Showing 228001 words to 231000 words out of 304363 words

Chapter 77 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33372

ganin shi din muryan innace daga falo take fadin wai har yanzun dai kuna kansa bai lafa bane ?
Yafito mana yaje asibiti kada kuma dare yayi ya hana mashi shakat umma ki masa magana ya tashi ko matarsa saita rakashi zuwa asibitin mana.
Amma kun zauna kun sakashi gaba kuna mashi aikin tsubbu haka har wani abu yazo ya sameshi ciwo daban magani daban.
Haba haba inna don Allah ki sakewa yarinyar nan mara mana bafa ita tayi min hayakin nan ba ninace Dije tayi min don abinda nake ji a jikina bana zuwa asibiti bane.
To ubana kada a fadi laifin matarka ko koma ita tayi aicewa zakayi uwatace tunda dukkan ku an gama daku duka yanzu kaika sani ai jikin kane.
Naji din jikinane ko amma you better mind your tongue she's your mother and for perhaps is look like she is worry about your health now, so please don't misunderstand her.
Na fada ina fita sai ya bini da kallo ya koma ya kwanta yana lulubewa da abin rufa bai kara magana ba kuma tun lokacin.
Tun zuwan dan nasa kasan yasa a yanzu baida wani kwanciyan hankali a tare dashi don koda yaushe duk abinda dan yakeyi idonshi na kai yana gani.
Badon komai yasa hakan ba don kada yayi wani abin shedana ya aikata irin abubuwan da yake aikatawa a can yazo yaji kunya a idon mutane.
Duk da dai yana iya kokarin shi a boye don ganin dan ya daina wanan halin don mutuncinshi da kimar shi a gun mutane kada ya zube a sanadin haka.
Asubace ganin hadari a gari yasa shi dawowa gida daga masallaci don yana fita yayi sallah asuba a cikin jam,i saboda yasan iri falala da tanadin da Allah yaiwa mutane a wanan lokacin.
Don idan kana son Allah ya azurta ya daukaka yakuma tsare ya shirya maka yayan ka ka tsareyin sallah asuba akan lokaci maza kuma su tsare sallah a cikin jam,i .
Insha Allahu zakaga mamaki a cikin zurian ka Allah zai azurta maka iyali a yadda baka zata ba idan sun taso Allah yasa mu dace da rahamominsa amin.
Yana kwancen yaji an turo kofa hakan yasa ya gyara kwanciya zakace barci yakeyi a lokacin yadda ya kwanta din juyawa yaji anyi yasa ya bude ido yana kallon ta sai akai sa,a ta juyo ta ganshi .
Ta juyo ta nufo wurin gadon tare da fadin ashe ba barci kakeyi ba Alh a wanan lokacjn zanyi barci kuma ya fada yana dan motsa jikin shi lokacin guda har tasbahan dake hannunsa yana ja tana dan sake kara hakan yasa ta gane abinda yakeyi watau zikirin safe a lokacin.
Yayi mamakin jin kallaman ina kwanan da ya fito daga bakinta a lokacin kafin ya amsa yaga tana kokarin samun wuri takai zaune daga can wajen kafafunsa.
Ya dan bi da kallo don ba yarda da tuban mazurunta yayi ba har lokacin kawai dai yana kokarin danne zuciyanshi ne akanta da yanuwanta .
Muryan ta yaji tana fadin Alh dama kasan da halinda yasir ke aikatawane baka taba fada min ba kokuwa yanzune kaima kasani kamar yadda nima na sanin a yanzu.
Kallota yayi yana kada santala santalan kafafuwan shi dake a harde lokacin kafin ya danyi wani irin ya kallota don jin abinda take fada game da dan nasu.
Wani hali yakeyi sabo kuma yanzu wanda baki sani ba ko kuma son da kike masane ya hana kisan haka din tun tuni.
Nan ta fara rantse rantse da cewa ita bata san wanan halin shaye shayen da yakeyi ba don ba wanda ya taba fada mata haka ke din yabi wace irin uwace wai ?
Har zakice baki san da yasir na wanan halin ba tunkan yaje karatu waje ke wata irin uwa kika kasance wai ga yaranki inko har hakane baki da saka idanu akan dabi,un yaranki kin zamo sha sha shan uwa a yanzu gaskiya.
Agaskiya ban taba sanin wanan zance ba Alh ka yarda dani dacewa bansani ba dinne sai yanzu ko yanzun ma Allah ya nufa in sani na shiga part dinshi nagananwa idona hakan.
Da meye nufinki yabi kina nufin kalan tarbiyan da kike ba yaranki ba abinda zaki girbaba ke nan a wurin su kiri kiri koni mahaifinsu sai ki saba min idan na taba maki diya.
Naji duk laifin yanzu a kaina zai kare tunda nice ban kwabasu ba akace amma yanzu meye mafita don gaskiya hankalina ya tashi sosai yadda na samu yasir din a cikin wani hali don bai ma sanda na shigo part dinshiba lokacin.
Kin tambayeshi tsowon yaushe ina masa fada kan wanan halin don hakane nace ba zan barshi yaje karatu waje ba kika nace harda hada min banga kan sai ya tafi waje karatu ni kuma abinda nayiwa gudu ke nan a lokacin nasan kara lalacewa zaiyi a can din.
Duka hannu biyu ta dora akai lokaci guda kamar karamar yarinya ta soma rera kuka cikin takaici tana fadin na shiga uku Alh shine baka sanar dani wanan halin nasa ba tun lokacin ?
Kallon mamaki yayi mata don bai taba zaton jin hakan daga bakinta ba yace a yanzu da kika gane ina matsayin mahaifi a garesu zan yi hakan ko lokacin da ke kanki baki daukeni da daraja ba balle diyan ki su daukeni wata tsiyan zanyi hakana.
Aina ba yasir kadai ba har ita saliman idan baki sani ba yau ki sani tana bisa kan tarbiyan da suka bakind don dai Allah ya gyarane ita na samu tun wuri na shawo kan lamarin amma ba zance ta daina halin duka ba sai nan gaba idan na tabbatar da hakan gareta.
Baki bude ido waje take fadin Alh salima kuma ita kuma saliman wani matsala ta koyo kuma badai shaye shayen takeyi ba itama ta fada tana kallon shi cikin sonjin amsa daga bakinshi.
Ya dan gyara kwanciyarsa yana fadin zaki iya zuwa ki tambayeta ta fada maki da bakinta tunda tana gidan yanzu ko kuma ki kyale ki saka ido kiga wasu halaiyane takeyi na nuna rashin tarbiya a gareta.
Da badon Allah ya taimaka saman gado take ba a lokacin da ba abinda zai hana ta fadi kasa a sume a lokacin don gigicewan da tayi lokaci guda.
Kuka takeyi sosai yana jin kukan nata na kara bata mashi rai don duk laifinta ne yasan alhakine Allah ya fara jifanta dashi tun nan duniyan hakan ke bibiyan diyan
da suka haifa tare dashi din.
A hankali ya yaye bargon daya rufa dashi yana kallon katon agogon bangon dake manne a bangon dakin mai hoton masalacin ka,aba a jikinshi.
Uku da rabi na rana lokacin ya nuna masa abinda yasashi yin motsi ke nan yana zabura don lokacin sallah da yake ganin ya shige mai a lokacin.
Motsa jikinshi dayayine yasa ya tuna zazzabin daya rufeshi tun a hanyan shigowa su Nigeria wurin dawowa daga tafiyan da sukayi hakan kuma yasashi kokarin tuno da abubuwan dasuka faru dashi din wayen wan garin ranan.
Tabassa wani abin aljabi da ba zai iya fada ba ya faru dashi tun bayan shan maganin nan da tsohon nan daya hadu dashi a garin mutane da sukaje ya bashi don watau irin nasa kuma ya yarda yasha alhalin bai taba sanin wana mutumin ba a rayuwanshi.
Ka tashi ya jikin naka muryan na ya katse mashi tunanen daya fara a lokacin jin hakan yasa ya gane bashi kadai bane a dakin ba lokacin sai yayi kokarin kallo inda yake jin muryan.
Zaune nake saman sallayan dana idar da sallah ina kallon shi da tasbaha baka a hannuna ganin ya kalloni ne yasa na kara mashi sannu ina tambayanshi karfin jikin nasa tare da kokarin mikewa a inda nake zaune din.
Na nufoshi ina fadin yanzu Dije ta tafi itama tun dazun ai tana nan ta sakaka a gaba yau maigida ba lafiya hankalin uwar gida ya tashi ainun sai yanzu data duba taga kayi zufa shine ta tafi ta dauko abin fitara ta dawo ta dauka zafi kakeji nasan.
Dan murmushi ya sake kafin ya sauke kallonshi kan tasbahan da nake ja din yana lumshe idanuwan shi a hankali cikin hakan ne kuma yake fadin.
Sallah nake son in sauka inyi zahra kuma banjin kamar kafata zata daukeni gaskiya don jin jikin nan nakeyi kamar banawa ya fada a dan marairaice cikin nuna har lokacin yana jin jikin nasa.
Ina zuwa na fada na dora tasbahan saman gado na juya zuwa bandakin na kara tsabtace kafin na fito ina fadin muje na taimaka maka ka samu kayi alwalan a bandaki.
Da taimakona na samu ya shiga bandakin ruwan dumi na tanadar masa yayi alwalan dasu na sake kamashi ya fito muka dawo dakin yayi sallah kafin ya idar naje na hado masa tea mai kauri na kawo mashi da kyat na samu yasha rabin kofin ya koma ya kwanta a kasa yai shiru.
To ashe ya falka ina can na tsaya fada da yar banzan nan naje na samu tasha min rake a kofana taki kwashewa dole na tsaya na share na rufo kofan .
Ganin tana magana hankalina yana kanshi yasa tace Amadi yayane wai kodai na fita in sake dubo malam Tanimu din ne hannu ya dago mata alaman a,a.
Tace to ka zauna haka da ciwo a gida ba a san meke damunka ba nifa hankalina ya soma dagawa tunda ba wanda yasan garin daka fito hakan ma ?
Yayi sallah yanzun daya tashi shine ya koma nan ya kwanta naga kamar ya rage jin sanyin da yake ji yanzu karfin jikin ne baiji ko yunwa zai iya haifar mai da kasala.
Amma na hada masa shayi yasha shine ya kwanta a nan din sannu kedai yar albarka kinyi dabaran yin hakan gaskiya ko zai iya cin abinci sai a fita ayo cefanai ki dafa masa.
Muna da abincin dana dafa dazun da safe ba wanda yaci a cikin mu aiko kema ki diba kici ku taru bakuci komai bane kuma harki fadi kema saboda yunwa ba mai kama wani kuma ?
Zanci ai na fada jin hakan yasa ya kallo inda nake yana fadin zahra jekici abincin kada yunwa ya tayar maki da ulcer kuma mana ai naji sauki nace maki ba ciwon komai nakeyi ba sai gajiya da dajin da muka shiga ya jawo min hakan.
Baka dai kara shiga irin wanan dajin gaskiya ka tsaya a cikin gari ka nemi kudinka duk abinda muka samu ya wadatar amma irin wanan wahalan haka meye ranan sa .
Insha Allahu wahalan ya kusa karewama gareshi mu dai matsa da addua Allah yasa muji alheri nan da yan kwanaki duk inna na tsaye muke wanan maganan.
Sai naji tace daga inda take tsaye din tana sauraren mu wani abin zai samu halan da kike fadan hakan ko wani dan uwankine zai samo mashi aikin yi tunda yaki ubansa ya tsaya yana hangen arzikin uban wasu da bai ishesu ba suma har kika fara fadin hakan.
Ai inna ko wani da da sunan ubanshi yake amsawa in kin debe marasa godiyan Allah dake canzawa kansu suna zuwa sunan wani amma aishi master nan yafimu sanin abinda yake shiryawa akan mahaifinsa lokacin hakane kawai baiyi ba.
To abinda aka kitsa mashi ke nan ashe to yajiera lokacin har zuwa lokacin da mahaifin nasa zai sake fushi ya juya mashi baya indai wanan bakin fulatinin uban nakune dan lokaci yake baku kawai yanzu.
Wai yanzu meya kawo wanan zancen ana zancen lafiyan bawan Allah nan ni nakan rasa irin hankali naki Rashida a hakan kike fatan shiga cikin manya ki zauna hankali bai isheki ba ?
Dawa niyi ina son shiga manya ni umma kinkan fara irin maganganun ki ke nan koma nace ina son komawa gidan na manzon Allah ai ba wani abin kunya bane garenu yanzu tunda kowa yasan irin rabuwan da mukayi dashi a baya.
Dadin abin dai banu na kashe maki auren ba lokacin don ko wa yanda suka kashe maki auren yanzu naga baki ganin laifinsu sunema abokan shawaranki a yanzu don kunga abin duniya suna sonci ta dalilin ku yanzu ko.
Haka kuma uban wasu din da kike fadi ai yayi muna komai wanda ya dauki danshi yaba naka ba don komai ba aiya gama maka komai inga tunane.
Don haka nake zama a wurina don nasan danazo nayi magana nice mai laifin don ita gaskiya daci gareta daya hakkura ya karbi mahaifin shi yadda yazo mai aiduk wanan wahalan da yanzu baiyi shi ba.
Gaskiyata daine ba a son a fadi tunda ana ganin zaifi mutane nan gaba shiyasa ake kulla mashi makirci shi kuma ya kasa gane hakan yafi bukatan ya labe a gidin mace yana cin arzikin su.
To dama magana kecin zuciyarki ashe kike rikewa don wanan zancen ba zancen yazu duk ya kawoshi ba dama hanyan fadin abindake zuciyan ki kikeyi.
Batayi magana ba a lokacin sai tashi fuuuu da tayi tabar dakin cikin bacin rai tana fadin babu yadda za ayi ace idan ba asiri ba wai da yaki mahaifinshi haka kawai don wani dalili da aka kulla mai a zuciya tunda yaza mijin tace ko.
Duk binta mukayi da kallo harta fice kafin nace Allah ya gani idan da hannuna ko wani nawa a cikin wanan zancen amma yanzu ashe laifina ake gani cewa nina hana hakan gareshi.
Ai nima idan ya yarda da hakan dadinane tunda ki gidan mu ina da yan adawa masu nuna min cewa ina auren mara gata wanda baida asali.
Hannu master din ya daga alaman don Allah na bar zancen ya kalli tsohuwar yace Dije zan samu in karayin hayakin abin nan na dazun ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/19, 8:05 AM] Mmn Bibo: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣0️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Gidan kamun ya cika da mata yan zuwa buki ga al,ada ranan kamu yakanfi ranan buki cika don wasu idan sunzo kamu ko basu samu zuwa sauran event din ba ya wadatar dasu da mai bukin.
Daya daga cikin atamfam aurena na saka don shi master yafi son in saka kayan da yai min idan zanfita wani sha,ani na buki cikin family mu bansan meye manufansa hakan ba.
Korene da adon fari da baki jikin manyan ganye da aka zanawa atamfan sai dinki three quarter da akai mun dashi hannatu cema takaiwa tellanta yai mun dinkin.
Bazan ce duka ba amma tunda muka shigo nida hannatu idanuwan mutane ke kan mu bansan meyasa hakan ba ko kuma nice me tsarguwa da hakan oho ?
Gaisawa muka farayi da idon sani wasu na min korafin sun dade basu ganni ba wasu kuma kallon dai gayanan dai yadda suke minshi a wurin.
Har muka kai inda yan gidan mu suke zaune muna gaisawa sai naga suna wani kawar da kai gefe kamar basa son su gaisa dani a lokacin.
Nan na barsu na ketara wani dan fili dana gani a bayan su naja hannatu muka ketara wurin muka tsaya muna kallon wasan da akeyi mata nata kwasan rawa ga mai Dj na sake kida garesu.
Mutane kiri kiri suke zuwa kaga mace komai girmanta ta tsugunawa Aisha da Rukkaiya suna gaida su niko bama wanda yasan Allah ya aikoni wajen a lokacin.
Ada idan naga hakan farkon aurena nakan damu amma yanzu abin yabar damuna saiga hjy tsohuwa an fito da ita dungwi dungwi har inda suke zaune din ana kokarin kafa mata kujera a tsakiyan su.
Kai duniya abin tsoroce gaskiya watau kadai idan baka dashi dakai da babu duk dayane a wurin mutanen yanzu zan iya cewa zurian mu kaf a wurin gwaggo shafa nake jin dan sanyi saiko matan baba iro dake gwada min kawaici cewa ni diyan baba Iro dince .
An fito da amarya ana likin kudi gwaggo shafa ta matsa dayi min hannu wai in fito dole yasa na fito din nida hannatu na fara zuba yan dari biyu nan mai kirari ta dan wasani tana fadin ai bansan kina wajen nan ba yar gidan Ali custom ruwan sanyi masu aiki sannu ance bel,bela cikinta baki saman ta fari toke bel,belace ta masar cikin da wajen ki duk farine sai mai hankali yake gane hakan .
Wanan kirarin ya kara jawo hankalin mutane a gareni da akace yan gida su fito zalla su fanshi amaryan su ma na fito na zuba dari biyar biyar sabbi fil dasu sai abin yabawa mutane mamaki kuma.
Ni da nake matar fakiri ina na samu wanan kudin nake famsan kaina nazo zan koma inda muke tsayene naji anty Aishan mu ta jawoni na dawo baya na gane magana take son min don haka na dan tsuguna a gabanta take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login