Showing 66001 words to 69000 words out of 304363 words
anjima kaka .
Sannuku da kokari yaran nan angode Allah kara arziki da nisan kwana Allah ya kade shedan da raban rayuwanku a kullun sai mun ga abin sallah kuma in Allah yakai rayuwan mu lafiya ba matsala kaka tunda kinga wanan ai kishi yana tafe in sha Allah hanne ta fada.
Har lokacin jna rakube a bayan shi cikin tsoro da tashin hankali ganin na kasa wuce yasa ya dan juyo idona yana rufe shige man ku tafi zarah ke take jira ku tafi.
Kamar wace ta farfado na dan zabura ban tsaya mata ko sai anjima ba na bi bayan zarah muka fita har ina hadawa da dan gudu kadan don sauri.
Muryan shine a bayan mu yake fadin kiyi hakkuri zarah akuyan na bata komai haka take idan taga mutane don son mutane ne da takeyi aina fada mata haka akuya take idan ta saba da mutane.
Munkai bakin motan lokacin yaran suka fito daga gidan da sauri suna fadi mun daure ta hanne tace a, a kudai dan abinda mukace zamu baku kuka biyo dai ga hamsin ku tafi jin haka yasa na bude baki da kyar nace.
Wani irin hamshin kuma ku jira nazo zan sallameku na bude motana na zaro kudi daga cikin jakkata dan dubu daya sabo kar na mika masu nace mungode kunji.
Kai amma zarah kan dan wanan abin zaki basu har dubu daya nace haba dai ai sunyi kokari sosai hjy mungode Allah ya kara arziki da wadata na amsa da amin.
Yana tsaye yana kallo mu kafin yace kin daiki jin maganata zarah wanan dawainiyan haka ga kuma uwargarke data tsorata ki haka kuma.
Inbanda ke wa yake tsoron akuya zarah a lokacin na zauna da kyau a cikin motar na dago kai na kalleshi nace ban taba zuwa inda ake kiwon su bane kuma bana son kukan nan nata ina jinshi wani iri sosai har cikin raina.
Yayi murmushi yace kardai tsoro gareki haka kai mata ke nan meke a cikin akuya kike tsoranta haka sai anjima na fada ina tayar da motan nawa.
Yana tsaye har muka bar wajen muka fice daga unguwar nasu ya juya ya shiga gidan ya samu Dije na bude kayan tana ganin ya shigo ta fara washe baki tana fadin sun tafi ko ?
Eh sun tafi ya samu wuri yana kaiwa zaune tare da kallon abinda tsohuwar keyi tana fadin in Allah yaso ka da arziki tsuntuwa yake baka.
Haba Dije bai kamata kina nuna hakan ba a gaban su gaskiya yarinyar nan Allah ne ya hadani da ita kawai jinin mi yazo daya daga taimako abin ya koma muna zumunci a tsakanin .
Amma don kinga sun kawo wanan kika kasa boye zumudin ki kan wanan abin don Allah me kuma nayi yanzu akan hakan na zubar da mutunci Amadi ?
Kudine ta jawo a cikin ledan yasa ta juyo tana masa kallon tambaya a cikin mamaki yar nan da abin arziki take har da wani kudi ta dora a kai bayan wanan wahalan.
Kudi kuma ya tambaya yana kallonta tace gasu kana gani kuwa nan ta shiga kirga kudin tana gamawa tace a, a a dubu ashirin cif ikon Allah wanan yarinya lalai tumfafiyace ita raban ta alheri ne a garemu gidan nan.
Ashe uwargarke taga abinda tagani take mata wanan godiyan haka har muna hanata hakan taga abinda ta gani ashe a jiki yarinyar ke nan ?
Mikewa yayi ya ciro yar nokia din shi tsohuwa data sha dauri ya danna kira na sauke hanna ke nan naga kiranshi ya shigo min a wayan na dauka.
Bai jira mu gaisaba ya fara fadin zarah don me zaki min hakan tun farko ina munyi wanan maganan dake ba wanan a tsakanin zaman mu dake ko ?
Wanan sai mutane su dauka saboda irin hakan yasa nake tare dake dama sai su mace mutumcin da ke tsakani na dake a dauka abin hannun ki yasa nake mutunci dake ashe ?
Amma kasan bakai na kawowa kaya nan ba ko kuma ba gidan ku kawai na bawa ba don Allah ka daina min irin haka idan nayiwa kaka Alheri.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
2️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Tsoki naja nayi wurgi da wayan ina dana sanin zuwa wanan gidan a ranan da banje ba da hakan bai sameni ba ai sai naji duk wani farin ciki da dan walwalan dana samu ya gushe a zuciyana sai zallah takaici da haushi tare da wani kunci daya tokare min zuciyana.
Ban iso gida ba sai wajajen magariba ganin kofan gidan namu ba yawan jama,a yasa na gane cewa Abba ya tafi ke nan shi da Amaryan shi.
Gwiwa mace haka na fito daga motan na rufe na rataya jakata zuwa cikin gidan namu da sallama na bude kofan part din mu da ake rufe tun shida kamar yadda musulunci ya koyar ayi.
Ummah ne falon zaune da kanne na jin karan bude kofan yasata dago kai gareni tana fadin yau ina kika tsaya haka baki dawo da wuri ba ?
Dan daburcewa nayi kafin na samu natsuwa ajikina nace mun tsaya summit din assignment ne ummah bana son wanan dadewan haka a waje kisani dai ke mace ce.
Toh ummah na fada don a matse nake na isa dakina ina shiga jakka da yan takardun dana riko na wurga saman gado na fada ban daki fitsari nayi sosai kamar ba zai tsaya ba a lokacin yadda na zubashi.
Sai lokacin na fara samun sa,ida a jiki na mike kayan jikina na kalla kafin nayi shawaran kwabesu cikin bandakin tare da wankan dana darji jikina da kyau da soso da sabulu masu kamshi na fito na saka doguwar rigana a daidai lokacin an fara kiran sallah.
Don haka na tayar da sallah dama da alwala na fito daga bandiki din ban fito ba saidana sauke isha,i nayi addua na mike na fito don na samu abinda naciwa cikina.
Dining na nufa na bude abinci ina diba kani dake bi mun yazo yana fadin anty zarah nima ki zuba min banyi magana ba amma ji nayi kamar ya dora min wani aiki mai nauyi akaina.
Na jawo plate na zuba mai nasa sanin halinsu yasa na zubawa kowa nasa a lokacin bankai ga zama ba sauran suka fito wurin dan suci abinci basa wuce takwas zuwa tara basu barci ba sai ummah kadai muke bari tana tsabgoginta.
Nan muka fara cin abinci sai karan cibi kakeji a wurin da dan surutun yaran dake tashi ummah ta budo kofa tafito daga daki zuwa falon .
Ai ki basu abincin ne ashe yasa najisu shiru basu shigo damuna ba munan tare dasu tun dazun na bata amsa auta da kanki kikecin abincin ta kalli yar kanwar mu dake ci a wahalce.
Kafin nayi magana kanin mu ke fadin ummah tace bata son anty ta batane karban spoon din tayi hannun yarinyar ta fara bata daga can kanina yace ummah yaushe Abba zai dawo ?
Ummah wai sun tafine na tambaya ina kallon fuskan ummah din a inda take zaune, tace dazun da karfe hudu suka tafi take naji wani iri a raina lokaci guda.
Don gaba daya na kula wanan zuwan na Abba iyayyen mu gaba dayansu basuji dadin zuwa nasa ba don sai shi da Amaryan shine da yanuwan dake sintiri a gidan namu da sunan zuwa ganin amarya don ace tana raba masu kyauta idan sunzo yasa sukai ta tururuwan zuwa ganin ta din.
Lokacin na fahinci cewa da wata manufa sukayi hakan duba ga yadda a dasuke bin mama suna banza da ummah watau sai inda akalan Abban ya juya a nan suke suma ke nan don neman abin duniya.
Magana ummah take min amma sai taga ba saurarenta nakeyi ba na shiga dogon tunaneni a lokacin wai me kike tunane haka wai ?
A,a ummah na fada ina nisawa kafin naci gaba da cin abincin dake gabana ummah tacigaba da fadin ai gara da suka tafi yau din don zaman su zai iya jawo fitina a gidan nan tunda dan zuwan nan nasu Allah kadai yasan iya fitinan da hakan ya haifar a gidan nan.
Yanzu zama yake sosai a cikin gidan nan tunda an hada hardani waini makirace tunda na girka abinci dasu kamar yadda yabada umurnin a girka masu har kwana nawa zatayi ta tafi inda tafito da zan tsaya yin kishi da ita.
Ita bata gane cewa hakan yafi muna rufin asiriba da ace sai an dauko abinci daga gidan hjy an kawo nan mu muna kallo zaifi zafi da cin zuciya a garemu.
Yanzu ba gashi sun tafi ba an dai rabu lafiya aurene baka da hujjan hana namiji yin abinsa idan ya tashi don me zan tsaya fadan kan abinda nasan bada maganin sa .
Iyaka dai inyi fatan Allah ya hau dani saman kansu duk wani sheri ko mugun fata mutum ya nufeni dashi ya koma kansa ni kuma ubangiji Allah kada yabani ikon tunanen da zan cutar da wani a cikin su.
Amin na fada ina lumshe idanuna lokaci guda kafin nace sai azumi ke nan Abba zai dawo yanzu bana ba zai fara azumi tare damu ba a nan ke nan ?
Tunda yana da mata a can yanzu ba zaizo nan ba sai azumi ya raba tsakiya ke nan zaizo rabon sallah ga mutane yadai bada sakon ku nan ya bayar a baku yana hannuna.
Mungode muka fara fada duk da Abban bai kusa damu a lokacin amma hakan bai hana munyi godiya gareshi ba yadda muka sabayi a gaban shi.
Ummah mutanen nan dana kaiwa kaya dazun suna ta godiya sosai wallahi tundai tsohuwar nan dana kaiwa gidanta tayi tasa albarka sosai wallahi tana maku addua.
Kallon mamaki ummah ke min a lokacin kafin tace dani wace tsohuwa ke nan kika kaiwa sadaka na dan natsu nace kakan wanan din Ahmed din na na school din mu wanda ya taba taimakona din nan har ya kawoni gida.
Kinsan gidansu ne ta tambayeni nace eh mun taba zuwa da yawan mu gidan mu gaidashi don shike taimaka muna a school sosai sai muka hada kudi dubu bibiyu mukaje gidan gaidashi.
Maamah kin fara yawo daga school ba tare da sanina ba ke nan da sauri nace a, a ummah wallahi banda nan ban taba zuwa gidan kowaba wallahi ko in group mukaje yau kuma tare dasu hanne kawayena mukaje gidan.
Ban dai son hakan idan zaki wani wuri daga school ki dinga fada min na sani kada ki kara zuwa wuri ba tare da sanina ba a gidan nan nace kiyi hakkuri ummah.
Daga hakan ba wanda ya kara wani magana kuma a cikin mu kowa da abinda yake tunane a zuciyar shi kan hakan daga baya ne na mike nabar falon zuwa dakina.
Wajajen karfe hudu na asubahi Dije ce kwance tana barci a dakinta sai tayi mafalki ga mutum tsaye a kofanta yayi mata sallama ta dago ta amsa mai yace.
To uwargidan mu ni zanyi tafiya ga amana nan na bari a hannun ki duk da nasan kina da rauni a wani fannin amma ki kula ki kara kulawa don mai yuyuwa zan dauki lokaci ban leko nan din ba.
Baki na rawa Dije ta tambayeshi yace amman dai aiba wani sabo bane a wurin ki illa amanan wa yanda kika saba riko gidan nan ga tsiro nan garine wurin wanda yafi garin ga baki daya a wurin nan.
Idan kunyi gigi ko gangancin cireshi kunyiwa kanku hasara mai dinbi yawa a nan Allah ya kaddara saduwan mu wani karon idan da rabon mu sake ganawa a duniya .
Kamar zai tafi ya tsaya yace kibada goyon baya ki karfafawa mai rauni zuciya ki daure ki bashi goyon baya alheri hakan zai zamo maku wara rana.
Yana fadin hakan tanemeshi ko kasa ko sama bata ganshi ba bataga inda yabi ba adaidai lokacin ta falka daga barcin kunnuwan tane ya fara jiyo mata kiran sallah ladanin can kasan unguwar su yana kiran sallah.
Ga wani zufa dayake karyo mata ko ina a jikin ta sai zancen mafalkin ya fado mata a rai take takai kallonta ga kofa kofan yana rufe yadda ta turashi ta tangale da katon kuttuture ice yadda take turawa idan zata kwanta.
Ladanin masalacin sune yayi kwance kwance ya kira sunan ubangiji da karfi har ta dan kadu don firgicin dake tare da ita a lokacin.
Motsin fitowan Amadi daga dakinshi taji hakan yasa hankalinta dan kwanciya budan kofa tayi saidai bata fito ba tana ciki tana dan kimtsawa saida taji fitowan jikan nata daga bandakin tafito daga dakin nata.
Kin tashi Dije ya fada yana kaiwa duke eh barkan mu da fitowa an tashi lafiya yaya daren me yuyuwa iya gaisuwan da zasuyi ke nan a ranan sai kuma dare su kara tashi.
Tambayan shi takeyi da ba a daiga wata ba ko yace wallahi Dije har na kwanta na dade banyi barci ba ina dako ki za,ayi shelan cewa anga wata mu dauki azumi sai naji shiru.
Toh gamu dai sai mu kama baki zuwa safe mu gani ko zamu samu labarin ganin watan a gari tunda mu nan bamu da redio ko abin sani tashige bandaki yayi akwala ya shige dakin shi.
Wayan shi ya dauko ya haska sako ya gani a wayan da baisan da shigowan shi ba tun daya na dare sakon ya nuna ya shigo mai number zarah ce take sanar mashi da cewa anga wata .
Da sauri ya fito yana nufar inda Dije din take zaune yana fadin Dije wai ashe anga wata tun jiya amma ba a sanar ba ko meyasa basuyi yekuwan cewa anga watan ba yadda aka sabayi a baya can.
Ikon Allah anga watan ke nan ta fada saimu wuce da saje ke nan don yanzu ba halin cin abinci don kadan ya rage a kira sallah.
Duban lokacin yayi yace zaki iya gagautawa ko ruwa kisha don akwai kusan minti ashirin yanzu kafin a tayar da sallah.
Hakan sukayi shi dai Amadin ruwan fura yasha sai ruwa daya kora bayan niya daga haka ya fice zuwa masalaci yayi sallah itama Dije ta shige dakinta ta fara gabatar da Nafila lokacin.
Garin yayi tsit baka jin motsin mutane ko ina haka ba yawan mutane a titin sai jefi jefi haka yan makaranta da ma,aikatan dake fita aiki suke dan fitowa a gidajen su zuwa wajajen tsabgogin su.
Haka na shigo makarantan shima shiru ko ina kamar ba mutane mota na parker na fito ina kullewa naji muryan shi a bayana yana fadin.
Barka da fitowa Zarah na sheda muryan shi don haka na juyo ina fadin ina kwana brother lafiya ya bako jiya kin taimakemu sosai wallahi da yau saje zamuyi dagani har tsohuwar kakata a gidan mu.
Ban tashi ganin sakon ba sai bayan har nayi alwala ina shirin fita sallah na dauko waya nagani mun gode kwarai Allah ya nuna muna karshen shi lafiya nace Amin.
Kana ta godiya kamar wani abu wanan hanyace ta taimakon juna ai nasan ko kai kaji zaka aiko muna da hakan ya dan murmusa kafin yace.
A gaskiya zarah naso ganin ki dama muyi magana kan wanan dawainiyar da kika dauko yi muna a gidanmu haka ina gudun abinda mutane zasu fada kan hakan .
Gara mu tsaya da mutunci haka a tsakanin mu don kinsan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba a duniyan nan hakan zai jawo dan tsegumi da zai iya bata muna suna ga alakan mu dake.
Ban tsanmanin duk abinda da za a fada na bataci ne a tsakanin mu don kowa yasan mutuncine tsakanin nida kai hakama wasu dauka suke cewa mu yan uwane na gaskiya dani dakai din yanzu.
Don ganin irin mutuncin dake tsakanin mu dakai so duk abinda zasu fada su fada nidai nasan nice ke karuwa dakai yanzu ba abinda kake gudun su fada ba din ne.
Amma dai duk da hakan don Allah ki dan rage nayi murmushi kafin nace dashi abu daya zai saka na rage shine wanan akuyan dake firgitani gidan ku da ba hakan ba kullun sai nakaiwa kaka abin shan ruwa da kaina gidan ku.
Haka kike da kafiya ba kafewa bane na bashi amsa ina dan murmushi nace idan munbi ta mutane ko gaisawa zai zama matsala a tsakanin mu nan gaba don ko yaushe idon su akan gulma yake.
Tare muka jera har kofa building din mu ya kaini mukai sallama ya juya ya wuce wanan rana shine zance rana ta farko da muka tsaya nidashi mukai magana mai tsayi a tsakanin mu irin hakan.