Showing 144001 words to 147000 words out of 304363 words

Chapter 49 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33346

da bakin cikin mahaifin mu.
Yan kawo amarya sun koma cike da mamaki tare da labarin abinda idonsu ya gane masu a gidan kowa saidai ashe mu munbar baya da kura don Aisha dai ba a samu kaita nata gidan mijin ba.
Saboda mijin nata yana nan aka bakan shi naya fasa auren nata tunda har tai sanadin data tozartashi a gaban mutane ya baiyana halinshi a cikin rashin sanin kanshi lokacin.
Wanan yasa ya rufe gidan shi ya juya zuwa portakut inda yake aiki ya fita zancen su ya kumabar sakon cewa ya fasa sai ya dawo suzo su kwashe kayan su.
Mamakan da yarta ranan sun kwana da bakin ciki ita kuka yarta kuka ga zagi da Abba ya dinga surfan su dashi na tozarci a bainan jama,a kowana jinsu.
Tsab hannatu ta gyara dakin ko ina duk hjy kubura na tsaye har aka saka kamshi kafin ta kara lekani inda nake kwance mukayi sallama ta fito tabar su hannatu su uku a dakin tare dani.
Tana jin daga dayan lungun da akace na iyayyenshine ana fadin wai Dije mutanen nan sun tafine basu kawo muna amaryan nan dakin ba ko meye ?
Ato ina muke da kimar da zasu kawo muna yarsu nan ai bai nuna masu cewa muna da wanan matsayin ba gareshi aiko zanga yadda zaiyi yau yace zai shiga lungun nan.
A,a ki barshi ai yana da hankali koma meye dalilinsu nayin hakan zamuji ai daga gareshi suna hakan sukaji sallaman hjy kubura duk sukaja bakin su sukai shiru.
Su biyune suka shigo ta gaisa dasu take fadin kun jimu shiru ko wallahi mun kawo yarmu sai ya kasance bata da lafiya tana can kwance kafin mu fito saida akai mata allura amma kuyi hakkuri idan Allah ya kaimu gobe zamu kawota gareku.
Yanzun ma na shigone in fada maku don kada kuga kamar an raina makune anki kawota nan wurin kune ayi hakkuri don Allah lalura ya kawo hakan.
Nan take su Dije aka shiga fadin jam Allah ya bata lafiya daga jigilan buki sai kuma ciwo haka Allah ya sauwaka.
Tayi masu sallama ta tafi mahaifiyar Ahmed dake tsaye tana jiran kaucewan ta tace aiko ba gidan nan ba dama nasa badon Allah aka aura mashi yar nan dole da wani dalili a kasa da yaron nan yake boye muna.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣0️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Sautin kukan ne ya kara dakan kunnuwa lokaci guda zakice a cikin dakin akuyan ke wanan kukan jin hakan yasa na zabura da sauri na mike na nufo kofan falon da sauri mukai karo da juna dashi har sai da kowan mu ya kadu.
Shi yayi saurin fadin subbahanallahi zahra lafiya kuwa na ganki haka a firgice a daidai lokaci akuyan ta sake sake wani kukan da karfi kuma jere da juna batako ajewa take sake wani.
Ai bansan lokacin da nayo cikin shiba a firgice na cakume shi ta baya shiko yana fadin wai akuya kikewa wanan tsoron haka dama zahra ?
Akuyatace kila abinci takeso ko wani abin barin fita in dubata ga kayan karyawa nan a falo na aje maki don na shigo na samu kina barci na fita zuwa wurin su Dije.
Ganin har lokacin a tsorace nake don ban sakeshi ba yasa shi fadin dawo nan ki zauna a falo har in dawo sai in hada maki ruwan zafi kisha.
Sallaman hannatune mukaji tana ta kwada sallama daga waje bata kai ga shigowa cikin part din namu ba, ba kuma wanda ya karba mata sallaman ta a lokacin.
Saishi ya daga murya daga ciki yana amsa mata tare da dan takawa nima nabishi baya don har lokacin duk a rikice nake ta turo kofa tana fadin gaku kamar fita zakuyi mana naganku ?
Ke san amaryan tawa motsoraciyata akuya kawai tayi kuka shina kika ganta haka a firgice ta barima in fita in duba me akuyan keso ta hana yanzu.
Ashe ciwon kan ya lafa dan hakane fa na fito don hankalina jiya wallahi ya daga sosai yadda muka barta a kwance ashema da sauki don gata na ganta garau yanzu.
Gaskiya master ka iya jinya daga dare zuwa yanzu jikin har ya lafa haka a cikin sauki sai naga ya sake wani shu,umin murmushi a fuskan shi yana kokarin jayewa daga rikon da nayi mashi
Sai lokacin na sakeshi nima don na fahinci me take nufi, na nufi wurin kujera na zauna ina sauke nufashi koshi don naga hannatu ne a dakin nasan koma meye zata iya cetona kanshi ai.
Daga haka shi kuma ya fice ya barmu tare hannatu din ta kalleni tace aina dauka ko kofa baku bude ba yanzu har inno tana ce min wai waya fada min ana wanan sakkon haka gidan amarya da ango ?
Wani kallo na watsa mata tare da fadin ai gaskiya ta fada maki uwar gulma kin dako uban safiya haka kinzowa mutane gida don ki damesu.
Yar iska da ace kedin ba matsoraciya bace zakice min haka jiya nan kika tayarwa mutane da hankali waike ciwon kai don bakin tsoro kawai kin dagawa dan mutane hankali har yana sabari a gaban abokanshi.
Tsuki naja tare da fadin dama shi ya kawoki ko yanzu sai ki kara nadewa ki tashi ki gyara min wajancan don bamson kura kin sani.
Ai wallahi baki isa ba ni fa naman nan nayo samako naci don nasan baki iya cinyeshi duka jiya tunda tsoro ya hanaki lakka.
Kaji munafuka amma cewa kikayi don jikina kikayo sanmako yanzu din kuma kin buge da fadin a baki ragowan nama kici to anki a baki din .
Nasan koma zakici ba zaki cinyesa duka ba don haka ba zan wani damuwa ba don nasan yana nan nawatsa mata wani kallon takaici nace idan kina so je yau a daura maki aure kici.
Ai muma zamuyi auren nan dai muji don gashi jiya jiya anfara muna gorin akanshi babu ko kunyar hakan kamar ba jiya kike nan kinawa su mommy raki ba.
Murmushi na sake daga inda nake zaune nace kedai kika sani in zaki tashi ki dauko cup kizo ki karya ki tashi kafin wani ya shigo kuma.
Ai kuma kin fada min gaskiya abari ya huce shike kawo rabon wani ta mike tana fadin hakan ta fita zuwa kitchen din kafin ta dawo nakai kwance saman kujeran.
Ta shigo tana fadin waini har yanzun ina mamaki na shigo ina ta sallama ga kannen Master ina gani amma sunki karba min saida naji muryan master na shigo nan.
Wata kila basu jiki bane amma ayi sallama su kyaleki kuma a lokacin ya shigo da alama ya dauraye hannayen shine don ganin damtsen hannun shi da nayi da ruwa.
Hannatu dake duke tana hada shayi taji kunya sai cewa taji yayi kinko kyauta min hannatu da kike hada maku tea din nan bari ni in shiga in dan watsa ruwa in fito.
Ya shige ya barmu nan muna hiran bukin wanda hannatun ce ke firan sai jefi jefi nakan dan bata amsa don irin yadda nake jin kaina a takure a sabon wuri ji nake kamar bakunta nazoyi a wanan wajen da anan yanzu zanyi rayuwa.
Ire iren wanan tunanen ne suka tsaya min a zuciyata inda nayi sa,a shine na kula Ahmed mutum ne mai tsabta sosai shi da wana na danji daman wani a rayuwata yadda nake da tsanda din nan yasa ko a gida kowa baya shiga dakina ba a kuma taba min kayana.
Gashi yanzu zanyi rayuwa tare da wani wanin ma namiji a daki daya tare dashi kaya kan iyayyena sun kashe min kunya gaskiya duk da gidan ba wanigidan fada ba amma gyaran wurin ya tsaru da kyau komai an matsashi an saka min a dan wajen nawa.
Ya fito tsab dashi cikin wani sabon dinkin shadda mai ruwan toka sai alaman saura dan ruwan wankan da kakanga shafin a jikin maza wani lokaci idan sunyi shiri wanda suba mata bane da zasu tsaya kakale kansu wurin gyaran jikinsu.
Hannatu kina nan ko barin dan fita na dawo don Allah ga matana nan ammana na bar maki sai hannatun tace kai Master ban dauki wanan amanan ba ai saidai ka bar mata ni amana matsayina na bakuwan ku a yanzu.
Nikan hannatu karki kasheni don Allah na fada ina dan murmushi ya dan sake murmushin jin dadin ganin mu na fara sakewa shugowan hannatu gidan.
Ya dago yana fadin to madam Master ni zan fita ko akwai wani abinda kike so a sayo maki idan na fita ya tambaya yana kallon fuskana na dan girgiza kai ina fadin Allah ya bada sa,an fita ya dawo min da kai lafiya.
Amma kuma baka karya ba naga zaka fita daka dan tsaya ka saka wani abu a cikin ka kafin ka fita ai na fada ina mayar da hankali a gareshi.
Wanda na fadi hakan ne don hannatu don nasan ba zata kyale ba lokacin aiko ban kai ga rufe baki ba naji muryanta tana fadin a, a, a su aure manya har an fara yiwa miji fatan alheri irin haka ?
Da wani marairaicewa missa baki tashi tun asuba kin hada mai abin karyawan ba zaki barshi ya fita haka yanzu ?
To Yarsa ido shiya kawoki gidan nan tunda safe haka don ki dinga sakawa mutane ido ni har kinsa ina son auren yanzu shidai ya fita yana murmushi don yasan tsakanin akwai yar haka dama.
Yana fita muka canza topic din hiran mu dan cewa hanne tayi a gaskiya zahra kamar zakiyi aiki da mutanen gidan nan don fa yanzu da zan shigo nayi ta sallama ba wanda ya amsa min .
Saima lekowa da wata budurwa tayi tana ganina a kofan nan taja tsuki ta juya tun dazun abin ya tsaya min a raina wallahi.
To meyasa hakan ke baki kula ko ranan da sukaje gidan ku da sunan zuwa ganin amarya ai haka sukai ta wani mere baki suna maganan gidan naku wai ba a darajasu ba don angasu basu da komai.
A lokacin ne mommy ta aiko a kawo masu abin zama da drinks a nan fa suka so raba hali a tsakanin don sun manta ina wajen don akwai yan unguwar nan dana sani cikin su.
Har wata na fadin waisu ba a basu abincin da suka gani ana ta rabone saida wata cikin su ta tsawata masu tace kada su barwa Master abin kunya don Allah suka natsu.
Saiga abincin kuma mommy ta aiko masu dashi suka kuma karba murmushi kawai nayiwa hannatu din kafin nace kai irin wanan ni bai faye damuna ba yaushema nake da lokacin suni ?
Ai dole kiyi lokacin su tunda yanzu dasu zaki zauna ya zama dole kiyi taka tsantsam da kowa ki fahincesu kada kiyi saurin sakewa dasu tundai kanen nan nasa da alaman rashin kunya a fuskan su.
Shiru nayi ina tune kafin na nisa son na hango alaman wani matsala kuma a nan bayan wanda na baro a gidan mu can anayi wanda har yanzu ummah tana cikin fuskantan shi.
Da farko dai ki mayar da hankalin ki sosai Zahra wurin yiwa mijin ki biyayya ki nuna masa kauna kamar yadda shima yake nuna maki a gaban kowa don tsakanin daren jiya zuwa yau na fahinci wasu abubuwa game daku.
Kada ki yarda koda wasa a samu matsala a gurin ki zahra don mutane sun bude kunnuwan su sun kuma baza ido sugani ko zaki iya zama da master a hakan.
Ko ita mama data masa sunyi hakane don su bata maki suna a karshe a koma ana zagin ki cikin gari wanda kuma su da kansune zasu baza maganan naki a gari.
Sun dauka ba zaki iya rayuwan talauci irin haka ba don idan anyi daga baya kin kasa zama a dawo ana maki lissafin dakin auren ki.
Hausawa sunce idan ka kure dakin farko yanada wuya ka sake samun irinshi a rayuwan ka din haka zahra ki kwanta ki bisu da halinsu ki kara hakuri bisa ga wanda kike dashi a baya.
Shi aure dama dan hakkuri komai dacen mace da gidan hutu ko inda takeso saifa ta hada da hakuri a zauna lafiya don haka ki zamawa Master diya .
Shima haka ya zama maki da don kinyi mai abinda bako wace yarinya bace a yanzu zata iya hakan ga namiji duba ga yadda rayuwan ya koma yanzu kowa na son jin dadinsa.
Amma in akwai ci dasha da sutura duk wanan mai saukine sai mace ta zauna tayi hakuri don ba wanda yasa ya gobe zatazowa bawa karshe.
Haka ki jajirce dkn Allah ki kula wurin bashi hakkinshi na da namiji ki kawar da komai a zuciyar ki kada ki dauka wai kin fishi gata a gidan ku a, a zahra ki kwanta mashi Allah ne ya basu su maza wanan matsayin.
Haka karki yarda koda wasa kiyi rauni a wurin girki don ko ba komai kiyi kokari ki girka masa abinci ko wani irine don kinsan an camfa matan yanzu a wurin girki an barsu baya.
Don haka yanzu an saka ido an baza a dandana girki aji dama kuma an dauka diyan masu hannu da shuni baku iya aikin komai ba hakane ke yawan jawo matsalan aure da yawa yanzu.
Zama na gyara na lumshe idanuna ina jin maganganun hannatu din kamar na wani babba can a kunnuwa kiyi hakkuri wata rana sai labari insha Allahu dan hakin daka raina shike tsonema ido.
Shiru nayi sosai ina sauraren ta don nasan iya gaskiyan da duk mai kaunata tsakani da Allah zai fada min ke nan irin wanan zance da hanne ke fada min a yanzu din.
Sallama akayi a kofa hakan yasamu katse zancen mu su mommy ne dasu mama Geshuwa yar ummah sukazo don na daukama sun tafine don naji a ranan ne zasu tafi.
Saidai basu shigo part din direct ba kamar yadda hannatu tayi su sun wucene part din mutanen gidan suka gaisa dasu tare da masu ya gajiyan taro kafin su fito zuwa nawa part din.
Suna shigowa na mike ina gyara mayafin kaina na rungumesu daya bayan daya ina gaidasu suna min ya jiki ya kuma kwana a bakon wurin ?
Na danyi murmushi kawai bayan sun dan zauna can mama Geshuwa ta mike mommy ta bita da sauran mutum hudun da suka shigo dukkan su bakine sunzo sha,anin bukin ne lokacin.
Kitchen suka shiga sun dan dade a ciki kafin su fito da wasu buhuhuwa suka hada da kayan da sukazo dashi mommy kubura tace oya tashi mu shiga ki kimtsa mu kaiki wurin sararkanki ku gaisa.
Don tun jiya suka fara korafin wai ba a kaiki ba kun gausa an basu darajansu gareki Allah yasa naji na dawo ba basu hakkuri kan baki da lafiyane.
Ta tafuto hannatu tace zo mu shiga ki tayata kimsatsawa hannatun ta taso muka shiga dakin tare shiga na kwarai na alfarma mommy da hannatu sukai mun.
Muka fito gaba dayan mu zuwa part din nasu suna zaune da wasu baki mukayi sallama aka shiga nan suka fara kame kamen gyaran wuri da kyar muka samu inda zamu zauna.
Nan aka shiga gaisawa kafin mama Geshuwa tace dasu to inna ga jikanki nan kuma yarki mun kawo maku ita amana don Allah idan tayi ba daidai ba a tsawata mata a sakata a hanyan daya dace.
A,a ga uwayen su nan zaune tsohuwa Dije ta fada nikan kakace garesu amma ba laifi ai wanda yace yanayi da danka ya gama maka komai a duniya.
Zahra ki saki jiki nan kamar gida kikazo ga uwar mijin ki nan ga kannensa muyi zaman mu lafiya keji kaina a duke yake kasa kuma na dunkule a tsakankanin gwiwana sai hawaye ke zubo min lokacin.
Wanda ba zan iya fadin kona meye ba gadai hawayen ina zubarwa zan baka tausayi sosai a yadda nake zaune can sai naji muryan mahaifiyarshi na fadin.
To kesan dai muna da yara mata a gidan nan dole sai kin hada da hakkuri wurin zama dasu mommy ce ta katse ta da fadin ai ko gida tana da kanne itama .
Iyaka dai kowa ya tsaya matsayin shi su bata girmanta na matar wansu itama haka ta dubesu a matsayin kannenta saikuyi zaman ku lafiya dama hakane.
Me zai kaisu wurinta in ba sa ido tana gefenta suna nasu kudai Allah ya bamu zaman lafiya ya kawo kazantar daki da wuri tsohuwa dije ta fada kamar tana katse zancen da aka dauko din lokacin.
Nan dai naji mama Geshuwa tace ga dan abinda ya samu nan daga waje na uwayen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login