Showing 297001 words to 300000 words out of 304363 words

Chapter 100 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33318

kada innan mu ta dauka gaskiyane haka zancen yake gashi har kin zugata takak ga dauka yanzu anyi yadda kike so.
Indai gidan namu kike son zuwa ai kije su inna tumba sunan nan zaune kin dai san zaman da sukayi da innan mu ai sai ki koma ki zauna ku zuba dasu.
Karshe zama nayi kamar yadda ya zauna na zuba masu ido ina kallon ikon Allah har dai a karshe ita inna tace ta wuce tunda umma kin juya maganan ya koma gareki yanzu amma ni ba manufata ke nan ba.
Kina farashi ki canza zance yanzu don idonki ya rufe da farko nasan ba yau kika fara fadan haka da dai kowa yasan ke kika haifi abinki ai ni kuma uwarki na tayar maki dashi tsakani da Allah har ya zama hakan da kikeyiwa.
Dije don Allah ki bar fadan hakan in ma naki inna shin laifine aima nayi kokari tunda har nasan ke mahaifiyatace har nake kokarin sauke maki hakkin ki na haihuwa gareni.
Nan Dije ta matsa sai naje inda kuke muka tara kudi nabi malam Auwalu ya kaini wurin ki a gaba mijinki yace sai nasan inda zan sauka shi ba zai yarda ki kawo mai dan agola gida ba.
Inna maimakon ki nuna min ni dankine a lokacin budan bakinki sai cewa kikayi naje wani makarantan allo in kwana can washe gari in koma gida.
Naje na kwana a cikin almajirai ban san ya akayi ba dana zo da safe kan komawata gida kikace na bari amma zan dinga bin mijin ki gona muna aiki tare.
Kirikiri inna zanje in wuni a gona inyi aiki in dawo da yamma kuce abinci ya kare sai naje nayi bara garin Nufawa in samu abinda zanci.
Har aka kare aikin gona mijinki yace sai na shirya in dawo gida shiya gaji da agola yana shigo masa gida haka kuka turoni cikin babban mota na dawo gida ranan nayi kuka nayi dana sanin zuwa duniya.
Amma danazo gida har yau ban fadawa dije komai ba illa dai ita dijen tayi fada ganin yadda na dawo kuma na koma wani iri sai ragga amma duk da haka ban fada mata komai ba.
Yaran ki kawai kika sani inna daga Aisha sai Asmau ban nuna komai ba amma yau ke da kanki kike kyashi akan matar data rikeni tsakani da Allah don Allah inna bakiji nauyi fadan hakan ga Dije ba.
Banyi fushi ba da mijin ki ya mutu ya barki da yara banda komai lokacin amma haka na zauna da duk wani lalura naku har lokacin dana auri zahra tana dan taimaka min amma duk baki ganin hakan.
Inna ya kike so yanzu ki fadi don Allah na tura a gyara maku gida da wurin ku da inda muke da amma yarki ta koro min masu aiki tace wai ban fada mata zan turo su ba shin inna duk wanan bai isa ba ke nan ?
Sai kin biyo mu nan kin dagawa mahaifiyar ki hankali kuma kina sukanta da magana a kaina ni Dije tayi min komai wallahi don da Allah na dogara ga dije kuma na dogara don itace uwana itace ubana.
Duk abinda na zama yau su biyun nan sune silar hakan don ta dalilinsu na samu komai don haka inna ki tausasa lafazin ki garesu don Allah a zauna lafiya.
Gida kuma yau din nan mukayi da masu aiki zasuje su fara kafin nazo ki tabbatar da kin kwashe komai naki kin koma gidan mahaifinki kinji na fada maki don ba zan yarda inbar ki a tsakaninsu ba kina hadasu fada irin haka.
Sai dai in tare zamu bar maku gidan har in kace sai Asma ta koma gidan mahaifinta ba zan yarda taje can tana gantali ba tsakiyan gida gidan dako daki baibar masu gado ba ina kake son taje.
Kai nikan naga tujara ranan wurin wanan ahalin don master ya turje kan lalai sai Asmau tabar gidan nan a wanan ranan, inna zatayi magana dije tace gidansane halak malak kowa ya sani a garin nan.
Don haka yana da ikon yin komai dayaso da abinsa ran innace ya baci sosai da jin kalamin mahaifiyarta data goyawa danta baya sai kawai ta mike tana fadin shike nan ai yanzu na gane umma.
Har ni dai kuke son nabar gidan ke nan yau din ko dayace a yau din zamu bar gidan dagani har Asmau din basai gobe ba yayi yadda ya keso ga duniyan nan.
Ta fita tana kuka ya mike zai bita dije ta daga mai hannu ya zauna kyaleta ko ina bata zuwa wanan duk burgan aikine take maka yace dawai zansa driver ya kaisu gidane tace ka barsu kadai kawai tura masu aiki suje su fara aikinsu.
Inna tana fita tare suka fita da Asmau din da take tafiya tana waigen baya ko zataga yayan nasu ya fito amma har suka fice get din gidan basuga kowa ya lekosu ba.
Ga kuma hadari ka,in dana,in ya game gari ko ina har an fara yayyafi a lokacin daga bayan inna Asmau tace yanzu inna yaya zamuyi ke nan ki dai bari mu karasa gidan muyi magana.
Allah ya taimaka suka samu mashi sukai overload su biyu amma saida ruwa ya bugesu kafin sukai gida haka suka shiga tsamo tsamo cikin gidan.
Bayan sun kwabe tufafin jikinsune har wayau din Asmau tace yanzu inna gidanwa zanje gidan mu dai kinsan su inna tumba ba zasu barni na zauna dakunan su ba.
Asmau kema kin faye iya shege da tsiyan banza kinsa yaron nan yana iya bakin kokarinsa damu amma kedai kullun abinda zaki hadani dashi kike nema kiyi don kawai kinga nafi sonki dashi.
Yau ga irin abinda kika ingizani nayi masa bai fadi karya ba don mahaifinku akanku ba irin abinda baiyi masa da yake raye don mashi din mai dubaiyane wallahi da wanine ba zai rike mashi kuba bayan ransa.
To ai baba yai masa bamu ba duk dije take saka yai haka dama kin nuna zaki mai baki ai dole ya saitu yabi abinda kike so wani kallo tayiwa yar nata kafin tace.
Yau nasan baki da hankali nayi mai baki mu lalace tare mu koma zaune duk wanan kokarin da yakeyi damu ina masa baki nima ban dagawa ai umma zatayi min baki kedai in kina binsa ki aje duk wani tsayatakun ki ki aje kibi dan uwanki a zauna lafiya shine rufin asirin mu gaba daya.
Ita Aisha data bisu ake zaune lafiya kinga ya tsanane koya korota gidanshi ba gata can ta saje dasu ba an zauna lafiya kece dai bansan irin halinki ba sai kije ki dauko rigiman ki kice sai nashiga nayi maki yaki ke karama a cikinsu kice baki bin manya.
Nina gaji wallahi in ba iskanci ba da tsiya irin naki ko bakin cikine meya kaiki wurin masu aiki ki koresu ai yanzu ga abinda kika jawowa kanki nan sai ki koma ki bashi hakkuri.
Tace cabdi Dije na gidan da matarsa zan koma yadda dije ta tsaneni din nan ai sai tasa yayi min dan karan duka a gidan ni dai yanzu kisan yadda zaki gyara maganan don gaskiya ba zan koma gidan wanzamai ba in zauna saidai in kama dakin haya.
Wai ma da gaskene dama gidan nan nasane danaji dije na fadi kullun nasane mana mahaifin mu ya bashi tun yana karami kowa kuma yasan da wanan zamcen sai ta danyi shiru tana tunane kafin can tace.
Shi komaima da zamu samu duniya ya kwashe shi kadai da yaranshi shine uba mai kudi shine shine shine haba don Allah gashi kuma ke baki samu kansa kina juyashi yadda ya dace ba.
Uwar ranta yana bace bata samu bakin bata amsan wanan maganan banzan da take sakewa ba a lokacin sai suka koma kowa na tunane gashi ruwa ya hana fita balle su dan fita su samu abinda zasuci ga kamshin soye soye a can gidan zuciya ya hana su tsaya suci.
Kai shima baba kome yasa ya tsanesa haka har yake fadi yanzu a gaban mu uwar tace a hasale abinda yasa kika tsaneshi ke ma a yanzu hassada da bakin ciki kikewa dan uwan naki ashe ya kwashe komai .
Kada ki manta shi arzikinsa gada yayi gun ubansa nice dai matsiyaciyar da banci na ubasa baci na naku uban ba sai tsiya sai kawai Asmau tasa kuka wai inna tayi mata gori ta fada mata magana a cikin zance.
Mama ke zaune a falonta tayi shiru tana tunane abin duniya ya isheta ga talauci ga bakin ciki tana kallo ba yadda zatayi maganinsa sai kallo.
Uban tsuki taja tana fadin makaryatan banza a fili sunci kudina kawai a banza har yau banga komai ba sai cigaba a wurinsu maganganu takeyi ita kadai a dakin don ranan ba wace tazo gidan don basu da kudin mota Aisha ta bugo zatazo intazo akwai na Napep tace wallahi ban kwana da ki kwandala ba a gidan nan jiya.
Wanan yasa Aishan bata shigo ba a ranan ta zauna a dakinta sai zuwa yamma da wata kawarta ta shigo ta bata dari biyar kamar tsafi ta shirya zuwa gida din wurin mama.
Suna nan zaune a tare ya musa ya shigo dubu biyu ya zaro yaba mama tana kallonshi cikin mamaki tace ina kasamu kudi haka har kake kyauta dashi kai tsaye yace wurin zahra nakai ziyara ta ban kudi jiya shine na baki kema ki sheda.
Wani haushine ya kama mama ta kalli kudin ta kallesa tace maula kuma kajeyi gidan kanwarka kome baba ?
Yace maula kuma don naje yin zumuta ta ban kudi shi za a kira da maula yanzu mama kinsan tsakanin sufa dama suna shiri sosai da ita to ni dai banson zubar da girma da aji ka rike girman ka har ina abin yake da har sukewa mutane daga kai yanzu.
Mama ke nan don kawai ita zahra har mijinta basu da rigimane aida yanzu gari an sheda wallahi mama akwai kudi yaron nan ba karamin kuru bane ya karatu sosai don babbane a can ma,aikatansu.
Don Allah baba ka rufa min baki da abin takaici shine me don ya zama babba kaiba kasan waje kayi karatu ba ka shiririta kanka waikai dan maye a yanzu.
Mama don Allah ku bar zancen ya isa hakana yaya kana da abin hawa tare da kaine ka saukeni gida yace eh ai na gyara motan Hjy dazun a cikin kudin yanzu haka ita nake dan dagarawa.
Barin biyoka ka saukeni gida dare ya soma kada yara suyi barci ban koma ba haka yasa ta mike da sauri tayiwa mama din saida safe suka fita wanan kudin bai kwana ba mama ta aika aka sayo mata kati da kayan tea ta kashesu.
Can kuma cikin mota Aisha ce tace wallahi ina son zuwa kodon naga gidan nasu ina tsoron bacin ran mama ya musa ya juyo da sauri yana fadin me zatayi maki kuje kawai idan kunyi niya.
Ni ba gashi naje na samo ba kuma kudin yayi amfani tunda na gyara mota mu samu na hawa dubu dari fa zahra ta bani cas dinsu kai yaya dubu dari fa a wanan lokacin yace wallahi ko Aisha.
Shine ranan da inna tazo bayan an dauke ruwa ina daki kwance Aisha tazo tana fada min anty ga yan uwankin nan sunzo su biyu suna falo.
Na dago nace anty Aisha tace su kun basu abin sha tace na basu komai shine nazo fada maki nace kice gani tafe na sauko na gyara kaina na fito a cikin fara ata sune dai din kuwa sukazo.
Suna zaune sai bin ko ina da kallon mamaki sukeyi na iso ina fadin manyan baki anty Aisha kune tafe a cikin sanyin nan ban zauna ba saida na karbi dan dake hannun Rukkaiya ina fadin kai malam ya kake nakai zaune tare da yaron a hannuna.
Ina gaidasu da kwana suka amsa nake fadin wallahi yau mukaso zuwa gaida mama amma ruwan nan ya hana dama master ne bai nan tunda sukayi tafiya dasu ummah sai jiya ya dawo garin nan.
Dama shiyace sai ya dawo muje tare kada yayi laifi gun mama din ai kuwa mama zatayi fushi idan bakuje ba nan muka zauna muka wuni dasu komai tare kyautan da nayi masu da zasu tafi saida sukai mamaki nasa mota ya kai su har gida.
Washe gari kuma tunda munyi niya gida mukaje wuni don tani na gidan namu zaune da kanne na tana masu komai a part din mama din muka zauna mun dade sosai ta nuna ba komai a zuciyarta sai fira muke zubawa da ita kafin na fito na koma wurin kanne na nan master ya barmu sai dare muka koma gida.
Amma bayan fitowan mu wurin mama ya sa a shiga mata da tsarabanta da muka zo dashi har da kayan abinci da kudi tunda Abba bai kasan wanan dole yasa mama tasowa zuwa part din ummah tana fadin tsarabace haka duk ni kadai.
Nace a a mama Amir ne yace tunda Abba bai kasan yana son yayi masa kwace aka kwashe da dariya tanawa yaron sheri ta dan jima muna wani hiran kan ta fita ta koma part dinta a cikin bakin ciki da takaici dake cinta.
Don saida muka cika mata falo da tarkace a ranan da kayan abinci wanda an dan dauki lokaci ba a shigo da irin shi ba a gidan mu sai ranan dai haihuwa tayi ranan ta.
Duk da dacin da mama keji a kasan ranta hakan kuma bai hanata jin dadin ganin wanan alherin data samu a wurin mu ba don abune da yanzun yake mata wahalan samu a rayuwanta karfin hali kawai akeyi irin na rayuwa dama.
Sai gashi washe gari yaran nata sunzo kamar yadda suka saba zuwa din sunga canji kwarai gareta ranan tun wurin kawo masu abinci datasa akayi sukaga abin miya wadatatace nan suke fadin yau kan mama da nauyin ki gaskiya.
Saida ta tabe baki tace eh jiya wa yan nan sukazo suka kawo muna abubuwa wai tsara kayan abinci kuma don Alh baya gari ko yana garin ma yanzu ina zan samu wanan din tunda komai ya kare ga Alh yanzu.
Kallon juna sukayi kafin uwar tace in kun gama ku shiga ciki ku duba kuga abinda suka kawo min ni super din ma su sukafi daukan hankali da kayan abincin nan wallahi.
Mama muma fa mun tafi gidan kuma taji dadi tayi muna alheri sosai wallahi tsoron fada maki mukayi muje gulmane amma sai ta taremu cikin mutunci ta rasa inda zata sakamu tana ta fadin yan uwan tane na haihuwa sukazo mata wuni daga gidajensu.
Wallahi mama dole muka sake jiki aikai sha,ani zamu tafi a motan mijinta aka kaimu kowan mu gida tare da abin arzikin mu tace idan an kwana biyu zatazo tayiwa kowan mu yini a gidan ta.
Humm,uwar tace tana sauke ajiyan zuciya tace tayi gadon kinibibin tsiya kamar uwarta baka taba gane gaskiyan cikinsu sai suyi ta nuna haba haba a gaban mutum kamar su din na Allah ne.
Mu ina ruwan mu mama muma sai mu dauka kawai kamar yadda ta dauka a rufe ayi ta sha,ani sai Rukkaiya take fadin amma mama gaskiya suna da hakkuri koma dai meye su suna nuna mu nasune gaskiya .
Yanzun da kikaga wurin ci kika gane hakan tona rabaki da yan uba da yar kishiya don ba zasu taba son kici gaba ba saidai ki koma baya.
Kamar yadda yanzun suke ganin muci baya sun koma gaba aini Alh haruna ya ban mamaki sosai daya hana waj aje dani indiyan nan kiri kiri dan uwanka yai maka bakin ciki.
Mama shifa baba haroon haka yake waishi fadan gaskiya duk za ayi abu sai ya nuna rashin dacewan abin idan yaga ba daidai ba nan take zai fadi gaskiya ga mutum.
Nifa mama kwantawa zanyi don in gane kan shegiya kwana biyu kafin in fito mata da true colour dina in fara cin ubanta a mumuke a dafa kifi da ruwanshi zan mata ku barni da shegiya.
Zahrace fa kada ku manta haka take kamar mai ira izai dake fada mata wahayi yarinyar akwai shegen wayaun tsiya da ita tun da can da wuya ka gane takon zahra wallahi.
Ni yanzu ba wanan shirmen da kuke karantowa bane a raina abinda ya dameni shine in banyi hankali ba muna kallo komai na gidan nan zai koma hannunsu nan gaba kadan .
Tunda yanzu Alh dai badai shi wanan yar matsiyatan ta yaudareshi a banza taci kasuwan ta tayi wasa da hankalinshi ta tattra komai ta tafi dashi.
Shima Abba ai yayi sakaci wallahi Aisha ta fada tana jan tsuki cikin takaici da bakin ciki tana kawar da kanta gefe daya haka sukai ta hira wanda bana alheri ba har yamma kafin kowansu ya kama gaban shi zuwa gida.

Ubangiji yabawa buby zahra lafiya Allah yasa a shiga da ita dakin theater lafiya a fito muna da ita lafiya Amin wa yanda suka tamakawa iyayyenta ubangiji ya kai lada a kabarin su Amin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/19, 5:57 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login