Showing 165001 words to 168000 words out of 304363 words

Chapter 56 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33347

a zuciyana.
Naga laifin me nayiwa innan su Ahmed haka ta tsani sai naji ina son yin wanan zancen da wani ko zan samu mafita duk ban taba yin wani zancen ta da kowa ba ni kadai nake shanye abina a raina duk abinda akai min din na cin fuska.
Saida ba zan iya wanan maganan da ummah ba don nasan itama tana can da nata tarin matsalolin datake fuskanta gidan wanda kullun bai karewa garesu.
Hannatu ya kamata na kira zuciyana ya bani hakan duk da shekarun mu dayane ba wani shawaran zansamu da zai gamsheni ba amma ita din ya kamata na kira na fara jin me zata fada min kan hakan.
Kiran dana danna mata sai gashi ya shiga ta dauka tana fadin yar halak yanzun nan nagama zancen kifa a raina wallahi tun shekaran jiya ba muyi waya dake ba.
Wai kina inane yanzu ko kin samu tafiya sokoto din ne na tambayeta don mu katse zancen data dauko din a lokacin nasan tana iya bata muna lokaci da surutunta a hakan.
Wallahi ina gusau dai ban tafi sokoton ba har yanzu don wanda zanbi din baizo weekend ba nace kai hanne akwaiki da son banza yanzun don dan kudin motan da zaki biya kike garin nan nan har yanzu ?
Bayan kin sakawa gwaggo ran zuwan ki yanzu ki zauna kina jiran bati a nan tace ke an fada maki kowa irin kine da Master ya kamawa kina yadda kikaga dama.
Humm wani master ni dama na kira najine idan kina gari akwai zancen da nake son muyine dake don abin ya daure min kai sosai wallahi.
Da sauri naji yanayin muryanta yai kasa tana tambaya meke faruwa kuma zahra nace sai kinzo zakiji komeye but kada ki damu ba don ba komai bane mai yawa.
Da haka muka kashe zancen da ita akan washe gari zata shigo wurina mukai sallama ta kashe wayan har lokacin ina faman sake sake a zuciyana nako in fada mata ko kuma nayi shiru kawai in bar zancen a ckkin raina.
Saidai wanan zancen tafi karfin na barwa cikina shi don in dan tuntubi wani inji wani shawara zan samu na sake cusa kaina gun uwar mijin nawa da nake ganin hakan shjne mafita a lokacin.
Sun fito daga lectures yana sauri ya koma masaukin su don azumin daya wuni dashi a bakin shi ga azumi ga kuma faduwan gaba da yake ji a ranan yana damun shi wanda hakan yasa shi kara zama shuru a lokacin.
Ya iso gidan da suka kama suna zama shida abokin shi babu kowa haja yasa ya bude dakin ya shiga ya samu wuri ya kwanta don akwai sauran lokaci da zai dan gangara bakin titi ya dan sayo abinda zaiyi buda baki dashi lokacin.
Barcine ya daukeshi a hakan ba tare da niyar hakan ba a lokacin can ya fara mafalki da ya bashi mamaki don mahaifin shine ya gani a gaban shi yana tsaye nisa dashi kadan .
Sunawa juna kallon kallo kafin yaga ya miko mashi hannu alaman yazo gareshi sai yaga wata mace tazo da sauri ta shiga tsakanin su yana ganin hakan shi kuma juya ya bar wurin da sauri kafin mahaifin nasa ya farga da hakan .
A daidai lokacin kuma ya mike zubur daga barcin nasa tare da wani irin zufa dake karyo mai duk da yabar kofan dakin nasu a bude amma zufa yakeyi har yana tsiyayo mashi ya jike sharkaf duk jikin shi.
Zai iya cewa wanan ne karo na farko daya taba mafalki da mahaifin nasa irin haka sai abin ya fara bashi mamaki gashi shi kadai a dakin nasu lokacin.
Macen nan fara da yaganine ta fado mashi a rai yake mamakin ita kuma wacece a garesu datazo ta shiga tsakanin su a lokacin da baisan abinda mahaifin nasa keda niyar fada mashi ba.
Daba don yamma yayi a lokacin ba da zai koma barcin ko zaiyi sa,a yaci gaba da wanan mafalkin da baisan dalilin zuwan shiba gareshi a wanan lokacin.
Haka yasha ruwa a dadare ranan bai samu tabukawa kanshi komai ba don ko dan karatun da yakayi bita a lokacin bai samuyi ba don yadda yake jin kanshi cikin damuwa a lokacin.
Waya dai ya samu yayi da sahibarsa Zahra yaji lafiyanta dana mutanen gida a bakinta a nan take dan fada mai zancen bukin da za,ayi a cikin gidan nasu da suke kira da babban gida a wajensu.
Take ya katse ta da zancen yana fadin Zahra kibarsu da bukin su don mutanen nan ba kaunata sukeyi ba zahra kinsan sani ba wanda cikinsu da yake nuna damuwan shi a kaina don haka kija nisa dasu kamar yadda nima nake nisa dasu a yanzu din.
To amma Master kasan akwai hakkin zumuci tare da hakkin makwabtaka dasu ba zasu dauki hakan da laifinsu bane sai suga namu laifin ne a yanzu.
Haka kuma Allah ba ruwan shi da wanan dalilan donshi ya sharada da ayi zumunci a tsakanin zumu kaga hakan sai, , ,
Zahra ki barsu idan lokacin yayi zamuyi zumuncin dasu amma ba yanzu da suke muna kallon fakirai ba a idanun su.
To shike nan ta fada a sanyayye yadda tai maganan yasan zancen bai mata dadi ba a ranta amma gudun bacin ranshi yasa ta amsa mashi kamar yadda yake son ayi.
Irin wanan halin nata yasa yake kara jinta a rashin don zahra ta daukeshi a na gaba da ita sosai yake jin sonta a ko yaushe yana kara shiga zuciyar yadda bata nuna cewa ita din mai gatace fiye dashi a zaman su na aurataya tana tsayawa a inda ya ajeta a rayuwan ta.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[22/04 3:41 PM] +234 806 730 5151: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣7️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Barkan da wanan lokacin yan uwa musulmai ubangiji Allah ya karba muna ibadun mu Amin Allah ya bamu ikon jajircewa a wanan watan mu samu falalan dake cikin sa Allahuma Amin.
Duhune ya mamaye dakin baka ganin komai a lokacin sai duhu a hankali ya dago santala talan hanayen shi ya kaisu ga makunin wutan gefen gadon dake dakin ya kuna.
Hjy Yabice a gefensa kwance tana kwasab barcin ta a lokacin dan hasken daya kunna bai hanata barcinta ba a lokacin don asalima ita bata san ya kunna wanan wutan ba a lokacin.
Bin dakin nasa yakeyi da kallo zakace bakoneshi a dakin ranan ya fara ganin dakin nasa don yadda yake bin ko ina na dakin da kallo lokaci guda.
Hankalinshi ne ya karkata zuwa mafalkin daya tasheshi a lokacin tabbas yasan a yan kwanakin nan mafalkin wanan matashin na yawan damun shi a cikin barcin shi.
Saidai ya kasa tuno inda yasan fuskan yaron mai zubi daya da nasu don yasan ba danshi yasir yake gani a mafalkin nasa ba son wanan yafi yasir din shi tsayi da haske da mugun kama dashi wurin kamanni .
Mikewa yayi zuwa bandaki ya dauro alwala yana kokarin tayarda sallah lokacin ne matar nasa ta dan falka ta sauke kallonta gareshi .
Idan ba gizau idon take mataba sallah yake kokarin yi a lokacin duk da mamakin sabbin halaiyan shi a yanzu nauyin barcin dake idon ta bai barta taci gaba da cigaba da mamakin nashi ba.
Kamar yadda shima a yanzun yake mamakin kansancewarta matarshi don gani yake komai ya faru dashine a cikin rashin sani ko a malfaki.
Iya abinda zai iya tunowa a baya shine irin tsana da tsangwaman da bangarenta suka nuna mashi a baya kasancewan shi da daya tillo daya fito a wurin mahaifiyar shi kafinta bar duniya.
Da yadda ya taso a cikin shi suna nuna mai hasada da bakin ciki irin na yan uba a lokacin wanda badon shi din ya iya kanshi ba da ba yadda zai taso a gaban ita uwar rikon yabi din wace kishiyar uwane a gareshi lokacin kuma mahaifin shi ya hana bangaren uwan shi dasu daukeshi.
Yabi yar kanwar Attuce data rasu tabarta tana karama a cikin yan uwanta su hudu duk Attu din ta kwasosu ta rikesu lokacin a hannun ta tana tayar dasu a cikin gidan mahaifin nasu.
Kasancewanta ita din matar basarkene a lokacin kuma mai abin hannun shi don yana da dukiyanshi da abin hannunshi sosai don haka abinci bai masu wuya koya katse masu a gidan yasa ta dauko yaran ta hada da nata ta rike
Akan yaran tana iya sabawa da kowa a gidan a wanan lokacin don yadda ta daukesu a ranta amma diyan mijinta kiri kiri take nuna masu kiyayyanta a fili.
Kowa yayi mamakin batan habu dan gaske da suke mai lakani da hakan don kasancewan shi da daya dasha wuyan kishiyoyin uwarshi kuma yana raye a cikin su ya tashi hakana.
Lokacin daya fara bude ido da kasuwanci mahaifin nasa ya dauki wani kason daya gada a wurin mahaifiyarshi sai wanan matar abin yai mata bakin ciki sosai a zuciyar ta .
Duk da mijin nasu ya fahintar da ita cewa kason shine na mahaifiyar shi ya fara juyawa amma sai bata yarda da hakan ba tayi ta kokarin ganin ta hada kai da sauran iyalan gidan aiwa mijin nasu banga kan hakan sai sauran basu mai da kai ga hakan ba.
Wanan yasa taje wani dutse wurin wani boka yai mata aiki suka turashi uwar duniya daga tafiya ba a kara jin duriyan shi ba kuma har tsawon wani lokaci.
Fahintar hakan da amin nasa sukayi sune suka shiga suka fita sukai masa aikin dayafi nata har Allah ya dawo masu dashi gida kwatsam aka ganshi ya dawo a jirgice babu wani abinda ya dawo dashi lokacin.
A binciken mahaifinsa ne ya gano cewa yayi aure acan inda yake harda karuwa amma ba hausa ya aura wanda su kuma basu son hada jinin su da hausa don sunyi yakinin cewa hausawa ba abin yarda bane.
Wanan yana cikin shawaran tsohuwa mallam a lokacin ita ta shiga ta fita data gano cewa dole fa sai tabi ta wani hanya sanan bukatanta akan habu din zai biya.
Don hakane ta dauki yarta datake gabanta a lokacin ta mika masa da sunan irin hadin su na fulani wanda mutane da yawa a lokacin basu so hakan ba.
Saidai zaman ta mai fada aji a gidan yasa kowa yaja bakin shi yai shiru ya zura ido suga manufanta duk da sun san me hakan da tayi ke nufi amma babu halin magana akai.
Shima din uban gayyan bai cikin hankalinshi don gaba daya juyashi akeyi akan komai har zuwa lokacin nan da abu ke shirin faruwa dashi din.
Sallah ya tayar don neman sauki a wurin ubangiji bai daga ba har dan gyangyadi ya fara daukan shi wurin kuma anan ya sakeafalkin daya daga mashi hankali sosai.
Ina zaune muna fuskantar juna da ita mamakine a fuskanta karara wanda take mamakin abinda nake fada mata din a lokacin kafin ta nisa tana fadin.
Ni abinda nagani shine kifita zancen kowa zahra ki kama mijin ki tunda bashi ke maki hakan ba kuma shi har yana nuna rashin son hakan a fili kanki.
Don me zan fita zancen hakan yanzu ina yake ina tare dasu ya tafi ya barni a nan zaune kinga ke nan ya zama dole in gyara zama tsakanina dasu tako wani hanya.
Kaita girgiza tana fadin Zahra ke nan ki rabu da irin matan nan masu kishi da matan diyan su duk abinda zakiyi ba zataga hakan ba don idonta ya rufe ga son danta a yanzu.
Tana ganin komai ya samu akanki yake karewa duk abinda yake masu bata ganin hakan ita gani take keyske kashewa ke kadai a yanzu.
Kada ki rage ki kara ita irin matan nan ne masu adawa da hassada tana ganin kin fito gida akwai kin fisu kina daga masu kai ko tana ganjn kedin baki cancanci hakan ba garesu ai.
Ta manta Allah ke bayarwa a inda yaga dama shike zaba yaba wanda yaso a rayuwa har ma ke wani hali itin na diyan masu kudi kike dashi zahra tunda abinki bai rufe maki ido ba ga kowa.
Ita bata tunanen arzikin kine master ya shafa har ya dago yakai haka a yanzu idan ita bata san wanan ba kowa ya sani a gari don da yaya dan nata yake cikin garin nan yana yawo a kafa a talauce zabar tausayi.
Murmushi nayi ina fadin hannatu ke nan wanan kuma wani hukuncine na Allah ya nuna hakan amma ai ban isa in masa arziki bani.
Nasan da hakan amma mutane sun camfa hakan kuma hakan maganan yake don ko last week saida su munir sukai zancen ku irin wanan .
Don haka ni in nice wallahi zan bita a yadda take son mu zauna don nasan ba zata iya sa master ya sakeki ba saidai abinda ya fito daga Allah.
Hannatu bawai akan hakane na nemi shawaran kiba a yanzu na nemi sharankine naji hanyar da zan fito mata mu zauna lafiya shine dalilin dana nemeki shawara yanzu .
Akan hali irin nakiba zahra na sanyin hali amma inda nice wallahi daidai zamuyi da wanan matar amma tunda kince haka yanzu ai shikenan .
Shawaran da zan baki shine ki kara harkuri ki bita da halinta sai kuma yaran nan kiyi kokarin jansu a jiki kina masu dan alheri kinga insunga hakan ba zasu biye mata wurin shirmenta ba.
A karshe kuma kila ita din ayi sa,a ta sauko don ance idan kana son kama uwa kaso danta fiye da ita zaka kama zuciyarta a dan kankanin lokaci.
Shiru nayi ina nazarin zancen ta wanda ba komai nake tunane ba a hakan ta ina zan farane yanzu don iya bi da kyautatawa ai naga ina masu amma duk bata ganin hakan ita.
Kamar tasan me nake tunane sai naji tace irin kayan ki dake aje baki amfani dasu din nan ki dan rika basu shi idan sunyi kwaliya da bai maki ba kikirasu ki gyara masu da hakan har dai ki jawosu zuwa jikin ki kubarta can tana haukan ta ita.
Wallahi wanan shawaran yayi kamar kin shiga zuciyana dama kingani hannatu don ina son masu hakan ina tsoron matan nan don sam bata boye kiyayyarta gareni kada tace nabawa diyan ta kwance sha tusa don naji ranan tana zagin kanwarta da hakan data aiko mata da wasu kayan jikinta.
Haba dai zahra wasu kayan ba amma ba dai irin nakiba da wasu sakawa daya ko biyu kikai masu a jikin ki ina za,a hada da wanan da nasu kilama yasha wanki ashirin albarkahakan
Kai kajiki da wani zance yanzu dai zan gwada wanan shawara naki in gani idan anyi nasara zanfi kowa farin ciki da hakan.
Don wallahi hannatu wanan matar ta daga min hankali sosai niba auren da tace zataiwa master bane yadameni kamar yadda take fita tana aibantani wurin mutanen ta.
Kada hakan ya dameki da baki da alhakinta ai gashi har dakin ki akazo aka fada maki komai kunya kuma ya rage a gareta ranan da zata gane gaskiyan hakan.
To amin na bata amsa ina mikewa na fita na debo mata abincin dana girka don zuwanta don nasan halinta bata wasa da cikinta.
Na samu takai kwance lokacin tana duban wayanta dake hannunta na dire abincin a gabanta kamshin yasata dagowa tana fadin kai don haka nake sonki mutumiyar.
Kamar kinsan wallahi a matse nake nan ina shirin tambayan ki ko akwai abin tabawa na taba sai gashi kin kawo min tana mikewa zaune take fadin haka .
Fita nayi na dauko muna drinks da cups na kawo muna na zauna muna ci a lokacin ne Aisha ta leko part din tana fadin .
Matar yaya kina cikine kin kwanta tana lekowa ta ganmu zaune a falo muna cin abinci hannun ta rugume da kayanta sai kuma ta dan dare daga kofa tana fadin ashe kina da bakuwane.
Ina wuni hannuta ta amsa mata ba wani sakewa nayi saurin kawar da hakan da fadin ashe baku tafi ba aina dauka kun fita tun dazunne wallahi naji gidan shiru.
Muna nan wallahi innace dai tun safe take can yanzun ma Asma,u ta dawo take fadin wai inna tace maza mu shirya mu zo za,a fara Dj .
Dj kuma hannatu ta fadi hakan cikin mamaki koni naji wani iri yadda tai maganan nayi saurin fadin ba bukin gidan su akeyi ba keko taso ace nata sunje mana koni don Master baya garine aida tare zamu dasu.
Nace don Allah ko iron dinki na kusa in dan goge tufafina kafin nepa su dauke wuta nace eh yana nan dama ke baki gogeba tun jiya bayan kinsan yau akwai buki ?
Nifa ba wani damuwa da wanan bukin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login