Showing 105001 words to 108000 words out of 304363 words

Chapter 36 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33352

mommy dana kasa fassara manufabta a kaina yanzu.
Daki na shiga na fara gwada kayan a jikina gaskiya kayan ba laifi ba dinkin ba ba kayan da akaiwa design din ba duk ko wani abin a yabane.
Tunane yazo min bayan na gama ganin kayan shin me wanan matar take nufi dani hakane abinda ban yarda dashi ba shine dole akwai manufa ga zuciyan wanan matar a kaina.
Saidai ban gane me take nufi ba take min hakan dole dai nasan akwaishi amma zan bita a hankaki har in gano hakan inda na godewa Allah shine banda rawan kai da zai hanani gane hakan da take min din.
Gashi ga lissafina saura kwana biyu mu wuce zuwa kano kamar yadda ta fada min a baya dole gobe in bayar da kayan da zantafi dasu a kara wanke min a goge hakan yasa na lalubo wayana na kira ummah ina fada mata komai daya faru.
Ki dai kula da kyau kuma ki natsu ki kula da kanki banda rawan kai Allah ya tsare tunda ba yadda zamuyi don Alh ya tsaya mata nan kuma suna ganin kamar wani munafuncine na kulla ga yin hakan.
A sanyayyena amsa da toh ummah in sha Allah zanyi yadda kikace min din muka dauko hiran kanne da ita har ta basu wayan na gaisa dasu din .
Saidai na yanke a raina muna dawowa zan koma gida don nagaji da zaman Abujan ba yan uwana da mahaifiyan mu a kusa saboda hakane nake zama a takure gashi ba wani sabawa nayi da mommy din ba sosai kamar yadda na saba da mama a baya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣5️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Makewayin ba laifi don an shafeshi da siminti gashi da gani yana samun kula wajen tsabtaceshi ko uaushe haka kuma baka ma dauka gidan marasa karfine kake.
Tufafin jikin shi ya fara cirewa kafin ya watsa ruwa ya dade yana cuda jikin shi ya kuma ji dadin ruwan sosai ya kwara ya fito take yaji wani iska mai sanyi yana dukan jikin shi.
Da dan sauri ya karasa wanan sakin da Shattu ta nuna mai ya shiga bai sauya kayan ba gadon da ya gani a dakin yakai zaune a kai.
Sai lokacin natsuwa ya fara zuwa mai ya fara bin ko ina na dakin da kallo babu wasu kayan jin dadi a dakin sai wanan gadon da wani mattacen kujera mai zaman mutum biyu kawai a dakin.
A hankali yakai kwance saman gadon sai lokacin ya gane cewa saman gadon kara yake zaune ashe saidai yadda yasha gyara ba zaka gane cewa gadon karane hakaba.
Tunane ya fara yi kota ina zai farayin abinda ya kawoshi wanan kasan don yadda yaga garuruwan yana da wuya a iya gano mai mahaifinshi haka kai tsaye.
Dan dama saukin da yaji shine cewan da tsohon yayi zaibi masu irin sana,an mahaifin nasa a baya ya bincika masa.
Yana cikin wanan yanayin na tunane har barci mai nauyi ya daukeshi a wurin na tsawon lokaci yana kwance yana barcin gajiya don akwai gajiya sosai a jikinshi gaskiya.
Karfe biyu ya falka koshi ba don yaso ba sai don lokacin sallah dake ratsa jinin mai kula dashi da duk lokacin yayi zai tashi kome yakeyi yayita a cikin lokaci wanan ne ya falkar dashi daga barcin nasa a lokacin.
Shatu kawai ya gani a tsakar gidan tana yan aikace aikacen ta a lokacin ya nufi ban daki ya kewaya ya fito ya fara alwala don sallah.
Yana dakin zaune har akai la,asar ya fito waje ya samu itama Shattun tana daki lokacin hakan yasashi fita wajen gidan don dama maza ba a san su da zaman gida ba su sai mata.
Sannu a hankali yake takowa daga inda yake tsaye kofan gidan bayan ya gama bin unguwar da kallo yana nazarin wurin can ya tako zuwa inda dabbobin gidan suke killace kamar yadda ya hango a sauran gidajen unguwar suma sunyi.
Nan ya tsaya yana karewa dabbobon kallo yana mamakin irin kiwon da suka samu suka cika haka sukai kyau da dadin gani kafin idon shi can ya sauka kan wata akuya dake kiwo a cikin awakan dake cikin garken.
Uwargarke sak yagani a idonshi saida abin ya firgitashi lokaci guda ga kuma akuyan na kallon shi ta tsura mai ido kamar yadda uwargarke kan kafa shi idanu tana kallon shi din wani lokaci.
Kasa boye mamakinshi yayi don saida ya furta a fili yana nunata yace uwargarke ke nake gani ko gizo idona keyine ?
Yarona ka samu tashi ashe yaji an fada daga bayanshi jin haka yasashi juyowa yana fadin eh baba ashe barci na samu nayi tun fitowana daga wanka.
Ai hakan yana da kyau sosai gara dai daka dan samu ka runtsa din zaka samu ka dan walwale kadan gashi yanzu har kazo duban dabbobin mu.
Eh baba kiwon sun samu kula sosai gasu sun banje suyi kyau sosai gwanin ban sha,awa tubarkallah masha Allah.
Kazalika dana ai kiwo kula sukeso indai ana kula dasu ana basu abinci yadda ya dace sai kaga Allah ya tarfawa abin albarka kasan kuma mu filani ba a rabamu da kiwo ko da na kazane kuwa.
Ya dan murmusa har lokacin idon shi na kan wanan akuyan yana kallonta cike da mamakin haka a zuciyarshi.
Baba dama akuya sukanyi kama da junane ya tambayi tsohon alokacin da bai shirya hakan ba yaji tambayan ya fito a bakin shi lokaci daya ya furta hakan ga tsohon.
Murmushi mai sauti tsohon ya sake ya dora da fadin yaro mutane ma anyi su da kama balle dabbobi da halittansu duk iri dayane .
Sai kuma ya kawar da zancen ta hanyan fadin yanzu daga wurin abokina nake na soma tambayan shi labarin mahaifinka ko Allah zaisa a dace amma hakan bai samu ba don ya nuna min bai san wani wanda ya taba zama a wanan nahiyan na sokoto ba gaskiya .
Saidai zai saka bincike a kai shima ta hanyan tambayan mutanen su don shima wani tsohon mafataucine daya jima yana wanan harkan na sayar da dabbobi a kudu.
Sosai Ahmed din yaji dadin jin bayanin da tsohon ke mashi a lokacin nan dai ya kara kwantarwa yaron da hankali tare da bashi tabbacin cewa ya kwantar da hankalinshi muddin mahaifin shi dan kasan mambilane za a gano mashi shi in sha Allahu.
Suna wajen suna hira har akai kiran magariba abinda yasa su dagawa ke nan shi Ahmed din ya shiga gida ya debo masu ruwan alwala ya kawo masu.
Tare dasu akai sallah jam,i a masallacin unguwar suna cikin wa yanda suka dakata har a idar da sallah a lokacin bayan sun idar din suka nufo gida kai tsaye tsohon na gaba shi Ahmed din yana bayan shi.
Ya dade a zaune yana maimaita kallon photo don shi kanshi yasan yayi kama da wanan guy din sosai sadai kamar wanan din zai dan darashi da fari da kuma tsawo haka kuma ya dan fi shi yasir din dan budawa kadan.
A ina fattu ta sami wanan photon kuma wayeshi din na cikin photon da har yake da kama dashi haka kama ba kuma na wasa ba ?
Da badon yasan cewa shine dan fari ga iyayyen shi ba da yace shima wanan din jinin sune don kamarsu har ya baci sosai.
To a cikin dangi shi din dan waye da har bai sanshi ba bai taba jin wani yayi maganan shi ba kuma ko ta kamanin su duk da dai shi ba wani sanin yan uwama yayi sosai ba.
Well zai kira Fattu din yaji waye wanan guy din kila a wurinta zai samu karin bayanin da yake son sani amma tabbas itama Fattu din taga kamar sune dashi yasa ta turo mai wanan photon da aka rubutawa Master namu.
Master ?
Master din me ya tambayi kanshi kafin yaja tsuki yana aje wayan a gefen shi ya dauko littafin shi yana dubawa.
Naji dadin zama a dakin tsohuwar don kuryan ba hayaniya ko gittaiyan mutane kamar wancan dakin dana baro na farko da muka sauka sai nan din yafi mun can dadin zama.
Saidai da alaman abokiyar zamanta a dakin itama tana ji da kanta don tun shigowan ta lokacin banyi barci ba muna waya da ummah ta shigo muka gaisa bata kara bi ta kaina ba sai harkokin gaban ta takeyi na shirin kwanciya ta fita batuna nima haka.
Washe gari ma hakane mun daiyi gaisuwan safe da ita bayan mun sallame sallah daga haka kuma bamu kara yin wani magana ba karshema na saka earpiece a kunnena ina sauraren kira,a nayi barci don haka ban sam me akeyi a gidan ba kuma.
Sai wajajen karfe goma naji ana tayar dani daga barcin na bude idona tsohuwan dakin ne mahaifiyar su mommy a kaina.
Da sauri na kai hannu na cire abinda ke kunnena na dan yunkura ina gaida ita da kwana duk dana lekata da asuba nagaida ita tana fadin kina barci haka baki karya ba har wanan lokacin yar nan ?
Zan karya na fada a sanyaye ina dan murmushi a fuskana toki tashi ga abin karyawan ki nan uwarki ta aje maki a falo tun dazun su sun fitane zuwa Na,ibawa gidan wan mahaifinsu.
Na amsa mata da to ina kokatin mikewa zaune tana fita take kara fadin idan zakiyi wanka sai in saka a kawo maki ruwan dumi kiyi hakan yasa na gane ba zan samu ruwa a bayin ba ke nan lokacin.
Nace wanka zan fara saina karya tace barin zo ta fita zuwa can saiga wata matashiyar mata ta shigo da ruwan wankan tana gaidani na amsa tace ga ruwan hjy tace a shigo maki dashi nan din.
Nayi mata godiya tazo zata fita na kirata na mika mata dubu daya nan take ta washe baki tana min godiya ta karba ta fita tana murna ni kuma na mike zuwa ban dakin nayi wanka tare da brush na fito.
Kamar yadda na saba idan ba makaranta zan fita ba ko wani waje nakan tsaya in bata lokacina a daidai wanan lokacin nayi sallah nafila na rokawa kaina saukin rayuwa da dacewa ga rahaman ubangiji da nemawa iyayyena gafara.
Nan ma din hakan nayi don nayo alawala na fito nayi raka,a biyu na zauna ina addua a daidai lokacin wanan yarinyar da muka kwana saman gado daya tashigo dakin .
Kallona tayi ta dauke kanta gefe taci gaba da abinda takeyi har zuwa shiga ban dakinta don ta kewaya sai gata tafito kuma a lokaci guda tana fadin.
Don Allah a ina kika samu ruwan wanka ne nace wata mata ta kawo min nayi daga haka ta fice daga falo can naji muryanta tana fadin.
Nima a saka a kawo min ruwan mana zanyi wankan yanzu kifita min a ido yar nan ko ita wanan bata da lafiyane kuma bakuwace ita kinga dole nu kula da yar mutane ko.
Bandai san ya sukayi ba naga wanan ta dauko ruwan da kanta tashige bayi tana wanka har na gama shirina na nufi falon tsohuwar bata fito ba.
Ruwan shayi na dansha koshi ban iya shanyewa duka ba nabar saura na mike na koma cikin dakin na haye gado wanan din na sama tana shiri kallo daya tayi min ta kawar da kanta gefe har tagama ta fice ta barni.
Ina nan ni kaidai a dakin tunda ba sanin kowa nayi ba zuwa can rana sosai na fara jin muryan mommy sun dawo sunawa mahaifiyar su bayani.
Zuwa can mommy din ta leko tana fadin daughter na tafi na barki ke kadai sai ta sameni a shirye na saka wani atamfa blue da adon farin filawa a jikina sai dan kwalin shi da gyale fari mai kyau a gefena ajiye koda fita zai kamani.
To kinyi wanka ko nace eh hjy tasa an bani ruwan wanka nayi OK kin karya dai ko ta tambayeni eh na bata amsa cikin ladabi to mike ki fito waje mana cikin mutane ki zauna kin kunshe kai a daki ke kadai kamar amarya.
Ko wurin kawar taki ba zaki fito ba kya zauna ke kadai ina abune a waya aina fita na dai dawone na fada ina ita maryam din ?
Wace maryam na tambaya cikin alamun rashin ganewa wace kuka kwana a nan tare oho ta fita dazun na bata amsa.
Taso muje ta fada ta juya tana fita daga dakin na mike don dole nabi bayanta wacan dakin da muka fara sauka muka nufa da ita na zauna a nan wanka mommy din ta shiga ta fito duk ina zaune saman gadon na dan kishingida a lokacin.
Hankalina yana ga wayana ina duban sakonni wanda ya waci da yan course din mune nake charting don banda wasu abokan kirki da zan rika hira dasu.
Muryan mommy ne ke fadin anjima za aje kamu na fada maki kayan kamu wanda mu zamusa yan gidan ango jin hakan yasa na dago kai na amsa mata.
Ta shiga ta fita a dakin har yamma yayi aka fara shirin fita zuwa wurin kamu din lokacin na mike na koma dakin hjy inda kayana suke yanzu tana falo na gaida ita na shiga.
Nan na samu wanan yarinyar maryam tana shiri itama duk da nasan zata girmeni gaskiya ko ba a fada ba na shigo banyi mata magana ba bayan sallama na shige ban daki dan ruwa kadan na samu a ciki saidai hakana nayi amfani dashi ina tsanda na fito .
Falo na nufa na tambayi wanan matar ina kwatance sai gata ta shigo dakin da gani irin matan unguwar nan ne dakan dafa wani su samu inda zasuci abinci suma a cikin rufin asiri don yadda naga tana aiki kuma ana sata yi da wasu aike haka.
Bayan mun shigo daga ciki nake fadin kin gane dakin nan nake son a wanke robobin ruwan nan a dinga saka ruwa ko wani lokaci don Allah.
Wani kallo wanan maryam din ta jefoni dashi amma tana ganin na jawo jakka ina fadin don Allah koda wanine ki saka yayi muna hakan ga wanan kiba maishi don Allah a bar barin ruwa yana katsewa a ciki.
Godiya matar ta fara tana fadin ai angama yarinyar arziki kada ki damu da komai baki jin babu tunda kema kina bayarwa ai har abinda bakice nayi ba za a dinga maku a dakin nan insha Allahu.
Matar ta juya ta fita tana godiya ina jin muryan hjy mai dakin tana tambayan ta tana fada masu yadda mukayi naji tsohuwar tace ai tayi maganin ku shine daidai daku.
Tare dasu mommy karima zaku fitane naji muryan maryam din dake ji da kai tana ganin tafi kowa a dakin ta fada na dauka waya takeyi yasa na shareta.
Dake nake nace da su mommy zaku fitane ko mu fita tare don ni ba wai nasan su bane sosai nace ayyah wallahi ban sani ba gashi dai ina shiryawa .
Maryam din ta fara saka kaya a jikin ta kafin in saka tana wani zuwa tana dawowa tsakanin falo da dakin kafin nima na saka kayan na fito shar dani a cikkn tufafin.
Zuwa lokacin kusan duk wanda ke gidan ya saka ankon shi a jikinshi ana fita waje mommy ce ta shigo dakin da sauri tana fadin daughter kin gama shirin kuwa ?
Eh mommy nagama mama ai tare zamu tafi maryam din dake saka wani abu a jakkarta ta fada sai naji mommy tace shike nan ma da kunsan wuri sai nace a baku key kuzo tare da angone kuma ku shiga cikin su.
Wa zaija motar maryam ta tambaya naji mommy tace zahra mana wace keda mota babba na shiga wurin milayan biyu da rabi naji ance bayan wanan ma kina da wata ko ?
Na dan gyada kai a hankali yarinyar ta kara kallona cikin mamaki mommy dai ta juya tana fadin barin gani ko za a iya yin wani abu ta fice daga dakin kai tsaye .
Sai zuwa can mommy din ta aiko wai mu fito mubi wani usman a motanshi driver ya fita da motan da take son mu shiga din.
Ba ruwana don haka yadda sukace zanyi don duk a takure nake zaune dasu mun fito din wani guy ne wace tazo kiran mu ta nufa tana fadin ya usman gasu nan sun fito.
Yana magana da wasu ya juyo ya kallemu suma sauran kallon mu sukeyi a dan sama sama muka gaidashi ya amsa yana satan kallon mu can yace kune zan tafi daku ko maryam din ta amsa mashi.
Nikan baya na nufa maryam ta bude gaba ta shiga wanan data kiramu itama ta biyo mu muka shiga zuwa wurin taron kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login