Showing 156001 words to 159000 words out of 304363 words
tana fadin Dije ko baki min gori ba nasan na tafi na barku a cikin wahala shekara da shekaru nima kuma hakan ai ba laifina bane tunda aure nabi.
A, toh ni dai na fada in kina cire ido ga yaran nan ki cire don arzikin su yazo data idan kinyiwa dan ki sawal, walin tsiya kuma ya rabu da yarinyar nan wanan kuma kinwa kanki don dai ki sani.
Shine kwana biyu naji shiru ta daina shiga harkan mu tama dauko fita in tabar gidan tun safe sai yamma zata dawo.
Da yan kushin abubuwan irin su rake yalo karas lemu mangoro ayyah da sauran su a nan zasu baje saman tabarma da yaranta suci sai wata rana wata rana akan debo min akawo min dan kadan.
Saidai Allah bai sako min kwadayin irin kayan nan ba wata rana in karba in aje idan ya shigo shi zaici wata ran kuma ba zan karba nace a mayar nagode.
Sai su cinye abinsu ko wanda ake kawo min din ma ita yar babban yar nata Aishan ce kecewa a diba min sai karamar ta yatsune baki tace abinda baida yawa zatace wai sai an dibamin shi.
Haka dai zasuyi ta fada a tsakanin su har ta kawo min ruwa kuma koda sanina koba da sanina ba haka zasu shigo su bude fridge su dauka susha saidai wanan bai dameni ba kamar yadda sukanyiwa fridge kamar da gaiya zakaji an rufe shi da karmi har sai mutum yaji shi har cikin ranshi .
Irin hakan wata rana ya faru yana gidan Asmau tazo ta dauki ruwa ta buga marfin saida duk muka zabura lokaci guda.
Ya mike yana fadin meye hakan da kyar na iya dago kai na bashi amsa da frige ne aka buga wata kila wanine ya dauki ruwa a ciki.
Ya juya ya fita a hasale ya samu yarinyar Asmaun daice ma lokacin yayi mata tas saiga uwar ta fito tana fadin don ruwan da nace ta dauko min din shine zaka zo kana kokarin fadawa mutane maganan banza.
Ke karbi ashirin ki karbo ruwan ki mayar masu don Allah kuma daga yau kada wanda naga ya koma shiga sashesu da sunan dauko wani abu.
Innan mu bafa fadan an dauki ruwa yakeyi ba yadda asmau ke buga masu marfin fridge dine yayan mu ke magana a kan shi.
Wani tsawa ta dakawa yar nata da saida ta kadu lokaci guda ta koma ta rakube a bayan Dije tana ci gaba da sauraron uwartasu dake sake magana.
Inna nifa ba ruwa nace meyasa ta dauko ba yadda take rufewa yarinyar nan fridge ne bai mun ba don Allah ai mata magana ta bari.
Yana fadin hakan ya juya ya tafi ya dawo dakin yana cicika kafin muji muryan Asmau tana sallama tare da fadin ga ruwanan ance in kawo.
Ya mike ya fito da sauri yabi bayanta yana kiran tazo ta dauke ruwan ko ya saba mata abin taron kurciya dukansu sai ya kwasa ya bita da gudu ita kuma ta koma bayan uwar dake hasale ta boye tana leken shi a inda yake tsaye yana wa uwar kallon mamaki.
Dake fada tana fadin don ruwa kawai zaka taso min ya a gaba zaka doketa ina dai don ruwan kake wanan hasalan gashi kuma na sayo na mayar maka da abinka.
Mama don me nake sayen ruwan ba don asha bane nake sayowa ni magana nake mata cewa ta dinga kula mata da kaya kada a bata matashi.
To ai shina nace mun daina tabawa ruwan kuma dana dauka nasha gashi nan mun biya koba shike nan ba ta fada tana mai wani irin kallo na tsana.
Kai Amadi maza koma ka zauna in fita zakayi kuma tai zuwa inda zaka ke kuma in dai radhin kunya abin yine ki biyewa uwarki gara ita takamanta a yanzu na haihuwan shi da tayine keko fa ?
Ina shi din daine gatan ku garin nan don in kun iya ko abinci sai ku daina cin wanda yake sayowa kunaci din karewan dai ke nan ke yar banza ko mutum daya kun gani gidan nan da sunan dangin uban ku halan ?
Zaki biyewa uwarku da bata san ciwon kanta ba kunawa yaro iya shige iri iri idan yai magana uwarku ta tare maku tundai ke Asmaun nan ba ma,un arziki kike ba wallahi don duk wani iskanci da iya shige kece ummul,abasin shi a gidan nan yanzu.
Ko shekaran jiya in kula dake da kika gama wanki yarinyar nan tana shigowa kika dauki ruwan wankin nan kika watsa mata da kadan a jikinta in ba Allah ya gyara ba.
Ido waje yace kin gani ba kingani ba Dije ni idan zasu takurawa yarinyar nan ne gaskiya saidai nabar gidan nan mu koma haya da ita don ba zan dauki hakan ba a rayuwata tunda yan uwanta ni basu raina min ba don me ni nawa zasu dunga wullakanta min ita ?
Jeka ai abin baikai na barin gida ba yar banza maganin shegiya mara kunya zanyi gidan nan tun kan aika ga hakan asirin mu ya tonu idan ka bar gidan nan yanzu da dan Amo ya gwajesu yaran banza kawai.
Ya juya ya tafi har ya shigo part din kuma yasa kai ya fita zuwa wajen dabbobinsu a nan Aisha din kanwarshi ta bishi tana fadin.
Yayan mu kaiyi hakkuri nima ynzu na gane gaskiya abinda akai wa amarya ba a kyautawa ko ranan ni nishigarwa maganan da Dije ka hwadi dazun da niyi magana innan mu ta dawo Asmau ta kwashi karya da gaskiya ta hwada mata.
Kije ai ba komai duk abinda mutum yayi don kaine don kuma baku san irin gidan da zaku hwada ba ai ga amre don Allah yayan mu kayi hakkuri damu da innan mu.
Ya duka yana gyara wurin dabbobin yana fadin ki tahiyar ki ai komai ya wuce garan nikan bandai yadda a rainawa matana da wayo don na aurota gidanga shin hakan laifina ?
To in abin yayi min yawa daukan mata zanyi mubar garin in koma gidan ubana mu zauna don su can basu gudun mu duk wanan abin na kula cewa dani innan ku ke adawa kiyayyana ne ya shafi Zahra yanzu itama.
Yarinyar tayi shiru na dan lokaci kafin ta furta don Allah kayi hakkuri ta juya ta tafi dama ya fadi hakan ne don yasan sako ya bata zai isa kunnen mahaifiyar nasu.
Yasan kuma ba zasu taba yarda dacewa ya koma gun mahaifin nasa ba a yanzu don irin yadda suka kulla shi a ransu irin yadda suke ganin yayi banza dasu a baya sai yanzu da yaro ya fara tasowa zaice zai koma garai.
Tana shiga ta samu suna maganan tsakanin Djje da innar tasu nan ta samu wuri ta zauna tana sauraren su kafin a kawo inda ta tsoma baki tana fadin.
Ai yayan yace tahiyatai zaiyi gidan ubanai wane uban ne ubanai uwar ta tambaya a hasale tana kallon yar nata.
Lokaci daya suke kara tambayan junan su da cewa wane uba kuma to ai yanzu kin gani kinji hukuncin da dan naki ke kokarin yankewa zuciyarshi yanzu akan halin da kika dauko mashi a yanzu.
Sai in bani raye hakan zai faru mutymin da yai tahiya tai bai ko taba tunawa da muwa ba a duniya sai shi da rashin zuciya ya daukeshi ya kaishi inda yake .
Yan uwanai sunka taho nan da barazana waisu ga dangi wagganshi ko yasan inda yake yanzu maganar banza da wofi kawai.
Ki dai natsu kada wani abu yaja maki bacin rai daga baya wanda ba maganin hakan a gareki yanzun dai kekin ka rage da shawaran da zai fusheki inba haka ba kina kallo danki ya gujeki saboda halinki na banza.
Shiru tayi har tsohuwar tagama ta naji tayi shiru tana nazarin zancen tafiya gidan ubanshi da kanwar nasa ta fada masu lokacin.
Ina kwance ina karatun handout a hannuna don abin ya dan shige min duhu shi kuma baida lokacin zama ya koya min karatu yanzu sosai.
Sallama nake ji a kofa yasa na aje takardan na mike zuwa falon din don ganin wace ke min sallaman Tani ce mai aikin ummah bansan lokacin dana sako fara,a a fuskana ba lokaci guda ina fadin.
Tani kece da yamman nan ta karaso ciki tana fadin wallahi uwar dakina yau dai nace barin lekoki muji lafiyan ki kwana biyu shiru koda yake hjy tace min ai kuna gaisa.
Tani ai nayi fushi rabon ki da gidan nan har na manta na dauka kema ke manta dani ai yanzu takai zaune inda taga alaman nake nufin ta zauna don ganin na cire filon dake wajen .
Uwardakina aure kan ya karbe ki kinga yadda kika koma kinyi kiba hasken ki ya karu ai kan zaijewa hjy dake cikin damuwa akanki da wanan labarin mai dadi wallahi.
Kin kyauta da kika rufawa kanki da mahaifiyar ki asiri inyi hakan ne garuku dan a cutawa rayuwan ku kekan alheri wanan aure ya zama maki yanzu.
Ba irin auren yan uwanki ba da yanzu ya komawa iyayyen ciki kullun ana gida tare da uwa shiyasa nake fadawa hjy cewa hakan yafi maku in anyi da sunan kuntata maku yanzu ya zama alheri a wajem ku.
Don ga zahiri na gani nikan walle hjy zataji dadin labarin nan nawa dama damuwanta shine ba komai kike iyaci ba a rayuwanki.
Banda matsalan abinci ko abunsha don gaskiya ina samu iya karfin shi Tani ba laifi yana iya kokarinshi dani alaman jin dadin hakan dana fada ya baiyana a fuskanta dkn bakin danaga ta kara washewa lokaci daya tana fadin.
Haka akeso ka godewa Allah da mai maka idan har yana maka ko da kadan ne watarana idan ya samu zai maka wanda yafi hakan ai.
Ki kara hakkuri sosai sama da wanda kikeyi din yanzu insha Allahu zuciyana tana bani cewa kinyi dace da miji nagari wanda kowa keson samun irinsa nan gaba.
Don nasan baki sani ba duk jumma,a yanzu zaije gidan ku ya kwashi kannen ki yaje masalaci dasu idan zasu dawo kuma ya hadosu da tarkacen makulashe ya dawo dasu.
Haka duk ranan talata yakan zo ya gaida mahaifiyar ki har yayi kokarin masu alheri hjy taso hana hakan amma nayi mata magana ta daina kinga kuwa ko hakan abin alfaharine gareta yanzu.
Aiko kinga bai taba nuna min yana zuwa gidan mu ba fa koda wasa bai nuna min hakan ba yakan dai kira waya ya bani mu gaisa idan yana gida wanan kawai nasani ni.
Na fada maki hakan ne don ki kara rike mijin ki da zuciya daya kamar yadda shima ya rikeki har cikin ranshi.
Muka dan taba hira wanda taso ta fada min halin da Aisha da Rukkaiya ke ciki a gidajen auren su nayi saurin tarewa da fadin Allah ya kyauta yasa su gane gaskiya su rikesu amana ta amsa da Amin.
Da zata tafi na hado mata clean da sabulun wanka da yan tarkace harda soyayyen nama tana ta godiya muka fito na rakata ta gaidasu Dije munyi sa,a inna ta dawo har ita suka gaisa tana ta kallon ledan dana rikowa Tani din tana son tantace abinda ke cikin ledan lokacin.
Bayan na dawo daga rakiyanta din zan koma part din mu naji muryan Dije tana kirana da yaki nan amarya nazo take fadin.
Nace matar nan ya kuke da itane wai na dan sake murmushi ina fadin mai aikin muce ita keyiwa mamata aiki ai.
Bana fada maki basuda alaka ba dama wanan yar garita sosai yar unguwan tudun wadace ai shinagani haka kawai mace ta mayar da kanta baya taje tanawa wata katuwa aiki kamarta.
Uwar Ahmed ta fada hakan yasa na dan daga kai na kalli gefen da take take naji raina ya baci har yanayina ya canza taci gaba da fasin baki fini ba don kwadai kina kwance da yayan ki ni ina maki wahala.
Muryan Dije naji tana bata amsa da fadin yafi mata alheri don hakan yafi mata yawon tallan gida gida wai kayan mata ana daukan ta yar iska mara kamun kai .
Inno tallan nawa shine na kika kira da iskanci ta fada cikin tashin hankali sai tsohuwar tace aikin nemam na kai da rufin asiri ma an zageshi mai zai hana masu yawon talla kica kica suna gogaiya da maza ba a zagesu ba.
Nan ta soma cewa ni dai waga sana,an bari nai nikai gara inyi zama hakan tunda ya zama illa garan yanzu kuma .
Nidai na wuce da mamakin su a raina ina mai jin zafin irin yadda uwar mijin nawa takan jefeni da kalamai haka masu zafi kai tsaye.
Ban taba fadawa Ahmed ba saidai idan shi yaji ko yagani idan yana gari ya dauki matakin hakan don yakan dan debi kwanaki yana school zaria inda yake hada masters din shi yanzu.
Yayin da ni kuma nake nan gusau ina hada nawa digree din wanda a lissafina saura shekara daya da yan watani na hada karatun nawa lokacin.
Tani kuwa ta koma da labari mai dadi wurin ummah wanda hakan yasa ummah farin ciki tayiwa Allah godiya don ko tani bata raga komai da taji ko tagani ba a ziyaran data kai min din harma da kari.
Ba abinda yaiwa ummah dadi a cikin labarin sai jin da tayi nayi kyau daki sosai a bakin mutane ga kuma karatuna yana tafiya daidai haka kuma ina zaune lafiya da kowa a gidan.
Dama damuwanta ke nan dani idan ta tuna cewa bana son yawan mu,amula da mutane sosai a rayuwana gashi kuma Allah ya jefani gidan yawa yanzu.
Satin shi biyu a can zaria din ya dawo ya dubamu ya samemu lafiya saidai ya samu wai kayan abincin su ya kare dole ranan ya fada kasuwa yayo masu sayayya ya kawo masu dan ledan semo da kubewa danye ya riko muna jin karan ledan yasa uwar kyala idonta akan roban tana son sanin meya dauko a ciki a zaton ta wani abin dadine ya sayo min.
Aisha ki dauki ledan nan ki kaiwa Zahra ta tuka muna shi don naga nata ya kare ya fada don kawar da wani zargi a zuciyar mahaifiyar nasa lokacin.
Da sauri yarinyar ta dauko ledan zuwa part dina ta sameni a dan kitchen dina na dora ruwa don ranan nasan yana gari zan girka muna abincin dare ke nan ranan.
Don in baya nan saidai nasha tea ko complain in kwanta ban damu da girka komai ba tunda ni kadaine kuma abincin bai dameni ba ni .
Amarya yayan mu yace in kawo maki ki girka ta fada tana miko min ledan dake hannunta din na juyo ina kallon ledan kafin nace me kuma ya kawo yanzu har na dora ruwan zafi zan zuba shimkafa a wuta ?
A gaban ta na bude komai ta gani tace na bata kubewan taje ta gyara min sai hakan yai min dadi sosai don dama shine abu mai wuya ga aikin nake gani gashi kuma ta taimaka min da gyaran shi.
Don haka na hada na wanke da kyau na miko mata tare da abinda zata gurje min shi ta tafi wurin su dashi ni kuma naci gaba da aikina.
Duk daba saurin aikin nake dashi ba amma ina kwantar da hankalina na girkashi da kyau yayi dadi saida saurin aikin da bandashi kawai ne matsalana.
Sai gani nayi Aishan ta dawo min da kubewan data fara gurza ranta kuma bace tana fadin anty kiyi hakkuri ban kai ga gamawa ba innan tace in dora girkin mu.
Na mika hannu na karba ina fadin aiba komai ko hakanma nagode ai saura kadan ki gama min ba zan dade ba zan gyara shi yanzu.
Tace bari dai in tsaya nan in karasa maki kafin na koma ita innan mu bansan abinda ke damunta ba haka wallahi dan wanan zatace din me na karbo maki aiki in tayaki bayan ga namu nan har na dora tukawa kawai zanyi yanzu ida na gama.
Muna magana tana gurza da sauri tana kallon hanyan shigowa part din namu saura kwara uku ta kare nina juya ina kokarin yin talgi mukaji muryan mahaifiyar nasu a bayan mu tana fadin.
Kekan anyi mara wayau da rashin sanin ciwon kai na rasama me zan kiraki dashi naji sanyi yanzu kece don rashin sanin ciwon kai zaki dawo nan kina kamawa wata aiki kin bar na uwarki can yana konewa ?
Kiyi hakkuri mama don Allah na fada daga inda nake tsaye nasha jinin jikina don banson wani abu ya hadani da matar nan ko kadan don ban hango kaunata ba a zuciyar ta.
Don Allah ki rufa min baki idan ba lalaci ba wanan dan girkin ne za ace sai an kama makishi ko me ko idan kin dafa damu zakuci ?
Naga yar nata ta kallota da sauri tace ke kuma munafuka kallon me kike min don na fadi gaskiya tasan ba