Showing 153001 words to 156000 words out of 304363 words

Chapter 52 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33317

ina bashi amsa da kai don ban iya magana da baki don yadda nake ji a lolacin nadai nuna mashi ba komai a lokacin .
Yace zahra idan kina wanan yanayin ba zanji dadi ba don sai in dauka ko nine bakiso ko yanayin gidan namune bai maki ba .
Yana fadin hakan na mike na shige daki na kwanta rub da ciki naci gaba da kukan da nakeyi harda shesheka ina hadiyan zuciya.
Can ya shigo ya dan tsaya yana kallona tare da fadin o,o zahra tun farko gudun haka yasa na fada maki kiyi girkin ki iya bakinmu mu kadai.
Can kuma ya kai zaune yana fadin haba zahra idan na bata maki rai ko wani nawa don Allah ki daina kukan nan kiyi hakkuri don Allah.
Da kyat na iya budan bakina murya ciki ciki nake fadin No Master ba hakana bane na daiga na zuba masu abincin ai kuma zasu dawo har yarinyar na nema tayi min rashin kunya haka ?
To kiyi hakkuri ki daina kukan nan ni zan dauki matakin hakan da kaina don ko zan hanasu shigowa part din nan ga baki daya.
No ka barsu idan kayi magana tsanata zasuyi ga baki daya kaga kuma hakan ba zai min dadi ba don Allah ka kyalesu kawai nima ba zan kara kula haka.
Ya zauna yai shiru ya dade zaune a hakan ba tare da yai magana ba sai zuwa can yace kiyi hakuri don Allah nasan ki da hakkuri ki kara har zuwa lokacin da Allah zai bamu namu wurin mu tashi daga nan din insha Allahu.
Ba komai nace na juya nayi shiru kowan mu yana tunane kafin a kirani a wayata na duba ummah ce don yanayin muryata naki dauka.
Ya kalleni yace waye ke kira ba zaki daga wayan ba ki amsawa maishi ummah ce na bashi amsa yace ki dauka mana sai hawaye ya zubo min na kifa kaina a filo ina kuka ganin hakan shi ya daga wayan ya dauka.
Tare da sallama yace ummah ina kwana ta amsa mai yake fadi cikin ladabi wallahi ummah gata kwance bata jin dasin jikintane tayi barci.
Allah ya sauwa ummah din ta fada tare da fadin dama kannen kune suke son a kawosu wurin ku tunda basu da lafiya a bari sai wani jikon ya aida an barsu sunzo ummah tunda gani.
Tace su bari wani jikon sazo yau dai kan suyi hakuri kuma takardun ta suna nan kaf na hada mata a wuri daya zansa Tani tazo mata dasu anjima ta duba jikin nata yayi mata godiya ta kashe wayan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[28/03 11:59 AM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣3️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Duk wata mace data shiga dakin ta tana fatan ta zauna lafiya da kowa da zata sama a sabon wurin da zata samu kanta don bata fatan ta samu matsalan rayuwa a lokacin.
Nima hakanne ya faru dani don dai sam ban taba kawo wanan a raina cewa zan samu irin matsalan nan dana fara fuskanta a yanzu tun ba a kai ko ina ba.
Na gama girkin rana ban daddara ba na kara zuba masu wanan karon ma daidaicin kula babba na na farkon a cikin saiti na zuba masu miya kuma na cika kulan aka kai.
Saidai ba,a dawo da kayan ba har zuwa yamma banda niyar sake dora girki don ya fada min da zai fita sai yamma zai dawo don an kawo masu kaya ana saukewa ranan.
Don haka baici wanda na dora din ba sai na aje muci da rana saiko yamma don ya dawo bayan sallah ishe ina cikin part dina sai yan bakin da nakeyi masu zuwa ganin amarya da kuma yan gulma kamar dai yadda akeyiwa amarya idan an kaita sabo sabo da wayanda ta sani da wanda bata sani ba.
Wanan ya debe min kewa har lokacin daya dawo din yana shigowa part din mu ya nufo sam cikin gidan basu san dawowan shi ba lokacin ina zaune kanwarshi ta shigo tana fadin.
Ance in taho in dauki abincin muna dare kafin na kaiga mata bayanin dalilin rashin girkin darena sai naji ya bata amsa daga kofan bedroom din mu yana fadin.
Ku baku girka bane kice na bata dokan kada ta kara saka abinci a cikin gida iya namu kawai zata girka nan ba tsayawa yarinyar da bam san sunnan ta ba har lokacin ta juya sudu sudu ta tafi bata tsaya min rashin kunya ba.
Ya juya ya koma ciki dama dagashi sai tawul a jikin shi yana tsane ruwan kanshi lokacin da dan wani karamin tawul a hannunshi ya fito bata amsa lokacin.
Ya gama ya fito falo ya sameni zaune gashi ba wuta sai fama fitar nake da maficin roba a hannuna O lord rashin wutan nan ya dameni wallahi nasan baki saba dashi ba so nake na samu dan kudi zuwa jibi in sayo muña generator a dinga kunnawa koda rana idan sun dauke wuta.
Ka barshi ai ba komai na fada ya kai zaune a gefena har ina jiyo kamshin mandaya shafa da turaren shi a hancina.
Yace aiba ke kikace na saya maki ba ninaga hakan ya kamata zan saya din insha Allah tona gode na fada ya dan dago yana mamakin saurin godiyana hakan gareshi.
Ga abincin can fa don nasan bakaci komai ba ya dan kai kanshi baya saman makarin kujera ya jikina yana fadin nasan Monday zaki fara fita school.
Don hakane nake son naji yadda zamuyi kafin na wuce komai adaidai zan samo maki na dinga biyan shi yana kaiki tunda an karbe motan ki a hannun ki.
Gaskiya ba zan boye maki ba karban motan nan yana daya daga cikin abinda ya bata min rai sosai don saboda ni aka karbe motan a hannunki kingako hakan bazai min dadi ba.
Idan na tuna nakan ji kamar ace ni din wani mai haline a yanzu da zan saya maki motar da duk garin nan babu mai ita zahra amma muyi addua ko nan gaba Allah yai muna falalan hakan.
Na dan zauda daga zaunen ina fadin kada ka damu da wanan wani hani ga bawa baiwa ga ubangijin shi ni sam hakan bai dameni ba dama ba fita nake da motar ba iyaka school ne dashi don haka kuma aka saya min shi dama.
Kiyi hakkuri zahra nasan nina ja maki duk wata tsana a wurin Abba duk abinda sukai maki duk saboda haduwana dakene hakan ya faru.
Ban dauki hakan da komai a zuciyana idan na runa da nasihan da ummah tayi min akan abinda ya faru din don duk saboda a musguna matane akai min hakan ita kuma ta nema min albarka a dakina fakat.
Naga yayi shiru kamar mai tunane kafin ya zabura ya mike kamar an tsikareshi yana fadin subbahanallahi na manta shaf da batun dabbobin nan nasan kuma ba kula min dasu wa tan nan zasuyi ba sai aukin abasu suciwa bakin su.
Nan dai ya fita ya barni a wurin ya jima a wajwn kafin naji ya shigo yana rufe kofan part din daga nan ya zauna yaci abinci ya shigo dakin lokacin har na sauya kayan jikina zuwa na barci duk da zafi ya addabi rayuwana sai faman juyi da nakeyi saman gadon.
Shiyasa na damu wallahi don nasan cewa zaki wahala da zafin nan tunda baki sababa ya fada yana tsaye yana kallona daga inda yake tsaye ni kuma ina kwance.
Bandaki ya nufa ya kara gyara jikin shi har brushe yayi a lokacin a nan dai na fahinci yana da tsabatan shi iya gwargwado shima ba wai idan zai fita bane kawai yake tsab.
Yana gama shirin shi ya nufo gado ni lokaci har nayi barci don dan aikin da yanzun nakeyi ban saba yi a gida yakesa ina saurin gajiya yanzu sosai.
A cikin dan barcin daya daukeni din naji harshen shi cikin kunnuwa abind yasani falkawa a zabure ke nan da sauri hankalina a tashe don a tsorace nake kwana a gidan nan balle akuyan nan nasu idan tayi kuka nakan jishi har cikin raina.
Sannu a hankali yake bin ko ina najiki da sallon irin na maza tun ban kula da hakan ba na fara dan yunkurin ina nisawa har yakai ga gangara ya cinwa manufarshi a kaina aka zama daya a ranan bai barni ba saida ya mayar dani cikakar mace.
Yadai sha raki don shima yasan za a rina don ko kallo daya zakai min kasan ni din agidan hutu na fito don nidai bawai wani jikine dani ba.
Farace sol din nan son farin yasani tsakiya ta uwa ta uba haka kuma ni din ba gajera bace ban da kuma mugun tsawo saidai ina da tsayi madaidaici da akeson mace ta kasance.
Banda jiki mai yawa yanayi a daidai yake a fuskama na debo gidan mu sosai amma kuma na biyo ummah a wurin hanci da dan tsayin fuska shi ya dan bambamtani da sauran yan uwana don ina da zubin ummah wanda kuma shine ya kara haddasa min kiyayya gun mama.
Don yawan cewa da Abba keyi ke kan kin kwaso suffan uwarki ba ki tsaya a gida ba kawai ta kuma lura da yana ji dani sosai saidai a cewan ta son da yakewa ummah ne yake min ya fake ga sunan mahaifiyar shi.
Ranan dai Ahmed bai barni ba son sai daya cire min kunya a tsaknin mu don tare muka shiga bayi dashi mukai wanka muka fito ya gyara muna shimfida muka kwanta yana rungume dani a jikin shi.
Sai asuba muka tashi na dauka daya fito zai fita zuwa sallah kamar yadda ya saba saidana fito bayi na sameshi a zaune yake fadin ke nake jira muyi sallah don yau a gida zanyi .
Da mamaki na kalleshi cikin dauriya yace yes ba inda zan tafi yau ina gidan nan don zanyi jiyar matatace ayau tunda nayi laifi.
Dan hararan shi nayi na turo baki na nufi wardrobe na dauko hijjab dina kafin na juyo ya tayar da nafila nima shina shirya na fara gabatarwa
Muna zaune muna addua mukaji anyi kiran sallah muka tayar da sallah a baiyanai yake addua yana muna fatan Allah ya zaunan damu lafiya.
Allah ya bashi abinda zai kula da rayuwan mu Allah ya bamu zuria masu albarka Allah yasa mu gama da iyayyenmu da duniya lafiya.
Ya shafa nima dake zaune bayan shi na shafa muka mike a daidai lokacin mukaji dukan kofa anzo tayar damu sallah asuba din.
Ji nayi kawai ya kamani yana fadin koma ki kwanta kada kiyi maganan hakan jna jinsu a inda nake kwance din maishi ta dan jima tana dukan kofa lafin na daina jin hakan.
Barci sosai mukayi zazzafi da taunan jikine ya tayar dani daga nauyayyan barcin dana samu a lokacin hakan ya jawo min kaduwa da har jikina ya mannu da nasa .
Can cikin barci yake jin yadda nake kaduwa ya falka salati ya fara da dan jijigani yana kiran sunana na asali da zahra meke faruwa meya sameki subbahanallahi.
Ina ke maki ciwone ki tashi muje asibiti na samu na bude idona da kyar na sauke a kashi ya kwance yai min rumfa da kirjinshi yake tambayana cikin dan rudewa.
Ka bani bag dina akwai maganina aciki na fada a galabaice ya mike da sauri ya dauko jakkar yana miko min na tashi da kyar na fara lalube na dauko maganin shi kuma ya mike ya dauko ruwan ya bare mun maganin na hade .
Maganin kawai kai kasan masu tsadane ba irin maganin nan na banza bane da akesha anyhow na hade na koma na kwanta naci gaba da kaduwana.
Dama ga raki sai na kara narke a wurin sai zuwa wani lokaci na fara samun relief a rayuwana barci ya daukeni ganin nayi barcine yasashi mikewa daga gadon ya sauka.
Bandaki ya dan shiga ya fito ya fice zuwa wurin iyayyenshi donsu gaisa ya samesu a waje zaune da alama rayukan su a bace yake ko kuma suna wani magana mai muhinmanci a lokaci.
Sallaman da yayine Dije ta karba mashi da sakin fuska ya nufi wajen iyayyen nasa dake zaune har lokacin a cikin yanayin daya samesu din.
Har kasa ya duka ya gaidasu suka amsa mai ya dago zai mike mahaifiyar shi Rashida take fadin ka manta yau uwarka zata koma Anka na ka shige daki kaki fitowa ?
Bakin fitowa nayi ba inna ina sashen mu matana bata da lafiya da sauri suka kara kalloshi tare da tambayan halan missameta ?
Zazzabina ta kwana dashi zazzabi shin kwana uku da aure ace amarya ta fara zazzabi ko dai sai kuma tayi shiru.
Har ya daga ya kallosu yana fadin ciwon daga darene zuwa safiyan nan zazzabin ya kamata kuma duk ni na jawo matashiya.
Saboda ya fitar da zargin da yaga suna son dora min ne don ya fahinci me suke nufi da hakan da suka fada suna kokarin zarga min abinda ba shiba yasa ya rufe ido shima ya basu amsa a funkaice .
Yau Allah ya gwada min da mara kunya Amadi wai kanka daya kuwa duk kabi ka sauya lokaci guda haka kan mace ?.
Shin talauci hakana don dai ka dauko wagga diyan kaka kokarin canza dabi,unka da muka sanka dashi sai kokarin nuna ta fimu gareka kai.
Dije ya nufa yana gaida ita bata samu amsawa ba sai tambayanshi takeyi mi samu yar mutane Amadi ?
A, a Dije rashin lafiyan alherina kesan yarinyata karama dole taga canji a yanzu ai magani nika son hita in tambayo ko mi aka basuwa ga macen da ta fara sanin haka ?
Kai yau Allah ya gwada min da sagartace ta fada tana mikewa tsaye don fahintar abinda yake nufi ya faru dani din lokacin.
Tare suka shiga dakin da ita tana gaba yana binta baya a hankali zuwa ciki ina kwance takure yadda ya barni din suka shigo .
Nan dai ta fada mai yan dabarbaron da zai min kafin in tashi ya sayo kaji dakwale an gyara min da kayan yaji sai kamshi ke tashi gashi kasala da samun saukan zazzabin ya hanani tashi ina ta sharar bacina sosai.
Shiko yana zaune dakin yaki fita duk a dakin yai sallah sai falkawa nayi wajajen karfe uku na samu hanne daya kira tazo harta gyara min dakin nawa.
[28/03 11:59 AM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
5️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Sannu a hankali wani irin shakuwa da sabo yake shiga tsakanin mu wanda hakan ya kara kwantar min da hankali a gidan matsalata dayane zuwa biyu shine irin matsalan dake tsakanina da uwar Ahmed da kannen sa har ma dai ita karamar tafi shiga min ido sosai.
Don dayan ba zance ga wani matsalan daya taba hadani da ita ba saidai kawai ba sakin fuskane itama daga wajen ta kamar yadda uwar da yar uwan keyi min.
Sai tsohuwar gidan ce mai sake min fuska don ina zaune zanganta a parrt dina ta shigo mu danyi hira ta kuma ta ban hakkuri na daure da yanayin dana tsunci kaina a ciki wata rana sai labari.
Nakanyi mata godiya idan ina da abu na dan bata ko nayi dafuwa in saka mata da dan yawa duk da nasan bata iya cinyewa ita daya .
Don su din na kula da sunyi fushi kan zancen abincin da master yace a daina sakawa dasu din gashi koni din bako yaushe yake bari inyi girki ba a part din mu din.
Saidai idan zai dawo ya sayo dan wani abu mu danci harda ma yan cikin gida wanan sallon kuma yasa mahaifiyar shi saka ido ga hakan da yakeyi din .
Tana fada ranan a gabana cewa wanan ai salon kashe mata dane aka dauko wai ace mace ba zata girka abinci suci ba sai an fita an sayo abin kwalan a kasuwa taci.
Da Dije taji fadan yayi yawane ta fito tana fadin kai kai Rashida baki biyo halina ba wallahi baki da godiyan ubangijo ko kadan dake watace sai ki godewa Allah daya hada danki da yarinyar nan a yanzu.
Koda yake ba abin mamaki bane don kinyi hakan a yanzu don baki san irin wahalan da muka fito a cikiba a baya har zuwa ranan da Allah ya hada dan naki da yarinyar nan abubuwa suka fara bude mashi.
Fadin hakan da tsohuwar tayi sai naji maman ta saka kuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login