Showing 210001 words to 213000 words out of 304363 words

Chapter 71 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33281

Dije ta soma fada tana fadin aiga irinta nan.
Yarinyar nan taga aiki a wahalce ta kawo maku amma ke da yarki mara kunya kuka dinga musgunawa kuna fadin abinda kuga dama akanta ga abincin nan cinshi ya gagareki a yanzu ai.
Nan Asmau ke fadin ji Dije da wani magana don Allah anga abinda baiyi daidai ba ba za a fadi ba ke nan ni ai gishirine nace baiji ba inna tace yayi yaji kuma ?
Da yake kuna munafukan Allah ba wanan abincine za ace yana da matsala inji dije din sai Aisha tace nidai wallahi banji matsalan komai ba a girkin nan banda dadin da yayi kamar na sayarwama.
Murmushin yake nayi na juya zuwa part dina wanka na shiga na fito bayan na daura alwala nayi sallah Azahar kafin na saka kaya a jikina bayan na shafa mai na koma kuryan dakina na kwanta don indan samu hutu a lokacin.
Cikin ikon Allah sai barci ya dan fara daukana har da dan mafalkin gidan mu da yan uwana can cikin barcin nake jin kukan akuyan kuma again haka yasani bude idona a lokacin.
Wayata na samu tana ta kara a lokacin ina dauka naga number kasan wajene a zatona Ahmed ne yake kirana da sauri nakai hannu ina danna dauka.
Muryan bature ne a layin yake magana tare da fadin koshi waye mai karatu idan baki manta ba kin tuno da wanan dai baturen da sanadin sayar da gwanjon Ahmed yasa muka sanshi a baya wanan karon ma shine dai me kiran layin nawa don da shine mukayi amfani lokacin muka kira layin shi da muka gani din a baya cikin kayan gwanjon.
Shine yake min bayanin cewa shine a layin lokacin na nuna farin cikin sake jin ya nememu yake tambayana Ahmed din nan nake fada mai cewa yana nan yazo US yin wani interview.
Wani turancin nasa ba ganewa nakeyi ba duk da nima a cikinsa zance na taso don duk karatuna a private schools masu tsada na Abuja nayisu har na soma hada digree dina a nan kafin mama tasaka a dawo dani nan zamfara da kaddaran aurena da Ahmed ya kirani a nan din yanzu.
Don sam ban kawo zancen aure haka a rayuwana ba koda nan da shekara biyar masu zuwa amma kaddara ta riga fata gareni.
Ina da burin inga na taimakawa rayuwan ku duk da bansan ko baku bukatan hakan a addinin ku ya fada cikin yi da muryanshi kasa alaman damuwa karara a muryan nasa.
Zanyi shawara da mijina zan fada mashi komai game da kai duk abinda ya fada kabamu nan da two days ka kira kaji yace ya gode ya kashe wayan nayi ajiyan zuciya a bangarena ina aje wayan a gefena.
Idona rufe a hankali ina ci gaba da tunanen abinda zan fada masa gashi tun bayan tafiyan shi bamu samu waya ba balle nasan halinda ake ciki a can gashi ba wanda yasan inda ya tafi saini dashi da ummah data san da zancen.
Gabanane ya fadi lokaci guda don shedan daya kawo min wani tunanen cewa wai idan brother Bisi yayi wani tsafinsu na yarbawa dashi fa a can me zan fadawa iyayyen shi ke nan.
Nan hankalina ya kara tashi na jawo waya na kira ummah hankali a tashe bayan mun gaisa nake fadin ummah har yanzu fa tunda ya tafi bai kirani ba.
Tace Ahmed din nace eh ummah hankalina ya fara tashi kada wani abu ya sameshi a sanadina iyayyen shi suyi kuka dani duk da ba wanda yasan da zancen tafiyan a cikinsu don yace kada in fadawa kowa sai idan zancen ya tabbata a sani.
Addu,a zakiyi masa a duk inda yake Allah ya tsare shi ya dawo muna dashi lafiya gaskiya ya fada na rashin fadin komai a yanzu din don yadda yanayi ya koma a yanzu.
To amma rashin sanar dasu din su iyayyenshi hakan baiyi daidai yanzu dai kija bakin ki kici gaba da addua Allah ya dawo manu dashi lafiya yasa tafiyan ya zamo mashi alheri damu gaba dayan mu na amsa da amin ummah hankali tashi tadai dan kwatar min da hankalina mukayi sallama.
Yayi mamakin ganin abokan nashi Abuja saidai tunanen shi ya bashi akan matsalan shi da hjy yabi da take damun mutanen da tasan suna da muhinmanci a a wajenshi da kira shine ya kawo su a lokacin.
Taro na muhinmanci sosai akai masu kafin su natsu su fara maganan daya kawosu din akan matsaloli biyun da suka tako zuwa Abuja don su gana dashi akai.
Matsalan ita hjy yabi din suka fara gabatar mashi tare da bashi hakkuri a kai yana jinsu tare da kallon wanan bakon fuskan da baisani ba a cikin su lokaci lokaci yake dan dago kai ya sauke a kanshi din ya kuma kawar da idanun nasa.
Saida ya gama sauraren su yace dasu ba mamaki don a yanzu kunzo da kanku har nan akan nayi hakkuri na sake zama da yabi a gida a matsayin iyalina.
Saboda yawan damuwa da magiyan da take maku ko yaushe a waya ko ku kuma kuke ganin hakan bai dace da ita ba a yanzu don kuna ganin ita din matatace ko ?
To kada ku manta da yabice silar lalacewan komai a gareni a baya har kun manta da rabani daku da tayi da irin cin fuska da zarfin data dinga yiwa duk wani na tare dani don kawai a barta dani su juyani yadda suke so ita da yan uwanta.
To duk ba wanan ba sai irin yadda ta shiga ta fita harta fitar min da zuciyana ga yaron dana haifa a cikina saboda son kai irin nata kawai.
Ta yaya kuke ganin zan iya sake zama da wanan matar yanzu a rayuwata bayan irin wanan cin amanan dayi mun haka a rayuwana wanda da badon Allah ya gyara ba da hakan wata,kila da zuciyana ya buga a wanan lokacin.
Ba abinda ke cin zuciya kamar zancen yaron nan da bansan halinda yake ciki ba a yanzu shida uwarsa wanda nasan alhakinsa ba zai barni na zauna lafiya ba.
Insha Allahu zaka zauna lafiya ai alhaki a kanta ita datayi asirin data rabaka da dan naka wanan bakon fuskan yayi magana na farko tun zaman su a falon bayan gaisawan da sukayi da juna.
Ya cigaba da fadin ka godewa Allah dayasa warware maka matsalanka tunkan ka makara lokaci ya kurema zuwa lokacin da gane hakan baida amafani a gareka nan gaba.
Amma Allah da ikonsa sai gashi ka kurto daga kaidinta da makarici a cikon lokacin da ake bukatan bawa ya koma ga Allah a lokacin zai dinga istigifari.
Malam ai munayi don da taimakon hakan har aka samu na samu kaina daga sherinsu da bansan inda makircinsu zai kaini ba nan gaba.
Kwarai kuwa Dan gaske kayi magana daidai gaba don wanan bawan Allah daka gan mu tare dashi a yanzu nasan kana mashi kallon rashin sani a fuska yanzu.
Ya amsa da sauri da fadin kwarai kuwa dan tun zuwan ku nake masa kallon inda na sanshi abaya don fuskanshi yana min kama da wanda nasani abaya can amma kuma na manta da inda nasan shi.
Ba lalai bane ka sanshi amma shi din yana daya daga cikin wanda ba zaka taba mantawa dashi ba idan kaji abinda muke tafe dashi game da wanan fuskan a yanzun.
Zama ya gyara irin na manya yana fuskantarsu da kyau tare da fadin na,am cikin rashin gamsuwa da maganan da suke fadin.
Alh jabbo yaci gaba da fadin a yan lokacin daya shude kadan a baya shi wanan bawan Allah ya hadu da wani yaro dayazo daga arewa maso yamma.
Yazo da sunan neman mahaifinshi da baisan a ina zai sameshi ba jin hakan yasa bai yarda ya sake yaron hakana ba yayi mai masauki a gidanshi suna bincike a hankali.
Da bai fahinci komai ba yaron ya tafi ya barshi da bincike bayan ya nema bai gane komai ba sai yayi amfani da sanin da Allah yayi mai ya gano wasu sirin abubuwan dake boye game da kai da iyalinka.
Hakan baisa ya fito a lokacin yayi bayani ba sai daya zauna yayi aiki sosai a kan hakan har Allah ya taimaka ya cinwa makarin abin yakumayi aiki sosai akai ta hanyar yakar wanda ya aikata kulli a ruhinka.
Wanda har hakan yayi nasaran kariyan komai dake kulle da ruhinka a wanan gabar kuma ya nememu a matsayin muna aminan ka na can baya don a san yadda za a tunkareka da wanan zancen.
Zama ya gyara yana masu kallon ni za a aiwa wanan rainin wayau don sunga ina cikin damu har abin yakai yanzu suyi amfani da wanan daman a hada kai dasu a yaudareni ?
Idonshi nakan Alh jabbo din dake bayani lokacin shiko yaci gaba da fadin a cikin hakane yaron ya sanar dashi cewa zaiyi aure shine lokacin da wanan malamin ya nemomu yake muna bayani komai .
Kuma ya sanar damu komai daya sani a takaice dai in gajarce maka zancen munje buki a zamfara an daura aure mun tsaya mashi a matsayin iyayye a gareshi mun karba mashi aurensa.
Wani kallon mamaki yakewa abokin nasa na kasan abinda kake fadi kuwa yace kwarai abindana fada dai atakaice danka Ahmed yana raye kuma mu munsa da hakan .
Kawai dai munbar zancen ne a tsakanin mu tunda mun fahinci baya cikin zuciyar ka a lokacin fitowan shi ya baiyana a gareka hakan na iya haifar da wani matsala sabo ..
Alh Jabbo ddana fa kake nufin cewa kunsan da inda yake har kunje kun tsaya mashi a matsayin iyayyensa ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA[6/20, 5:58 AM] Mmn Bibo: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣4️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,


Kofan part dina da aka turone yasa dukkan mu muka kalli wurin Dijece ta shigo tana fadin ina amarya ki fito ku gaisa da mahaifin naku kuma kuzo ku gaisa dashi da cewa su Aisha.
Jin hakan yasa na figo hijjabin sallahna muka fita tare lokaci guda suna da yawa a wurin ganin haka yasa naji kafana yana hardewa.
Daga can bayan Dije na labe ina gaidasu da zuwa duk suka amsa muna lokaci guda suna kallon mu kafin wanan tsohon yace wanance sarakuwar tawa ko yana nuna ni.
Dije ta bashi amsa yace jijiga kai tare da fadin Allahu akabar duk inda kake arzikinka saiya bika yarinya sannu da hakkuri ki dan kara saman wanda kikayi a baya alherin ku kamar yashigo hannune ko gareku.
Watau Alh wanan yar da kake gani itace mabudin komai ga dana don itace silar komai dake faruwa a yanzu saidai ba za a gane hakan ba don hankali baikaiwa a gane komai.
Anyi gaiya da zaton kuntatawa a garesu saidai gaiyan ta alherice ga kowa nan gaba kadan insha Allahu arzikin su dayane ya dago yana kallon inna dake zaune kofan dakinta a lokacin takure don ta raina kanta da ganin mahaifin master a yanzu yadda ya koma.
Shi mai hakkuri baya taba tabewa a banza don haka yarinya ki kara hakkuri akan wanda kikeyi yanzu kada zancen wani ko wata ya daga maki hankali ko kadan komai na duniya mai zuwa ya wucene ga bawa.
Allah ya dawo maki da mijin ki gida lafiya abinda yaje nema a sanadin ki Allah ya bashi ke ai alherice a wurinsa da kowa nasa insha Allahu.
Kan kowa dake wurin ya daure yadda tsohon ke fitar da zance a dunkule ba tare da ya nuna ga inda zancen nasa ya dosa ba a lokacin dije ta karba mai da fadin kwarai hakkuri komai tsayinsa akwai alheri nan gaba don ni zan fadawa mutane hakan .
Don ko akan Amadi naga hakan a baya haka yake dawo min da kuka an kirashi da shege ko an goranta mai rashin uba mara asali wanda ubansa ya gudu ya barshi haka zan shura takalmana naje fada wasu su ban hakkuri wasu kuma su sake goranta min a gabanshi.
Yau gashi da rayuwana na fara ganin haske a gare shi bayan irin kunci da wahalan rayuwa da muka fuskanta abaya tun tasowan yaron nan inba malam Tanimu gashi nan da yakan dan tsaya masa wani lokaci tun bayan rasuwan ladan zance a cikon kunci da bakin ciki yaron nan yake rayuwa .
Sai ko haduwan shi da yarinyar nan gata tun haduwan sune abubuwa suka fara walwarewa a garemu yake dan samun abinda zaiyi har muka fara girki a cikin gidan nan yanzu muce masha Allah.
Don dai, , , , haba Dije wanan maganan ina ya fito haka a bakinki kuma yanzu ai adai godewa Allah tunda mahaifinsa ya dawo gateshi yanzu.
Wani daga cikin yan uwan kakanshi masu nuna masa tsana a baya ya fada da sauri sai Alh jauro yace dashi ka bari ta fada munsan zafin da take ji a yanzu a zuciyan ta komai ta fada daidaine don an saba masu a rayuwansu ga hakan.
Balle ita zance ai gaskiyace ko bata fada ba dolece ansan zata fuskaci wanan rayuwan tunda anyi ba sau daya ba muna gani sai dace da mutanen arziki ankan samu saukin zuciya idan irin hakan ya faru da mutum.
Har lokacin mahaifin nasa baiyi magana ba yana zaune ya dukar da kanshi kasa zatin shi da kwarjinsa kawai ya haska wurin ta yadda ba mai iya fada mai zancen da bai dace ba.
Haka ko duba ga yadda yan uwan suke girmamashi ya isa mutum ya gane shi din wani babban mutum ne a cikin al,umma a lokacin.
A hankali ya dago kai ya juyo inda nake gurfane ya dan kalleni kafin muji muryanshi a karo na farko a zamansu wurin yana fadin yarinya waye mahaifinki garin nan ne ?
Jin hakan yasa na dago da sauri na dan kalleshi farine sol karfafa dashi duk da girma ya fara kamashi lokacin da ganinsa kudi da mulki sun zauna a jikinshi sun zama jinin jikinshi a wanan lokacin.
Don haka dole ya tambayene haka a cikin gadara da izza da isa amma sai nake ganin ai nima idan na fadi sunan nawa mahaifin zai ji izzansa ya gushe a lokacin don nima nawa mahaifin sanane sosai a wurin suna a kasan amma ganawa tunanen.
Yarinya dake ake magana wani daga cikinsu ya fada don tunatar dani a inda nake lokacin don haka na dago kaina a hankali nace Mayanan Gusau.
Kallon alaman bai fahinta ba yayi min na sake fadi ina dukar da kai kasa Alh Ali custom mai ritaya na garin nan ya juya ya kalli su malam tanimu dake zaune sun zuba ido da sauri Baba sani yace rankaidade ai wani mai kudine yana zaune a abujane yanzu iyalinshi suna nan garin da zama su yace.
A Abujan nan dai yake zaune yaya akayi ban taba jin hakan ba ko sunanshi a garin sai kawai naji ba dadi a raina lokacin don hakan kamar rainine gareni ai.
Don jin hakan yasa na dago kai ina fadin yana zaune a maitama da zama shidin kuma yanzu business man ne a can yana kuma siyasa saboda ritayan da yayi.
Masha Allah kice mahaifin naki duk mune ashe yan kasuwa hakan nada kyau sosai zan binkinta na nemeshi mu san juna idan mun koma Abujan don nima a can nafi zama idan ina kasan nan da iyalina.
A raina nace tofa kaji manya sai idan ma yana kasan ke nan yake zama a Abujan da iyalinshi ke nan a waje ya faye zama ke nan zancen shi ke nufi sai naji ya katse min tunanena da fadin.
Mijin naki zai dade a can ne ko ya kusa dawowa a yanzu na dan girgiza kai kafin nace nan dai da one month zai dawo kila yace idan sun gama course din nasu.
Ok wani irin program ya tafi yi ke nan nace Abba bansan ko wani irin course bane yaje yi yadai ce an daukesu zuwa can din don yin course din .
Sai naji yayi murmushi yace kai da kyau hakan yayi min dadin ji sosai wallahi Allah ya bada sa,an abinda akaje nema a can nace amin sai na dukar da kaina cikin ladabi don a takure nake a wurin don tambayoyin sun min yawa a lokacin.
Amm,mm ko zan samu layinshi a wurinki wanda yake kiranki dashi a hankali na dago kai na amsa da ehh Abba akwai layin wayansa saidai ba a samun shi idan bashi ya kira mutum ba.
Ok dama waje ya fitane ko kuwa sai nace ina ganin cikin kasanne suke kafin naci gaba yace ok dama hakane kinsan wata kila course din ba mai son damuwa bane sun zama special people ba ko yaushe bane yanzun za a samesu ba ke nan .
Duk da haka ina dai son in samu layin nasane a wurina don nan gaba saboda kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login