Showing 234001 words to 237000 words out of 304363 words

Chapter 79 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33314

fadin me muka samu kuma wurin ummah haka harda wahalan taso da Tani tayi.
Ba kaje gidan gaida itaba shine ta hauni da fada wai ban fada masu cewa zaka dawo bashine take tayi min fada kuma ta aiko Tani da wanan din nima bansan ko meye a cikinsa ba don ban bude ba.
Allah sarki uwata ninasan cewa a yanzu ummah tafi sona akanki ai don wallahi har na dawo ta kan kirani a kai akai taji lafiyata keko kina can kina kayan fushi dani.
Aina sani tunda naje gaisheta ta hauni da fada wai na fito baka gari dole tasa na dawo gidan nan ban shirya ba a ranan kai amma ummah tayi min daidai wallahi haka nake fata dama in samun uwa mai mutunci da sanin ciwon kai.
Kinga nafi dace da sa,a don ni nawa uwar matan tana sona keko uwar mijin ki gakunan kullun sai anjiku a gidan nan kuna rigima da ita jin hakan na danji sanyi a raina nace.
Ki inna ai zata daina watarana kawai dai tana amfani da zugin wasune tana ganin laifina a yanzu amma wataran zata gane gaskiyan hakan insha Allahu .
Gyara zama naga yayi yana lumshe idanunshi can ya bude yana fadin naji dadi da har kika fahinci hakan zahra ni kaina yanzu nagane cewa tana amfanine da shawaran wasu a kan ai.
Ledan hannunshi na kalla daya bude kai wanda bakatsina ta haifa a duniya taji dadin ta haka idan bakatsine mahaifin ka ka more uba a wajen kara da mutunci ga ilimin sanin duniya a tare dasu.
Don wallahi yana bude ledan farko kifine aka gyara anyi mai gyara na alfarma anyi gunduwa gunduwa dashi an soya mai yawa sosai a ledan haka leda na biyu alkakine ya soyu yaji shuga sosai manyan dauri.
Sai na ukkun dambun namane shi din mai yawa sai yaji da kuma naman soyayye kule a wani ledan shima shiru mukayi muna kallon kayan kafin yace ashe yau ba girki ke nan gareki don wanan ya isa muci musha ruwa mu kwanta.
Bari na samo wuri na juye sai a dibawa su dije suma su dana da sauri yace ina ni aka kawowa da zaki fara kyautar min da abu yana kokarin jaye ledojin a gabanshi.
Aiko bakaba kowa ba ka bari a dibawa dije da inna ko na fada ina fita dana kawo wajen shi da kanshi ya zuba lokacin nake fadin ashe ka sayo kayan miyane dama ?
Yace eh shina koma na saya dana fita din nan bayan mun gama fada da inna da sauri nace fada da inna kuma ya karbi robobin a hannuna yana zuba alkaki a ciki yake fadin mun kwasa mana kan nayi mata magana ta bar fada da Dije don Allah .
Naga ya zuba komai a ko wani ruban ina tsaye ina kallinshi a fili amma a zuciyana fadi nakeyi cewa su wanan ahalin haka suke kowa ya dinga fada da mahaifinshi .
Magana nakeyi fa na dago na kalleshi yace me kike tunane hakan wai nace humm,umm mamaki nakeyi yadda harda kaima kake rufe ido kuyi ba dadi da inna haka.
Innace duk ta kawo wanan abinda kike tunane din a yanzu don gaba daya yanzu ta juye ta canza halin ta ya fada ya mike ya fice da kayan a hannunshi na bishi da kallo a raina ina fadin mafarin yaja min zagi gun inna din kuma ke nan tace har aikenshi nakeyi ya kai min abu kamar yarona.
Bai fadawa kowa shigowan shi kasan ba sai ganin shi kwatsam duka iyayyen nasa sukayi a lokacin falo ya zube inda ya samu mahaifin nasa yana shan, iska suka tareshi a cikin murna tare da kallon yadda dan nasu ya koma yanzu.
Ga dai girma yazo mai ga kuma wayewa son kana ganinsa kaga mazaunin turai ba zaka taba zaton shi din tsatson fulani ba haka uban ya daure zuciyar shi ya nuna farin ciki da zuwan nasa.
Hjy murja da bata san da zuwanshi ba shigo falon tayi wurin maigidan don ta tambayeshi abu shine ta samu sunyi bako a gidan wanda rabonta dashi tun tsawon wani lokaci mai tsawo sosai.
Duk da baigai da ita ba amma haka ta daure tana fasin wanake gani kamar yasir a gidan nan ya dago kai yai mata kallo guda ya kawar alamun shi bai santa ba a lokacin.
Mahaifin nasu yace step mum cefa hjy murja ko baka ganeta bane yace OK itace abinda kawai ya fada ke nan yaci gaba da magana da uban nasa ya fita batunta.
Haka bai hana data gama abinci ta sako masa nasa ban ba amma sai cewa hjy yabi tayi da yar aikin ta mayar ta fadawa murja cewa danta yafi karfin ta mallakeshi ta dai tsaya ga ubanshi shidata samu.
Sako yazo mata kuwa murmushi tayi tace aiko nayi babban kamu indai na kama uban wake ta yaro ga babba a hannuna don dole dai ace min matar ubanshi ai.
Ran hjy yabi ya baci sosai da martanin hjy murja din don haka takai karanta tana haki ko alokacin suna zaune da yaron suna tataunawa akan zaman shi turai.
A gaba dan ya aika aka kira hju murja din tazo yake tambayanta abinda yasa ta aikowa hjy yabi da wanan maganan dan murmushi ta sake kafin ta juya ta kalli hjy yabi din tace.
Ba aiko mata da bakar magana nayi ba amsa na bayar a fada mata na sakon data ban nan ta kwashe komai ta mayarwa mijin nasu wanan shine farkon abinda dan nata ya fara cin karo dashi don daddy bai bata gaskiya ba.
Shima dan ya nuna yana bayan mahaifiyar shi don a wajen ya bude baki yace yes uwarshi nada gaskiya aiba ita bace ya kamata ta bashi abinci.
Jin hakan yasa Alh fadin kana nufin ka goyi bayan mahaifiyar kada a zauna lafiya ke nan a gidan nan yace ba haka yake nufi ba idan zasu zauna lafiya duk daya a wurin kawai dai mahaifiyar shice mahaifiyar shi kowa yasani ai.
Alh ya gano tsegerancin da dan nasa ke ji dashi a lokacin yasa ya kyaleshi don daga shi har uwar ya shirya yin maganin su nan gaba kadan kuma a yanzu a shirye yake da duk abinda sukazo mai dashi.
Tun ranan kuma bai kara saka dan a idonshi ba haka kuma kwana biyu da zuwanshi itama salima tazo garin suka hade hakan ya kara tabbatar mashi da zuwan nasu yana da wata manufa.
Shi kuma sanin cewa dan nasa ko a turai dan dabane don irin abokan da yake yawo dasu a can yasa ya karawa gidanshi security bada sanin su ba.
Kallon kayan cikin mamaki mama tayi tare da tambaya tana kallon yayan nata dake zaune dukkansu biyu lokacin da aka kawo kayan a part din ta tace .
Dama mijjn Zahra ya tafi turaine ban sani ba yaushe har yaje turai din bamu da labari ko ku kunsan da zancen ne baku fada min ba ?
Tana tambayan yayan nata cikin mamaki Rukkaiya ta kalli kayan kafin tayi magana tana fadin mama ina zamu sani muda ba shiga part dinsu mukeyi ba daga inda Aisha take zaune tace mema ya tafi yine turai ?
Kilama fa ba turai yaje ba wani kasane nan kusa yaje yawo buga bugansa in bashi ba uban wa zai kaishi kasa turawa kiga tani din nan mai aiki karkadin tsiyane da ita wallahi.
Nasani ai duk wani shige shige da kutse kutse itace keyiwa Salmashi a garin nan don nasan a banza sukeyi yasa ban damu da haukan su ba don sawun giwa ya take na rakumi ko ba abinda zasu iya yi dani maimuna.
Meko zasu iya mama gata nan kullun wai ita musulma sai kayan hijjabi da takeyi wai ace mata saliha nan ko muguwace ta karshe wallahi.
Kai haba Rukkaiya barta da hijjabinta kinsan fa bakauyace dama ummah ni wanan fa bata gabana don banga abinda suka tare min ba a duniya.
Baki ganin ko buki akeyi yyanzu Zahra ta daina zuwa ba irin wanan kauyancin na uwarta wani kauyanci kodai ba abin daurawa a shiga kunya dai bai bari ta taka gidan buki kawai.
Hakane kuma jifa kayan datasa kwanaki da sunan yar nan da Rukkaiya ta haifa zarban kunya ita ta saka nikejin kunya koda yake suma ai hakan zasuso ganin mu a ransu.
Kai dole na bincika ina ya tafi da wanan tsaraban haka wai mama kin kira Abba kuwa zancen kudin nan ina son nayi manyan dinkuna ne na fitan bukin Nusaiban da za ayi tunda nasan Man bazai munsu ba yanzu Aisha ta fada daga inda take kwance.
Ke Abban nan naku kwanan nan bansan abinda ke damun shi ba ko ka kirashi sai fada zai hau mutum dashi kamar wanda kare ya ciza yake.
Zan dai kara kiranshi inji don ya turo min da kudin yanzu bai bambaruwa wasan dadi sai rayuka sun baci kafin kudi ya fito hannunsa .
Yama dade baizo gida ba wanan karon Rukkaiya ta fada sai uwar tace waya damu da zuwa nasa yanzu tunda in zaizo sai ya kwaso wanan bakar kilakiyar matan nasa sun taho tare.
Niko naki jinin in bude idona inga yar banza a gidan nan kuma nasan da gaiya take zuwa garin nan don kawai ta nuna muna ita din issasa ce a wurinshi.
Bari ma na kira nasan yanzu basa tare ta fita office yar iska ta labe ga aiki tana aikata alfasha a gari wanan kuma ita ya shafa dashi mu dai kada ta dauko muna ciwon wahala azo a mana muna muna zaune kalau.
Kai don Allah mama ki bar wanan zancen ai Abba yana da hankalinshi bai yarda insha Allahun hakan ya faru yar iska taga tana samune a wurinsa yasa taki fita gidan ai.
Amma tasan kowa bai sonta inba wa yancan munafukan ba ai zahra taban mamaki wai harda zuwa abuja wurin su fa lokacin.
Ai kinji yan iyan nan sun tare a lokacin wai Abbane ya saka taje gwalmodiya,i da ya saka dayan ku zuwa mana idan gidan nan bai tashi ba akan fitina.
Bin kayan daya aje a gabansu tayi da kallo kafin Dije tace wanan abin arzikin haka daga ina kuma muka sameshi yana zama gefenta yace daga mahaifiyar zahra ta aiko min dashi na tariyana.
A, a a duk wanan hakan ikon Allah su dai yan binni sai su nuna sufi mutum wayau ko yaushe wanan abin kaida gani ai kasan da biyu akayishi badon Allah aka kawoshi ba gidan nan.
Don ki aka kawo koda baya gari kannen yarinyar nan basuzo muna gidan nan da abin arziki ba mai yawa kuma kowa yaci ni har da goro kursa kursa aka dauro min lokacin har yanzu shi nake dan bantala inaci gidan nan.
Inna watau dai na kula ba zasu taba burgeki ba ke nan kinko ga nida zan aje abina inci a daki zahra ta matsa saina diban maku kuma shine na debo dan wanan din na kawo maku.
Ciki ciki tace ai dole ta matsa don a mallakemu duka gidan ni yanzu na gane wayau mutanen nan a haka ake kama mutum a rufe mai baki karshe baida katabus ga komai.
Ikon Allah kaga miko min nan nikan naci kaga saisu mallakenini da tushe daga can bayan inna Aisha tace nikan abani nima zanci wani mallaka inna kullun kina cin abin gidansu Asmau ta fada tana mikawa Dije roban kusa da ita duk sun matsu a basu.
Don ya karawa inna takaici ya dauka yakai a bakinshi ya mikawa kannen nasa guda guda cikin alkakin tana kallo taja tsuki ya dan zauna suna hira da Dije na irin halin ummah tana ji bata tanka masu ba.
Nagama komai na gyaran part har lokacin bai shigo ba saida aka kusa kiran sallah ya shigo yayi alwala zai fitane suka hade da wasu yan uwana da sun dade basuzo gidan ba wurina.
Sai ranan suka gaisa yasa kai ya fice daga gidan ya barmu dasu bayan mun gaisane suke fada min ai sun kawo min iv ne na bukin Nusaiba na karba ina masu fatan alheri na debo masu wanan alkaki da abinsha na kawo masu.
Mun dan dade dasu muna fira kafin suyi min sallama suka tafi na kara gyara dakin naje nayi sallah kafin ya shigo muna da abin sanyi da zamusha.
Muna zaune muna firan tafiyan shine wayan shi yai kara ya dauka naji yana fadin baba kuna lafiya ya kwana biyu ya wajen su umma shatu.
Yana kokarin dagani saman jikimshi nayi saurin dagawa ya mike ya bar gidan suna magana saida ya dade bai shigo ba don haka nikan na kwanta barci ya daukeni don gajiya.
Koda ya shigo banma sani ba saida ya gama abinda yakeyine ya kashe muna haske ya kwanta lokacin ne nasan da shigowan shi dakin.
Washe gari ya rigani tashi saida zai tafi masalaci ya tayar dani na tashi nayi wanka na dauro alwala bayan na idar da sallah ta na mike na fara fitana kunna wutan abinci na dawo ciki na fara gyaran daki har na gama na shiga wanka bai shigo ba.
Ina mamakin dadewan shi a ranan har dai na kawo komai akan dan table din cin abincin mu na ajemasa na koma na shirya don gaskiya bana son nayi wasa da karatuna.
Don shekaran karshe nake duk da ban shiri da Abba kan auren Ahmed amma hakan bai hana ya biya min kudin school fees ba da lokaci yayi sai wanan yasa banson naja abinda za hadani da Abban ya sake bata rai dani kuma.
Gashi a yadda naji wai saida yaja kunnen ummah kan kada ta gayawa kowa zancen kudin daya bayar din lokacin daya bata tabani hakan ta kara jamin kunne.
Shiyasa a yanzu nake dan fahinta duk da ummah bata yarda in dauka hakanen cewa Abban yana tsoron a gane yana kula mahaifiyan mu damu .
Kuma wanan dalilin yasa ita ummah din bata fita gidan Abba ba don yana nuna mata kulawanshi a boye yadda ya dace baidai fitarwa filine wasu sun da hakan tsakanin su.
Haka ta koya min hakkurin da muka tsunci kanmu ciki agidan mu ta bangaren mahaifin mu da bangaren kishiyarta mama da kuma mahaifiyan Abba din watsu kakan mu hjy.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/19, 8:05 AM] Mmn Bibo: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣9️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Yau wace rana don haka tayi mamakin ganin mijin nata a dakin dakanshi ya shigo wanda ba zatace ga iya watannin da suka dauka bataga hakan ba tun bayan faruwan abubuwa da dama a garesu.
Har ta fara tunanen ko yaran nata harsun gana da mahaifin nasune a lokacin don haka ta fara tunanen kalan wullakacin da zata yanka masa tunda ya dawo hannunta a yanzu din.
Dago kan da tayine ta kalleshi yasa shi gyara tsayi yana fadin dama nazo in fada maki cewa zan yi tafiya a yau din nan ta gagawa sai zuwa jibi zan dawo.
Kallon mamaki ta dago kanta tanayi kafin tace dashi tafiya haka ga yaran nan duka a gari ba zaka samu lokacin zama dasu ba ?
Yara ya tambaya cikin mamaki tare da dorawa da fadin wasu yaran wai kike nufi har kike magana akansu kada nayi tafiya gasu ?
Wasu yara ka tambaya kadana wasu diyane da sukafi yasir da salima da kannensu ina da mana ko kin manta da ina da wani da kafin yasir din yazo duniya don haka ki rika sakashi cikin jam,in ki idan kin tashi magana daga yau din nan.
Baki ta bude da zuman fadin wani da kuma sai ta tuno ai a baya ance yana da da amma ai sun share babin wanan dan nasa tuni acikin rayuwanshi ko ?
Ko hakan daya fada yanzu yana nufin boyayyar maganan dan ya dawo mashi a zuciyarshine yanzu wai inko hakane zama bai ganta ba ashe da magana kuwa sabo gareta nan gaba.
Juyowa yayi ya katse mata dan guntun tunanenta da fadin tare da hjy murja zamuyi tafiyan don haka ke kadaice a gidan tare da yaranki sai yan aiki ke nan yana fada ya fice a dakin ya barta cikin bacin rai a lokacin.
Tunane ba zai kaita ba don haka ta mike da sauri zuwa dakin danta ta tasheshi ga dakin sai tsamin giya yakeyi da taban dayasha ya dirkawa cikinshi kafin ya kwanta.
A ciki tashin hankali take kwala masa kira kan ya tashi da kyar ta samu ya falka kuma falkawan bai kara mata komai ba don yana cikin maye a lokacin.
Dakin salima ta nufa itacema ta samu suka fita tare saidai suna zuwa motanshi ta karshe tana fita get din gidan hakan yasa takaici ya kara kumesu a lokacin.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login