Showing 102001 words to 105000 words out of 304363 words

Chapter 35 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33319

Yanzun zamu shiga hawan Mambilane daga nan mun fara tasan ma nahiyar mu na mambila ke nan daga nan ya zakaji yanayin garin ya sauya ma daga nan .
Saidai tsohon bai gama rufe baki ba yaji driver na fadin banga mota nabi hanyar nan ba idan mun kai nan ga kadan mu tambaya muji lafiyan hanyan yaya yake.
Nan yaga yan cikin motan a tsorace suna fadawa driver cewa ya dakata kawai su kwana a dan kauyen gaba zaifi da asuba sai mu kama hanya na gaban motan ya fada.
Bari dai mugani malam idan hanyar zata biyu sai mu mike zaifi inji drivern shidai yana jin su yana zaune a bayan mota yayi shiru yana addua.
Ummah ce zaune a falonta da safiya Tani maiyiwa ummah din aiki ta shigo ta sameta suka gaisa take tambayan ummah din ko anji mata motsin uwardakinta anyi waya ko da ita ?
Ta kira jiya mun gaisa kin santa da shiririta ko sakarcine wai tayi mafalki ta falka da safe duk jikinta ya mutu ita tana jin tsoro ko waya fada mata mafalki gaskiyane oho ?
Da sauri Tani din ta kalli ummah tace hjy kune dai baku daukan abu da muhinmanci a yanzu ai bai kamata ko kice haka ba da sau ki tambayeta kiji akan me tayi mafalkin aji ?
Duk da dai ba duka mafalki yake zama gaskiya ba amma da haka dan karamin abu yake zama babba watarana saidai sakaci irin namu na mutanen yanzu ke hana mu dauki mataki kan abu sai yazo ya girma yadda bamu iya dauka muce muna neman sauki a kan abin.
Yarki ta girma yanzu ba za,asata a sahun marasa wayau ba don tasan ciwon kanta yanzu kama yayi kiji irin mafalkin kinga in na sadakane sai ai mata sadaka a nan Allah ya tsare zaifi.
Wanan ne kuma Allah bai ban ikon yi ba ko ince zan mata sadakan banyi ba gaskiya ummah ta fada a dan damuwan hakan don maganan Tani din yayi tasiri a zuciyar ta.
Tasani cewa tun tana karama wani lokaci manya kance sunyi mafalki bari suyi sadaka don Allah ya mayar da abinda sukai mafalkin alheri garesu.
Amma gashi ita bata bada daman hakan ba ga yarta sai binta da tayi da fada tana kira mata sakarci komai sai ta saka arai ya dameta don mafalki zatace tana jin ciwon jiki.
Iyayye mu farga da wanan maganan a yanzu a kan yayan mu don a yanzu zamani na tafiya ne da nau,i biyu wayewa da jahilci don har yanzu akwai masu jahilci dake sihiri akan mutum kuma Allah zai iya nunama a mafalki wanan baiwane da yawancin mutane da yawa kedashi a cikin rashin sanin hakan garesu.
Mata mu farga da yawaita yin sadaka ga yayan mu don min sadaka riga kafin masifa ne ga bawa sadaka baya tafiya a banza inji masana addini komai kankanta abin sadakan zaiyi amfani ga maishi.
Musan man sadakan abinci, kudi, tuffafi kosai sugar kuli,kuli alewa naira darin ki sai yai maki riga kafin rayuwan ki dana yayan ki duniya da lahira.
Amma yanzu wata ana sati daya ko fiyema da hakan bata mika wani abin ba da sunan sadaka saboda Allah da Annabi Allah ya kare ya tsare ya bada ikon yin hakan Amin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣3️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Suna tsaye inda suka parker motan a wani dan kauye wani mutum yazo wucewa yake fadin yau tun karfe goma ai hanyar ba lafiya kunyi arziki da kuka tsaya nan din ai.
Jin haka yasa driver fadin sai mu kwana a nan ke nan da safe sai mubi hanya zaifi idan mun fara ganin motoci sun fara tafiya dama wani lokaci sukanyi haka irin wurin nan saidai ba ko wani lokaci hakan ke faruwa ba.
Da zakabi zance na kawai mu mike in sha Allahu ba abinda zai faru damu dattijon ya fada da sauri driver ya tareshi da fadin a,a baba kada muyi gangancin yin hakan mu dawo muna da mun sani mu dai bari ido na ganin ido mubi hanyan da safe kawai.
A nan suka kwana cikin motan zaune barci rabi da rabi sai da sukai sallah asuba suka ga wata babban mota tabiyo ta wuce da kyat suka samu drivern motan ya tsaya suka tambayeshi yace hanya da sauki yanzu.
Suma suka dauki hanya zuwa hawan mambila lokacin duk suna a takure don sanyin da yaiyawa a lokacin gashi babu wasu tufafi masu nauyi a jikin su da zai kare masu sanyi a lokacin.
Ikon Allah Ahmed din ke kallo a lokacin don yanayin wanan wajen da bai taba zaton ko tunanen cewa akwai irin wanan yanayin ba a kasan nan.
Don dubaga yanayinsu na zamfara na zafi daya fito cikin shi ga iskan zafi da rana a ko wani lokaci suna cikin hakan su a zamfara.
Amma sai ga yanayin nan din ya bambanta da yanayin su kuma wai a kasa daya duk ake da wanan bambamcin yanayi din yana faman kiyasta hakan a zuciyar shi.
Samari mun fara shiga yankin mambila fa daga nan da ace kasan barin da mahaifin naka ya fito kaga sai mu ajeka a daidai inda zai sadaka da gurin shi cikin sauki.
Zama ya dan gyara don fahintar cewa dashi drivern ke magana a lokacin yace wallahi baba ban san ainihin garin da yafito ba na dan san cewa ance yace shi din mutumin chedewane.
Zaka sha wahala koda zaka gane amma sai ka wahala sosai a gaskiya don gane mutum irin haka bai yuyuwa cikin lokaci daya haka kai tsaye dole yana son lokaci mai tsawo sosai don bincike drivern motan ke fadi.
Hakane kan gaskiya na gaba motan ya amsa shima yana fadin ai irin wanan tafiyan yana son bincike sosai kafin mutum ya fito daga gida.
Amma ka fito haka bakai bincike ba ka kamo hanya daga kai saikai zuwa neman mutum a irin wanan wuri haka kamata yayi kazo tare da wani ko ka bincika yadda zakayi saurin ganewa kafin kazo din.
In sha Allahu ganewa zaiyi ai me tambaya baya bata tunda ya fito da niyar alheri a zuciyan shi Allah zai sadasu a cikin salama wanan tsohon na gefen Ahmed din ya fada.
Allah yasa don yana da wuya a wanan zamanin ya iya ganeshi haka kai tsaye babu wani sheda da zaikaishi inda yake drivern ya kara fadi.
Gaskiya yana da wuya kan ya gane haka kai tsayen nan yadda ya fito neman shi nan saidai a gwada kawai ko za,ayi sa,an hakan daya mutumin ya fada.
Ina ganin aiga baba nan don yace shi a Gembo zai sauka kaga sai yai masa masauki ko wani taimako ga hakan don gaskiya idan ba haka ba kan zaka sha wuya gaskiya ga wana lamarin drivern ya fada a cikin muryan kulawa.
Haka ba matsala bane idan zai iya zama dani mu dai tallakawane sosai ba wani gidan zamanine gareni ba donshi naga kamar dan masu haline ?
Ta hali akeyi yanzu ya samu wurin mafaka shine abu na farko da yakamata ya farayi idan ya sauka din inji diban motan.
A a fa ai kaji abinda baba ya fada daganin shi gidan masu hali yake ciwon hakane kawai ya fito dashi daga gida kaga kuwa aisai hotel irin wanan.
Ba irin gidan su baba don baba yace shi tallakane baida hali kaga saukan irin wanan bakon ai matsalane wanan dayan mutumin ya fada.
Ahmed din yana zaune yanajin zancen da kowansu ke fadi a lokacin har saida yaji driver na fadin kaiko dai ai sauki ake nema mashi yadda zai samu saukin lamarin ba zancen jin dadi bane a nan kaji yaro.
Ahmed din yace hankalina yafi kwanci da nabi baba gidan shi tunda har ya amince da hakan saukine ai Allah ya kawo min ga hakan.
Kaji gaskiyan kenan yaro ka fadi gaskiya ba karya Allah ne ya kawo saukin lamarin ya hadaka da baba a motan nan har tafiya ya hadaku inji drivern.
Ya kara da fadin Allah yasa a dace kaji nasan irin abinda kakeji a zuciyan ka na zafin hakan don wasu ma na iya shegantaka su kiraka da sunan banza duk da sun san hakan ba laifin ka bane laifin iyayyen nakane ya jama hakan ?
Insha Allahu zanyi iya kokarina kaji yaro ai da na kowane Allah dai yasa mu dace aganshi a cikin sauki yanzu dai muyi fatan Allah ya kaimu lafiya tsohon ya fada.
Dijece tunda duku dukun safiya ta sallamawa malam Tanimu a cikin tashin hankali tana fadin malam tanimu kasan yaron nan bai taba irin tafiyan nan ba.
Yaje haka ya dade ba tare da ansan inda yake ba ko yaje ni abinda nake son ku gane ke nan hankalina yaki kwanci jiya a raye na kwana ina tunanen ko wani halin yake can ciki ?
Malam Tanimu ya nisa yace Dije nima lamarin ya fara dan taba zuciyana don tun jiya nakai dare a waje ina dakon ko zanga dawowan shi banga ya dawoba har na shiga gida.
Bakaji ba ina fadi kuna ganin damuwata yanzu ba a wasa da lamarin batan mutum gashi ya tafi bai fadi inda zai tafi ba balle aje can din aduba ko lafiya yake ?
Shike daga min hankali Tanimu Dije ta fada a cikin wani murya mai rauni yace yanzu dai barin fita zuwa bakin kasuwan su na yan hatsi in tambaya ko Allah zaisa in samo labarin shi a can.
Tare suka fito cikin gidan malam Tanimu din iyalinshi na masu fatan Allah yasa a gano inda Amadi din ya shiga bayan sun fito wajene malam Tanimu din yacewa Dije ta koma gida shi zai karasa zuwa bakin kasuwa din ya binciko halinda ake ciki.
Ya kama hanya ya ita kuma ta kasa shiga gidan sai kawai ta juya ta shiga dayan gidan dayafi kusa da gidan nata ta shiga taba labarta masu halinda take ciki na tashin hankali din.
Suma sun nuna nasu tashin hankalin sosai a hakan sun dai dan jajanta mata sun bata baki ta danji sanyi ta koma gida tana dakon dawowan malam Tanimu din daga bakin kasuwa daya tafi.
Malam tani ko a kasuwa yayi neman labari amsa daya yake samu shine rabonsu da Amadi kwana biyu ke nan amma dai yabada kudin hatsin shi ga ubangidan shi kuma an sawo mai har sun samu shiga sun zama kudi.
Haka ya juyo ya dawo zuwa gida a sabule jiki ba karfi don rashin sanin inda yaron ya shiga ya samu iyalinshi a cikin jimamen maganan.
Nan yake fada masu abinda ya jiyo a kasuwan tare da uwargidan shi suka dunguma zuwa gidan Dije suje su sanar mata da halinda ake ciki.
Sunyi sallama sun samu Dije saman dutse da suke zama suyi alwala a sama ta zauna tayi tagumi da hannu daya tana faman tunane.
Sallaman su yasa ta dagowa tana amsa masu ta gaida malam Tanimu din da dawowa gida tare da tambayan shi a gagauce da anyi sa,a ab gano inda yake din ?
Girgiza kai Malam Tanimun yayi yana fadin wallahi Dije abin ya fara cin tura don kaf wurin nan nasu na zagaya babu labarin shi labari daya na samu shine yaba da kudin hatsin shi yace ba zai samu zuwa daukowa ba a ranan.
Kuma har sun dauko mai suma suna dakon zuwan shine a yanzun don har sun sayar mashi dashi kudin yana hannun shugabansu na wurin da suke aiki tare.
Kuka Dije ta saka masu lokaci guda tana fadin shike nan dan marayan Allah ya bata ke nan sun ingiza min keyan shi ya shiga duniya dan anga ya fara tasowa mun fara fita a cikin talauci shike nan sun kaimu sun baro.
Yau in yaron nan ya bata har ya tabbata kurciya akai mashi me zan fadawa iyayyen yaron nan ni Dije sai kuma ta sake sake kuka cikkn tasshin hankali da ban tausayi.
Har makwabta suka fara shigowa gidan kafin ance haka gida ya cika da mutane masu zuwa jaje labari ya fara baza gari cewa Amadi ya bata an masa kurciya ya shiga duniya.
Sai gashi har an fara sakawa a median cewa ya bata abu ya fara yawo a cikin gari wa yanda suka sanshi sun shiga damu hankalinsu ya tashi a irin hakane har hanne ta gani a wayanta ta fara neman layin zahra hankali a tashi .
Barci nakeyi wayan hanne ya shigo min da kyar na iya dagawa na amsa sallaman da take min din na dauka take tambayana wai naga labarin dake yawo a yanan gizo kowa ?
Ban gani ba hanne na fada gabana na faduwa tace wallahi nima yanzu nagani cewa wai Ahmed ya bata ya bar gida an masa kurciya a wurin sana,an shi abokan gaba sunga ya taso sun batar dashi cikin duniya.
Ahmed din na sake tambayan Hannatu din tace wallahi Zahra ashe bakiji ba shine ai yasa na kiraki yanzu in sanar dake ki san halin da ake ciki.
Dan murmushi nayi nace to naga jiya munyi waya dashi da dare yace min yana Taraba state ya tafi wurin mahaifin shi kinga ko ashe ba bata yayi ba ke nan ai.
Dan Allah ki bari Zahra kunyi wayafa dashi kikace nace zan maki karyane kan hakan nikan wallahi munyi waya yana hanya yake fada min.
Amma kinga don Allah ki iya bakinki tunda bai fadawa kowa inda yake ba don yanzu kina furta hakan sai a canza maganan kuma ya koma wani magana na daban har Abba yazo yaji ya gane muna tare dashi har yanzu.
Hakane kuma zahra Allah ba zan fadawa kowa ba tundama har kinsan inda yake ai dama hankalinane ya tashi da zancen batan da akace yayi wai an masa kurciya ya bar gari.
Don Allah dai na rokeki hanne kada ki kuskura ki furta wani abu har ace nina fadi kinsan Abban mu zaiji zan kuma shiga cikin matsala ke kin sani.
Tace wallahi na fada maki banyin zancen nan da kowa idan Allah ya dawo dashi ai zai nemi wanda ya bata mashi sunan aji ta fada.
Nikan muna gama waya da hanne din nayi ta tirayin din layin shi baya shiga amma hakan bai dameni ba daga nan na fita zuwa kitchen na samu mutane mukayi ta hira har ma na manta da zancen.
Don ban dauki zancen da ma,ana ba a zuciyana haka yasa banji komai ba a lokacin kan zancen har zuwa lokacin dana daidaici cewa mutanen gidan sun kusa dawowa na shige daki daga sunan sallah ban sake fitowa ba nayi wanka na fito nayi sallah na sake komawa na kwanta.
Sai shida na fito gaida mommy don nasan ta dawo gida a lokacin saidai ashe shigowan ta ke nan gidan wai ta biya wurin tellan data bawa dinkunan buki ta karbo.
Tana zaune a falo sai gani na fito da fara,a a fuskanta ta na karasa wurinta ina mata sannu da zuwa tace come come my daughter yanzun nake zancen in tura a kiraki.
Kizo ki gwada kayan nan ko zasuyi sizes din ki don kwatancen ki kawai nayi mashi ya dinka maki duk da naso yazo ya ganeki ko kije amma yace aiki yayi masu yawa sosai.
Na karasa zama ta miko min leda da kaya a ciki na dadu dasu sunsha guga na karba ina fadin thanks mom haba dai gwada mu gani ko zasuyi maki idan ba matsala ga dinkin.
Karba nayi na fara budewa tace yawa kinga wanan shine za a saka ranan kamu namu ankone na gidan ango wanan din.
Abu na farko dana fara dubawa shine dinkin bujen don ban saka bujen daya matseni sosai don haka Allah yayini ni bana son kaya su matseni tam a jikina sai in koma ban walwala ko sakewa karshe ma saidai in kyautar da kayan.
Naji dadin ganin akwai space a dinkin tellan koda ya matse zan iya budeshi haka nayi ta dagasu har kala biyar tana min bayanin kayan da ranan da za a sakasu din.
Bayan na gama ganine na hada a wuri daya na mike daga inda nake zaune na durkusa a gabanta ina fadin mommy na gode tare da dan fadawa saman jikinta ta dafa min baya tana fadin haba haba dai ki bari don Allah zahra .
Kkme nayi maki kin cancanci hakan gareni tunda kun yaba dani har kuma kun yarda da zamana a cikin ku ba tare da nuna min hassada ba ko kishi don me nima zan gaza daku yanzu.
Shigowan Abba yasa na mike da kayan a hannuna bayan na gaidashi na shige ciki ina tunanen irin hakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login