Showing 279001 words to 282000 words out of 304363 words

Chapter 94 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33376

lokacin kafin na dago ina fadin Abba ina kwana ya amsa da fadin .
Zahra kunzo lafiya ya hanya da zaman jirgi jikin naki da sauki dai ko na amsa da fadin Alhamdullahi Abba mun sameku lafiya ?
Kana na sake dagowa nace mommy ina kwana ya gida mun sameku lafiya ta amsa a sake cikin sakin fuska da nuna jin dadin ganin mu.
Kana nayiwa sauran jam,i da fadin kuna lafiya ya muka sameku dacewan yaran dake wurin da suka zuba muna ido suna kallon mu for the first time a cikinsu a lokacin.
Na daiji an amsa ba zance ga wa yanda suka amsa min ba a lokacin saidai ina tunanen cewa amma badai wanan matar bace ta haifesu duka amma zamu sani gaba ai.
Duk abin nan master bai dago kansa ba don jin yaran ba wanda ya iya gaida dije a lokacin inka debe hjyn data gaishe ta hanyar fadin mama sannun ku da gajiya ya hanya ya kuma zaman can ku dai sha turai sun baki wahala.
Shine ya dago yana gaisheta sai kuma wasu yan mata mutum biyu da suka fito daga ciki tun kan su zauna suke fadin a,a sannunku da zuwa yaya hanya anty sannu da zuwa .
A cikin fara,a suma suka gaida dije din dayan harda ba,a tana fadin tsohuwa kinsha hanya sannu da kokari ai naso ku iso idon mu biyu sai gashi kunzo munyi barci lokacin.
Hjyn tace idan idonki biyu me zaki mata tana dariya tace wai na kamata ta fito mota mummy kinsan tsufa to baku daiga fitowan nata ba ai.
No yaya ya daukota ko anty mungani ai a cikin mafalkin mu daga can daya daga cikin wa yanda muka fara sama a wurin naji muryan daya na fadin nifa na daukota zuwa mota amma yanzun zata rama wahalan daukota da nayi don abinci zata ban a baki naci .
Aka kwashe da dariya yaci gaba da fadin yau ai har goyon nan na kaka saitayi min shi a gidan nan nima tunda Bros kawai kike goyawa shi kadai mu kin barmu nan ya fada yana tasowa zuwa inda take ya duka tare da riko hannun dije din ya dora akansa yana fadin ki fara saka min albarka kafin mu gaisa.
Dan murmushi yake master yayi yace kai daka daukota a bayanka tun jiya aita gama saka mata albarka a wurin nan dai sukai ta jan dijen da firan jika da kaka kafin ya dago zuwa wurin dan uwan nasa ya zauna a gefenshi yace.
Bros ya hanya ya aiki kuma da mutanen can yana mika masa hannu a cikin fara,a dan uwan nasa da har lokacin fuskanshi a daure yake falon yace yasir ya kake ya aiki kuma ?
Wallahi lafiya kalau Bros yau Allah ya nufa zamu hadu kwanan nima na dawo bai one week ba ina gani kana ya dago yana dan leko kai yace madam ya kike ya yara kuma ?
Na dago na amsa mai a lokacin Abba ke fadin Alh dai jiki ya kiya nacewa mijin ki ya kaishi indiya in yaga jikin har yanzu sai a shirya a fita dashi zaifi.
Nagode Abba na fada cikin girmamawa a gareshi so sorry Dad dinkine baida lafiya shine dalilin zuwan mu kasan Master ya bashi amsa ayyah sorry ko a cikin kulawa.
Cikin dakewan murya yace hjy fa ko tayi tafiyane hjy ko kana nufin mummy din mu yace eh bata nan ne banganta bane ai tun jiya din shiru yasir din yayi kafin karamin yace wai daddy ya koreta a gidan nan saboda , , ,
Musty ka faye surutu kai aka tambaya ta dago tana fadawa yaron haka a cikin harara yace mum fa ya tambaya sister shine ka rufa min bakinka a nan ta fada da dan tsawa.
Yaron ya soke kanshi cikin wani murya mai kaushi muryan Abba ya ambaci sunanta yace ke Salima bakiga babban yayanku bane da matarsa da suka shigo falon nan ?
Daddy na gansu mana ta fada a tsiwace tana mayar da air piecer a cikin kunnuwanta yayin da jikinta yake saye da wani dan riga fari mara hannu mai aniniyaiya zuwa kasa karshen hannun rigan an takwasheshi daga can ta hammatanshi.
Sai dan wando pink wanda ya tsaya mata iya sharaban kafa shima wandon kuma an masa anini a karshe ya matse kafan wanda hakan ya kara fito mata da yan gajerarun kafaduwanta farare a waje.
Don gajerace mazan sun dan darata da tsowo saidai basukai Abba din ba da alama uwarsuce gajera suja kwaso yanayinta a nan saidai akwai fari kan sosai gaskiya.
Duk da nima farace mijinama farine sol amma hakan bai hanani ganin farinsu ba yayin da ita kuma hjy murja farace ba dai sol haka ba ita da nata yan matan yanayinsu daban ne a gidan hakan zaisa ka gane ba uwa daya bace ta haifesu ba a gidan don yanayin daya bambamta garesu.
A cikin harshen turanci Yasir din ke magana yana fadawa dan uwansa ai mum bata nan sun samu matsala da daddy tana wani gida zaune ne yanzu ita .
Jin hakan yasa master ya kalli mahaifin nasu ya dukar da kai kasa tare da fadin please Abba kayi hakkuri ku zauna lafiya da matar ka kada ya zamo dukkan mu bamu da uwaye a tare dakai su yarana kuma sun taso tare da uwarsu dakai a gidan nan sun bude ido da hakan .
Yanzu zaman su ba tare da itaba zai iya jefa rayuwansu a cikin wani yanayi kun girma kunsan kanku mune zamu kwatanta hakan kuyi muna fada komai tayi ma taci albarkacin diyanta a gareka ai.
Hannu ya dagawa dan nasa alaman ya dakatar da zancenshi a lokacin hakan yasa yaja bakinshi yayi shiru kowa a falon yayi shiru na dan lokaci kafin can ita macen ta mike tana jan tsuki ta nufi hanyar shiga part dinsu a cikin takaici.
Muryan Dijece take fadin hakkuri akeyi da iyali yadda kuka kai din nan bai kamata ace wani abu mai muni haka ya fito a tsakanin ku ba ai ayi hakkuri ta dawo dakinta dai.
Nagode mama ya fada ya mike don zuwa wurin cin abincin da aka tanada suna aje yake fadi da yaren fulatanci a kaiwa Dije nata a can part din mu.
Yan matan nan suka mike suna kwasan wasu kuloli suka nufi can dasu master ya kalli dije yace ku koma can kuci abincin ina tafe idan na gama ni da yaran jin hakan yasa na riga kowa mikewa na fara tafiya dijema ta biyo bayana nasan magana zasuyi a tsakaninsu lokacin.
Amma mahaifin nasa bai basa daman yin wani magana ba a lokacin don ya hana zancen gareshi nikan ba wai komai nake ci ba layin ummah na kira ta dauki waya nake fada mata bayan mun gaisa ai muna shigi jiya da dare.
Tace tun shekaran jiya da dare nake kiran layin ku baya shiga in fada maku cewa jikin Alh ya kiya yanzu ma haka muna asibiti a nan cikin gusau dashi.
Jin hakan yasa na mike zaune daga kwancen da nake ina salati a daidai lokacin ya shigo yana tambayan meke faruwa wayan na basa suka gaisa tayi mai sannu da zuwa.
Nan take masa bayanin halin da Abba din ke ciki amma irin karfin halin hausawa sai cewa tayi ai yaji sauki ba kamar yadda suka kawoshi asibitin ba yake yanzu ai.
Ok da sai jibi zamu shigo amma insha Allahu gobe idan Allah ya kaimu zamu shigo gusau din ummah a gaida muna shi don Allah dije ma tana gaidaku sai mun iso.
Ya aje wayan ya kalloni inda nake kuka yana fadin meye haka kuma kamar baki da tauhidi a zuciyar ki makin ki bisa da addua zaki zauna kina masa kuka haka ?
Master ba dole nayi kuka ba Abbane fa yaushe rabon dana gansa saidai a waya bana manta son da Abba ya nuna min a baya yanzu lokacine da zan dubashi nima yasan ya haifeni amma kuma ciwo yana son rabamu a yanzu dashi.
Haba dai matar Amadi kibar wanan maganan haka shi ciwo ba mutuwa bane manzone na ibada ga bawa mune bamu gane hakan insha Allahu zai samu lafiya.
Yanzun kikaji Abban ku yayi magana a falo yake fadin idan gida baiyi a kaishi waje da yardan Allah zai samu lafiya .
Yanzu ba masu maganin gargajiyane a kasan da ace daurine da ko a na gargijiya an samu maganin matsalan a saukake ba kamar yanzu ba da aka baci da asibiti komai ace asibiti.
Kinga mijin ki gashi da kinsan wani ciwo da ya taba yi a baya ba zaki fadi hakan ba lokacin daga kuraje ya fara har ya kaishi kwance yana yaro.
Duk kauyu kan nan na gusau daya dayane ban taka dashi ba a lokacin don mu samu magani amma abu yaci tura ga mahaifansu bako mutum daya a kusa don a shekaran ne uwarsa ta koma can cikin naija da zama.
Sai fa da Allah ya kawo min wani bawan Allah irin mutanen nan masu sayar da magani suna yawo tsoho dogo haka dashi da dan buhunshi da sanda yana dogarawa a wurinshi ne na sama mashi magani don kamar sihiri ina amfani dashi ya warke sumul.
Tun lokacin kuma ya zamo mai mu,amula da tumfafiya don shine ganyen danayi ta dafa mai a lokacin har nake tunanen ko yana zaton tumfafiyan maganin komai yakeyi da yake yawan debo minshi a daki kamar yadda na baki labarinshi a baya dai da ganyen tumfafiyan.
Wani kallo gaba dayan mu muke mata yada ta daina magana da takeyi din tana kallon mu itama a cikin mamakin kallon da muke mata din tace wallahi tun wanan lokacin nayi neman mutumin na kara amsan wani sani a wurin shi tunda ba mai zama bane ban kara ganin shi ba .
Lokacin tun fa Amadi yana yaro wanan hiran da nake maku a ina zangansa yanzu kuma ta fada a sanyaye cikin bata rai a karshe kai maza sun kwanta dama tare da sanin su wallahi yanzu sai makaryata da yan sheri aka barmu dasu.
Dije wanan mutumin yana yawo da irin buhun nan na dacan goye a bayasa tare da dogara sanda yana tafiya a duduke har ya rankwafa ko ?
Ke ina kika sansa Master din ya katseni da wanan tambayan ita kuma dijen tana fadin kwarai kuwa Allah ya barki haka yake dogo dashi nace da saje farin gemu a fuskanshi ko ?
Tace Allah dai ya barki yar nan haka yake yadda kika kwatantashi din nan sosai wallahi shine har inkinsan shi to shi din daine toni ko yau na gansa a cikin mafalkina haduwan mu kuma na farko dashi a hanyar makarantane da safe na fito zan tafi school ranan muka hadu dashi na dan tsaya ina tunane kafin nace.
Ina ganin that was day da muka fara haduwa ai dakai a school din a ranan na fara ganinsa sosai ranan nan ne na fada ina lumshe idanuwana.
Ke kin sansa ke nan dai na bude ido ina fadin indai shine nasan sa sosai don ko yau din nan saida nayi mafalki dashi da asuba din nan.
Kuma a fili kin taba ganinsa nace kwarai kuwa na fadama a wanan ranan da muka fara haduwa har ka taimaka min a ranan ne na fara ganin shi kuma a yanzu sai nake yawan mafalki dashi lokaci lokaci.
Shiru yayi yana tunane can naga ya mike yana fadin zan je gidansu Nabil yayi aure muna can idan na dawo zamu shiga mu kara tsaraba a nan wanda zamu gida dashi don mutane.
Na gane Nabil abokinshi yake fadi nace ya gaidasu ina mashi fatan alheri ga zamansu kiba babana maganinsa tasha in sha biyu yayi ban dawo ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣5️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Bai dawo gidan ba sai karfe shidda na yamma kuma tare da Nabil din suka dawo a lokacin kuma suka zauna a wurin daddy ashe tare da kaninsa yasir suka fita.
Case sukayi sosai a ranan kan daddyn nasu yaki saka Nabil a harkansa na kasuwanci shine suka sameshi a office dinsa sukai magana dashi ta fahinta.
Ida daddy din ya dorawa Yasir din wasu dokoki daga nan kuma shi yasir din yai fushi yace an tauyeshi da yawa a cikin harkan.
Saida kyat master ya samu ya lalashi mahaifin nasu inda daga shi har ita salima din aka samu inda aka sasu kamar yadda suka bukaci mahaifin nasu yayi masu tun baya yaki don sanin halinsu da yayi.
Suna fitowa wurin yasir din daya kwasheshi sai gidan da hjy yabi take zaune ya kaisa inda ya samu harda yarta suna nan gidan da farko data ganoshi ta firgita da ganinsa tare da jin wani iri.
Amma gaisuwa irin yadda ya gaida ita din sai jikinta ya fara sanyi dashi yace mummy jiya mun shigo na sauka a gida sai na samu baki gidan.
Dana tambaya sai Abba ya nuna min bai son maganan na barsa ne banyi maganan ba a lokacin har sai nazo na ganki don inji ra,ayinki akan hakan .
Don baidace ba ace yanzu kin bar gidan Abba duk dadewan da kukayi tare sai lokacin da hutu da samun natsuwa yazo maku lokacin da yara zasu dauki nauyi ace irin wanan matsalan ya fito a tsakanin ku har abu yakai ga barin gida haka ?
Duk kokarinta naso ta yaba mai bakar magana bata samun fuskan hakan ba gareshi saboda wani irin kwarjini da yaron yayi mata gashi da gani komai ya zaunu gareshi ya waye fiye da tsamaninta zakace shi din ya dade a turai ba danta yasir ba a lokacin.
Ba halin magana a yanzu gareta don hanyar komawa dakinta takeso ako wani hali saboda duniya gaba daya ta bata baya lokaci guda.
Yaci gaba da fadin babu dadi azo gida a samu duk manyan yayan gida babu iyayyensu a gida sai gidan ya koma kamar wani tsohon filin yakin da akai shekaru da barinsa.
Zaki koma dakinki kwanan nan mummy ba tare da an tsaya wani tone tonen abinda ya faru ba har ya kawo wanan matsalan mai karfi a tsakanin ku ba mu dai bukatan mu shine ki koma dakinki ki zauna ku rufawa junan ku asiri dake da daddy zai fi.
Ya mike tare da gyara kwalan riganshi yace zan tafi mummy da fatan ba za a samu matsala daga bangarenki ba sai kin jini yayi masu sai anjima tare da saurin fita daga falon don baison kallon jan fuskokin su kada ya fasa aikin alherin da yake son yi a lokacin kansu.
Don Allah ya gani a lokacin ba karamin dake zuciyar shi yayi ba har yakai ga yin hakan saboda abubuwan sherin da matar tayi mai aduniya.
Amma yau kawai dayaga yayanta a cikin halin maraicin uwarsu sai jikinsa yayi sanyi don yasan irin kuncin hakan duk dasu suna tarema da mahaifinsu a lokacin shiko baya tare da kowama alokaci da hakan ya sameshi.
Ita ko hjy yar hjy yabi kallon yar uwanta tayi tace Yabi kin gani ko kinga rokon Allah mu a inda ya fito muna ta hanyar da bamu zata ba wanan yaron nasan yasan komai boyewa yayi ya nuna baisan meke faruwa ba.
Makirine kamar ubansa ya sani ya nuna bai sani ba koma meye ai ni dai bukatana naga na koma dakina yanzu shine kawai burina a yanzu don ina kwana a zaune ina tunanen yadda murja zata juya min yarana bana gidan.
Ki duba gasu yasir na zaci hakan amma ban samu ba sai gashi wai wanda akai abin donsa shine ya dawo yake son mayar dani dakina a yanzu.
Ni ai yaran nan sun ban mamaki sai kace ba a kansu nake wanan yakin ba shine da su master suka dawo gidan shine ya zauna da mahaifin nasa suka kara zance kan aikin yan uwan nasa dakyat ya samu mahaifin nasa ya yarda har shi Nabil din ma daya rakosa ya samu nasa a lokacin wurin.
Washegari sammako mukayi na tafiya don akwai nisa tsakanin zamfara da abuja sosai muka dauki hanyan zuwa zamfara din cikin motan da nake zaton na daddy .
Muna cikin jeep din yayin da hilux yake bayan mu dauke da kayan mu yaran da basu saba da irin wanan tafiyan ba mai nisa sunyi kuka har sun gaji sai shidda na yamma muka shiga zamfara.
Shehu ya kira a waya ya fito hanya ya taremu shi yayi muna jagora zuwa sabon gidan daya gina a nan garin gidane na gani nashiga tsara a lokacin don ko parking space din gidan zai dauki mota goma sha.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login