Showing 174001 words to 177000 words out of 304363 words
yajawa inna matsala har ta tabo jinnu suke wahalal da ita a yanzu don malam yace ta nuna rashin imani a garesu ne.
Ai kaji irinta lokaci daya yarinyar nan ta canza halaiyarta dana santa dasu a baya wanan yawon ciranin bai kara Rashida da komai ba wallahi shiko ba abinda ya tsaya mashi a rai sai tunanen yadda inna din ta nunawa uwargarke a ranan.
Sai wanan abin ya tsaya mashi sosai a rai daya je basu abinci ya duka yana gyara mata wuri yana fadin uwargarke nasan inna ta bata maki rai kin kuma rama amma don ni da yan uwana ki barta hakan kamar da wasa yai maganan gami da kurciya lokacin tunda yaji ance dabbobi suna jin maganan mutane..
Abu kamar wasa saiga ina ta mike wasai washegari kamar ba ita ba lafiya ya samu tana ta faman kwasan barci kamar tasha maganin barci yana mata amfani a jiki.
Alh ban fahinci wanan sabon halaiyar daka tsiro dasu a yanzu ba matar ta fada cikin kunan rai a cikin harshen fulatanci.
Yana a yadda yake zaune zakace badashi take wanan maganan ba lokacin yadda baiko motsa ba ganin hakan ya kara bata haushe ta tako zuwa gaban shi ta tsaya tana kara maimaita abinda ta fada da farko.
Sai lokacin ya dago ya kalleta da tun kan ya bude baki yai magana ta hango zallah tsana da masifa a indon shi abinda bata taba hangowa ba ke nan a zaman su.
Don tana da tabbacin cewa duk yadda ta juyashiba nan yake tsayawa ba mussu gareta amma a yan kwanakin nan abubuwa sai kara bata mamaki yakeyi na sabon halaiyan shi.
A ranan sai ya koma mata dangasken shi data sani ba Alh ta ba da take juyawa gabantane ya yanke ta fadi sosai tasan akwai matsala babba dake shirin faruwa da rayuwanta nan gaba.
Ke ki fita daga dakin nan tunkan rayuwan ki yakai ga baci ya fada cikin kakausan harshe gareta dole tanaji tana gani ta juya zuwa part din ta cike da fargaba a zuciyanta.
Kallo takaici ya bita dashi har lokacin data rufo kofan ya sauke idon shi ga kallon rakiyan dayai mata din na takaici.
A yanzu yake nadama da dana sanin tare da tambayan kanshi na hada iri da wa yan nan mutane marasa kirki a yadda yasan su a baya a yanzu ga zuria sun shiga tsakanin su dasu haka.
Ashine tambayan da yake yawan yiwa kansa lokaci lokaci a yan kwanakin nan gashi ya kula duk wani dan uwa nasa na jini a yanzu bai tare dasu sai yan tsiraru haka daga cikinsu din duk halin hjy Yabi ya koresu gareshi.
Kai ya mayar baya saman makarin kujera yana mai sauke ajiyan zuciya a hankali ya dan runtse idanunshi a hankali yayin dayake dan kada kafanshi a hankali.
A haka barcin ya dan daukeshi yana wanan tunanen ya kwana biyu da wanan mafalkin sai gashi yayi a dan barcin daya daukeshi din lokacin.
Yaron nan daine mai kama da yasir dinshi duk da bayan shi yake yawan gani lokaci lokaci amma kamaninshi da danshi yasir yana da yawa ko a hakan da bayan shi yake gani kawai.
Zubur ya dan zabura yana waige waige a falon ta ina zaiga wanan matashin daya shigo mai yanzu yana maganan akan hakkin shi wani haki nasa zai basane haka wai ?
Hannu ya yakai a fuska ya shafo kafin ya tsayar da hannun zuwa goshin shi yana dan murza kadan kadan tare da tunane a zuciyan shi.
Inda tunanen nasa ya tsaya cak ga abokanshi na kurciya dake gida zaune a yanzun cikin halin irin na rufin asirin bawa duk da yaci ace ya taimakesu a yanzu amma ya kasa hakan a garesu.
A hankali ya bude ido kafin ya mayar ya rufesu a hankali yana mai jin wani irin zafi a ziciyanshi don ya kasa gane dalilun haka a gareshi bayan yasan irin gudunmawa da suka bashi a rayuwansu a baya suna yara dashi.
Yanzu meye abinyi ya tambayi kanshi a take zuciyarshi ta bashi amsa a wurin da ya nemi dan Jauro donshi gaba daya cikin su yafisu natsuwa da sanyin hali ga sanin ya kamata.
Bai karasa tunanen shiba yaji jauro din yana masa sallama a cikin waya jin haka yasa ya katse tunanen shi ya amsa masa sallaman shima.
Ikon Allah yau dan gaskene da kansa haka ya kirani ko batan layi kayine ya fadamai cikin zolaya dan murmushim manya ya sake tare da fadin ba bata nayi ba kaidin dai na kira muyi zumunci.
Murmushin ya mayar mashi shima tare da fadin aikuwa nagode gamuma tare da jabbo yanzu haka a kofan gidanshi jauro ya fada .
Wani iri yaji a ranshi kafin yace dasu kai haba dai kuce ni kadai kuka ware dama ina Alamu yanzu yabar nan zuwa asibiti shima duban yakumbomsu da aka kwantar jiya.
Idonshi arufe yace jam balafiyane haka har asibiti yace eh wallahi kasan tsufa da yan ciwarwatan zamanin nan na yanzu da ba a rasaba.
Badai kuna lafiya da iyalin naka ba nan duka ko kuna kasan wajenne yanzu don baku zama a cikin kasan nan sosai ku ?
A,a muna nan duk lafiya suke to madallah Allah abin godiya nagode nagode Allah ya bar zumunci amin tunda ka tuna damu har munji lafiyanka a yau.
Don ko jiyan nan saida Alamu yai maganan ka nace tunda mukaji shiru lafiya kuke don shiru ke nuna lafiyan mutum.
Tau lafiyan dai amma ba lau ba don wani abu ke damuna ya kuma daure min kai sosai a yanzu jauro shine naga ba wanda ya kamata in nema yaban shawara illa kai sai gashima kana kusa da Jabbo ashe.
Jam jam dangaske meye wanan abin wanda yai zafi haka ya daurema kai kuwa ku manyan kasa daku sai yai masa murmushi irin nasu.
Wayance ta dauke ya barsu suna faman fadin hello hello don sunzaci cewa shiru yai masu yana jinsu sai daga baya suka gane cewa wayance ta katse ashe.
Shigowan yarinyarshi yasa ya kashe wayan yana saurarenta don zancen data zo mai dashi lokacin wanda tambayanshi takeyi Dad mekayiwa mommy take kuka ?
Don yaran tashin falone kai tsaye suke zance da iyayyen nasu saboda gata daso dayai masu yawa a rayuwa sun tashi basu da kwabo ko kadan.
Balle su san basuyi daidai ba gashi uwar kamar itace uba a gidan duk komai na rayuwan gidan itace ke gudanar dashi .
Don hakane sukafi ganin kimarta da uban nasu sosai yanzunma data samu uwar a daki ta gama waya da yarta ta tambayeta meya sameta shine tace daddysune.
Bata tsaya jin meyafaru ba kawai ta juya ta fita zuwa wurin daddyn nasu ta tambayi ba,asi taji abinda yaiwa mommy din nasu.
Itama kamar uwar ya barta da mamajinshi ranan don ya koma mata tankar wani zaki agabanta yadda ya daka mata tsawan da saidata kadu ta koma tana mashi kallon mamaki lokaci guda.
Don cewa da tayi dashi bayan ta fado mai falon a hasale yana zaune yana waya lokacin da abokan nasa.
Tace dashi da daddy mekaiwa mommy mu na samu tana kuka akan ka kuma ban saba ganin hakan gareta ba sai yau ?
Ya dago kai cikin mamaki tare da kashe wayan yace you are very stupid Ni,ima you are more than stupid da zakizo kina min wanan tambayan haka ba respect a tare dake ?
Yadsa yake maganan yasa ta kaduwa don gaba daya ya canzawa sanin ta a ranan ya koma irin mahaifin da take gani a cikin film ko a wasu gidajen .
Kofa ya nuna mata da yatsa alaman ta fita mashi daga falon tayi saurin juyawa zata bar falon yace dakata daga yau karki sake shigo min falo haka kai tsaye babu sallama understand ?
Ta gyada mashi kai alaman taji ta juya ta fita zuwa part din uwan nasu hankalinta tashe tana tafiya kamar tababa a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
6️⃣0️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Mommy daddy lafiya yake kuwa ta fada tana shugowa dakin a firgice yau bakiji irin voice din da yayi min ba don na sameshi natambayeshi abinda ya faru.
Na fada maki aida baki jeba don akwai matsala dake shirin faruwa da nake hangowa don haka dole mubishi a hankali har mu gano inda matsalan yake.
Mommy mu hadashi da Grandma kawai ita zata taka mashi burki don ba zan juri ganin hakan ba gareki dolene daddy ya dawo normal.
Zan fada mata amma ba yanzun ba sai nan gaba idan abin yafi karfina zan nemi taimakonta ta fada tana kawar da kai daga kallon yar nata dake tsaye a kanta lokacin.
Cikin takaici ya kawar da fuskanshi daga kallonta na dan lokaci kafin ya dora hannayenshi saman haban shi ya shiga dogon tunane akan matakin da zai dauka yanzu ga iyalin nasa.
Har daki ya sameta bayan sun gaisa yai mata ya karfin jiki ta amsa da lafiya Alhamdullahi jiki yayi sauki sosai na rage wanan mafalkin da nakeyi mai firgitani yanzu.
Alhamdullahi Allah tsare gaba saidai inna ya kamata wasu abubuwa yanzu ki daina don in kaiwa wani ya kyale ka wani ba zai kyaleka ba hakama dabbobi tsakanin mu dasu tausayine da jin kai.
Don baka san irin baiwan da Allah yaiwa wani dabban ba kana tabashi bai baka bashin hakan Allah ya tsare gaba tace amin ya mike ya shige wurin Dije su gaisa da ita.
Ya fito daga sashen sune ya dawo daki ya karya ya fita don yana son yai sayayya don ya koma makaranta wanda sayayyan duk na gidane shi a can yakan dan sayi abinda zaiyi amfani dashi.
Gashi dan break yazo don matsalan fargaban dake damun shi sai laluran ciwon inna din ya tsayar dashi har tsawon sati biyu ake nema yanzu sai faman kiranshi abokin karatun shi keyi akan ya dawo zasuyi test.
Hakan ne ya daga mashi hankali yake shirin komawa a lokacin bayan fitan shine ina zaune a falo ina kallon wasu photuna a wayana na bukin wasu diyan abokin Abba da akayi akai shagalin karya sosai sabanin na bukin koda yake aurena ne ba ai wanan ba da aurensu Aisha sun dayi wasu event da akeyi cikin gari.
Naji wayana yana kara na dauka na duba ummahce a layi take kirana lokacin na dauka da sauri tare da sallama muka gaisa tayi min ya mai jiki na amsa da ta samu sauki sosai yanzu.
To na kira in fada maki cewa yar uwarki Aisha ta haihu dazun da safe yanzu haka tana gidan nan sun dawo daga asibiti idan kin samu lokaci ki shigo ki dubata.
Murnane ko mamaki ya rufeni nace ikon Allah ashe cikin dama har ya isa haihuwa to Allah ya raya yasa dadin musulmine tace amin zanzo ko yau ko gobe insha Allahu.
To sai kin shigo kidai ta hakkuri komai na duniya dan hakkurine wata rana sai abin ya zama labari idan bawa ya iya hakkuri daga jerabawanshi.
To ummah nagode na bata amsa tare da fadin zanshigo kafin Master ya koma Allah bada iko ta fada ta kashe wayanta lokaci guda na lumshe idona har lokacin ina jin wani iri a zuciyana.
Kamar yadda duk wata mace keji a rayuwanta a lokacin da taji wani ya haihu ko wata nada ciki yar uwan aurenta don abin yana taba zuciyar mace sai dai idan hakan bai sameka ba.
Gashi yan uwan master ko ince mahaifiyar master tana ganin cewa nice banson haihuwa da danta nake planing don kada in haihu dashi har take ikirarin cewa zata auro mashi wata mace a lokacin duk da bamu dade da wani aure ba.
Balle yanzu taji cewa Aisha da akai muna aure rana daya da ita harta haihu ni ko batan wata ban taba yi a gidan nasu ba ai nasan zata sake min zance a ranan.
Nisai nasan Master gwarzo a wurin kwanciya duk da yasan nidin ba gwanan hakan bane amma bai kyaleni sai bukatanshi ya biya yakan barni.
Don haka nasan abin na Allah ne shike bayarwa a inda yaso kuma yaga daman hakan ga bawanshi a lokacin da kuma yaga dama.
Anan ya dawo daga kasuwa ya sameni saida ya nuna mamakinshi a fili yake fadin badai wai har yanzu kina wurin nan zaune ba ya fada.
Na dan rausaya kai tare da fadin harka dawo ina nan ina kallon waya photuna bukin gidan Dr nake kallo tundazun sai naga yayi murmushi tare da fadin ance ansha buki kan gaskiya a wurin.
Ga kayan nan ki duba abinda na manta sai na koma na sayo ya fada a lokacin da nake mikewa zuwa kitchen ruwan da muke sakawa a gora na dauko mashi tare da cup na kawo mai duk da baida sanyi sosai.
Ya karba tare da godiya yana sha na bude kayan ina duba tare da fadin ai akwai komai nake gani yace a,a ki dai duba naga kamar na manta da wani abu a ciki.
Idan na tuna sai in aika asayo min ai a, a na fada maki banson kina min ciko komai da yake hakkina ki dinga fada min in saya don Allah don in sauke nauyina akanki.
Sabulu da omo ya rage na fada yace da man shafaki naga ya kusa karewa ai eh amma akwai wani wanda ban budeba ai yana cikin drower aje.
Ok ita inna tace saina karo masu kayan miya don in na wuce sai ta saya wani abin wani lokacin wai ina bambanta sayaya in sayo maki mai yawa su kadan bai kaisu har inyi sati biyu in dawo.
Tana ganin kamar nafi sayo maki kaya mai yawa fiye dasu kinga dole in koma kasuwa in karo masu in ba hakaba magana zai zama min nan gaba.
Murmushi nayi nace nace a fili dole kan ai sai an kara don suna da yawa balle mace sai tayi cikon wani abin dama girki ke kammala.
Amma kinga abinda na sayo masu kuwa hali daine irin na inna nason kure mutum don har Dije saida tayi magana kan hakan itama amma bari dai din na karo.
To shi dai yafi gaskiya inda hali ka karo masu ai ba komai bane ina fadin hakan na bashi ina kwasan kayan yace yanzu dana huta zan koma na sayo masu ai.
Ya fada akasalance nasan ya gajine sosai lokacin yana so hutu nidai na dauki kayan na nufi kitchen dasu nakai kofa na juyo tare da fadin.
Aff kaga na manta ummah ta bugo waya dazun tana tambayana jikin inna, kafin naci gaba da magana yace Allah sarki ummah akwai kokarin kulawa wallahi nima takirani shekaran jiya tana tambayana jikin nata ai.
Tace Anty Aisha ta haihu yau da asuba ta samu ya mace har an dawo da ita gida tana nan gidan ban karasa ba yace wace Aisha dai kike magana wai ?
Nace Anty Aisha tamu dai ta gidan mu mana ita nake nufi ta haihufa kikace yana kallona cikin mamaki nace kodai baka gane Anty Aisha din bane ?
Nagane mana gani nayi dai tare akai bukin mu aiko nace ashe kaganeta yace shine kuma ta haihu yanzu ko wata takwas din bamu cika sosai ba ai don saura kwana goma sha yanzu mu cika wata takwas.
Gabanane ya fadi don sai lokacin nagane mai yake nufi ai da sauri nace to shine abin mamaki mata da mijinta yanzu ina abin mamaki ciki .
Kuma kasani dan wata bakwaine yaron yace zai yuyu kuma gaskiya Allah ya raya nace amin a sanyaye gabana yana faduwa.
Idan hakane kuwa akwaita kenan na fada a zuciyana na shige kitchen din mu ina aje kayan don a nan nake akewa duk da nagane ana diban min wasu kayan aikin nawa wani lokaci idan na aje a nan irinsu maggi tomatoes curry da mai tundai mangyadana na miya.
Don hakane su na barsu a dakin sai na dawo na adana a cikin dakin gashi na fara jin inna tace abinda aka sayo masu baya isa kenan dama da nawa ake karawa ayi yanzu kuma nayi wayau ina sakawa daki dukda haibaicin da inna kan min da ba kayan gidan ubbana bane dai saukin abin.
Nasaba da irin gorin inna son haka abin bai damuwa nake shayewa sai in nuna kamar bansan dani takeyi ba ma idan tanayi don kawai a zauna lafiya.
Kodana koma dakin yana zaune yana gyagyadi lokacin ya ban tausayi nasan in nayi motsin daukan ledan zai iya falkawa don haka nabarsu a wurin na shige uwardakan mu na jawo wayana.
Hannatu na kira na samu ta dauka na fara labarta mata zancen haihuwan Aisha din amsa dayane tabani irin nasa cewa wata Aisha dai kike nufi zahra ?
Tamu