba duk akwai saura a jikinshi game dani amma an kasa gane hakan .
Gashi ba dama in fadawa wani wanan maganan sai a dauka shirmene kawai irin na kurciya nakeyi don hakane naja bakina nayi shiru saidai ban yarda mu hadu sai lokacin da abinda suka fada ya faru zan yarda in tsaya dashi din.
To shine ko Dije ba zakaiwa bayanin haka ba ita zata fahince ko kowa bai yarda da hakan ba nasan ita zata fahinci me kake nufi shiru yayi na dan lokaci kafin yace wai zahra kodai kaddaran mu dayane dake dama ?
Kaddara kuma kamar yaya kaddara mu daya dakai dama ki barshi kawai ya fada ya mike zuwa kitchen ya dauko ruwa ya dawo yana sha kafin ya zauna yace.
Cikin Matan da mahaifina ke aure akwai muguwa a cikinsu duk da bansan su ba amma ana nuna min a mafalkina cewa sune matar farace gajera mai dan jiki tana da tsaga irin na fulanin asali a jikinta.
Abinda kawai zan iya shedata ke nan a fili dashi ke kadai na fadawa wanan zancen don ina yawan ganinta sosai a cikin mafalkina don haka nake son na shiryawa tunkaranta kafin mu hadu.
Shiru nayi tare da nazarin maganan shi a cikin zuciyana haka kawai zancen gidan mu ya fado min a rai nan nake bashi labarin abinda ya faru a wurin buki dani.
Baiyi magana ba saidai idon shi ya ja sosai a lokacin kiran wayanshi ya watsa mu wurin don nadaga na tafi dora girki a lokacin shi kuma naga ya fita bayan ya amsa wayan.
Yadda ya dawo a cikin damuwa yasa ta kasa tunkaranshi a ranan do baiba da kofan da kowa zai shigo wurin shi saboda ya rufe dakinshi.
Washe garima sai rana sosai ya bude dakin ya fitp don neman abinda zaiciwa cikinsa don yunwa daya dameshi saboda rabonshi da abinci tun safiyan jiyan da sukayi karin safe a gidan ubangidanshi da yanzu tsofa ya kamashi sosai kuma arzikin ya tafi baida komai sai hakkuri da tawakkalin ubangiji.
Yaji dadin zuwan yaronsa a lokacin wanda da kyat ya ganeshi koshi don zurian yaron daya bari akai mai kwatance da Amadi din ya ganeshi har yake tambaya ina dan yake yanzu ya daina ganinshi .
Amma wani lokaci mai tsawo tsohuwa tazo ta fada mai zancen aurenshi balafiya bai samu zuwa ba yadda yaso anyi auren kuma yana garin nan saidai bai zama garin yanzu don yana karatune a zaria.
Falon ya fito babu kowa dan haka ya nufi wurin aje abinci nan ma babu komai da aka aje a lokacin cikin mamaki yake kallan kofan part din matan nashi.
Kafin ya maida kallo a kofan kitchen inda yaji motsin fitowa hjy murjace tafito daga kitchen din take gaidashi don ganinshi datayi girshi a lokacin gabanta.
Da sauri ta nufo dinning table din tana bashi hakkuri da bata san ba a girka abinci ba don barci ya dauketa data tashine Indimi ke fada mata ai ba a girka komai ba gidan shine ta fito yanzu ta girka masu yayi hakkuri.
Kai ya gyada alaman gamsuwa da zancenta don yasan hjy taki girkine saboda tana zaton tare sukai tafiyan a lokacin, abinda bata sani ba kuwa shine.
Suna cikin Abuja ya ajesu wani gida nasa dako hjy bata sanda shiba ya sayeshine don ita hjy murja din ta zauna a ciki sai kuma yayi shawaran hadasu wuri daya don tasan irin illan da tayi mai a baya.
Wanan zaton nata da yake mata shine kuwa shine yasa tabada umurni ga Ladi mai aiki akan kada ta girka masu komai na karyawa a gidan don tasan diyanta ba matsala bane dan ba damuwa da abincin sukayi basu.
Zama yayi ya karya gurguje zai fitane a lokacin ta fito don taga ya zasu kwashe da yunwa a gidan sai ta samu yan matan hjy murja din suna kwashe kulan abincin dayaci ya raga zuwa part dinsu .
Hakan yasa ta gane sun gitka abinda zasuci ke nan ashe tarkon data dana baiyi amfani ba don inda dane tace kada a girka hjy murja bata isa ta dora tunkunya a gidab ba da sunan wani dahuwa.
Amma yanzu hakan na kara nuna mata cewa powern ta ya fadi sosai a gidan tunda har hjy murja zata iya yin abu bada izinin ta ba.
Hanya fita daga falon ya nufa kamar bai ganta ba a lokacin mamaki bai kare mata ba don haka a fili tace dashi Alh wai fita zakayine dama bai juyo ya daga mata hannu kawai alaman ta dakata kawai daga fadin abinda take son fada a lokacin.
Yasa kai ya fice daga gidan tabi bayan shi da sauri kafin ta isa inda yake har yashiga mota aka ja suka fice gaba daya daga gidan.
Mun gama cin abincin dare muna zaune kowa hankalinshi na a naji muryan shi yana fadin Zahra in Allah ya kaimu gobe zanyi tafiya zan dan kwana biyu a can kuma.
Kaina dago ina kallon shi ina fadin inane zaka yace kinsan garin da ake cewa Illo to can zani wurin wani zai ketara dani zuwa kasan Benin republic akwai abinda zamuje yi a can.
Ashe tafiyan mai nisace da har sai kun fita kasan nan yace eh zan tafi na duba yanayin kasan ace ana samun abinci da sauki a wuraren don ina son na dan kara habaka sana,ata ta saida hatsi da nakeyi.
Ubangiji Allah ya bada sa,a da rabo na alheri yasa a dace da nasara ubangiji yace amin nagode da adduan ki gareni zanje in fadawasu Dije don asubanci zamuyi mu bar garin nan goben.
Da goben kuma nake son na roke zuwa gida nagaida dasu don na kwana biyu banje na gaudasu ba ki tafi idan Allah ya dawo dani lafiya kuma sai mu koma tare.
Ya mike ya tafi ya dan dade a can din kafin ya dawo hakan yasa na gyara wurin da mukaci abinci din har na mike na shiga kitchen na hada kayan miya na fito don ina sonyin asubacin girka mashi abinci kafin ya tafi duk da yace asubanci zasuyi ga tafiyan don haka ba lalai bane ya samu wani yaci abincin ke nan.
Karfe hudu na tashi na fara soyan dankali baiji motsina ba har na fita na gama don ba yawa na kwashe sai gashi ya tashi sallah bai ganni ba dakin ya fito nema shine ya samu ina kitchen a lokacin .
Ban yarda ya bar garin ba saida ya karya don koda ya tafi bai karya ba ki gane cewa ke mai karatun labarina hakan ba halina bane waina gjrka abinci don yaci kafin yayi tafiya.
Amma haka kawai naji yana da bukatan yaci abinci tunda tafiya zaiyi mai nisa suka tafi yana min godiya na dawo part dina na kara rufewa dije kuma tashige nasu part din.
Na gama na shiga na gaidasu su Aisha na juyewa sauran abincin daya raga din na jawo kofata na rufe nafice zuwa school.
Munyi lactures mun fitone nake fadawa hannatu zancen tafiya amma kinsan me hannatu ni sai naji zuciyana bai bani ba ga tafiyan nan na master don bai taba tafiya naji hakaba a raina.
To kiyi sadaka koma meye kike tunanen zai faru Allah ya mayar dashi alheri gareshi nace amin idan mun fita ki tuna min nabada sadaka ga almajirai.
Da maka tashi batama tuna ba ni naga almajiri da dan jagoranshi na saka hannu a jakata na dauko dari biyar na mika mashi.
Ya fara fadin bayan dan jagoran ya fada mai abinda na basu yake fadin sarkin da ar sarki ya karba ya biya maki bukatun ki na alheri.
Sarkin da akaiwa ya sani ya shige maki gaba ga bukatun ki mayafiyan mu Allah ya tsare ya kare ya dawo muna dasu lafiya.
Kallon juna mukayi lokaci guda da hannatu kafin mu amsa da amin baba mun gode muka tafi shima ya doshi wani wajen mashin muka tare muka hau nida ita kowa ya nufi gidansu.
Banje gidan namu ba don nasan ummah zatayi min fada idan nace da ita baya gari yayi tafiya yasa na fasa zuwa saboda na tuna da fadan da tayi min ranan



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/19, 8:05 AM] Mmn Bibo: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣8️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Suwaiba wacece kuma suwaiba dije suwaiba da daka sani yar gidan sidi wani kallo yaiwa dijen na baki san ma me kike fadi ba tsohuwa kafin ya mike zuwa hanyar fita daga gidan.
Bata kyaleshi ba ita a zatonta sakina zaije yayi lokacin ta biyoshi tana fadin nace kada ka aikata hakan akan yar mutane jjn hakan yasa yaja ya tsaya ya juyo yana fadin Dije koma ciki ni abin miya zanje in sawo mata yanzu na manta bansayoba na dawo gida.
Ja,iri ni har ka daga min hankali ga banza yayi murmushi tare da fadin ko kare ya cijeni aiba zan saki zahra ba don ta gama min komai a rayuwana da inna nake wanan zancen tunda muradinta ke nan a kanta kuma na tabbatar da zata iya aiwatar da hakan akan ka.
Ashirme ke nan Dije ki koma gida fita zanyi yanzu saina dawo zan shigo muyi maganan dake ya fada yana tare abin hawa ya wuce ya barta tsaye tana zancen zuci.
Allah ya dorawa mata son jikan nata fiye ma da yayan nata biyu data haifa don hakane bata son abinda ya samu rayuwanshi ko kadan kalaman yarta Rashida akan jikan nata yana daga mata hankali shiyasa a yanzu bata dagawa yarta kafa a zancen jikan nata ko kadan.
Lokacin ina daki bansan duk abin dake gudana ba don wayan da ummah ta bugo min a lokacin ya dauke min hankali inda take fadin bayan mun gaisa ashe mijinki ya dawone shine baki sanar muna ba.
Ke wani irin sakarcine gareki wai mahmah in ba don yazo gidan nan ba ashe da ba zaki kira ki fada muna ba ke nan wallah ummah yanzu nake shirin kiranku in fada maki.
Ta katseni da tsawa tana fadin rufe min baki shasha ga dai Tani nan zuwa ta kawo maki sako saura kada kiyi amfani dashi idan ankawo maki din ko wurin sakarci har ki bari ya gani.
Fuska na bata duk da ummah bata ganina don dajin hakan nasan ko sakon meye a lokacin kina jina ta fada na amsa a sanyaye da inaji ummah .
Tace kuma mijjnki yazo dan albarka ya kawowa yaran nan tsaraba harda muma dazun da rana nace ni bani gida yanzu na dawo aiya fada kina makaranta yanzu ke don baki da hankali har kika fita zuwa school yau mijinki yaje ya dade haka bai kasan ya dawo kice kinga wurin fita ?
Shiru nayi saida tagama fadan tayi min sallama na amsa muka kashe wayan ina sauke ajiyan zuciya a daidai lokacin da Tani mai aikin mu ta shigo gidan da abu dunkule a cikin hijjabinta.
Saida muka gaisa tayi min barka da dawowanshi ta fara min bayani kuma ta umurceni da in tashi in boye kafin ya shigo hakan nayi a gabanta saida na fitone take fadin tsaraba haka hardasu mama aina zata ba zata karba da aka kai mata sakon sai gashi ta karbe harda godiya.
Ban kaiga magana ba naji shigowanshi ya dawo hakan yasa mukayi sallama a gurguje ta fito tana gaisawa dashi cikin dan kame kame ya amsa a cikin nuna kulawa a gareta ta tafi ina fadin tayi muna godiya wurin ummah.
Kodana juyo na dawo na samu ya shiga dakin yana tsaye gaban kayan dake cikin leda ina shiga yakai zaune yana jawo ledan tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login