Showing 30001 words to 33000 words out of 304363 words

Chapter 11 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33369

Kana zaune arziki ke sama ka har gida yau ai tunda aka kawo motan nan mutanen gefe ke cike da bakin ciki a gidan nan ko motsin su bakya ji tun dazun nasan ana can ana kitsa wani sherin ke nan kuma ?
Suwa ke nan na tambaya da mamaki tace yan hana ruwa gudu mana na gidan nan dkn ita giwanyan tamaki fitowa taga motan sam sai cewa tayi mota wani irin mota kuma ya saya maki yanzu.
Kai Tani uwar tawace ke bakin ciki don yaya musa ya saya min mota kada ki mata sheri mana na fada ina nufar inda ummah take zaune na ajiye jakkata kafin nakai zaune.
An maki albishir baki ko je kinga motar ba kin zauna yanzu da a gaban shine haka zaki nuna mashi ke nan ina hanaki wanan rayuwan ko in kula naki do ba halin kwarai bane hakan da kikeyi .
Ummah na gajine sosai yau wallahi barin cire kayan nan naje na duba na leka mama a dakin in fada mata da bakina kada tayi min fadan rashin sanar mata da kaina.
To ki gwada ki gani ai hakan yana da kyau ban wani dade a dakin ba na fito cikin wani simple riga irin na zaman gida waje ire iren su ummah ke sayomin muna Abuja don ban faye saka kayan dake matseni ba duk da ina dasu ban damu da sakasu ba.
A hankali nake takowa daga cikin gida na nufo waje lalai bana cikin hankalina lokacin dana dawo school zan shiga gida tunda har banga wanan farar motar ba parado dake aje a wajen gidan mu lokacin.
Parado ce karama fara kal tana daukan ido a hanzarce na karasa wurin zagayen motar na farayi kanne suna bina abaya sai ihu sukeyi har na zagayo zuwa kofan motar na tsaya kafin naje gaban motan dake dauke da lamban Abuja a gaban shi .
Tsoro da mamakine ya kamani lokaci guda nakai hannu na dafa motan a hankali tare da bissimillah idanuna na runtse inawa Allah godiya.
Ako yaushe ubangiji abin godewa ne a gareni irin yadda yake min baiwa iri iri a duniya a saukake naci gaba a rayuwana wanda alokacin ban san dalilin shi ba sai nan gaba.
Ummah ummah ummahn mu nake kwalawa kira tundaga kofa a cikin murna da daukin ganin motar ummah da ke shirin alwala zata dakanci magariba tayo waje wurina a cikin tashin hankali ta dauka wani abune ya sameni har jikinta na bari muka hade a falo.
Ummah wai kinga motar nan kuwa kaf gidan nan fa babu me ita har mama kai amma naji dadi wallahi ya musa Allah ya saka mai da alheri.
Dan Allah maamah yanzu murnane haka kika dagawa mutane hankali da magariban farin nan haka haba maamah naki kala farin cikin ke nan haka ?
Makin ki godewa Allah ta hanyan nafila ko daga hannu ki kara neman kari a gareshi tare da godiya ga ni,iman daya wadatar dake haka a cikin yan uwan ki.
Ummah zanyi in sha Allahu don ko a waje nayi zanje nayi sallah yanzu don naga lokaci ya gabato kamin na gama fadi har ummah ra juya ta shige cikin dakin ta ko a lokacin.
Sallah na idar a cikin doki don har lokacin kamar a mafalki nakeyi nake ganin kaina wata iri ni fatimatul zara,u nice Allah yaiwa wanan daukakan haka lokaci guda.
Don wanan aiba karamin cigabane na samu lokaci guda haka don banyi tsamanin motar mama tafi nawa wani tsada ba don farkon fitowan motar ne lokacin ashe da gaiya ya musa ya zabo min shi duk da uban kudin dakega motan lokacin.
Shiga gidan da uwar garke ya fara tozali tana kwance yarda ya barta tano tuka da hakoranta yadda dabbobi keyi idan suna gyaran abinci ya fada masu a ciki.
Ikon Allah ya fada a ranshi ya karasa wurin turken da sauri yana fadin Dije mutumin nan bai biyo sawun akuyan nan bane har yanzu ?
Sai lokacin Dije tasan da dawowan shi gidan tafito tana gyara daurin kallabin kanta tana fadin tun safe nake zaune ina saka ido naji sallaman shi har yanzu banji kowa ba saikai dinnan daka shigo yanzu.
Ina zuwa Dije tace ya juya zai fice daga gidan tace cikin daga murya ina kuma zaka ko kasan gidanshine dama ?
Wurin malam Tanimu zan tafi ya bata amsa yana tafiya bai tsaya ba ya fice daga gidan kai tsaye ta figi zani a rataye tabi bayan shi itama.
Malam tanimu dake zaune a kasa buta a gefen shi yana shirin alwala ya hango Amadi din ya nufo inda yake zaune kamar hankali a tashe.
Hankalinshi ya mayar kan matashin dake tafe wurin shi tunkan ya karaso yake tambayanshi da Amadi lafiya kake tafe haka ?
Wallahi malam akuyan nan uwar garke na dije da jiya bakon ka ya saya shine ta gudo daga gida shi ta dawo gida mun dauka zai biyo sawun ta yau sai gashi har yamman nan na dawo na sameta a gida baizo ya dauka ba.
Bako malam tanimu ya maimaita cikin mamaki yana kallon Dije dake biye a bayan Amadi din tafe itama a rikice ta karsso tana fadin malam tanimu ka ganmu a wanan lokacin ba.
Ina ya fadama akuya dai ta dawo yanzun haka tana gidana nayi bata abinci wunin yau taki cin komai saidai ta sunsuna ta kawar da kai gefe daya.
Gaba dayan su kallonta sukeyi lokacin suna sauraren bayanin ta kafin malam tanimu da yaji tayi shiru yace.
Bako gaskiya banyi wani bako da kuke wanan zancen ba, eh malam Tanimu gaskiyane jiya yazo nan ya sameni ni kadai a zaune lokacin na dawo daga gidan jabbi mahauci nakai masa tallan akuyan na samu yaje kauye.
Na sake zuwa gidan yanka shima bayanan ya shiga gari shine na dawo na zauna nan inda kake hutawa ban dade da zama ba wani dattijo yazo yai min sallama yana neman ka.
Nace nima ban sameka ba bari na sallama na tambaya mashi shine na shiga akace dani baka nan kaje daji daukan ice na karbo mashi ruwa na kawo mai.
Shine yake fada min yazo wurin kane ka taimaka kai masa jagora yazon sayen dabbane gashi kuma bai sameka ba ni kuma jin hakan yasa na tallata masa uwar garken mu yace a kawo mai ya duba.
Bayan na kawo mashine yace ai masa kudi daga sama na yanka mai amma ya tsaya a nan bai nemi ko ragowa ba har dubu biyar na mayar mai daga ciki amma yaki amsa haka yasayeta jakka arba,in cif.
Ikon Allah to waye wanan malam tanimu ya sake tambaya cikin mamaki yace dogone fari ya dan rankwafa yana da farin gemu a fuskanshi.
Dewa ya,i ni wanan mutum wanene kuwa don wallahi ban gane shi ba sam kuma dana dawon iyali basu fada min zancen wani yazo nemana ba.
To shine shi Amadi ke fada min dazun wai yayi mafaki mafarki da asuba da mutumin na fada mai cewa ga akuyar nan ya dawo muna dashi kudi kuma tayi amfani dasu yabashi su halak malak.
Kai malam Tani ke faman juyawa kafin yace lamarin da daure kai yake don sam ban gane waye wanan mutumin ba anya ba buda ido akai makaba kuwa Amadi.
Kamar ya buda ido kuma dije ta fada a dan firgice ko hasale bayan ga kudi a hannun mu mutumi ya bayar kuma ya tafi da akuya dawowa tayi kawai.
Watau Dije zancan nan ne da daure kai yake don sam na kasa gane mai wanan kwatancen da Amadi yai min yanzu.
Saukin abindai yaga gida koda ya dawo ya sallama za a bashi abinshi kudi kuma wanan mafalkin wanan abinda zai farune kila yasa kayi wana mafalkin haka.
Don haka ba laifi bane indon wanan ne sai kuyi laluran gaban ku da kudin koma waye tunda yasan ni ai ya kwana gidan sauki ga kuma akuyan shi nan a daure sai ya dauki abinshi.
Yanzun lokacin sallah ya gabato don haka ku koma gida sai aje ai hakan nasan maishi zai dawo neman ta nan kadan wanan ba abin damuwa bane ai.
Allah ya kyauta Dije ta fada ta juya zuwa gida tana magana ita kada tana ganjn laifin su ga sakacin da sukayi na barin akuyan ta dawo gidan nasu tunda yanzu ba hakkinsu bane uwar garken .
Shi kuma Amadi ya tsaya sukayi alwala da malam tanimu su mike zuwa masalaci don yin sallah magariba da aka kira a lokacin.
Ina idar da sallah hijsbi na kwabe zan nufi part din mama don muyu zancen motan da ita saidai ina fitowa fallon ummah na zaune ta zubawa yara abinci.
Haka nazo na wuce ta na ji muryan ummah din na fadin ina fatan baki dauki key ba zuwa wurin ta ba, juyowa nayi ina fadin a, a ummah ban dauka ba ai yana nan dakinki.
A to idan dai kikaje mata dashi karbe key din zatayi a hannun ki wanan karamin aikinta kin sani wurinta haka mai saukine.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[31/12/2022 9:17 AM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
AL KHALIQ ,,,,,,,,,,
1️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Sallama nayi part din suna zaune falo sai mamace ke dakinta gaidasu nayi na nufi dakin mama don lokacin banda shamakin shiga dakjn nata don da suke lagos nakan je hutu daga Abuja.
Bata nuna mjn banbaci ga komai duk yadda yaranta keyi haka nake mata lokacin wanan ya jawo shakuwa mai yawa a tsakanin mu duk faruwan hakan ya samo asaline bayan dawowan mu gida gusau da mukayi ana zaune wuri daya.
Nakai kofan naji muryan mama na fadin ain fada maki Saratu da cewa yarta idan banyi da gaske ba yaron nan musa yana son yafi karfina ne ba halinsu daya da Jafar ba shi sam baya tsorona .
Wai shi ya nuna min ya isa zaiyi dalilin saya mata wanan motar mai uban kudi ta hau ita din yar waye datafi sauran jikan tallakawa kawai.
Lokacinne nafada dakin duk da kunne yaji hakan ina sallama cikin rawan baki ta dakatar da wayan tana min wani irin kaskantacen kallo tana jifana dashi.
Har nakai tsakiyan dakin ta daka min wani uban tsawa daya sani kaduwa tana fadin ke ubanwa yace ki shigo min daki har nan kina ko da hankali kuwa zarah yadda yan uwana ke kirana ranan babu maamah din.
Yi hakkuri mama bansan kina busy bane na fada a sanyayye zan juya na sake jin muryanta tana fadin uban mema ya kawo ki nane wai yanzu ?
A,a mama dama nazo fada maki zancen motane shine bansan kina busy ba na shigo mota? motar banzan ku can dake da wan naki munafuki inba sakarcin shi ba komu yaga mun shiga irin motar nan ne a garin nan balleke zarah.
Na dago kai na kalleta jin yadda take kiran sunana a ranan kai tsaye bayan ita ke fada a da can baya idan yan uwana suna tsokana na da Fatima zarah.
Yau wai itace ke fadin haka kai tsaye da bakinta tana kallona a fusace tacigaba da fadin ina key din motar take na bata amsa nima da yana hannun ummah.
Jeki zan karba na juya rai bace zan fita daga dakin naji tana fadin kada ki kara gigin shigo min daki daga yau idan kin fita kija min kofana ki kiramin Aisha ko Rukkaiya.
Na amsa da to mama na fice mata dakinta tare da jawowa na samesu falo na fada masu sakonta kamar basuji ina magana ba don hakane nima banyi zancen motar dasu ba na fita.
Ummah suna falo da yan uwana suna cin abinci na shigo sukuku kamar kwai ya fashe min a ciki kanina ke fadin wai anty zarah gobe ke zaki kaimu school cikin sabuwar motar ki ko ?
Zama nayi saman kujera gefen ummah ina fadin kai khalid wace motar motar da mama tace ban isa shigarta ba karban key din zatayi hannun ummah.
Karban key fa a hannuna aiko da rashin ta idon hjy maimuna yayi yawa Allah ya kawota tace in bata key din motar zata gane ba salman da nake ba yanzu gidan nan.
A,a ummah ki bata tunda dama danta ya saya min kinga ai shike nan dama kafin na shiga naji tana waya da mama saratu tana fadin wai yaya musa munafukine yana son yafi karfinta gidan nan.
Waini jikan talla, , , , sai kuma nayi shiru ummah tace ko baki fada ba nasan hakane dama duk bakin cikin ta ke nan a kaina ita din yar waye a garin nan banda Amadu sarkin teloli.
Allah ya kawota karban key din nan taga tsiya zan shayar da ita mamaki sosai a gidan nan kuwa mukaji an turo kofan Rukkaiyace ta shigo tsatsaye dinta yadda take ba ladabi tana saye da wani dogon rigan body hook a jikin ta duk ya matseta ga mazaunan ta a fili irin shigan yan Lego's na rashi tarbiya da mutunci shine dabi,an su don ma su yaya na taka masu burkine wani lokaci.
Duk idon mu yana kanta ba tare da gaida ummah ba take fadin wai mama tace ki ban key din motar da aka kawo dazun ?
Jeki kice mata tazo da kanta ta dauka yana dakina wani kallo ta watsowa ummah din kamar zatayi magana sai kuma ta juya ta fice daga part din daga haka ummah bata kara magana ba sukaci gaba da cin abincin su.
Saidai da gani kasan zuciyarta ba dadi a lokacin sosai don yadda fuskanta ya nuna a lokacin yanayin bacin raine karara a fuskan nata.
Shiru shiru muna nan zaune muna dakon zuwan mama karban key bamu ganta ba sai ummah data dago kanta tana fadin ba zakici abinci bane ke kina zaune tun dazun.
Nisawa nayi irin wanda ke nuna mutum ya shiga zurfin tunane a lokacin nake fadin na koshi ummah tace kin koshi me kikaci ko kin saka zancen nan a ranki ne ko ?
To banson sha shanci don maganan nan ba taki bace idan baya kama kiyi ba ki zuba min ido dasu a gidan nan don haka tashi ki debi abinci kici yanzun nan.
Kudin aljihunshi ya fitar gaban Dije ya sake lissafawa suna nan yadda suke aje din ya dago kai ya kalli Dije dake zaune ta zuba mai ido yace.
Dije ga kudin yanzu yaya zamuyi dasu zamu tabane ko kuwa mu aje har mai akuyan nan yazo ya kama abinshi kafin muyi amfani dasu .
Amadi akuya ai ya sayeta ya bamu kudin mu duk sanda ya dawo ga akuyanshi nan a daure ya kama abinshi ya tafi da ita meye namu a ciki yanzu tunda bamu muka sako mashi ita ta dawo nan ba.
Nisawa yayi mai nauyi yace dana yanke shawaran zan fara sayen gwanjo ina sayarwa layi layi ranan da ba karatu ko kuma nayi sana,an awo ina shiga kauyu ka ina sayo hatsi ina kawowa nan na kafa dan table a kofan gidan nan ko yaya kika gani.
Amadi kudin nan basu isanka wanan sana,an har buhu nawa kudin zai sayo maka da kake wanan zance kaidai fara gwanjon mu gani tukun abinda Allah zaiyi in yaso daga baya idan ubangiji yaima budi sai ka fara wanan din zaifi.
To Allah yasa mu dace gobe kafin naje school da safe zanyi asubancin zuwa kasuwa na zabo masu kyau da zasuyi saukin saye na gwada in gani tace Allah yasa albarka a ciki ya amsa da Amin.
Kwanon silver ya jawo wanda Dije ke saka mai abinci a ciki ya bude kanzone data gyara shi da ganye ya mike ya wanko hannunshi ya dawo dauke da ruwa cikin tsohon kofi ya zauna yana bissimillah ya fara ci yana tunane.
Washegari tunda safe daga masallaci ya wuce kasuwa da kafa koda yaje ya samu an fara bude kaya hakan yasa ya zabo wanduna da riguna na maza ya nufo school dasu duk da yasan ba masayan fili a nan don zasuji kunyar saya.
Amma shi ko a jikinshi ya kai wani wuri ya aje ya nufi department din su da sauri don yasan ya gama makara a ranan sai wadda Allah yayi zai samu shiga ajin safe.
Ummah ni zan tafi na fada tana tsaye ta juyo tana fadin ba zaki dauki kannen naki bane ki saukesu school sun gama shiryawa fa ummah ta fada tana kallona.
Nace Ummah aiba da motan zan fita ba tace don me ba zaki fita da ita ba ko ajewa zakiyi kina kallonta baki shiga ba don shiga aka saya maki ita ba.
Wanan kuma yaya zanyi da ita sai na ajeta ummah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login