Showing 162001 words to 165000 words out of 304363 words

Chapter 55 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33350

sai cewa yayi shafa koma meye ya kawo ku inji a wurin hjy gobe in na shigo ta fada min komai koke dake kusa in na shigo ki shigo muyi maganan dake.
Wanan zancen nan take ya bazu a cikin dangin mu yan uwa suka fara fadin albarkacin bakinsu kan haka har saida yakai kai ya rabu biyu a tsakanin su.
Har yakai labari yazo kunnen mu cewa ai mama itace tayi makarkashiyar karbe mota a hannuna wanda sai yanzu Abba din ke samun labarin hakan da akai min din.
Ban san a ina mahaifiyar Ahmed ta tsinto wanan labarin ba na daiji tana yada habaici a tsakar gida da fadin dama na sani ko a gidan ba wata tsiya bane ashe ?
Ba a bakin komai mutum yake ba dama ina za a dauki yarso aba mutum irin yaron nan da baida komai dole sai abin banza irin haka ai.
Dije ko ta fito ta bata amsa da fadin ai sun zama banzaye ke nan har dan naki da kike shirin aibantawa a yanzu don ba yar mutane kike wa wanan zance ba in kina da hankali dabaki fadi ba.
Ai tayi muna komai keda uban dan ya gudu ya barki da dan shekara da shekaru babu waige a gareku me kuka zama a idon jama,a yanzu ?
Sai amsan Dije din yai mata zafi tana fadin inna nidai bance ga wanda nake wanan maganan akamshi ba inma ubanshi ya gudu ya barmu ai hakan bayin kan mu bane nidashi.
Har dai zancen ya kaisu ga bacin rai wanda a karshe yana dawowa yaji wanan labarin a bakin makwanta suna sheda mai abinda ke faruwa yanzu a gidan ba dadi.
Saboda makwabta sun fara gane irin zaman da akeyi a gidan nasu yanzu wanda mahaifiyar shice ke jawo hakan ko yaushe.
Nikan na gama duk wani abinda zanyi a ranan na samu wuri na kwanta don ya fita da sunan samo muna shelto a fesa a dakin har barci ya far daukana ina dakon dawowan shi bai shigo ba.
Ya dawo yake tayar dani na koma falo ya fesa muna a dakin na mike da kyar na fito falon ya fesa a ciki har bayi can sai gashi ya fito dagashi sai dan boxer na maza a jikin shi.
Duk suran jikinshi a waje lokacin saidai kallo daya zaka mai ka fahinci zuciyar shi babu dadi a lokacin na saba da ganin hakan idan wani abu ya bata mai rai.
Dan zamana dashi da mukayi yanzu ya zaune kusa dani a inda nake kwance jin hakan yasa na jaye kafana daya dan zauna a kai.
Zahra wai sai yaushene inna zata daina halaiyanta irin haka a kan mu wai ace kamar inna tana zama tana sa insa da mahaifiyar ta wanda gaskiya ada can baya bansan ta da wanan halin ba haka?
Tayi wani abinda ba daidai bane kuma tayi mana duk daku baku fada min ba duk da nasan kedin ba fada min zakiyi ba har dije din da sukai hakan da ita.
Meya shafi inna da zancen motarki da aka karbe a gidan ku har suke sa,insa da Dije akan hakan ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[22/04 3:41 PM] +234 806 730 5151: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣6️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Zaune yake yana rubutu a jikin allonshi na karfe da sai lokaci lokaci yakan dauko shi yayi amfani dashi wanda iyalanshi tasan da hakan sai wani abu na muhinmin yake dauko allon yayi amfani dashi.
Idan yana hakan tana bashi natsuwa ita kanta tasan aikine na muhinmanci ya taso mashi dayake son natsuwa don haka takan jaye ga duk abinda zai iya dauke mashi hankalinshi a lolacin.
Ya dauki tsawon lokaci yana hada rubutun kafin ya wanke ya juye a cikin wani goran ruwa ya aje gefe ya mike zuwa ban daki inda ya kewa ya fito ya daura alwala a nan ma ya dauki lokaci yana addua kafin ya shafa.
Shatu dake zaune gefe tana zaman kadaici tare da dakonshi ya idarne tayi mai sannu tare da gabatar mai da abinci.
Don inda sabo ta saba yau kusan kwana biyar yana wanan aikin da ita bata san kona meye ba tadaiga ya tsiri aikin ne kuma kafin ya fara saida ya fada mashi dokokin shi.
Don kada tazo ta bata mashi aiki don mace shu, mace sosai idan za ayi wasu abubuwa ba,a son mace kusa kota saka hannu don a take take karyawa mutum shirin shi.
Don sanin hakan ya gargadeta da ta bar komai a yadda taganshi cikin yan kwanakin nan sanin halin mijin nata yasa ta kiyayye kamar yadda ya bukace ta dayi din.
A kwana na bakwai ya dauki ruwan rubutun dayake tarawa ya fice cikin dare zuwa inda yake da bukatan kaiwa a lokacin.
Babu kowa a lokacin don dare ya raba sosai kafa ya dauke gaba daya bakajin komai sai kukan kwarin dake rayuwa a cikin dare da sauran halittun Allah a lokacin da darene su maraya garesu.
Gadan gadan ya nufi wurin iccen tumfafiyan tun daga nesa yake ganin halittan icen ya juye masa ya zama kamar wani hallitan kosasshen doki a tsaye.
Saidai hakan bai razanashi ba don sanin irin waibuwan da wanan yar hallitan itaciyar yake dashi kala kala.
Da sallama a bakinshi ya kara wurin itaciyan yana fadin icen albarka icen siri nazo gareki cikin amincin Allah yadda wasu masana kafiran Allah sukai sihiri suka juya tsakanin da mahaifinsu haka nake son Allah ka juyo hankalinsu su dawo da alakan dake tsakanin su kamar yadda ka sharianta a daddinance ya Allah .
Ka karya duk wani kulli da minafuncin dake boye tsakanin habu na mazo da danshi Amadu da akafi sani da Ahmed.
Ya Allah ka dawo da alakan a tsakani kamar ko wani da da mahaifi a duniya yana fadin hakan ya mike ya bude wanan dan goran ya fara zuba wanan ruwan rubutun daya tara na kwana bakwai.
Yana ci gava da fadin wasu kalamai a bakin shi har saida ya juye wanan ruwan kaf ga icen ya yayi hamdala tare da godiya ga Alla ya juya don ya koma zuwa gida.
Ya bada baya yayi tako daya zuwa biyu sai yaji kamar ana binshi a baya yasan dokan hakan jin hakan baisa ya juya ko ya dakatar da tafiyan shi ba saima adduan da yakeyi a bakin shi lokacin na neman tsari daga shedanu da ba ganin su mukeyi ba a fili.
Can kuma yaji kamar daga gefenshi anja mashi tsuki a cikin bacin rai tare da fadin kai har ka isa ka sance kullin dake tsakanin mu shekara da shekaru.
Lalai ka shiga hurumin dabai shafeka ba dama kaine kake muna zagon kasa ashe ga aikin, , , kafin ya karasa yaji kamar ana ba mashi wani azaba .
Anyi sama dashi har ya shige gida bai kara jin wani motsi da zai tayar mashi da hankaliba kuma alwala ya dora yaci gaba da sallah har tsawon wani lokaci.
Yau gidan tsit gashi ba school muna hutu a lokacin da alama kuma mutanen gidan sun fita a lokacin don falkowan da nayi daga barcin daya daukeni na safe .
Na gane hakan ne don yadda naji wurin ya dauki shiru na dan lokacin dana falko ina sauraren yanayin gidan don in suna gida ba bace hakan yake ba don zasu cika gidan da surutusu sosai saboda Allah yayisu da daga murya abinda ba a so ga diya mace ke nan.
Don koshi wani lokaci yakan yi fadan haka dasu don zai fita ya tsawata masu har hakan kanso kawo sabani a tsakani shi da mahaifiyar nasa wani lokaci.
Wanka na shiga na fito na shafa mai ban tsaya wani gyaran jikina ba sosai sanin master baya gari yana zaria wurin karatun shi.
Sama sama nake jin sallama daga cikin gidan jin hakan yasa na fito ina amsa sallaman na bude kofa wata mace na gani tsaye kallo daya zakai mata ka fahinci irin matan nan ne masu zaman kansu.
Gaisuwa na mutunci da ban girma nayi mata ta amsa min kamar yadda nagaida da ita din take tambayana da ko maman Asmau na ciki nace ban tsamani amma barin duba maki su.
Na dan wuceta na nufi cikin part din tun daga nesa naga kofan su a rufe sai na Dijene bude lokacin don haka na nufi can ina sallama daga ciki dije ta karba min tana kokarin dagowa na leka na kara gaida ita da rana nake tambayanta inna tace tun safe suka fita ita da yarta Asamau Aishace dai ta fita bada dadewan nan ba wai ta tafi kitso tace.
Bakuwace dama inna din tayi basu gida Dije din ta kara fada matar tana daga tsaye a can kofa na juya ina fada mata sai bina take da kallo.
Tace kai ina kuma ta tafi bayan tasan yaune zanzo munyi da ita hakan idan ta dawo kice mata yar giwa ce tazo zata gane a, a mama aiba kya tafi haka ko ruwa baki sha ba na fada .
Don Allah ki shigo ki sha ruwa ki dan huta kan ki tafi sai naga ta danyi jim kafin ta sake murmushi tare da fadin nagode yar nan na bude part dina muka shiga na kaita daki na dawo kitchen na hada mata ruwan sanyi tare da dan kankara a ciki a wani jug din tangaran karami tare da kofi na kai mata tana zaune tana bin dakin nawa da kallo.
Saidana tsiyaya mata na mika mata cikin ladabi ta karba na daga na koma gefe na zauna tasha ta kara ta dago tana fadin nace ko kece sarakuwar nata dama ?
Dan murmushi nayi na dukar da kai nuna alaman kunya ga maganan nata taci gaba da fadin kai gaskiya idan kece ni banga alaman wani matsala a tare dake ba da gyara wandkn ke fada a kanki ko yaushe gaskiya.
Har in bakonta zaizo gidan nan bata nan ai masa wanan taro na mutunci duk da baki sanni baki san inda na fito ba amma ki karbeni haka hannu bibiyu babu kyama gaskiya na yaba da hankalinki ba zan boye maki ba.
Murmushi kawai na sakeyi itako tana cigaba da fadin kinga ki kara hakkuri tunda baki da matsala da mijjn ki banga abin damuwa ba a nan din har yaushe akai auren ku da zata fara korafin cewa baki samu ciki ba har yanzu ita aure zata karawa danta ai.
Nasan yadda kika min har naji dadin nan haka kikewa kowa a gidan nan amma bata ganin hakan ita tace kina masu daukan kakai kina juya mata da don kina takaman gidan ku suna da kudi.
Bayan tayi bincike ance bakowa kike ba a gidan naku da sauran dai maganganu irin na bata mutum a bakinta a kanki.
Bayan duniya sun sheda aure irin na soyayya kukayi keda dan nata kowa yasan da hakan ko kallonki mutum yayi yasan kedin ai ba kallan gidan nan bace amma ita ta kasa gane hakan.
Na rasa hankali irin na gyara wandon ka me takeso a duniya wanda danta yanzu ya rageta dashi kada kice na faye zuba daga zuwa na zauna ina sake zance haka ko munafuka nake .
A,a wallahi abinne na kasa hadewa a raina ko ita zan mata magana kan hakan idan zata gyara ta gyara ta barku ku zauna lafiya da mijin ki.
Don yadda ta dauki dammaran rabaku tako wani hali yanzu in ance wurin wani malamin nata ta tafi akanku ba a musu bayan an fada mata tun farko abune mai wuya abinda take so ya faru tsakanin ku.
Ni zan tafi na fada makine don ki sani don nasan ba wanda zai iya taron ki ya fada maki komai aka hakan a unguwan nan kaf don sanin halinta niko kar ta san kar da ita ai.
Numfashi na sauke tare da fadin mama nagode kwarai insha Allahu zan kiyayye ta mike nace ina zuwa na shiga daki na dauko mata turare da sabulu nasa a leda nafito lokacin har ta fita waje tana bin kitchen dina da kallo tana fadin .
Idan ba tsiya irin na gyaran wando ba arziki irin haka yacin ma har gida kai kace baka sanshi ba sai bakin kishin tsiya da matar danka da takeyi.
Daga bayanta nayi magana ina fadin gashi mama ba yawa ki rika da hakkuri nagode sai ga Aisha ta turo kofa ta shigo.
Irin yadda naga ta kalli mata ta gaida ita a taatsaye ta samu wuri ta zauna ya kara ban mamaki nake fadin bakuwar innace fa tazo bata sameta ba.
Tace aina santa taci gaba da kallon dan wayanta na nokia dake hannunta tafi batu mu nadan rakata iya kofana mukayi sallama ta tafi ta barni cike da mamakin maganganun ta.
Muryan Aisha naji tana fadin naganeta ai bandai son hurdan su da innace don matar irin matan nan ne yan karya masu zaman kansu.
Su innan mu yanzu take bi suna karya sun girma basu san sun girma ba ga yawan cin bashi da karya da suka sawa kansu kesan innan mu yanzu wani famfarewa ne kuma yazo mata tun rasuwan baban mu.
Koda yake kafin ma ya rasu din ko acan haka suke fama da ita da yawan dauko mashi magana a wurin matan nufawa da muke zaune dasu a can.
Zama nayi gefenta anan wajen ina fadin ba Djje tace min kinje kitso ba dazun ya naga kuma kin dawo baki kitson ba kuma ?
Wallahi naje na samu mai kitson ta tafi unguwa wai suna bukine yau kila saida yamma idan ta dawo ko kin iyane ki mun don Allah ta fada tana kallon fuskana.
Murmushi nayi nace ban iya kitso sosai ba amma ina dan kamawa tace ko yayane dai don Allah ki mun don gobe kada in shiga mutane dakaina haka kinsan akwai bukin nan cikin gida da za ayi goben ko ba a fada maki bane ta dago tana tambayana.
Wazai fada min Aisha kila sunga bukin bai shafeni bane yasa ba a fada min ba koma an fada kinsan Master baya gari ba lalai bane in tafi tunda bai nan.
Kuma gaskiyane don nasan yaya yaji labari kin fita zuwa buki baina yana iya yin fada gashi ko banza ba shiri sukeyi da gidan ba don sun tsani kowa namu.
Dijece make fada min dazun cewa abin ya samo asaline tun bayan rasuwan mijinta malam Ladan yan uwan nasa suka tsani yayanta din har muma abin ya shafemu.
Balle suna muna kallon tallakawane a cikin su ko abu sukeyi basu faye saka mu ciki ba tunda mu bamu da irin tufafin yan gayu irin su.
Ke Aisha ki godewa Allah kowa da abinda Allah ya bashi yake shiga yan uwa kin gani nan ban faye damuwa da irin abubuwan nan ba balle ko bamza ni ba buki nake zuwa ba dama.
Gara dake ko banza ku yan gayune ba wanda zai maki wanan kallon amma ita innan mu bata damu da hakan ba haka take kokarin cunamu cikin su wai sune dai yan uwan nata.
Ko wanan bukin kafin yaya ya tafi saida ta matsa mashi ya bata kudin da zata bayar na bukin a cikine naga ta sai wani atamfa ta dinka waishi zata goben muko kinga haka zamu shiga da tsofin kayan mu suna muna kallon banza.
Mikewa nayi na shiga daki na dauko cumb da tsinken kitso ina fadin zauna nayi maki kafin innan su dawo ta samu kin shigo nan din.
Wai ashe kema kinsan tana hanamu shigo wurin ki yanzu Dije tayi maganan hakan tace wai bata son wullakcine kada ki dauka don abinki muke binki nan.
Aiko hakan ma nagode kisan kowa da nasa irin fahintar ai daga hakan naja bakina nayi shiru Allah ya taimaka mukai kitson har lokacin bata dawo har muka dora indomie a wuta mukaci tare a plate daya muna hira tana ban hiran zaman su Niger.
Bamu dade da gama cin abincin ba sai mukaji shigowan su gidan ta tashi ta tafi lokacin nayi sallah na gyaro part dina na da muka dan bata.
Na koma zaman kadaici don Aisha din ta dan debe min kewa da sato hanyar da takeyi din ta shigo wurina nakan ji dadin hakan sosai a raina.
Don zaman kadaici baida dadi ga mutum ko ya yake kuwa gara kana dan magana da wani duk da bawai ina samun hakan bane ko wani lokaci kuma daman hakan ba damuna yayi ba.
Amma kuma gashi uwar su yanzun tana skn sakani wani hali a rayuwana wanda bansan dalilin hakan ba a yanzu.
A wanan zaman ne naji zancen wanan matar kawar inna data kira kanta da yar Giwa zancen tane tiryan tiryan yake dawo min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login