Showing 168001 words to 171000 words out of 304363 words

Chapter 57 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33344

nayi ba dama mutanen da sukewa mutane kallon banza balle kaje sha,aninsu yaya ke nan kuma idan mun kai kanmu cikinsu.
Haba dai keko har zaki yarda su raina maki ai shiga ta kamala zaki dinga yi idan zaki shiga wurin wanda kikasan akwai makiyan ki.
Murmushi tayi tana fadin inna dai tayi ita don ta saje dasu amma mukan ai wanda suka san mu dashi zamu sa mu fito kinga kuwa dole su raina muna wayau.
Ina zuwa na fada na shiga daki na barsu a nan ina ciki naji muryan Asma,u tana fadin kizo muci abincin mama Aisha.
Ke haba mana keba kanwarta bace daba zaki kirata da Anty ba ko yaya ai an daina irin haka ku kuwa sai a daukeki bakauya ko wata bagidajiya can.
Baki yarinyar ta turo tana shirin mata rashin kunya lokacin na fito daga dakin da kaya a hannuna naganta a tsaye daga kofa.
A,a Asmau kema baki tafi bane eh ban tafi dazun dai na leka da Dije ta aikeni shine inna ta bani abincin in kawo muci kuma abincin ba yawa dan kadan ne tazo muci yunwa nake ji sosai tana ja min rai.
A,a baga abinci a nan ba ku diba na dauka aikun tafine ba kowa a gidan shiga kitchen ki dibi mai isan ku kuci tayi dan jim kamar tana tunane sai kuma ta juya ta tafi .
A nan na zube kayan dana dauko ina fadin Aisha ki duba wanda zai maki a cikin wanan sai kiba Asmau sauran kala bibiyu ne na zabo masu lokaci guda.
Don ina da kaya birjit a dakin daba amfani nake dasu ba yanzu a cikine na debo masu wa yan nan din yanzu.
Da sauri ta washe baki tana fadin wai da gaske matar yaya nace da gaske mana gwada ki gani ko zasuyi maki idan kun dawo saiki goge wanan din kada inna tayi fushi dake bakuzo wurin sha,anin da wuri ba.
Takai hannunta saman kayan ta fara dubawa tana nuna farin cikin ta a fili tare da fadin ke Asmau taho kigani an bamu kayan da zamu saka mu fita.
Saiga Asmau ta bude labulen kofa tana fadin kizo kiga abincin ko zai muna nikan bancin wancan da anka bamu don wanga mai dadine sosai harda ganyen salad cikinai hwa.
Sai idon ta ya sauka akan kayan da yar uwan nata take duba tace kayan waye taho nice kigani matar yayane tabamu su mu saka.
Da sauri ta sake labulen ta shigo tana fadin mu ankabasu walle har naji dadi kasan raina muma zamu hito kamar kowa a bukin nan ashe ?
Ai dama daidai da kowa kuke idan kuna gyara Zahra kan bata da matsala in kuna hurda da ita fiye da hakan ma sai ku samu a wurin ta don wanan ba komai bane wurin zahra kowa yasani .
Ai walle innata taka hanamu hurda da ita dama wai sai ta mayar damu bayinta Asmau ta fada tana bude kayan kafinta washe baki tana fadin wayyo ji irin dinkinga da nai maitanai a baya don Allah.
Ke walle nika daukane bake ba wanga ina zai maki adaidai lokacin naji hanne tace bayi kuma don kana shiri da matan yayan ka shine wani abu kuma ?
Ai shina gani daka zowa muna dan hira halan ta mayar dani boyantana to nidai haka niji inna tana hwadi ko wani lokaci.
Yanzun dai ku shirya nayi maku kwalliya sai ku tafi hannatu ta fada sai sunci abinci aiko na fada daga inda na zauna.
Abinci walle saina dawo nikan saina dawo nikacinai kedai aje muna har mu dawo daga wurin bukin Aisha ta fada a cikin zumudi sai hannatu tace ai gara kuci kada kuje can baku samu wani abincin ba.
Hakan tayi masu kwalliyan tana jansu da hira nima ina dan saka baki wanda na kula da hakan yasa sun dan sake jiki sosai a wanan ranan dani har muna wasa da dari a fiye da kullun a cikin wata takwas din da nayi a gidan tare dasu.
Wanda hakan ba karamin dadi nima naji ba don har akalma da jakka da gyale suka saka mukai masu rakiya hannatu nata zugasu Dijema saida ta fito don jin yawan hayaniyar mu da takeyi daga sashen su.
Bayan tafiyan sune Hannatu ta gama yiwa Dije dan bayanin karya tana fadin ai kaka yan mata yanzu saida sa,oin su a gida suke gyaruwa amma a zauna ga zahra tare dasu muma na nisa muna cin muriyanta balle wa yanan dake zaman kannenta ai zaman lafiya yafi komai a rayuwa.
To shina gani yar nan uwarsu taki gane hakan gashi yau yar nan da take rainawa itace tayi tsaye ta gyara mata diya haka tsab zasu shiga tsaran su don wanan sha,anin ba lamarin wasa bane don kowa na wurin a cikin danginsu kinga ko aga naka cikin shiga ta alfarma ai abin a yabane hakan.
Tagama zuban ta ta dawo ta sameni ina gyaran part din ta kalleni tace to uwar tsabta koda zaki hakan ki dinga bari dai sai sun tafi don idan kina nuna wanan shagen tsabatan naki a gaban su haka zasu dauka kina kyaman tararyanki dasune.
Banyi magana ba don nasan gaskiya ta fada min saidai ba zan iya ganin wuri haka komai a yamutse ba dole sai na gyara zanji dadi amma dai zan kiyayye din gaba.
Mun dan taba hira ta wuce ina mata godiya na rakata zuwa waje a nan mukaga yadda jama,a suka cika unguwar don halartan wanan bukin mukai sallama ta tafi na dawo ciki nayi sallah na fito wurin Dije na zauna muna hira.
A nan ta jefo min tambaya da fadin yaushene mijin ki zai dawo daga tafiyan shi dan murmushi nayi kafin nace ina ganin sai karshe wani mako kamar yadda yace.
Saidai zuciya yana ban kamar zai dawo kafin lokacin yadda nake gani yar nan har ganin dawowan mijin naki kikeyi a yanzu sai nayi murmushi ina dan kame kame tare da fadin .
A,ahaa kawai dai ina jin cewa zai dawo a yan kwanakin nan ne don haka jikina ke bani ta kara tuntsurewa da dariya irin na tsofi lokaci guda.
Shigowan wasu mata wurinta ya dakatar muna da maganan suka tsaya gausawa da ita saidai ina zaune wurin har lokacin da suka fita bayan sun dan taba hira.
Fitan su take fada min irin alakansu dasu akwai zumuci sosai a rsakani su na iyayye wanda a yanzu mutane basu daukan hakan da muhinmanci sosai shi tallaka yana gudun wulakancin da uwa mai kudi don wullakanci.
Haka dan uwa mai kudi kuma yana gudun mamuwan dan uwa tallaka don bani bani don wasun su haka suke zubar da kiman su da roko a yadda Dijen ke min bayani kuma hakan gaskiyane a yanzu.
Muka dauko hiran zaman mu da uwar mijina tana kara ban hakkuri kan halayen da take nuna min na dai nuna mata ai uwace a gareni don haka ba komai.
Muna wurin misalin karfe biyar na yamma kawai Ahmed ya fado muna gidan kwatsam muka ganshi kamar an jefoshi a lokacin.
Daga inda nake zaune ina hango bacin rai a fuskan shi ganin part din mu a rufe don ya dauka na tafi wurin bukin nasu daya hanani zuwa kenan tunda ga part din namu a rufe don yasan bana shiga cikin gida in zauna haka.
Yana nufo part dinsu Dije din yai arba damu zaune tare da Dije din saman tabarma ya dan saki wani shu,umin murmushi a fuskan shi lokaci guda.
Mukai mashi sannu da zuwa a nan ya zauna na mike karbi dan jakar nasa da yake rataye a kafadan shi na nufi part din mu dashi a nan naji Dije din na fadin.
Allah ya horema mata mai halin kirki yarinyar akwaita da dattako da sanin yakama ka kara rike yar nan da hannu bibiyu don ba inda ta kasa da kai haka
Yayi murmushi tare da fadin kai Dije ai nima ina da wanan halin irin nata kaidin shu,umine wani lokaci don wanda baisan kaba ya hauka katkace sai ya zame.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[22/04 3:41 PM] +234 806 730 5151: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣8️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,


Kokarin dora girki nakeyi da let evening don dawowan shi lokacin ina tsaye ina kunna gas banji motsin shigowan shi part din ba sai ji nayi ya rungomoni ta baya yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin i miss you my princess.
Idona na lumshe a hankali don jin haduwan jikin mu da nasa a lokacin dan wani irin shock danaji har cikin raina zuwa zuciyana lokacin.
A hankali na sauke ajiyan zuciya na furta miss you too ya hanya ya karatu ina kokarin jiyowa mu fuskanci juna dashi a lokacin.
Saidai bai bani daman hakan ba don kara matseni da yayi a jikin shi yana fadin kada kice zaki dora girki bana jin cin komai a yau don sam bana jin dadin bakina two days ke nan ina hakan.
Da sauri na kwace jikina daga gareshi ina kallon shi cikin mamaki tare da fadin master meke damun ka baka da lafiyane ko me da hakan ya faru ?
Ina kallonshi ido da ido ina magana a rude kai ya rausaya min tare da ware hanayen shi ya bata fuska yana fadin gani nan dai bana dai jin dadin jikinne kawai kuma ba ciwo nake ji a wani wuri a jikina ba.
Yana fadin hakan ya juya zai bar kitchen din yanayin fuskan shi ya sauya a lokaci guda hakan da yayi ya kara tayar min da hankalina lokacin guda nabishi da kallo har ya shigewa ganina.
A hankali na aje ashanan dake hannuna nabi bayan shi zuwa dakin duk sauri na sameshi a zaune falon ya zauna ya mayar da kai baya yana tunane a lokacin.
A hankali nakai zaune a gefen shi ina me kura mashi idanu kafin nakai hannuna saman kanshi na shafo a hankali ina fadin meke damuwan kane master ?
Ajiyan zuciya mai nauyi naji ya sauke kafin ya dago kai yana kokarin kallona yana fadi wallahi kawai nake jin zuciyana ba dadi a kwanakin nan biyu.
Ga yawan mafalkin da nakeyi mara kyau dana kwanta barci hakan yasa na dawo ko zan daji saukin yanayin da nake jin kaina din ciki.
Shiru nayi ina kallon shi tare da dan kura mai ido don na fahinci akwai abindake damun shi da yake boyewa a zuciyan shi wanda ya shafi rayuwan shi shi kadai.
Mikewa nayi a hankali zuwa ciki bandaki na shiga na hada mai ruwan wanka na dawo na sameshi yadda na barshi a zaune yana tunane.
Hannun shi na riko a hankali bayan na zauna ina fadin shiga kai wanka kafin magariba ya karasa yi zaifi kadan samu natsuwa sai ya kalloni a hankali yana kakaro murmushi tare da fadin nagode my princes.
Yadanyi kamar zai mike sai kuma yayi zaune ya hade hanayen shi wuri daya tare da dukar da kanshi kasa kamar me tunane na kura mai ido bansan lokacin dana furta ya salam a fili ba ya dago kai yana murmushin kake tare da miko min hannuwan shi alaman in kamashi ya mike tsaye.
Haka din nayi mashi ya mike tsaye tare da dan dafa min kafada ya tausa ya shige dakin na bishi da kallo a raina ina fadin meke shirin faruwane hakan wai ?
Fita nayi zuwa kitchen na dora ruwan zafin da zan zuba a flask don shan shayi don nasan kobai ci komai ba zaisha tea din ya dan ji nauyin cikin shi a lokacin.
Kafin na fito zuwa dakin na samu kayan daya cire na dauke zuwa inda muke tara kayan wankin mu a dakin a daidai lokacin nake jin muryan su Aisha da suka shigo gidan a hargitse suna fadin.
Matan yaya kina ina kisha labari yau mun faso taro muma bakiga yadda ake kallon mu ba a wurin taron nan har ana wani dan ji damu a wurin yau.
Kai gaskiya yau kin fitar damu fili mun haska sosai wallahi naji dadi ashe sutura shine mace sai yau nasan da hakan wallahi suna fada cikin jin dadi da yadda mutane suke wani bamu girma kawai don basu ga wurin raina mu ba yau.
Gyaran muryan da yayine daga ciki yasasu natsuwa suna kallona Asmau take fadin yaya ya dawone halan tana tambaya ?
Kai na gyada mata alaman eh a hankali suka mike suka fara kokarin barin dakin ina masu dariyan hakan tare da fadin baku tsayawa ku gaisa dashi .
A lokacin ya fito daga dakin yana kallon su juyowan da Aisha tayi tana fadin bari mu dawo sukai arba dashi tsaye yana fadin barin dan fita daga masalaci zan tafi unguwa daga can.
Yaya ina wuni an dawo lafiya ta fada lafiya inna ta dawone ya tambayeta tace a, a tana can sai sun kai amarya zata dawo tace Asmau ma ta dawo suka gaisa daga hakan suka fita dakin.
Nayj mai a dawo lafiya ya fice na mike na shiga na gyara dakin har bandakin lokacin anyi kiran sallah na dauro alwala na fito.
Na idar har isha,i bai shigo ba can naji muryan inna ta dawo suna hira da Dije don haka na fito don nagaida ita kada inyi laifi ga hakan .
Na samu sun baza abinda ta samo a wajen bukin kamar yadda yaran dama suka fada muna da hanne cewa ko zasuci abin dadi na bukin sai inna ta dawo da dare don yanzun haka tana nan tana tara komai a cikin jakkanta.
Gashi ko na gani an baza a yanzu gabanta can nayi sallama kasan murya na suka amsa min haba haba kamar basu ba Asmau harda fadin matar yaya keta ?
Nakai zaune a kasa gefen su nace inna an dawo ina wuni ya gajiyan jama,a Allah yasawa aure albarka ta amsa da Amin tana mikawa yarta abu.
Na dan zauna shiru ina kallon yadda sukeyi kafin Dije ta fito daga daki kila sallah ta idar tana fadin shi bai dawo ba har yanzu ko yace bayajin dadin jikin nasane.
Na dan juyo tare da fadin bai dawoba har yanzu yace daga masalaci zai tafi unguwane daga can ya dawo ankace ko halan missameshi uwar ta tambaya har lokacim hankalinta naga ledan datake kokarin budewa a hannunta ashe alalaine a ciki ta mikawa yar nata.
Dijece ta bata amsa da fadin wayasan komi ka damunshi tunda ba fadawa mutane yakeyi ba so nasan ko matar shi ba fada mata zaiyi ba..
Nayi mamakin yadda batai wani nuna damuwanta ga hakan ba saici gaba da harkan gabanta tayi a lokacin na dan jima kadan na mike ina masu saida safe.
Ina tare da imanin matar a zuciya naji muryan Asmau a ranan ita ke fadin matar yaya zaki tafi baki tsaya anci kayan bukin dake ba mana nagode nace masu nasa kai na suce zuwa ciki abina.
Ina shiga sai gashi an biyoni da kayan wanda alalaine sai wani guntun tuwon amala bakikirin dashi miyar ma ba komai a cikinsa baida dadin gani a ido.
Karfe tara da rabi na dare ya dawo ya samu ni har na kwanta a lokacin bayan ya shigone yake fadin har kin kwantane princesses ?
Na dan dago ina fadin eh ban dade da kwanciya ba ki tashi ga abu nan a falo muci ya fada yana kokarin rage kayan dake jikin shi a lokacin.
Duk da banjin cin komai amma haka na mike ina fadin ba zakasha tea ba ke nan ashe da har na zubama ruwan zafi a flask ai.
Wanan ma idan na samu naci zai wadaceni ba sai nasha tea din ba zan kwanta akwai dai bread a cikin kayan idan zaki shane ya fada ya shiga bayi.
Falon na fita na samu leda guda biyu saman table ya aje na bude tun ban kaiga karasa budewa ba na fahinci abinda ke cikin ledan namace gashin maza.
Sai youngt mai sanyi da tarkacen zaki da bread guda biyu a ciki na fita zuwa kitchen na dauko plate na juye dayan ledan kazan a ciki an yanka tun a can wurin daya sayo din.
Ya fito ya zauna a lokacin nake fadin kun gaisa da innace tadawofa daga gidan bukin ban shiga ba saida safe ya fada yana daukan goran freshmilk daya daya sayo duk da tsadan shi hakan wata rana zai kwaso muna shi asha.
Duk cikin kokarin shi na ganin cewa ya kula da ruwana kada ya kasa da abindana saba dashi a gida duk da yasan cewa ba damuwana abubuwan sukayi bana sha koda ya sayo din.
Kallon shi na sakeyi ina fadin za a dibanwa su innane ko ina nufin abinda ya sayo din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login