Showing 141001 words to 144000 words out of 304363 words

Chapter 48 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33320

da dama da ake son mace ta kasance dashi.
Irin hakkuri da sanin darajan mutum tausayi da kuma kula da na tare da ita uwa uba ga kyau ga halita komai nata kamar ita ta zauna ta tsarawa kanta shi.
Yasan baikai matsayin da tun farko zai nuna kauna a gareta ba shiyasa ya fake da zumunta da ita da yanzu ya zame mashi alheri a rayuwan.
Yaso ace shi wanine a yanzu da saiya gyara mata wuri har yafi hakan da yayi a yanzu din ko yanzun ma zaiyi kokarim ganin ya killanceta ta yadda ba zata takura da yan gidansu ba ko saka idon tsofafin shi.
Yasan bata da hayaniya kuma ba zataso yawan surutu ba ga zuwan kannin shi da mahaifiyan shi yanzu gidan nasu ya koma masa wani iri da yawan hayaniyan da basu saba dashi ba a baya.
Allah cikin ikonshi yana fita ubangidan shi ya kirashi ya bashi gudun mawar kudi bai dawo gida ba ya shirya da maigina ya bada kudin komai da za a fara ja mashi katanga a part dinshi.
A tsare tsaren hanne ta tsara zamuyi waliman mune a gidan wan mahaifin mu baba Habu na mazon Allah kamar yadda mutane ke mashi lakani da sunan.
Ya kuma ji dadin hakan da mukayi mai don su Aisha duk tsare tsaren su zasuyi shine a gidajen kawayen mama masu fada a ji a cikin garin gusau din.
Babu wani program da suka kai gidajen ko wani dangi sai kuma hakan da mukayi din ya zama masu wani magana da yaso ya jawo muna kace nace a tsakanin mu dasu.
Inda mama keta fadan cewa ai munafunci ne irin namu yasa muka kai event din gidan baba Abu din wa zaije wanan gidan da baida tsari buki don dai bamu samu wurin yi bane muka dahewa gidanshi ai kuma dama ai can ne daidai damu.
Shiko baba habu sai jin dadin hakan yakeyi duk inda ya hadu da yan uwa sai yace kai waga diyan yar albarkata kunji wai gida zahra ta zaba zasuyi walima.
Wagga diya Allah ya rufa mata asiri duniya da lahira wadda tta nuna mu ubanantana Allah yasawa aurenta albarka yasa ta gama da duniya lahiya.
Yan uwa aka shiga fadin maganganu kowa na fadin albarkacin bakinshi a kan mu hjy Asiyace kawar mama da tazo daga Abuja tasa ayi odan abincin da za aci a wani hotel da zasuyi muna duk abincin da za aci har na taron bukin da za ayi a fannin mu.
Don haka saika dauka cewa babu wani shiri ko tanadin da akeyi a namu fanin sai gulma ya tashi ga mutane cewa ummah ta lafai bata komai tana jiran Abba yai mata komai.
Alhalin kowa yabawa kudin shagalinshi har fannin yan uwanshi saida ya basu nasu kudin da zasuyi komai nasa ba tare da wani ya matsawa wani ba har aga laifin juna.
Ta koma fadin cewa ai kowa ummah bata gaiyata ba ga bukin don tasan cewa kunya zataji kai maganganu dai marasa dadin ji gasu nan zuwa garemu mama tana sakewa gari ya dauka.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
4️⃣8️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Kai yadauki zafi kowani part na gidan mu ana sha,anin buki amma hakan bai hana a saka ido aka ummah ba don ganin abinda take gudanarwa a nata bangaren.
Don mutane da yawa suna kokarin son zuwa suba idanun su abinci don su samu abin fada gaba idan magana ya taso wurin yinshi duk da ansan tallaka zan aura amma bai hana mutane kwadayin son zuwa gidan nawa ba su ganewa idon su abinda ake fadi game da auren nawa.
Yan fammanin mahaifina sun tafi sunyi min jere da kayan da Abba yasa hjy karima ta saya min washe gari kuma kayan ummah suka iso suma aka kaimun su gidan aka jera min su sai aka fitar da nasu Abban aka mayar a dayan dakin a take part din nawa ya koma abin kallo .
Duk sunyi wanan abin ne ba tare da sanin kowa ba sai gwaggo shafa da gwaggo Ai da suka tausaya muna kan irin abinda Abba yake nuna muna a bukin.
Dawowan sune har wasu daga cikin dangi sukaji irin dukiyan da ummah ta kashe min wanda al,adan uwan kasan hausane ta fitar da duk wani tanadin a bukin auren yarta idan ya taso.
Haka mutane zasuyi ta sintiri wurin zuwa ganin daki da abinda aka kaiwa yarinya a dakinta koda kuwa zuwa nisan inane garin sai an samu wanda yaje ya gano ya dawo ya fada.
Hakan ne ya faru dani don su gwaggo na dawowa suka fara fadin hidiman da suka gani a dan gidan nawa da mutane suka raina saiga labarin abinda ummah da yan uwanta sukayi min ya karade kunnuwan mutune lokaci guda har yakai kunnen mama da hjy karima har zuwa wurin Abba din.
A gaskiya Abban yaji mamaki yadda za ace wai kudin daya bayar har ummah tafishi yimin kayan kwarai sai jikinshi yai sanyi da jin hakan kamar wanda aka tunatar da wani abu daya manta a baya.
Munyi walima gidan baffa Abubakar na mazon Allah an dauki waliman na yaku bayi da farko amma ganin yadda yan uwa da abokan arziki suka tsaya suka tsara abin da yadda akai kwaliyan titin unguwar gabaki daya da malaman da akaji an gayato sai mutane sukai ta tururuwa zuwa wurin waliman har ma da wanda ba a gaiyata ba lokacin don sauraron wa,azin.
Ga kawayen ummah sunzo da sebeniya masu kyau na rabo sai hakan ya kara daukan hankalin mutane har yaja kowa zuwa wurin waliman don komu bamu zaci hakan ba gaskiya.
Har an fara taron lokacin da mukazo tare da yar ummah wace ta tayar da ita a kaduna har Abba ya ganta ya aureta da kawar ummah da wata gwaggon su ummah din a cikon dirkekiyar motan da tazo dashi.
Nayi adon lafaya mai shegen tsada takalman kafana kwaliyansu daya da lafayan jikina hakama jakkar dana rika shima kala daya da lafayan jikin nawa.
Sam bansan cewa an gaiyato Ahmed ba wurin sai ganinsa mukayi yazo da tawagarshi nan dai aka nuna masu inda zasu zauna shi kuma suka sa muka shigo filin a tare dashi.
Anan kowa ke dage yana son yaga mijin dana aura din da ake shati fadi a kansa din babu inda za a rainawa Ahmed wurin halitta saidai a kirashi da fakiri wanda baida halin ko zarafi something dai hakan.
Wa,azi akayi akan hakkin aure daya kamata namiji ya sauke da wanda ya haukan mace itama sai kula da hakkin makwabtaka da malama ta karshe ta fadakar damu lokacin.
Inda akasa nayi karatu a cikin suratul maryam shima yayi a cikin suratul yusuf ikon Allah malamin ya fada yace kafin nazo wurin taron nan nayi ta tsuntan maganganu a cikin wani unguwa dana sauka akan auren nan.
A gaskiya ni a ganina wanan hadin shine hadi irin wanda ya dace ayi a musulnce nan dai yayi bayanin yada ya dace ya wayar dakai yaja hankalin mutane akan hakkin aure.
Kafin aka fara raba abubuwan ci dana sha da kyaututuka na ban mamaki bamu tashi ba sai gab da magariba taron ya watse kowa na sam barka ga taron.
Mun dawo mun samu masu shirin zuwa dinner suna ta shiryawa masu bada labarin walima suna bayarwa abin mamaki saiga sako daga hjy mama cewa wai ummah ta shirya da mutanenta angaiyacesu zuwa wurin dinner su Aisha.
Tadai amsa amma ba wanda ya leka a namu bangaren saida safe muke jin cewa wai walimana yafi dinner nasu kyau sosai don ba a tsara abin yadda ya dace ba karshema fadane ya watse taron da yan gidan angon Aisha da tawagan mama a wurin.
Har mazan na fadin cewa sun fasa tunda mutanen banzane su inbashi da ya mayar da kanshi baya ba dama har Aisha macen aurene bayan kowa yasan irin watsewan su.
Shima angon yai fushi dama a buge yake ya nuna mama yace ta kwashi yarta ya fasa auren gobema barin zaiyi da safe dama ita ta matsa mai akan ya auri yarta.
Nan dai sukayiwa juna tonon asiri sosai itama da borin kunya tace ta fasa bashi yar nata mashayin banza da wofi kawai ai dama taimaka mashi tayi har ta dauki yarta ta bashi.
Zance dai har wurin maza da safe haka falon Abba ya cika da mutane kowa da kalan zancen da yake zuwa dashi itama Rukkaiya dai an samu matsala wai gidan da zai ajeta yayi masu kadan su kuma sukace idan bai masu ba sai a fasa.
Anan Abba ke jin cewa wai mijin Rukkaiya din ashe dan damfarane yana sayar da filayene a garuruwa da haka ya tara arziki yake karya dashi a gari.
Kai rikici dai gashi nan da tonon asiri kala kala kowa yazo ya fadi nasa gashi da karfe biyu za a daura auren mu ga abubuwa sun dagulewa mama sai jiki yayi sanyi a lokacin.
Dole Abba ya kira taron gagawa don samun mafita don abokan shi wasu na nisa harsun iso gusau lokacin gashi kuma rikici nata kara bulo kai.
An samu an sasanta da iyayyen angon Aisha sun yarda an daura auren bayan Abba yaje har gidan da kanshi yaji ba,asin fada nasu yaba da hakkuri kada yaji kunyan jama,an daya tara din.
Karfe biyu da rabi aka daura aure har zuwa ranan ba a kawo lefena ba abinda ni kuma mutane ke gulma a kanshi ke nan kaina wai duk talauci ne haka ya hana mutanen Ahmed su kawo min laife ?
Dangin mahaifinshi sukazo da kayan lefen nawa wurin daurin aure kamar yadda al,adansu yake sai bayan an tashi taron ne aka shigo dashi cikin gida aka gani nan gwaggo Shafa ta sake guda saida hankalin kowa ya dauku da hakan wajen.
Tana fadin Alhamdullahi aure ya dauru tsakanin Aisha da manbo Rukaiya da sha,ibu gaye Zahra uwa bada mama don sunar uwan mu taci da angonta Ahmed.
Alkawarin Allah bai tashi yau dai Allah ya nufa mun sheda wanan ranan kai ku shigo da abin arzikin nan a bajeshi tsakar gida kowa ya gani tana fadawa masu shigo da akwatinan acikin gida.
Ta sake aza wani gudan tana fadin lalai a haifi da arzikin shi yafi a mutu a barmai gado daki auri mai arzikin ga mara arzikin na shirin fidda yarmu a kunya wana kaya haka kamar matar dan gwauna fa.
Kayan sunyi kyau sosai don ba zakace kaya daga hannun mutum irin Ahmed mara gata suka fito ba saida wata yar uwa mu ta dakatar da gwaggo shafa ta daina sake magana.
Ni dai ko a idona banga kayan lefen nawa ba sai sha,anin buki da mukeyi saiga sakon mama cewa na bada key din motana inji Abba.
Wanan kuma wani irin zancene haka harda motan nata zai karbe saboda kiyayya wanan wani irin cin fuskane wai haka yayar ummahce ke wanan maganan ga gwaggo Sa,a datazo karban key din motana.
Don ita da mama aminan junane sosai a yadda naji ance itace kawar mama duk da suna da zumunci amma ta sanadin ta Abba ya auri mama kuma har yanzu suna tare duk da kowa ya girma.
No ku basu don Allah Allah ya horewa mijinta wata rana ya saya mata motan da kudin shi badai za a karbi rayuwanta ba ai iya mota zancen zai tsaya ai.
Motan da banje gidan Ahmed dashi ba ke nan kuma su ummah basu tayar da zancen ga kowa ba suka bada key din salin alin zancen ya wuce duk da hakan ya tabawa ummah zuciya sosai.
Motar yan uwan ummah dana kawayenta akai amfani dashi abindai kawai in fada a dunkule don zakace nidin ko yar rikoce a gidan ko wata yar rikon tafini samun gata a lokacin .
Don abinda mamaki yadda aka nuna min lokacin ko an kawo tsegumi wanan yayan ummah din ita ke daga hannu tace a kyalesu su fatansu Allah yaiwa aurena albarka.
Don hakane suka sani zama a sakin tare dasu wai gudun wani ya hure min kunne a can dakina nazo na tubure masu daga baya.
Gashi duk da banyi gaiyata ba amm hannatu ta gaiyato yan course mate din mu dama wasu da muke shiri dasu a school din namu dakin nawa ya cika fam da kawayen mu.
Magariban farko gwagwanin mu suka shigo dakin waina fito za a kaimu wurin Abba daga can za a wuce damu gidan hjyn su Abba sai gidajen mu.
Tunda na sallame sallah nake daman kuka don irin nasihan da ake min a dakin da jan hankalina na tsaya na rike aurena da hannu biyu don shirun da mukayi nida ummah harsu yana sakasu wasi wasin din mu.
Nikan kuka nake da daya da biyu har zuwa uku sau uku amma nabar komai a cikin zuciyana ina addua ashe banji abin kuka bama tukun sai lokacin da mukaje sallaman Abban mu.
Inda ya kara jaddada muna musanman ni kamar yadda yace don a gareni yake hango matsalan farko a gidan shi na ba yaji ba kuma zuwa gida neman wani abu don ya riga ya gama damu ko a cewan shi.
Kai har dai yar ummah data biyomu zuwa falon tare da babban aminiyar ummah din suka kai ga tankawa a lokacin inda tace kamar yadda akewa kowa fatan zama lafiya a dakin shi insha Allahu ko ita haka zata zauna a dakin ta lafiya da yardan ubangiji.
In har ana gason hakkuri a duniya ai Zahara ta gaji hakkuri a wurin uwarta meya rage na hakkuri yanzun wanda bata sani ba kuma ai saidai wanda ba,ayiba a duniyan nan.
Kowa yayi shiru sai cewan da gwaggon mu daya tayi ku tashi mu karasa gidan hjy kuyi mata sallama daga can zamu wuce daga can baya wata ke fadin su angwanan zahra sun kawo motan daukan amaryan sune.
Aminiyar ummah hjy kubura ta bude baki tace ko basu kawo ba mota ba matsala bane ai shima angon yanzu ya zama dan mu da akwai motoci sai mu kaita fatan mu dai Allah ya basu zaman lafiya aka amsa da amin.
Haka suka rikomu zuwa waje muka taka da kafa zuwa gidan hjy din nan ma irama tayi muna nata hudu ban mai kama da jurwaye tare da fatan lafiya gare mu aka kwasa akafito wajen gidan .
Ina jin mommy kubura na waya cewa sauran su fito idan an shirya motocin tafiya ba afi yan mintuna ba sai gasu gidan sun samemu da motoci hudu muka shiga gwaggo shafa tana cikin mu tare da wasu yan uwa da basu bamu baya ba marasa tsoro ke nan su.
Tunda muka shiga motan muna tafe suna fada min naja Tawakhaltu illallah lahaula wallakuwatu ina billahi aliyal azeem sau uku sai na dinga jan, Hasbunallahu wani imal wakil har zuwa shigan mu gidan shi na dinga ja a bakina ina hawaye.
Ba zan iya fadan ko hawayen me nake sakewa ba har wanan lokacin asalima ba bace ina cikin hayacina ba gaskiya don sai yadda aka juyani kawai nasan dai ina dan picking din wasu abubuwa dake gudana dani lokacin.
Jin mota ya tsaya lokaci guda ga guda da ihun yaran yana tashi lokaci guda yasa na lumshe idanuwana a hankali naji mommy kubura dake gefena zaune ta dan kwanto min tana fadin yawaita karfin zikirinki a wanan lokacin ki fara da ya Rabbi ya rabil ya rabil alamin ya Allah ina rokonka a ckkin kyawawan sunan ka daka baiyana suga bayin ka ya Allah ka suturani a dakin mijina har Abada ka kawar da duk wani shedan da shedaniya a tsakanin , , , , , , ,
Nasan ina maimaita abinda mommy din tace in fada daga haka na rikice masu har zuwa cikin dakin nawa saisune suka san halin da nake ciki kan gadon dakin ta kaini ta zaunar dani da bissimillah tare da adduan koran shedan gareni.
Anyi adduoi daya dace ayi a lokacin kafin manya su fara watsewa bisa umurnin mommy kubura dama suna sauri su koma suje kai sauran amaren gidajen su haka yasa bata samu wani matsalaba wurin sallaman mutanen.
Muka rage daga mu sai su su hudu sai yan matan dake falo su hannatu sai zuwa can na fara gane inda nake zaune duk da ban sheda a dakin da nake zaune ba lokacin.
Kai gaskiya idan Allah ya hadaka da mutanen arziki a rayuwanka ka godewa Allah don sai ka daukama sunfi wani dan uwanka na jini wani lokacin.
Don ko ni naga hakan a wurin uwata don ko yan uwa da abokai sun nuna mata gata sun fitar da ita kunyan kishiyoyi dana mutanen gari tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login