Showing 192001 words to 195000 words out of 304363 words

Chapter 65 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33364

Sai daya da wani abu mutanen gidan suka fara dawowa salimace ta farko sai uwarta data dawo a gajiye lokacin sai bayan ta hutane Asabe ke fada mata ai maigidan ma ya dawo lokacin.
Haka kawai taji lokaci guda gabanta ya fadi akaro na farko da ta taba jin hakan nan a zuciyarta game dashi ke nan ranan haka ta daure ta mike zuwa wajenshi saidai baya nan yana masallaci a lokacin.
Bai fito ba sai bayan isowan matar nasa amaryan nasa data iso mota biyu ita da yarinyar datake tayarwa sai kanwata guda datake riko sai yayunta biyu da sukayo mata rakiya da tsohuwa daya da aka hadosu da ita daga gida.
Nan aka fara shiga masu da kayansu cikin gida harsai da aka kusan gamawa sanan taji labari daga bakin yarta dataga shigowansu lokacin.
Tashin hankali a sukwane ta fada dakin uwar nasu tana fadin mommy su wayene sukazo naga wasu mata na shiga da kaya wanan part din da aka gyara.
Mata da kaya kuma ta tambayi yar a cikin mamaki tace eh mummy gasu can suna shiga yanzu haka da kayansu wallahi.
Ai a su kwane take saukowa daga kan gado har tana hadawa da rarafe lokacin haka ta samu ta sauko daga matakala zuwa falo.
Ja tayi ta tsaya wuri daya jin mijin nata yana yaren fulatanci da tsohuwar yana tambayanta mutanen gida a lokacin nan take fada mai duk suna gaidashi saida daga inda hjy yabi din take tsaye ba zata iya sheda ko wacece tsohuwar ba alokacin don ko muryanta ma bata sheda ba..
Cikin mamaki take karasowa inda suke yarta Salima tana biye a bayanta who is she daddy Salima din ta tambaya daga inda take tsaye a bayab uwarta din.
Jin hakan yasa ya juyo a lokacin ya dan kallosu kafin yace gwaggonane daga Gembo daga mambila suke ita da mummy ku na can.
Wani irin faduwan gabane ya ziyarci zuciyar hjy yabi lokacin har jiri na neman dibanta zuwa kasa sai da Allah ya gyara bata kai kasan ba a lokacin wa yan nan fararen yaran fulanin suka shigo daga waje suna jan akwatinan su zuwa ciki.
Mamakine karara a fuskan hjy yabi saliman ta kara tambayan uban da cewa so she now live in Abuja with us ?
Yace of course a nan zata zauna tare damu itama da yaranta ok she is welcome ta juya zuwa cikin ya bita da kallo kafin uwar dake tsaye kamar gunki tabi bayanta a fusace itama irin ga mace ta hasala da miji a lokacin.
Bai tsaya binta kanta ba ya juya wurin tsohuwar nan suka shiga ciki suna magana dashi.
Mataimakinta ta jawo watau waya ta dannawa yarta kira a cikin tashin hankali akai sa a kira biyu ta dauka tana fadjn yanzu naso kiranki dama sai gashi kin kira.
Naji gari ya dauka cewa kishiyar ki ta koma Abuja da zama jiya suka bar garin nan tace shina kira in fada maki yanzu.
Yanzu na gane inda barnan ya fito min yanzu na gano me min bandar kasa ashe nayi sake ina daukanta sakarai tana min kallon wawiya.
Tunda har yau Alh ya iya dawo da ita garin nan kusa damu mu zauna tare a nan da ita yanzu wasan zai fara a tsakanin mu dama ashe itace ke min saran boye ban farga da hakan ba ?
Yanzu shi meya fada maki yau din nan ya dawo da safe ko ganinsa banyi ba sai yanzun nan na ganshi a falo suna magana da salima yake fada mata a nan zasu zauna damu wai.
To kinji ki natsu don Allah kada ki yarda harta gane cewa akwai matsala a tsakanin ku yanzu ki bita da basaja ke inama ruwanki da itane wai kowa yayi harkansa kawai zaifi don ba wani shiri tsakanin ka da kishiya kowa naciki na cikine a tsakani.
Ke ni Alh ma ya ban mamaki wai yau shine harda daukan Murja ya tafi da ita Abuja yarinyar da abaya yake fadin baisan yadda zai kwanta da itabama.
Ohh ke kika saura rakiyan maza ki barshi kawai yanzu nuna masa ba komai a ranki ko zamu samu ta hakan mu koma daidai dashi inyaso daga baya sai mu san abinyi.
Anya kuwa zan iya yau nice na bude ido tare da wata mace a cikin gidan nan da sunan zamu zauna tare wai ?
Yanzu dai dole kibi sannu kamar yadda na fada maki in yaso daga baya sai muyi tunanen abinyi nan gaba muna can munata zaton ko iyayyen yaron nan nasane ke asiri ashe ga inda barna yake bamu sani ba.
Haka dai sukaita kulla tsiya a tsakaninsu har dai suka gaji suka kashe wayan suna sallama da juna akan sai ta kirata fada mata halinda ake ciki a gidan.
Da sallama a bakina na shiga gidan a waje duk na samesu Dije tana alwala su kuma suna zazaune nayi sallama tare da gaidasu daga can ban karaso ba.
Yar nan ina kika shiga haka har dare hankalin mu duk ya tashi baki dawo lokacin da kika sababa jin hakan yasa na dan dawo baya ina fadi.
Ayyah Dije wallahi naje gidan mu daga makaranta wanan yarinyar da akai suna jiyace Allah ya karbi abinsa ba dijeba kawai gaba dayansu har inna suka saka salati lokaci guda.
Inna dince ke fadin dama bata da lafiyane sai dije ke fadin gashi tana fadan ankaita asibiti ba wanda yasa rancewa ma zai ai sunan ga jiya amma uwartace ayi kawai.
Eh to uwar nada gaskiya aiko banza taiwa uwarta bara kinga da batayi dabaran hakaba da shike nan ai bata samu gudun mawar data samu a jiyan ba.
Nikan ina jin ta fara babatun ta na juya kawai zuwa kofana nasa key na bude na shiga duhu ya fara don haka na tsaya na lalubo wayata nayi amfani da haskenta na kunna wuta.
Na saka ki na bude kofan na shiga don ko,ina ina rufewa idan zan fita don da farko ban rufe part din amma yanzu dana fahinci ana min barna na fara rufewa idan zan fita din inna tayi korafin hakan ta gaji ta barni.
Jakata na wurga saman kujera na shiga uwar daka har na nufi bayi na tuna da kudin da Abba ya bani na fito na dauka nakai cikin wardrobe dina na boye.
Ruwa na watsa a jikina na dauro alwala na fito na tayar da sallah bandaga ba har akai isha na gabatar san na na mike na jawo rigata na dora sama.
Zan juya naga jakar na sake tunawa da kudin na dauko na zauna na kirga dubu darine cif a ciki wanan ne kyauta na farko da Abba yai min tun bayan aurena da Ahmed din.
Nayi mamakin hakan don a gaba yayi warning din kowa akan kada ya bani kudinshi sai gashi yau shiya bani kudin nasa da kanshi.
Dubu ashirin na zare daga ciki don na bawa mutanen gida suma su taba su lakaci arziki kamar yadda na samu nima don haka na debewa kowa biyar biyar na mike na fito da kudin a hannuna zuwa part dinsu.
Yadda na barsu a zazaune haka na dawo na samesu sai Dijece ke cikin dakinta lokacin nace to Dije sallah akeyine har yanzu shin naji tace na sallame dama yanzu nake shirin fitowa zuwa wurin ki in maki gaisuwa.
Kai ji dije mutuwar yarinyace sai kin wani binta kuma kin mata gaisuwa akanshi yarinya ai rayuwa gareta kuma jinintace ko ta fada tana fitowa daga dakin tana cin karo da kwanon da suka aje mata a kofa.
Kai masu wutan nan Allah ya shirya muna su ace tun jiya ba wuta mutane na zaune cikjn duhu da zafi haka yanzu dana kara dan dayan kafar mai dan lafiyan.
Da za a samu wani ya sayo muna mai da sai mu kara a tayar da injin din nan ko chajin waya mu samu da sauri Asmau tace indai akwai kudin kawo yanzun nan zanje gangare nasayo maki.
Nace to bari inzo a lokacin ne na mikawa Dije dubu biyar saina nufi wurin inna mai fadin kullun suna yar mai kudi a gidansu amma har yau ko kwandala basu taba ciba naji hakan ne a makwabtan mu rana dana shiga gaidasu tun ranan ban koma shiga ba kuma master ya hana.
Na mika mata ina fadin inna gashi jin gashi yasa ta juyo da sauri tana kallon hannun nawa ta karba Dije ko tana can sai zuba mjn addua takeyi na nufi inda Aisha suke suma na mkka masu nasu .
San nan na dago nace Abban mune ya bani kudi dazun shine na basu ai nan suka shiga godiya inda yaran ke ihun murnan samun kudin.
Na juya na dauko kudi dubu daya naba asmau ta sayo muna mai mu kunna injin din muga haske ta fita tana godiya bayan ta dawone muka fito da injin din muka zuba mai nika ba karfi amma haka na gwada don sun gwada sun kasa tayarwa dole muka kira wabi yaro yazo ya kunna muna gidan ya gauraye da haske lokaci guda.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[07/05 9:00 AM] +234 803 180 3449: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
6️⃣7️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Har na kwanta naji waya na ringing na dauka hannatuce cikin damuwa take fadin don Allah zahra kiyi hakkuri bansan cewa ranki zai baci haka dani ba.
Na dauka yadda nayi zai taimaka maki gun mahaifinkine amma naga ranki ya baci da hakan kiyi hakkuri don Allah ta sake fada a sayaye.
Bakomai amma gaskiya banji dadin hakan ba wallahi wanan matsalance ta cikin gida Hannatu bai kamata ki zake irin haka ba tunda nima kinji nayi shiru a lokacin gaskiya ban fatan irin hakan ya sake faru garemu.
Na fahinta yanzu Zahra in Allah ya yarda hakan ba zai sake faruwa ba kuma na kirga kudin da Abba ya bani har dubu talatin nagode kwarai wallahi.
Bakomai nina kwantane saida safe nace da ita ina hamma tace Allah ya bamu alheri amma barci da wuri haka ni dai na kashe wayan don ban iya surutu a lokacin.
Sati daya kacal da hakan sai ga kiran wayan brother Bisi fitowana daga aji ina bakin masallacin mu zan shiga naji waya na ringing na tsaya na ciro da sauri ina dubawa naga sunan shi a rubuce a screen din wayan yadda nayi serving.
Na dauka da sauri tare da sallama ya fara fadin takardun sun iso an kuma yaba da kwazon mijinki sosai a takardun nan.
Saidai zai barki ya taho nan suyi interview yaya kika gani ya tambayeni cikin son jin amsan da zan bayar a lokacin da sauri nace haba brother koya kama ya zauna can ne aiba abin damuwa bane agareni yanzu .
Muna maka godiya da wanan kokarin dakayi muna sosai saidai zuwa America yanzu gaskiya ba karamin abu bane a garemu gaskiya.
No kubar komai a hannuna nine zan dauki duk wani nauyin tafiyan nasa har yaje ya dawo insha Allah fatana kawai ya yarda da hakan don mu cinwa manufar mu na taimaka mashi da nake sonyi ?
Insha Allahu ba matsala don ya yarda dakai saboda na fada mai halakarmu dakai kana matsayin babban yaya a garenine sai naji yayi murmushi yace amma baki fada mai nine naso auren ki kamar in mutu ba ko ?
Nima dan murmjshin nayi tare da fadin ba aure a tsakanin mune sai zumunci irin haka shiyasa Allah bai kaddara muyi aure ba na dora mai da gidiya bisa karamcin da yai muna din don a katse wanan zancen na tuna baya.
Mukai sallama ya fada min na turo mashi da account dina dana mijina nace yayi hakkuri ya karbi na mijina kawai yakece min kona raina da abinda zai turo min din ne nayi min kadan ?
Da sauri nace a,a ko bansan ko nawa bane nasan masu yawane kuma mai amfani a gareni yace to na turo zai kara kirana insha Allahu.
Har na fito sallah ina tunanen zancen mu dashine haka kuma ban fadawa hannatu ba tun farko don na kula tana da yawan surutu Allah daine ya hadani da ita.
Bayan na dawo gidane na danyi girki nakaiwa Dije don na kwana biyu banyi girki ba shiyasa na dora donta kawai dama tun a get din school na sayo danyen nama da kubewa da alaiyahu nazo dashi gida.
Girkina a natse nakeyi yadda na saba har na hada tuwone Aisha data shigo ta karba ta tuka min shi muna hira muka saka a leda na bata ta mika min zuwa cikin gidan .
Wanka nayi na fito na tayar da sallah don lokaci har ya dan shige muna kitchen din bayan na idar na zauna na dan jawo jakata ina duban a lokacin idona yakai kan ledan da ummah ta bamu ranan bacin rai ya hana in duba tun ranan.
Danbun kifine dana naman kaza sai sai yaji naci a ciki da wani kwalban tutare mai kyau itin na Dubai din nan da ganinshi zaiyi tsada sosai don har da armpit dinshi daga gefenshi an rubuta mai Noor haiyat a jikinshi da larabci da kuma boko.
Bayan na gama duk sallolina na fito na dauko leda a kitchen na diban masu wanan dambun nashiga cikin gida dashi na kai masu.
Na gaidasu da wuni dije ta karba min tana kiciniyar bude ledan dana mika mata din daga can naji inna na fadin wai wai wai yarinyar nan ina kika fito da kayan dadin nan haka ?
Nace wallahi ya dade a dakina ummah tace tabani shi tun ranan da mukaje gida gaisuwan yar anty Aisha din nan ban bude ba sai yau shine na debo maku.
Nidai naji Dije na munko gode Allah ya karawa arziki albarka nace amma Inna ko uffan batace min ba sai zuwa can naji tace ai irin wanan abin haka bai kamata a fitar dashi a gidan nan ba tunda tayarwa mutum da kwadayi za ayi ga banza.
Jinta fara sakin magana haka yasa na mike tsaye lokaci guda ina fadin to saida safe ku zanje in kwanta.
Ban karasa fitaba naji Dije na fadin wanan rayuwa naki baiyi ba ke kan data cinye bata bamu ba shine nufin ki tunda bai isheki ba watau ta karo maki ko ?
Kai umma zaki fara juya zancen ki ke nan duk akai maganan daya shafi yarinyar nan saiki mayar ya zama naki ni bansan abinda yasa kike haka ba wallahi.
Banji amsan da Dije ta bata ba don nayi nisa a lokacin ba kwanciya nayi ba a lokacin don na samu wayata da miscalled dinshi don haka na sake kiranshi ya dauka yana fadin barin kiraki.
Bayan na kashe ina gyara kwanciya naji ya sake kirana lokacin na dauka muka gaisa yake tambaya mutanen gida da karatu na amsa da lafiya.
Kina cikin gida halan bakiga kirana ba ya tambaya na amsa da eh naje kawai Dije abune dama naso na kiraka tundazun sai aiki yai min yawa ban samu lokaci ba.
Meya faru nace dama brother Bisi ne ya kira dazun wai ka shirya zakuje interview a can kuma, , , ban karasa ba naji yace inafa ke nan zamu tafi ?
Can America din yace sai naji yayi murmushi yace kai zahra akwaiki da son wasa wanda ko lagos bai taba zuwa ba shine zai tafi har kasan America yin me a can ?
Allah kuwa kuma yace ka turo mashi da account din ka na bank zai turo maka da kudin da zakai visa da sauransu nima kuma na tura nawa ya bani wanda zaka barmin a nan yace.
Anya zahra abin nan baiyi yawa ba kuwa mutum ba dan uwanka ba ya kashe maka wanan uban kudin haka gaskiya ya kamata muyi nazari akan maganan nan.
Amma kasan bamu rokeshi ba shine yayi niyar hakan don ya samu lada masu halin alheri haka suke abinsu sai su duba inda akafi bukata su taimaka don ladan hakan ya kai garesu.
Tunda nasan shi da wanan halin na sanahi dashi gaskiya don lokacin daga mu har yayyen mu maza haka zai kaimu ayi shopping kowa ya dauki abinda yake so a dawo gida shiyasa muke jin dadi idan yazo hutu lokacin.
Wani irin ajiyan zuciya naji ya sauke kafin yace to shike nan ba kinada account dina ba ki tura masa mu gani idan abin mai yuyuwace garemu sai naje.
Mun dan taba hira mukai sallama na kashe wayan ina tunane kafin barci barawo ya daukeni can tsakiyar dare ina barcin na fara mafalki wai nakaiwa dabbobin su ruwa sai wanan bakar akuyar da suke kira da uwar garke take ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login