Showing 117001 words to 120000 words out of 304363 words

Chapter 40 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33336

gashi ya dawo gida kwantsam ba zato ba tsamanin hakan .
Acewar mutane shidin ya gaji arziki ta uwa ta uba duk ko wani bangare nasa suna da manyan garakan shanu a nahiyar nan .
Yanzun ko ya hada da ilimin zamani sai abin nasa ya kara bunkasa sosai don yanzun ma a Abuja yake da zama saidai yana yawan zuwa gida sosai idan yazo kuma yanawa mutane alheri sosai shiyasa kaga mutane suna ta tururuwa a gidan shi yanzu.
Lalaima wanan mutumin ya riku a kasa yadda danbayarin nan yake fadin dukiyan shi in dai ba abin fulani ba ace dukiya a daji suke aida yanzu sunan shi ya karba kasa ke nan .
Amma ba a gane hakan garesu don dukiyan a dawa suke sai wanda ya ganewa idon shi zai gano hakan su dai a kirga yawan shanun mutum daya tara ace wani yana da Nagge dari kaza ko wani ya tara nagge kaza shine alfaharinsu ba yawan kudin bane ya damesu .
Shiyasa hukuma sarakuna ko yan doka suke son yin sharia da bafalatin daji da mafi yawan yaransu na yanzu ke dauko masu magana zakaga sai an ware wasu garke an sayar kafin sharia ya mutu.
Wanda sam ba a san bafilatanin da da daukan magana ba haka don ko yaushe su a daji aka sansu da zama sai lalura ke kawosu cikingari a da can baya
Haka yan asibiti sunfi son bafilatanin daji ya kawo masu mara lafiya yanzu ne koda flagyl zasu bashi zasuce dashi dubu goma bajin zafin hakan zai fidda ya bayarne.
Fulani akwai arziki a garesu sosai saidai abin sirine a gareau ba kowa ke gane hakan ba garesu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣9️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Kusan sau uku ana zuwa nemana a gidan ban fita ba bansan ya akayi wani cikin samarin ya samu layin wayata ba ya dameni da kira karshe kashe wayan nayi gaba daya.
Gwaggo Ai ce ke fadin wai baki son muyi siriki a kano ne kome ya hanaki fita indai don mune ki tashi ki fita abinki tunda mu ba jikaki zamuyi musha ba a gida.
Sai gwaggo shafa kece mata indai mamace ai kyayi kya gaji ki bari don ba fita zatayi ba nina taba ganin yarinya irin haka da bata kula kowa a gida.
Sai matar baffan mu guda naji tace a,a wallahi wace indai mamace tana da mabidin ta hala kin manta fadan da akayi dakin hjy ne da uwarta da hjy maimuna.
Ai maganan har gaban su Alh yakai kuma an kira saurayin Allah yace baiji dadin yadda officer yayi mashi ba don yace yaci zarafin yaron sosai a ranan kuma nasan an zugashine tunda ba halinshina ba hakan ?
Ke yaushe ankayi haka bamu da labari gwaggo shafa ta fada cikin mamaki matar baffa din tace ai gata nan ku tambayeta ku jiya ai tasan komai da ankayi.
Gwaggo shafa din ta dago tana fadin wai haka ankayi maamah murmushi kawai na sake a fuskana ta gyara zama tana fadin wallahi sam ban san anyi wagga maganan ba.
Keko ina zaki sani maganan suta ta maza ai sunkayi tsakanin komu mujiya ran Alh gidan mune da ya baci shina har munka sani yake hwada muna.
Shi yaron dan wanena a cikin gusau gwaggo shafa ta tambaya to ai shina yakawo maganan mamanta fada taci gaba da fadin .
Wai ance yaron baida usuli, ke ke ke kibar wanga zance don Allah ?
Gwaggo shafa ta fada da sauri tace badai fadin mutane na ba yan hana ruwa gudu .
Sai gwaggo shafan ta juyo inda nake tana fadin keko maamah ashe yaya yafi gaskiya a,a kika jawo muna mara asali mu hada iri dashiya.
Ke wah hwada maki walle da ubane hwa hwadin mutanena kawai in baka da komai yanzu duk wani sherin duniya daukowa akai a dagwara makashiya.
Ance dai tun yana goye a baya ubanai yai tahiyatai kasan su yabarshi bai dawo garai ba ,har yau shina fa matsalan yaron dai da mutane ka hwadi .
Amma walle da ubanai ba shege bane ke dan gidan malam ladan na kwanan maigemu labil labil mana ai kesan yarshi Rukkaiya dai da aka hwadin boko tta aura dauri ya gudu ya barta da goyon da nai ?
To shina hwa aka magana nai yanzu ko ance shi office ya hwa sosai don wadda Alh ka hwadi ko saurarenai bayi ba a ranan ya kira yaron ya hwada mai ko sabulun wanka maamah bai mai jari.
Jin hakan yasa na dago kai da sauri na kalli mataAbbane ah nawa dake bayani wani iri naji har cikin raina don kalamin bai mun dadi ba quit oright nasan cewa Ahmed dai dan tallakawane.
Amma kuma baisan mahaifin shi ba ake nufi ko me gashi muyi waya dashi last yace min yana hanya zai tafi wajen mahaifin shi.
Ko dai mama ta zuga Abbane don kawai ta bakanta min rai idan ko hakane har sheri tayiwa Ahmed din bazan taba rabuwa dashi ba a rayuwana kuwa sai naji gwaggo shafa na fadin.
To in Allah yayi mijintana da ya hwadi mai wanga magana haka a a zaiyi da kunyane gaba baka sone da yarka ka sallameshi kawai yayi tahiyane amma ka hwada ma mutum irin wagga magana haka babu dadin ji.
Tsam na mike na bar wurin don ba zan iya ci gaba da sauraren su ba a lokacin dakin mahaifiyar mommy da muke kwana na nufa babu kowa a dakin don haka na samu wuri na kwanta abina ina tunanen mafita a garemu.
Gashi duk kwanakin nan idan na kira Ahmed din wayan shi baya shiga har hakan ya fara bani tsoro a raina don bansan halinda ake ciki ba dashi.
Sai can zuwa dare maryam ta shigo dakin ta sameni kwance take fadin au ashe kina nan nayi zaton kina can gun yan uwanki ai yasa na zauna dakin su mommy muna hira.
Kafin in bata amsa mommy ta fado dakin tana fadin Zahra ashe baki fita wurin yaron nan ba kika shanya shi haka a waje sanyi na dukan shi.
Yaron nan fa dan gidan manyan mutane ne bai fito gidan banza ba wallahi da nasan tun dazun baki fita wajen shiba da nazo na fita dake da kaina yarinya arziki na kiranki kin tsaya tsiya kada kiwa kanki tsiya wallahi kowa nason yazo wurinta kaf taron nan amma ya ganki yace ke yake so.
Mommy nifa ko gida bana kula samari kin sani barshi kawai ya wuce eh bakya kula wasu dai kinfi son irin samarin ki da kike tarawa yan karya masu tsamin hammata.
Wani kallo na dago nayi mata na mamakine kona tsana ban sandai zan iya mata irin kallon ba tana ganin haka ta juya ta fita daga dakin.
Hayene suka biyo fuskana lokaci guda ban kara magana ba na koma na kwanta sai maryamce ke fadin aina fada maki wallahi mommy karima bata da dadi ko kadan.
Taso tayi amfani dakene ta samu kudi don ita kudi baya isanta yadda kike da kyau din nan yasa ta daukoki tazo taci kasuwanta a nan dake .
Haka takeyi dasu small mum tana amsan kudin samari a wurinsu tana ganin kamar ba a gane me sukeyi ba dasu.
Har tayi ta kare zancenta ban taka mata ba sai gyara kwanciyana dana ina danasani yafi dubu a zuciyana na biyota da nayi har taso ta gurbata min rayuwa naki shine ta aza min sherin kazafi kuma.
Bin ko ina na gidan yakeyi da kallo yana mamakin ikon Allah yadda aka narka kudi akai aiki haka aka zuba a kasa kuma wai maishi bai faye zama a cikin gidan ba akace.
Bai kai ga kare mamakin shi ba yaji masu tsaron kofan na mashi sannu da zuwa suna kallon junan su tare da fadin ka shiga daga ciki yallabai sannu da zuwa.
Suna wani bashi girma suna kus kus a tsakanin su amsawa yayi ya kama hanya kamar zai shiga dan bayaro ya dan jawoshi yana fadin kai baka da hankaline malam kasan inda zaka shiga kuwa ?
Nan fa ba gidan wasan yara bane idan kana karban dan abinda zai bayarne kaje mubi layin can har layi yazo garemu mu karba mu wuce zaifi muna sauki kada ka jawo a lankada muna dukan tsiya a wurin nan yanzu.
Zan karba ko dan naga Alh da idona amma ba don nayi amfani da kudin shi ba ya fada can baya kadan ya tsaya duk wanda ya ganshi a layin sai ya danja baya ya bashi wuri.
Har wa yanda ke kula da layin suka farga da hakan suna duban shi sai da suka kadu kallon tsab sukai mashi suka koma gefe suna magana kafin dayan yazo ya nuna shi yana fadin zo ka shiga cikin tsarguwa da ganin shi.
Ya dan gyara rigan shi da kyau ya kutsa kai cikin falon da ake shiga din wani sanyi ya daki fuskanshi ga kamshi dake shiga mai hanci wani farin mutum ya gani a zaune wanda baiyi tsammanin haka zai ganshi ba.
Yana zaune saman kujera ta alfarma ya baza babban riga a jikinshi tana maiko sai kamshi ke tashi ga tulin kudi yan dubu dubu dari biyar biyar da dari bibiyu ko wani layin su daban .
Yana waya a lokacin Ahmed din ya tsuguna a gaban shi har saida ya kare wayan ya juyo yana fadin ehe saiwa kuma ?
Sukai arba da juna ya kalleshi tsab kamar yadda shima shi yake kallo kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya mika hannu wurin yan dari biyar biyar ya dauko dubu ukku ya miko mashi.
Ya mika mashi kai ya girgiza mashi yace bashi nazo karba ba nazone na gaida ka in fadama cewa yan zamfara daka bari suna gaida kai sun gode.
Yana fadin hakan ya mike ya fita sai kallon mamaki ya barshi dashi zaune wanda suke tare yace ka sanshine Alh ?
Kira min shi kawai ya iya fada ya mike da sauri suka fito saidai babu Ahmed din babu labarin shi don yana fita ya ja dan bayaro suka haye mashin zuwa unguwarsu.
Tambayan duniyan nan dan bayaro yayi mai sai cewa yayi a karshe yace kudin sun kare inyi hakkuri yace kai amma dai bamu da rabo wallahi.
Ai yau da muma mun dangwali arziki munci zakkanshi don ban taba yin dace da yazo ba yana rabon kudi sai yau amma zan kama zagaye in gani ko zan dace watarana nima in samu.
Suna zuwa dan bayaro yashiga mashi godiya shima gode mai yayi ya shige gida kai tsaye ya samu inna shattu tana sharan tsakar gidan su ya gaida ita yana kokarin karban tsintsiyan a hannunta.
Tace ya barshi shi namiji ina shi ina shara kuma ta kara da fadin hankalin mallam ya tashi yanzu ya fita ya dubaka yaga kun dafe baku dawo ba.
Ga abinci can a rufe ka zauna kaci yace zanci inna amma saina gama shara zan zauna inci dole ta sake mai tsintsiyar ya karba ya fara sharan gidan .
A haka malam musa ya dawo ya sameshi da mamaki ya karaso yana salati yace jam jam jam shattu bakona kika bawa shara yana da namiji dashi.
Haram gashi nan sai Ahmed din yace nina karba a hannunta baba bata so hakan ba itama au ce nake dai ita ta nemi ka taimaketa ai kasan halinsu na mata.
Tas ya share gidan saida sukai mamakin hakan ya gama kuma ya koma ya gyaro bandaki kafin su farga ya fara cika randar ruwan su na gidan.
Saijin karan zuba ruwa sukaji don duk kwanakin shike tashi da safe ya cika masu ko ina nagida da ruwa malam musa yayi fadan hakan amma ya roko malam musa din da ya barshi ya diba don Allah.
Bai samu kanshi ba sai bayan sallah isha,i daya dawo lokacin ya zauna ya dan tsankwari abinci kadan don bai iya cin komai a lokacin saboda yadda yake jin zuciyarshi na mashi zafi.
Dan aikin dole yayi ranan da gaiya don ji yake zuciyar shi na shirin buga mashi zazzabi ne mai kada mutum ya buga mai nan take ya fara rawan sanyi sai amai kuma ya biyo baya.
Hankalin mutanen gidan ya tashi sosai da ganin hakan malam musa ka fada yakewa Shattu cewa aikin da yayi ne yaja mashi hakan.
Da kyat ya bude baki yace ai da zazzabin ya kwana zuwa safene yaji saukin shi shine yanzu kuma ya tashi mai fita maigidan yayi ya dan jima sai gashi ya dawo da ledan magani a hannun shi.
Ya dan sha ya samu ya kwanta sai barci mai nauyi ya daukeshi bai kara falkawa ba ganin haka suka fice suka barshi ya samu barcin lokacin.
Nan hankalin kowa dake wurin ya tashi ganin yadda hankalin maigidan nasu ya tashi lokaci daya haka gashi duk wanda aka tambaya ina yaga yaron nan yabi sai yace dashi ai bai ganshi ba.
Sai wani mutum dayane yace yaga sun bi nan da sauri sun tafi amma bai kula da hanyar da suka bi gaskiya.
Kudin da baici gaba da rabo ba ke nan ya juya ya shiga gida a rikice ba tare da yayiwa kowa bayanin abinda ya faru ba.
Dakin shi ya shige yasa key bai sake fitowa ba donko matanshi basu ganshi ba a ranan sai washe gari yadda yaga dare haka yaga da safiya don ya kasa barci yana son tuno abubuwa da dama a rayuwan shi game da yaron nan amma ya kasa hakan.
Daga cikin makarraban shine aka samu wanda ya tseguntawa matanshi abinda ya faru hankalin ta farkon ne ya tashi sosai don tunawa da abinda bokatan ya fada mata cewa.
Kada ta yarda suyi ido biyu da yaron don duk ranan dayayi arba da wanan yaron asirin kwalban daya bata din zai kare .
Ba komai bane kuma sai adana duk wani tunanen shi kan yaron daya fada yana dashi a can inda ya fara zama din daya bata.
Sai gashi yau duk da ba a tabbatar ba an fada mata wani mai kama dashi yazo gidan har yaga Alh din inda hankalinta ya dan kwanta mai bata labarin ya fada mata cewa ai sam basu da kama ko ina da yaron na jini.
Hakan yasa ta kwantar da hankalinta tayi barcin ta harda nasari washe gari kuma tana tashi ta shige zuwa yola wurin buki dama shi suka shigo yi.
Don haka bata dauki wanan da cewa komai bane ta dauka gajiyane ya kama mijin nasu sai bayan tafiyantane balli ya tashi don Alh ya tubure kan cewa lalai danshine ya gani a jiya yazo gidan nan.
Abu tun matarshi ta biyu tana daukan hakan wasa har yakai ta bugawa yan uwanshi waya tana sheda mashi suzo babu lafiya fa don bata gane kan mijin nasu ba yau.
Bayan sunzo ne sai gashi ya fito falon suka gaisa nan suke tambayan shi meke farune wai ya dan murmusa yana gyara zama tare da fadin.
Yaya sale nayi sakaci da yawa sosai don tun dawowana garin nan na fada maku nayi aure a can har matar ta haihu dani mun haifi da daya.
Amma kuma sai wanan zancen ya fita min rai ga baki daya don ban taba zancen yaron nan ba daga baya ma sai na manta dashi sam ga baki daya a zuciyana.
To jiya yaron nan ya biyoni suna jin hakan suka fara kallon junan su kamar suna zargin ya tabune don dama zargin da sukan masa ke nan wani lokaci tunda ya taba barin gida da girman shi.
Yace kwarai don yanzun haka zancen nan da nake maku yaron nan yana cikin garin nan tare damu sai dai bansam a ina yake da zama ba.
Don jiya yazo nan wurin amsan taimako tabbas akwai kama sosai dani dashi dayasa na danji faduwan gaba lokacin dana kalleshi .
Amma kuma abinda ya fada min kafin ya fita shine ya tabbatar min da cewa shi din ne dai ya biyoni garin nan don cewa yayi.
Sai kuma yai shiru ya dukar da kanshi kasa kamar yana tunane ko takaicin abinda zai fada jin shirun yayi yawa daya daga cikin su yace muna jin ka .
Dago kai yayi da niyar magana amma kuma hawayen da suka zobo mashine suka hanashi magana suma jikin sune ya mutu don ganin halin da dan uwan nasu ya shiga ciki a lokacin sun san ba karamin zance bane wanan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
4️⃣0️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login