Showing 27001 words to 30000 words out of 304363 words
fito da ruwan randa mai sanyi an surka da kunu anyi farau farau dashi a kofi mai marfi.
Dattijon ya karba yana saka mashi albarka tare da mai fatan alheri yana fadin nagode nagode yadda ka tareni kaga tarbon arziki kaima a rayuwan ka har duniya ta nade.
Shima godiya yayi yana fadin amin baba nagode nagode kwarai baba ya fada yana kaiwa kasa muryan dattijun ne ke fadin.
Yaro kasan inda zan samu yar akuya ita nazo nema da yamman nan na dauka zan samu malam tanimu mu hada kafa muje tare.
Kallon mamaki yaiwa dattijo saidai fuskan dattijon na kallon wani wuri a lokacin yayi karfin halin fadi a cikin mamaki aiko baba akwai akuya da akai niyar sayarwa dama barin shiga inwa maishi magana sai a fito dashi ka gani in zai maka.
Ya mike zuwa gidan su bai jima ba sai gashi jaye da uwar garke a hannun shi yana ja zuwa wurin dattijon dake zaune saman kututuren da malam tanimu ya heke ya hada ice da ice a kofan gidan yana zama a sama.
Yazo gab dashi ya mike tsaye yana fadin kai wanan ai zatayi kudi da yawa da daidai yar madaidaiciya ce sai insaya ai
Zaka iya saya idan zatayima baba lalura yasa maishi fitar da ita aiko lalura yakai lalura wanda zaisa a fitar da guzuma haka iri mai kyau da ita yanzu zata kai nawa wanan ?
Tau baba maishi tace jakka arba,in amma sai ka taya a, a yaro ba zan taya ba idan har ta bari ga kudin Allah yasa ta amfana dasu har abada.
Kallon tsohon yayi cikin mamaki jin ko gardama baiyi ba daga sa suna har ya yarda da hakan shi ya banye wani kulli ya fito da kudin ya bashi ya karba cikin mamaki.
Dubu biyar ya kirga ya mayarwa tsohon dashi sai lokacin suka hada ido dashi gabanshine ya fadi ras lokaci guda duk da tsohon yayi saurin kawar da kanshi gefe daya.
Kai ya girgiza mashi tare da fadin jeka dasu yaro Allah yasa masu albarka abinda ka dafa yazama alheri a rayuwanka ya sake amsawa da amin baba yaja akuya ya tafi shi kuma ya koma gida cike da mamaki da al,ajabin wanan bawan Allah.
Mama ya akayi Zahar take amfani da wanan tsohon motan bayan kowa saya mai sabuwa akeyi idan zai shiga jami,a amma ita sai naga tsohuwar mota take amfani dashi na Aisha ?
Uwartace tace kazo ka tambayeni ko wa ?
Haba mama ya ummah zatayi min wanan maganan kuma nidai na ganta yanzu ta shiga wanan mota yasa zo na tambayeki meyasa haka mama ?
Haka naga daman yi don haka ka barta dashi amma mama baki ganin hakan ba da, , , , , , hannu ta daga mai tare da fadin kaga na fada ma ra,ayina don haka kada ka dameni.
Koda aka bata tsohuwar tafi katfin shiganshine ita din uwarta yar waye da yarta ba zata shiga motan da Aisha ta ajeba ?
Amma ainan gidan uban zarah ne bana wani ba don haka zarah daidai take da kowan mu a gidan nan ke nan irin wanan wallahi mama tauye hakkine fa hakan nan ?
Baba ni zaka tsare kanayiwa fada kome koni zaka nunawa hanyar gaskiya a yau din na bata wanan din kaje kayi yadda zakayi ina jiran ka.
Mikewa yayi tsaye ya saka hannayen shi cikin aljihunshi yana fadin alright ya fice daga part kai tsaye dakin shi ya nufa ya shiga wanka zuciyar shi na masa tukuki hakan da sukayi da mama din.
Yana fito part din ummah ya nufa falo ya sameta ita kadai bayan sun gaisa tace har ka karyane ko baba naga kamar fita zakayi ?
Eh wallahi ummah yau zan koma ka karyane ko haka zaka tafi tana kallon shi cikin tsure shi da idanunta a zuboma kunun gyada yace eh bani nasha kada nabi hanya ban karya ba.
Bayan ta debo mashi ta kawo mai inda yake zaune a lokacin yasa hannu cikin aljihu yana fadin ummah wanan sakon Zarah ne idanta dawo abata na fada mata zan barmata a wurin ki.
Kunyi sallama ke nan da ita ummah ta tambayeshi yace eh a gabana ta fita dazun amma ummah kina kallo akaba zarah wanan motar tana shiga ?
Murmushi ummah ta sauke a fuskanta tana fadin me motar tayi ai da lafiyanta wace Aisha ta ajene aka bata yafi ta dinga zuwa ana haya ai ko ?
Fuska ya bata ya dauki kunun yana kurbawa a hankali bai dade ba ya mike zuwa part din mama bayan tayi ma ummah sallama bai samu mama a falo ba sunce ta shiga wanka.
Ya bar sako idan ta fito a fada mata cewa ta wuce zuwa Abuja daga can zai koma lagos jin haka yasa Aisha mikewa da sauri tana kiran uwar duk da tana cikin bayi haka bai hana ta fada mata gashi zai wuce ba.
Saidai kafin su fito harya fita ya kuma kashe wayan shi da bai kara budewa ba sai bayan ya sauka Abuja ya nufi gidan Abba ya bude wayan nasa.
A lokacin ne sakon ya jafar ya shigo ya bude yana fada mai mama ta kira tana fada sosai don me bai jirata ba ya tafi ido ya runtse ya kashe wayan nasa ya tura aljihunshi.
Ya samu Abban mu baya jin dadi yana kwance ranan bai fita ba nan ya soma fada Abba ga irinta nan ummah na nan zaune ka dauketa ka mayar gusau gasu can basa komai suna zaune kawai kai kana nan kana wahala kai kadai sai yan aiki.
Murmushi Abba yayi yana gyara zama yake fadin to ya na iya maimuna tace sai su koma gida dukkan su ita ta baro lagos ita wana dake nan dole itama ta dawo gida su zauna tare dasu.
To amma Abba ya akayi Zarah take hawa wanan motar tana fita a cikin shi Abba wanan baiyi ba wallahi zan hada duk abindake gareni in sayawa zarah mota amma ba zata kara amfani da wanan motar ba daga wanan satin.
Dakata malam ai abin baikai can ba wanan zancen da kakeyi ban taba sanin motan da Zarah take jaba a yanzu ni dai na san muyi magana da maman ku cewa za a samawa zarah mota in kawo kudi.
Kuma na bata saidai bazan iya tuna komai yanzu ba kan hakan amma dai nasan an karbi kudin a hannuna kuma na bata yanzu kaje kafin tashin ku sai ka duba mata mota daidai da ita.
Kabar kudinka wanan nauyinane yin haka amma gaskiya Abba ku kula don abubuwa suna son suna son rikicewa fa yanzu gidan nan don a gaskiya ummah tana hakkuri da kawar da kai ga komai amma ya kamata a duba mata hakan gaskiya.
Baba nima nasan da hakan a yanzu na fara fahintar wasu abubuwan da nakeyi bai kamata ba amma ba yadda na iya don ban iya rikicin mahaifiyar kune.
Abba kaika ajesu fa bai kamata ace ka fadi haka ba idan baka fitowa mama ta baya ba gaba dayan ku zaku halaka kan nu baku sani ba
Sun jima suna magana na fahinta da dan nasa kafin ya fita zuwa ya duba motan kamar yadda Abba ya umurce shi dayi ya duba kuma ya samu mai kyau daidai dani anyi service din ta anyi komai ya dawo da ita gida Abba ya gani.
Duk da saurin da yakeyi don ya fita zuwa school tunda sauran duhun asuba haka bai hanashi gane cewa uwar garke tana kwance cikin yayanta ba lokacin.
Salatin daya sakane ya fito da Dije daga dakin yana fadin uwar garke kece kika dawo ko idona ke gizone wai yana kara nufar wurin da dabbobin suke kwamce fuskanshi dauke da mamakin hakan.
Dije cikin dan dingishawa ta fito tana dadin sai naji kana zancen uwar gareke ko saboda sabo da itace yasa kake ganin tana ma gizo a idanun ka kuma ?
Itama fitgita tayi tare da sake salati tana fadin Allah sarki uwar garke dawowa kikayi ta nufi waje tana cire mata igiya.
Dije daga gidan wanan mutumin tagudo fa ra dawo nan to kuma aishi yace min daga kauye mai nisa yake dakatar da abinda takeyi rayi ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki.
Kana nufi ba garin nan yake ba maishi yace haka ya fada min sai da sauki don abokin malam tanimu ne ai kuma yaga gidan dana fito da ita ai.
Zan fadawa malam tanimu din tana nan ta dawo sai suzo su kama abinsu su tafi dashi Allah satki sabone sabo yasa tayi hakan ai Dije ta fada.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[30/12/2022 10:00 AM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🔟
AL MUTAKABBIR,,,,,,,,,,
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Tsaye yayi yana karewa akuyar wace ke kwance tana tukan abincin dataci kallo kafin yaja kafanshi zuwa daki zuciyar shi cike da tunanen ina tafito gashi bai san wanan dattijon daya saye taba a cikin unguwansu ba.
Duk inda ta fito wuri mai nisace sosai to yaya akayi har ta gane hanyan gida ta dawo haka a cikin dare har ta shigo gida lalai dabba sai a barta inda aka ganta suma suna da kwakwalwa ke nan ashe kamar mutane.
Dukawa yayi ya dauki takalman shi mafalkin da yayi ne mai kama da almara ya fado mai arai har ya tashi bai makara ba a lokacin.
Yaro ga akuyan kunan na dawo maku dashi har gida na yafe kudin ta halak malak Allah yasa kudin ya amfane ka kai ya fada yana mikewa da sauri yayo waje Dije yake kwallawa kira ta fito har yanzu tana cikin alhinin akuyan tana dakinta tana mita tana fadin dama nasan za,ai haka dake uwar garke.
A nan kika bude ido fa nan kika saba nima tun tafiyan ki nake kewan rabuwa dake sai kuma ki gudu ki dawo bayan na karbi kudin ki.
A lokacin ne taji kiranshi cikin daga murya azotonta ta dauka akuyar ta gudune sai dai ta hangota a kwance yadda take lafiya Amadi da wanan kiran haka ?
Lafiya Dije wani mafalki nayi da asubah din nan yanzu ya fado min a rai wai wanda ya sai akuyan nan yake fada min ga akuyan nan ya mayar muna halak malak mu rike kinga kuma gata nan yanzu.
Kai Amadi ina aka taba haka kila don zata dawone kayi mafalkin hakan ko saboda sabawan da mukayi da ita kuma yasa ka fadin hakan.
Ba hakana bane yanzu dai nasan mai ita zai dawo insha Allahu ya biyo sawun abinshi kinga sai a bashi ko bana nan yazo zaki ganshi wani dattijo farine dogo ya dan rankwafa da farin geme a fuskanshi.
Wanan kwatance haka ai karewa halitta kallone bari dai yazo din mu gani idan shine yace to ni zan tafi sai na dawo ke nan tace Allah ya tsare ka dauki jakka biyar kayi amfani dashi cikin kudin akuyan.
Jin haka yasa ya juyo da sauri yana mata kallo mamaki kafin yace Dije ina zan taba kudin mutane ga akuya a hannu mu yanzu.
To kudi ai ya zama namu yanzu albashin idan mai ita yazo sai a bashi abinshi ya tafi ba shike nan ba a aje kudi ana kallonsune haka ba tabi?
Ya dai sa kai ya fice ya barta tsaye tana magana ita kadai a gidan tana fadin kaji mun yaro waishi ga uzzutazu yasan Allah ke nan ko ka wani ce kudin mutane mutanen bamun basu akuyan ba sakacin su yasa suka sake ta ta gudo.
Meeeeey meeeey akuyan tayi kuka lokaci guda ta juya gareta tana fadin uwar garke kin min gafara rashi yasani rabuwa dake amma na kwana dake a zuciyana jiya wallahi.
Ashe da rabon mu sake ganawa dake haka ruwa ta diba da guntun dusa ta kai mata tana fadin ci uwar garke gaki har cikin ki ya fada haka.
Sauri nakeyi sosai saboda na dan makara na isa school din a gurguje nake in isa department din mu muka hade dashi ina kwana nace ciki ciki shima haka ya amsa min din.
Na wuce da sauri saidai tun ka na karasa na hango wasu a waje hakan ya sanar min da wanda ke cikin ajin ne ya dakarar dasu waje din don makara.
Nima danazo yanzu a nan na tsaya haka na bayana suma suka tsaya kaina yana duke ina jin yadda sauran ke zagin malamin ban dai kula hakan da sukeyi ba.
Shine yazo zai shiga ajin magnet ka roka muna shi don Allah sai lokacin na dago kai mukai ar,ba da wanda suka kira din da magnet.
Wanan matashinne ya shige a yadda yake kamar kullun mutsu mutsu dashi naji wata na fadin amma dai kai wanan din ne zai roka muna wanan mutum maigirman kai ?
Ke kika ganshi mutsu mutsu ajiyan Allahne wurin nan baki sani ba don kaf department din nan na science babu kamar shi akace shine yasa ake kiranshi da magnet don kokarin shi.
Wanan din ta tambaya a lalace yace shikuwa da kike gani nan kinsan haka Allah ke abinshi shi bai damu da irin wa yan nan karyan na zamani ba.
Ya fito tare da malamin saida sukazo gap damu malamin ke fadin wacece sister din naka sai ya nunani yace wanan yau ya akayi kika makara tana da kokarin shigowa da safe ai.
Ya dubemu yana fadin ku shiga tunda wanan ya roka maku kunci albarkacin sister dinshi mungode na riga kowa fada a wurin yace ba matsala hope dai kina da kokari irin yayan ki ?
Murmushi kawai nayi na shige na barsu a wurin tsaye sauran ma suka biyo bayana muka shiga tare dasu aka zubo muna ido wuri na samu na zauna na fara fitar da takarduna.
Saiga malamin ya dawo yake muna fadan makara ga dalibi kamar bai dauki abinda muhinmanci bane yaja muna kunne sosai a haka har period din shi ya cika ya fita.
Sai lokacin na samu natsuwa kafin wani ya shigo muryan wanan guy din naji yana fadin ashe muna tare da kuraye ne ajin nan bamu sani ba kanwar over role student a cikin class din nan .
Kai na dago na dan kalleshi yana kokarin zama inda na kusa dani ya daga yana fadin to amma wai dai na tambayeki wai da gaske don Allah yan uwa kuke keda Ahmad ne ko kuwa dai ?
Amsan dana bashi shine ba kaji ya fada da bakin shi ba dazun wani amsa kake son ji yanzu kuma ya kalleni kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru.
Kafin yace amma shi yaya na ganshi haka koda yake baku da zubi daya alamu ya nuna dai irin zumuncin nan ne kawai a tsakani ku ?
Don Allah idan ba laifi ki muna hanya mana a wurin shi mu dan rika ganin shi yana muna group sai mu dan rika masa wani abu don ance gaba daya department din nan ana ji dashi saidai don ya kasance shiba dan kowa bane haka yasa ba a sanshi ba.
Shiyasa nayi mamakin jin ya kiraki da kanwarsa dazun har nazo na tambayeki ai yanzun zaki masa magana ko yaya ya tsureni da ido yana son jin amsata.
Nisawa nayi nace masa ka bari nayi shawara duk abinda ke nan zan sanar maka gobe ya mike daga rankwafowan da yayi yana fadin to shike nan saina jiki goben amma don Allah ki taimaka muna ya yarda kinsan mutumin hutsune sosai don shinema bai kula kowa wanan kan halin ku yaso yazo daya.
Daure fuskana nayi na mayar da hankalina kan karatun daya sama ina yi da farko ganin hakan yayi min sallama ya tafi ajiyan zuciya na sauke .
Na dawo gida da yamma lis nan Tani mai aikin mu ta tareni da murna waina bata goron albishir na dauko dubu daya a jakkata na mika mata ummah na zaune tana karatun wani littafin addini na addu,oi.
Bayan na bata take fadin yar lelen masu gida albishirin ki aina baki goron na fada a gajiye tace uwar dakina yau mun samu karuwa wani motar kuma yayan ki musa ya turo maki dashi yau din nan har wanda ya kawo ya juya ya koma Abuja dazun.
Mota na fada ina kallon inda ummah take zaune tace ke dai bari yau nayi murna nayi guda a gidan nan kamar ba gobe wallahi wanan shi ake kira da dan da Allah kewa fada bayayin fada .