Showing 285001 words to 288000 words out of 304363 words

Chapter 96 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33354

ina yaran ta tambaya na nuna mata su inda yake tsaye a kan Abba duk suka kai kallonsu gareshi.
Saye yake cikin shadda ta maza mai tsada da take maiko shining din ta kadai zai fadawa mutum tsadanta a lokacin sai yar hulan dara baka itama mai tsada a kansa.
Ya dauki Amir a hannunsa ya goya Bananh a bayansa amma cikin hakan ya nuna bai damu ba kowa da abinda ya darsu mai azuciyan shi lokacin don dole tunanensu yaje bambam a kan mu.
Shigowan likitan ya sa kowa dakin natsuwa yayin da aka fara fita daga dakin a lokacin saidai banyi yunkurin hakan ba kamar da can baya da ake korani daga dakin ace anyi yawa.
Mamace sai ummah damu muka rage yayin da Ahmed din yakewa likitan bayanin abinda yakeson anyi sai likitan yace ko an raina da nasa aikin ne ake gani yace wallahi a a aiyayi kokari kawai dai ana son fita dashi din ne don ya samu hutu a can .
Amma idan ya kara samun sauki za ai hakan suka juya zuwa waje tare inda akarshe suka gane juna ashe sunyi karatu a secondary tare dashi dan wani mai kudine a nan zamfara aka turashi karatu kasan waje.
Shima ya fara sheda Ahmed din kafin yai mai bayani ya ganeshi nan tsohon abota ya tashi sosai a tsakaninsu har sukai musayan number juna jin ai kusan aikinsu daya a yanzu.
Fitansu yasa mama fadin Alh ga faten waken an dafa maka sai dai ba a samu alaihu ba yau haka nayisa tana budewa don ta nuna mai abincin.
A raina nace humm,umm, ashe har yanzu barkadon na mama yana nan dai ga Abba din wai tayi hakane kada hankalin Abba din ya koma kanmu tunda daga mu sai shi da itane kawai muka rage a dakin lokacin.
Amma kuma sai naji muryan Abban irin ta mai ciwo yana fadin mijin uwata ya sayo min kayan gwagwani da zanci insha ita kuma ga abinci nan ta daho min daga gidansu shi zanci yau ya fada yana kawar da fuskanshi gefe daya.
Saukin abindai da namu din da ba a so yau aka samu lafiya bana ita zahran ba don ummah kada ta mayar da zancen wani abu tace fada mashi dai hjy namun dai aka saba dashi ai.
Abba a zuboma abincin ne yanzu tunda likitan ya shigo yace eh mamata zuba min kadan ina budewa dan warmer din idon mama yana kai tana bi da kallo taga ko meye a cikin kulan na dafo.
Tayi tozali da hadaden abincin irin hadin ganye din nan na gwangwani na salad wanda zallah diyan icce akai amfani dashi da kifi na dan zuba masa kadan.
Da kaina nake bashi yana dan karba ina masa sannu a haka su Aisha suka fado dakin suka samemu wuri suka samu suka zauna ana dan hira jefi jefi har lokacin na fahinci akwai wanan akidar.
Ta halin kishi kyashi da hassada irin tamu ta matan hausawa da ake samu a mafi yawan gidajen muna hausa irin gidan daya hada mace biyu zuwa uku ko hudu.
Zaki samu babu komai sai zama na hassada da kyashin juna komai hadin kan gida wanan akidar kamar a jinin mu mata yake na kyashin wanda kuka hada alakan aurataiya da ita daya shafi dangantaka na auren abu daya.
Saidai a wasu gidajen abin kan danyi sauki sosai in daya ta kwanta ta danne nata tanayi a boye sai ki dauka ba wani hamaiya a gidan idan kin shi dan yadda ake ganin suna al,amura a tare din.
Niko yaya musa fa da yaya jafar suna wani kasa yanzun don ko a waya na daina samun su yanzun mu gaisa wanan abin yana damuna wallahi.
Cabdi wai yaya musan mu kike tambaya aikuwa yanzun zaki ganshi wanan dan buga bugan tun jiya daya samu kan motar Abba ya dafe ya shiga sokoto sai yau din nan daya dawone.
Shinema ya dauko mu aida tun dazun munzo babu mota a gida tana fadin hakan wani iri naji a zuciyana saidai na dake ban nuna komai ba a lokacin ga kowa sai cewa da nayi Allah sarki.
Ashe yaya musa yana kasan da rabon zamu gana dashi ke nan wallahi ya dade dana ganshi a idanuna zakiko ganshi yanzun ai tafada cikin rashin damuwa ashe hakan yayiwa mama a zuciyarta.
Kamar hadin baki sai gashi yayi sallama ya shigo dauke da Amir a hannunshi master na bayansu yake fadin wai ashe mutanen turan nannsun shigo garin nan basu fadawa mutane ba.
Da sauri na mike zuwa gareshi ina masa murna da haduwan mu nan muka shiga hira dashi da master dani kafin yace ai nasan wanan wajen sosai wallahi mukan je mama ai wuri dayane da inda Bisi yake aiki.
Cikin wani basarwa tace oh lalai amma da yake su bisi manyane ai wata kila ba zasu san juna tunda gidajen manya dabanne dana kanana.
Ai wurin nan ba wasu gidaje dasukafi namu girma nasan sa sosai kuwa ba dan lagos din nan ba ai yanzu suna a old side ne mu kuma muna senior quarters so muna haduwa sosai dashi a wurin sallah jumma,a kona idi.
Itace ma ta ganeshi ranan da muka fara haduwa dashi gaba dayan su daga mama har Aisha fuska suka bata Rukkaiya tace yanzu ana nufin mijinki babbane bisa ga bisi Zahra.
Ni dai nayu murmushi naji ya musa yace ke kauce wallahi wanan babban officer ne da turawa suke ji dashi kina ganinsa nan nima gun wani friend dina naji dan kasar Cameron da muke hira.
Don kinsan musulmai acan kansu dayane suna da kungiyansu ta musulmai kowa na sanin wani din basu da yawa sosai a can .
Dan Allah ka rufawa mutane baki hakana da wanan shirmen naku mutum yana kwance ba lafiya kai sai bakin zuba kakeyi a kansa kamar baka damu ba.
To mama kuma yanzu me nace don Allah fira kawai mukeyi na mijin zahra na can shine kuma laifi don Allah barin fita dama nazo inga jikin na Abbane kuma yana barci.
Ina waje saika fito officer ya fada yana nufar kofan fita daga dakin da sauri nace yaya tsaya mu gana zaka wuce kuma bari na biyoka kada dai kaje masa yawo da mota mama ta fada.
Bin bayansa nayi don duk banji dadin yanayin danaga dan uwa nawa ba sam don na fahinci akwai wani matsala mumuna a tare dashi dayake faruwa.
Yaya musa nasa masa kira don baisan ina ma bayansa ba a lokacin har ya tura hannu a cikin aljihun wandonsa na jeans daya dan kode sai wata bakar rigan t,shirt a jikin duk tayi dauda yana tashin tsamin dauda.
Ya jirani yana murmushi yace kanwata kinganki kuwa kinga yadda kuka koma kamar wasu taurari daga ke har mijin ki wallahi duk inda kuka bi dole a kalleku sau biyu.
Kingani ko kina mamakine don yaga wani irin kallo da nake masa lokacin na mamaki karara a fuskana nace yaya meke faruwa ne don Allah na tambayeshi kamar zanyi kuka a lokacin
Zahra ki bari kawai abubuwa ma da dama wallahi bari zamu zauna dake ai kiji amma nasan koma meye alhakine yake bin mu a yanzu amma sun kasa gane hakansu.
Me kake fadine yaya na sake tambayan shi muryan mamane naji a bayan mu tana fadin to sarkin surutu tunda ka mayar da kanka haka yanzu ni kazo ka kaini gidan Ashibi.
Gidan Ashibi kuma mama don Allah me zakije yi gidan wanan yar borin matan yanzu kuma kudin ku kawai take ci banza fa wallahi da sauri mama din tayi mai dakuwa tare da fadin kaci ubanka nine zakayiwa wa,azi.
Na gane meke shirin faruwa yasa nace to yaya saika dawo ke nan ma hadu yace to zahra harna juya naji yace don Allah ko kina da dubu daya ki ban na samu abinda na karya dashi.
Innalillahi na ambata a kasan raina tare da wani irin shock nace dubu daya kuma yaya me dubu daya zai isheka yi don Allah ?
Barin zo na juya na tafi na dauko jakkata na fito can na hango mama da Aisha suna faman zazaga mashi bala,i ya rugume hannuwan shi cikin bacin rai yana sauraren su.
Ban karasa wurin ba wanan yarinyar mai mun aiki na kira na bata takai masa naji tace dani wancan mahaukacin na gidan su hjy ?
What me kikace tace nace wancan mahaukacin mai shaye shayen na gidan su hjy ko eh shi kai masa kice injini na tsaya har ta mika masa naji raina ya kara baci sosai.
Shiko yana daga can yana dago min hannu irin na ya gode din nan sai ya dawo wasu irin hawaye naji sunzo min na kara gane da matsala dai kenan babba a gidan mu yanzu.
Karfe daya yace zamu gidansu mu gaidasu mukayi sallama bani cikin walwala zuciyana a bace yake da abinda nake gani a wanan zuwan nawa gida.
Shiru nayi a cikin motan kafin shehu yace zahra na ganki da Musa ai kuna magana ina shigowa na boye kada ya ganeni ya tsareni.
Bari shehu amma akwai abindake faruwa dashi ko yace sosai ma kuwa ke bakiga alaman haka ba ai ruwane ya karewa dan kada bai gama wanka ba.
Ya dade da shiga wanan halin ba a kula ba sai yanzune abin yake baiyana sosai gareshi uwar tana nan tana yawon malamai wai hjy namuce tayi masa ya koma haka.
Kiji wani bata don Allah batayi masa ba tun yana karami sai yanzun daya girmane zatayi masa Master ya fada ba tare da ya juyo inda shehu din yake ba ya bashi amsa yana kallon hanyar unguwan nasu yace.
Yarima fa yayi kokari sosai da jahan nan amma ku baku gane hakan sai zaginsa akeyi wai bai maku aiki ba kasan halin mutane mu ba godiya.
Wai yariman bakura kake nufi yace kwarai kuwa shi yayi aiki a fakaice amma an kasa gane hakan sai zaginshi da mutane keyi kawai muna ji a kafafen redio ai.
Har suka kai suna hiran siyasa ina zaune nida dije da bamuce komai ba kowa da abinda ke zuciyarshi muna shiga unguwa tasu tun daga nisa na hango gidan nasu yadda ya yakuce a rashin shi na yan shekarun nan da baya nan.
Ikon Allah kangon mune ya kara yakucewa haka kamar ba mutane zaune a cikin gidan nan yanzun kai jama,a ta fada cikin takaici.
Muka sauko a motan malam tani yana zaune ya kara tsufa sosai yanzu ya kuro muna idanu yana son yasan kosu waye sukazo.
Dije ta taka zuwa wajen sa tana gaidashi nan danan mutanen unguwa suka shedamu aka fara taruwa a kan mu ana muna sannu da zuwa, nidai da kyat nake iya amsawa don abinda ke damun zuciyana lokacin.
Gaba dayan mu muka dunguma zuwa cikin gidan muka samu suna barcin rana Aisha kuma tana school muke ta sallama can Inna din tafito daga daki.
Kanta babu dankwali tana fadin wai wake sallama hakane da rana tsakan nan sukai arba damu tsaye yana bin ko ina na gidan da idanu ta fito a lokacin.
A a a umma kune ashe kuna tafe Asmau Asmau ke fito ga su umma sun zo ta tasa yadda zatayi sai faman kame kame da takeyi a gidan lokacin.
Ta fito da wani tsohon tabarman dije dana bata tun na kwanciyan zafi waje danazo gidan naga tsumman tabarman da take amfani dashi lokaci.
Bai zauna ba sai zagayawa bayan da yayi zuwa wurin dabbobinsa yaga wayau babu komai ga iccen nan na tumfafiyanshi ya bushe yayi wani irin ja duk wurin tarkacene da sauran kayayyaki yashe a kasa.
Ido ya runtse ya juyo ya dawo zuwa cikin gidan wai bisashe kaje duba ai babu ko daya tunda sukai ciwo na kwashesu na sayarwa rumjawa dasu.
Baiyi magana ba sai dijece ke fadin wai dabbobin nasane kuka sayar Rashida akan me kuka sayar mashi da bisashe bai baku bakin haka ba.
To me zayayi da kudinsu yanzu inji Asmau take ba dije din amsa a hasale kekan kin biyo halin uwarki da battalancin banza shekara nawa yaron nan yana kiwo abinsu sai a yan shekarun nan da bai garin kuka sayar masa da abu.
Dakinta ta leka ta ganshi a gyare saidai da alama na cikin dakin ya canza fasalin dakin muna zaune nace sallah zanyi don lokacin yin sallah yayi.
Part din mu ya nufa ya shiga yana dan dudubawa kafin ya fito yanawa she bayanin yadda za a gyara ginan ya koma don wai a nan dije zata zauna.
Don tace bata zama sabon gidan mu ita inda mijinta ya mutu ya barta take son ta mutu junsan matan hausawa da wanan camfin a zuciyarsu.
Sallah nayi a nan tsakar gidan na koma na zauna bayan na idar din ina bin ko ina na gidan da kallo kamar ban taba rayuwa a cikinsa ba a baya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/14, 7:58 AM] Zainab Idris Makawa Writer: .🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣7️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,


Aje yaran yayi ya fita sallah ya barmu nan da inna sai faman kame kame takeyi ita da yarta ga Dije wace ido kawai ta zuba masu tana kallon su domin ranta ya gama baci da jin wai an sayar masu da awakansu duka ga baki daya .
Saida ta idar da nata sallah ta juyo ta fuskanci inna tace Rashida baki da tunane baki kuma da tausayi balle imani da har kika iya daukan kayan yaron nan kika sayar haka cikin rashin tunane haba son Allah.
Wanan halin naki same yayi kama ace mutum haka zube baida lissafi idan shi dankine kina kurin abinsa nakine ni nawa alhakin ina zaki kaishi tunda kinsan ina da hakki ciki kuma ba baki nayi ba.
Umma lokacin auren Asmaune fa na sayar dasu na kara kudin ga sha,ani kinsan buki da cin kudi yadda yake dije din ta tareta da fadin.
Auren Asmau Asmau tana da gadon mune ko ita ina nata gadon da ubansu ya bar masu shi nasu ba na sayarwa bane a fitar da ita kunyar kanta ba ?
Wai Dije kina ta fada haka don kawai inna ta sayar da awakai ta kara ga aurena shine kike tayarda jijiyan wuya haka tun baki huta ba ?
Koni a turai din wai baki waye bane kika dunkulo kika dawo haka sai sababi a bakin ki kamar kina jirace da mutane dama haba dai don Allah don inna ta sayar da abinku ta fita kunya shine me don Allah dai ?
Ubanki , nace ubanki da wayewa irin naku ai gara in zauna haka bakauyata da na ci hakkin wani yafi min sau dubu don baku dauki cin amana a bakin komai keda uwarku yasa ki har kike kokarin fada min maganan banza yanzu ko ?
Bakin auren naki da kikaki zama dame ya karaku yanzun bayan maida mutane baya da kukayi ai cewa kuke kuda uwarku kuma gadon ku yana can kun baro a Naija meyasa baku koma kun sayar dasu ba azo ai maki auren gatan dashi ?
To ki kama kanki tun bakiki baijawa uwarki bacin ran dayafi haka ba a gareni don wallahi yanzu sai in saba maku kan wanan zancen daga ke har uwarku da bata da hankali.
Ke Asma tashi tai zuwa inda zakina don Allah kada ki dauko muna magana wurin katobaran ki yanzu kuma cikin gwanewa da tantiranci tace ni ai bakinta ko tayi tasan ba zai kamani ba tunda ba haihuwana tayi ba.
Amma yana kama uwarki ko dan Allah dai Asma kitai zuwa inda zakina nace kada ki tsaya kuna tonon asiri da umma kuma sai Dije din tace tonon asiri yafi wanda kikai muna.
Ki kama dukiyan yaro ki sayar bayan ya turo maki da kudade masu yawa da zakiyi sha,anin bukin bayan na gado daya turo maki da wanda zaki sauran kayan amfani amma haka bai naki ba Rashida saida kika kama muna dabbobi kika sayar wai da sunan wanan bakin bukin naku da baida rana.
Dije don Allah dije ki bar wanan zancen tunda an riga an sayar dasu ta juyo tana fadin ki bari yar nan abin akwai cin rai da kuma wullakanci a cikinsa.
Ace duk wahalan da yaron nan yayi da abinsa ba a barmasa ko daya ba wai an kwashe an sayar kan zancen bukin mara kunyar nan ai abin akwai ganganci a cikinsa.
Dije ku tashi muje tun ina waje nake jin muryan ki gashi ko abinci bakici ba don ko ruwa ban tsamani an baki da kuka shigo shine ya shigo yake fadin hakan daga bayan mu.
Ina take da tunanen yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login