Showing 213001 words to 216000 words out of 304363 words

Chapter 72 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33348

sai ki ban wanda yake amfani dashi ko wani lokaci.
To Abba na amsa na fada a hankali ina kokarin dagawa sai naji yace yanzu ke wani abin kikeyi a nan karatu kikeyi ko bakije gababa tukun saboda auren don shi a zaton shi ina matakin gama secondary ne kilama din yaga karantana a idonshi.
Sai na dan duka ina fadin Abba ina matakin karshe ne a nan jami,an ta gusau nake karatu yanzu insha Allahu mune zamu karasa nan gaba.
Sai ya dago ya sake kallona yana fadin kai dakyau ashe yaran nawa manyan gobene da mijin da matar Alh jabbo kaji wani ikon Allah a nan har yar nan kin kai wanan matakin na karasa jami,a a dan shekarun nan naki abin yai min dadi matuka a raina dolene na godewa Allah da iyayyen ki.
Don yadda kike diyar mutunci da daraja suka dauki yarsu sukabawa wanda akewa tunanen baida asali da gata a tare dashi duk da na fahinci kalman malam musa kamar da gaiya suka aura maki shi a lokacin dama.
Amma duk da hakan abin a gode masune a yanzu din gaskiya saboda namijin kokarin da mahaifin ki yayi wurin ingata rayuwanki haka da ilimi da kuma tarbiya don dan zaman nan namu na fahinci abubuwa a tare dake.
Jeki ki kawo min layin nasa kada dare yai muna don yau din nan zamu koma da ace mun samesane a gida zamu iya kwana garin nan donshi ayanzu ko tunda bai gida don haka yau din nan zamu juya mu koma abuja insha Allahu sai nan gaba idan mun dawo.
Sai dai ki sani da zaran ya dawo muka gana dashi zaman garin nan ya kare gareku ke nan don ni mutum ne meson ganin iyalina a kusa dani ko yaushe balle ku da kuka dade bama tare daku kinsan dole inso zaman ku a wajena yanzu don mu fahinci juna da ku kuma mama ta huta hakana itama yana kallon Dije.
Dan murmushin yake na sake na mike kowa na kallon yadda muke maganan a cikin sake jiki dashi naje part dina na dauko wayata na fara fada masa numbers din yana dauka a wayanshi.
Don koda na dawo daga dauko wayata na samu ya rabawa kowa dake wajen kudi don haka na dan ja na tsugunna ba tare da nayi wani motsi ba ina kallon yadda suke rawan jiki wurin amsan kudin daga hannunshi.
Basu kwana ba kamar yadda yace sukaiwa har da makwabta da mutanen unguwa wanda rabonshi ya ratsa alheri suka tafi suka barmu cike da alheru a cikin gidan namu don koni ya ban kudin da bansan ko nawa bane a lokacin.
Kuma kowa ya sa ido yaji ko ya gani na mayar da hannu a cikin hijjabina lokacin ga su Aisha na fadin wai inna kin taba rike kudi haka masu yawa a hannunki ko ?
Ke ni ba wanan ba kudinsa na banza kalman daya fada zai dauke yaran nan daga nan shine ya tsaya mi
Takaicine ke damun ta tun bayan dawowanta gidan da yan aminan mijinta sukaje bikonta suka dawo da ita dakinta taso ta saka tsauri ta nuna ita fa itace amma suka gargadeta da yin hakan don sun san zai iya bultse masu yace ya fasa idan yaji wanan dokan data kawo na cewa.
Sai hjy murja ta koma gida Gembo da zama kamar yadda suke zaune a da can tun bayan aurenta dashi din amma sukayi saurin kwabbonta da hakan dole haka ta hakkura ta dawo gidan akan zasu zauna tare su biyu a gidan kamar yadda ya tsara yanzu din.
Yau yai mata dadi don hjy murja zatayi girki amma kuma yayi tafiya zuwa sokoto kamar yadda ya fada masu a gidan da cewa zasu daurin auren wani dan abokinshine a sokoto.
Hakan yasa taji dadi don a yanzu duk wani hanya da zata kuntatawa hjy murja na fili dana boye shi tayi dammaranyi a gidan da ita har sai ta gaji ta bar mata gidan da mijinta.
Don ita ba zata lamunci wata kishiya ba can idan kuma taki a shirye take data salwanta da rayuwanta gaba daya tabar duniyan kowa ya huta wanan shine kudirinta na karshe a yanzu din .
Da wanan plan take kwana dashi take tashi tana kullawa tana warwarewa a zuciyar ta taga wanan ne a yanzu hanya mafi sauki a gare a daidai wanan lokacin Asabe mai aiki tayi sallama tashigo dakin ta duka tana gaida ita.
A wullakance ta dago kai tana kallonta tare da fadin lafiya kika shigo min daki haka ko wani abin kike nema kuma ni banson irin hakan na fada maki tun farko da banson ana shigo min daki idan bani na nemi mutum ba.
Hjy a gafarceni dama Alh ne ya dawo yana falo yana cin abinci naga baki fito ba shine nazo na fada maki don kije ku gaisa.
Alh ? Alh fa kikace mutumin daya tafi dazun da safe yace sai zuwa jibi shine zakice ya dawo yanzu don Allah ki dai duba da kyau ki gani idan ba wani kato ta kawo muna a gidan ba.
Dan dago kai Asabe tayi a hankali kafin cikin rawan murya ta kara fadin wlh Alh ne don har mun gaisa dashi da isowarshi.
Zubur Asaben taga ta mike tsaye a yadda taken haka ta fita daga ita sai dan rigan barci mai karamin hannu duk suran hammatanta a waje suke.
Ya mika hannu ya dauki ruwa a cup din da hjy murja dake gefenshi zaune ta tsiyayya masa zai kai baki ta fado masu dinning erea din kamar a firgice.
A hankali ta tako zuwa inda yaken tana fadin ashe tafiyan dama bana kwana bane kace zaku kwana biyu a can yace eh abinda mukaje yi an fasa don haka na dawo.
Ta danyi shiru tana kallo cup din ruwan dake hannunshi kamar tana son ganin wani abu a ciki lokacin kafin can ta dago kai ta kalleshi tana fadin Allah hutar da gaji ra juya zuwa part dinta sai a lokacin ta fara data sanima da bata fito ba garesu.
Daki ta koma zyciyarta yana azalzala lokaci guda kishi ya rufe mata zuciyanta harta fara anyana abubuwa mara kyau a garesu kafin taji wayanta yana kara ta dauka yarta salima ce data koma ghana inda take karatu a lokacin.
Takai hannu ta dauka murya ciki ciki take fadin salima kece da wanan daren haka tace eh mum haka kawai na kiraki inji lafiyan ki dana yan uwa daddy fa komai normal dai ko ?
Amsan data bata a lokacin yasa salima din tambaya da sauri mum kina lafiya kuwa naji muryan naki a slow mana lafiya ta fada tana jan tsuki tace daddy ku daine yake son kasheni akan matar shi.
Daddy kuma har yanzun dai mum na fada maki ki fita zancen shi kibarshi da wanan matar tunda ita yake so a yanzu sai suje suyi tayi da sauri ta katse yar nata da fadin.
Salima kina da hankali kuwa ta yaya zan fita zancen shi in barshi da ita har wani tsufa nayi da zan kyaleshi ina kallon shi da wata mace ranta ya baci bata san lokacin data fadi hakan ga yar nata ba.
Sorry mum kiyi hakkuri zan kira ya yasir ko zaiwa daddy din magana nima zan kirashi in masa masa magana muji abinda zai fada i promise you zamu ciwo kansa ki bamu gobe da jibi don Allah.
Jin yarinyar kawai takeyi don ita bata iya ciwo kansa ba sai sune zasu iya masa magana yaji da haka sukai sallama ta kashe wayan nata takai kwance ranta a bace har barci ya dauketa.
Yau sosai yake jin kewan gida dana matarshi hakan yasa ya kebe kanshi tun safe a daki tunda ba wani gwajin da zasu fitayi a ranan.
A haka barci ya daukeshi yana cikin yanayin tunanen gida yssani Allah ya dora mai son Zahar a zucjyanshi sai dai bai taba tsanmanin abin ya kai har hakaba a tare dashi.
Ya gane hakanne a yanzu da sukai nisa da junansu don tsanani yayi sati biyu ya juyo zuwa garesu tun bayan da sukai aure yau sai gashi yana neman share sati hudu ba tare dasu ba.
Yake jin kewansu na shiganshi hakan musanman ita zahran dake debe mai gajiyan shi yanzu rashinta a kusa dashi ya fara saukar mai da wani irin yanayi na daban.
Falkjn da yakeyi ne har sautin muryanshi yana fita a zahiri yana fadin na fada maku kada ku tsaya sauearen shi don babu abinda zaice damu yanzu tunda komai yakai karshe.
Ganin Dije da su inna basu saurara mashi ba yasa ya fara kwalawa zahra din kira da karfi har sautin kiran na fita fili a zahiri dakin na amsawa lokacin.
Hakan yasa shi tashi a zabure yana zufa tare da dan waige waige a dskin ko zai gansu ganin inda yake yasa ya gane mafalki yakeyi a lokacin ke nan haka yasa ya zauna yayi shiru na dan lokaci yana tunane.
Wayanshi ya jawo yana duba kudin dake ciki a lokacin ba zasu isheshi kira ba har yaji komai don haka ya rubuta sako ta whatsff ya bar mata daga haka ya mike yaje yayi alwala ya fito.
Dabi,an shine duk lokacin dayayi wani mumunan mafalki yakan kyautata alwala yayi raka biyu ya roki Allah sauki akan abinda yai mafalki akansa din tunda ba wanda zaibawa sadaka a kasan yanzu yadda dabi,an bahaushe yake da zaran yayi mumunan mafalki zaiyi sadaka don neman kariya da abinda yayi mafalkin dashi din.
Shida ba masu karban sadaka a kusa shine yayi nafila raka,a biyu yayi sallah ya roki Allah akan ko menene ya zama mashi sauki a rayuwanshi.
Wajen haraban masaukinsu ya fito ko zai dan samu sa,ida a zuciyarshi ya daina jin yadda yake ji din saidai abin kamar ana karawane lokacin ga mamakin shi wayanshice tayi kara ya tura hannu a aljihun shi ya dauko wayan yana dubawa.
Unknown number ya gani kuma daga Nigeria ake kiran nasa don lokacin cikon dan shakku da tsoro ya dana karbawa yana maiyin sallama ga meshi yana fadin .
Hello Salamu Alaikum kamar ba za a karba mashi ba sai yaji maishi yayi ajiyan zuciya yana fadin wa,alaikum sallam a bangareshi.
Sai kuma akai shiru lokaci guda ya daga wayan ya kalla kafin ya sake fadin hello waye ke magana a cikin harshen turancin tare da sauraren abinda za,a fada a dayan bangaren lokaci guda.
Sunanshi yaji an ambata full kamar yadda yake karbawa da Ahmed Abubukar ya sake amsawa maishi din again .
Sai yaji yace kana magana da Alh Abubakar dan gaskene mahaifinka daga nan Nigeria aka fada a cikin gadara da isa da izza irin yadda manyan da kafansu ya kama kasa suke magana da mutum wani lokaci.

ZAINAN IDRIS MAKAWA
[6/20, 5:58 AM] Mmn Bibo: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣3️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Ban fahinci me kakeson fada min ba jabbo kana nufin duk ku nan kusan inda dana yake ko kuma mai kama dashi kuka gani kuna zaton cewa shi din danane ko haka kawai kuka kawo zancenshi tunda ina neman dana a yanzu ?
Duk da rayuwan shi Alh jabbo din ya baci amma haka ya dake ya dan sake murmushu cikin takaici ya kalli abokin nasa yace.
Nayi zaton zaka fadi hakan ka dauka munzo ma da tsigar yaudara ko cin amma na don muna ganin kana da kudi mu yaudare ka saidai ka tuna cewa abinda ya shafeka mun dauka ya shafemu muma.
Duk da a yanzu munsan kai a wurinka ba haka bane abin yake kana ganin cewa zamu iya cuta maka mu yaudareka don kawai muci kudin ka saidai idan kayi wanan zaton a zuciyarka kayi babban kuskure dayin wanan tunanen.
Don munsan dankane yasa mukaje mukayi tsaye akayi masa gata aka wankeshi daga zargin da mutanen gari suka fara mai suna kiranshi da sunan Shegene baida ubba ko yana da baida gata don baisan ubanshi ba.
Wanan yasa wanan dattijon ya nememu muka tafi da motoci biya tare da sadaki da sauran abubuwan da duk ya kamata a samu a bangareka na uba muka rufawa kanmu asiri don munsan cewa dankane na cikin ka a lokacin.
Sun kuma nemi sanin kai kana ina yanzu mun fada masu cewa baka kasan ne yasa mu mukazo a wanan lokacin muka wakilce ka a matsayin mu na yan uwa kuma aminai a can baya.
Tunda Alh jabbo ya fara wanan bayanin ya dukar da kansa kasa bai dago ba don kunya irin na fulanin asali yana mai nadaman furcinshi na farko a garesu.
Alh Jabbo din yaci gaba da bayani yana fadin wani aure na gaiya ko na rabo ya fada kan yaron a lokacin yasa mu kuma muna ji bamu tsaya yin sanya ba muka tafi a madadinka muka daura mai auren.
Mun kuma boyema wanan zancen ne donshi bawan Allah nan daya bukaci muyi hakan gareka a lokacin don a wancan lokacin da abin ya faru idan ka sani a lokacin akwai matsala babba don haka muka rufe zancen a tsakanin mu.
Sai yanzu daya gama shirin da yakeyi a garekane yace mu tunkare yanzu duk wani sihirin dake aiki a kanka ya kare insha Allahu shine ka ganmu a yau din nan munzo.
Jin yayi shiru ga bayanin shi yasa Alh Habu din dago kai a sanyaye yana bin kowansu da kallo mai alaman wai haka akayi dama baku sanar dani ba tuntuni.
Alh sai hakkuri malam musa ya fada daga inda yake zaune din yaci gaba da fadin alokacin koda mun sanar dakai wani abu fadin baida rana don mumunan abu zai iya faruwa tsakanin ku a lokacin don asiri yana aiki akanka.
Amma yanzu insha Allahu komai yazo karshe da yardan ubangiji saidai fa ka kara dagewa wurin rokon Allah don har yanzu masu wanan makircin suna tare da kai.
Wanan dalilin yasa nace su fadama kada ka rabu da matarka don idan kun rabu din abinda zatayi zaifi wanan da sukayi yanzu ka barta a dakin ta shine mafita koda tayi bai taba tasiri a gareku din.
Tunda ya dukar da kanshi bai iya dagawa ba sai ja, jajir da idanuwan nasa sukayi don jin wanan labarin nan suka fara bashi baki tare da musalai akan kaidin dan adam a zamanin nan.
Nan dai ya dago da kyar yana masu godiya kan wanan namijin kokarin da suka taka masa ba tare daya sani ba a can kasan zuciyar shi kuma yana cike da tunanen fam na yadda zai kalli dan nasa da a yanzu ya girma harda iyali gashi can ya barshi a uwar duniya shima da nasa tarin matsalan rayuwan daya fara fuskanta.
Sun aje magana kan cewa zasu dunguma daga nan kafin su koma gida saboda yafi kusa suje garin wurin yaron don har lokacin akwai sauran kwankwanto a zuciyan shi dangaske din akan yaron kodai ba dan nasa bane wani sukaiwa wanan hidiman haka.
Tun ina saka danuwa a raina har yakai na dan cire tun bayan wayan da mukayi dashi din yake fada min koda zasu dawo sai nan da wata daya don wasu course da sukeyi akan abinda sukajeyi din can.
Na daina wahal da kaina da wani girki tunda Ahmed din bainan kafin na dawo gida nakan dan sayo abinda zanci a hanya tun bayan kwarewan da inna tayi da abincina take fadin wai ban bata da zuciya daya ba yasa hakan.
Ranan bama fita ko ina don haka na tsefe kaina naje wajen kitso ban dade ba sosai na dawo don ban samu kowa a gidan kitson ba lokacin.
Nan na samu sun dora girki sunayi sai faman fada inna kewa Aisha din nagaidasu na bude part dina na shiga ban dade da shigowa ba saiga Dije har kofana tana fadin .
Ga dan fura da kankara ki dama ki diba min yanzu na amsoshi nan gidan mai hura ba zan iyacin wancan girkin nasu mai kazantar tsiya ba haka.
Na karba da niyar damuwa a daidai wanan lokacin wani yaro ya shigo yana fadin ace idan Amadi yana gida ana masa sallama wai daga mambila.
Dije dake tsaye kofan dakina ta juya tana fadin wani Amadin za a gani gida yanzu koda yana gari wanan dan ujulan da bai iya zaman gida ko yaushe yana wurin neman kudi.
Yana can yau rabonsa da garin nan ai ya kai sati biyu ke nan nake gani ta fada tana bin yaron daya juya zai fita daga gidan don jin da yayi ance wanda ake nema din baya gida a lokacin.
Sai kuma ta juyo tana fadin waima yaushene mijin naki yace zai dawo don Allah ya gani ban faye son tafiyan nan nasa na aje a dade ba.
Yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login