Showing 300001 words to 303000 words out of 304363 words

Chapter 101 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33353

UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
1️⃣0️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Alhamdullahi jikin Abba yayi sauki sosai har yana tafiya da kafansa yanzu yake tashi yayi komai ba sai an kamashi bama kamar yadda a baya da ciwo ya kadashi ake masa komai yana kwance.
Yanzu kan Alhamdullahi gaskiya don ko yaushe muna waya dasu muna jin halinda duke ciki a can yauma wayan mukeyi da ummah da kannena da Tani takawo min su wuni a gidan mu.
Da yake weekend ne saina rikesu a nan basu koma ba shine nake fadawa ummah har muke hiran jikin Abba dasu a lokacin take fada muna yadda jikin nasa yake a yanzu mukayiwa Allah godiya.
Sosai muke kama da yar kanwata don kamarmu ya baci duk dakin mu mu hudu zubin mu daya mu matan kamanin mu ya fito sosai a fili.
Zaune take ta manne min a jikina tana game da dayan wayata dake hannunta mazan kuma suna kallon season film na cartoon a mbc ya shigo falon dawowanshi ke nan don ranan sokoto suka tafi yin wani harkalla ta business da abokinshi doctor Hamza.
Wanan da ganin ki haka mamata tashi nasan a lokacin tana karama itama da son jiki to daga kada ki danne min mata ki kashe mata jiki.
Yarinyar ta dago kai ta dan kalleshi tana dariya ta mayar da kanta a wayan taci gaba da game din hankali kwance kafin can ta dago tace dashi sannu da dawowa yaya ta kara mayar da kanta ga abinda takeyi a lokacin.
Yace ikon Allah komai iri daya wallahi har da kallon da shagwaban duk irin daya komai sak babu bambambaci lokacin na dago nace aini baka sameni lokacin da ake shagwabani ba.
Don koda muka dawo garin nan duk mama ta barar min da gwaunatina a wurin Abba saidai ummah a lokacin amma ai da ni yar gatace sosai gun Abba don da ya dawo zai fara fadin mamana ina mamana sai na fito ya ganni zai zauna.
Amma haduwan mu a nan zamfara dasu mama da muka dawo wuri daya shine ya bata komai gaba daya saida mama taga gwaunatina ya kifa a gun Abba ga baki daya.
Master yace ni tayiwa kafen bata sani ba da tasan cewa haka Allah zai juya al,amarin nasa da bata yarda ta aikata kuskuren da tayi take ganin kyatane a gareki ba.
Allah kanyiwa bayin sa wani baiwa da bawa zai dauka a lokacin ko Allah baya sonshine yayi masa hakan amma a wurin ubangiji wani tanadi na alheri a rayuwansane ya tanadar masa.
Mugunta da hassada ga bawa takine mafi yawan lokaci yana zama alheri sosai ga bawa tayi hakan ne a lokacin ganina Fakiri kamar yadda naji hjy tsohuwa ta kirani sau biyu da wanan sunan a gabana tana fadin fakirin mijin ki.
Dago kai nayi na kallesa yace kwarai zahra nasan komai wallahi duk da baki taba nuna min hakan ba nasani kuma naji saidai hakan baya damuna don lokacin duk haduwan mu da mahaifiyan ki ko a waya addua take min na fatan alheri a rayuwan mu.
Wanan addu,an har gobe har jibi kuma bata fasa hakan ba garemu yasa ban ganin kamar ummah da dije a zuciyana nina kasace irin mutanen ne da suke son ko meye suji addua ga bakin mutum zuwa garesu.
Na sani zahra nasan komai harma da wanda baki tsamani na sani ba alokacin don yanzu zancen duniya baya boyuwa duk ko da kokarin da kikeyi na boye min hakan .
Kin fuskaci matsala sosai a sanadiyar aurena da ake ganina fakiri ke diyan attajiri amma kuka shanye hakan kuka daure dake da mahaifiyar ki kuka zauna dani a cikin tsiyar tawa hakana.
Yau ya Allah yai ikonsa a kan mu mutane basu ganewa idan kaga mutum ka barshi yadda ka gansa don bakasan ajiyan da Allah yayi a nan ba in kasan yau bakasan gobe ba ga bawa.
Har gobe har jibi idan na tuna da yadda akai bukin mu ina jin zafi da bakin ciki a zuciyana irin yadda mama tasa akai ta nuna muna wullakanci zance a wurin daurin aurene kadai ba a samu wani matsala daya shafeta ba akayishi kamar yadda addini ya tanada a lokacin.
Zamuyi weedine anniversary din mu kafin mu koma ina son in nuwa wa yan uwa da duniya yadda kuke da muhinmanci a gareni.
Dariya ya bani yace yes idan lokacin anyi banda zarahi a yanzu Allah ya hore min abinda zanyi wanda yafi nasu a lokacin ina son in godewa Allah wanda bai sani bama ya sani yanzu Allah ya horewa fakiri.
Master da hakan ai kamata yayi kayi sadaka a inda ya dace ayi din garin nan muna da gidajen marayu ba iyaka da wanan abin ai saikasa a bincika ma gidaje a kowani unguwa ko gida biyar biyar kaiwa hakan alherinshi yafi wanan da zakayi din yawa.
Nasan da hakan saidai alkawari na daukarwa kaina cewa idan na samu halin zan aiwatar da hakan gareki don haka ki barni inyi don Allah tunda nayi niyar yin hakan akan mu.
Aisha ce ta fito tana fadin yaya dazun inna ta bugo waya wai tana neman ka idan ka shigo in fada maka kaje tana bukatan ganin ka ya dago yana tambaya da lafiya ko tace wallahi ban sani ba haka kawai mukayi dashi.
Kallon inda nake zaune yayi da alaman tambayan lafiya ko anyi wani abune bayanshi daya fita kai na dan rausaya alaman bansan komai ba nima.
Ok idan na fita zanje naji ko meke faruwa don nasan dole akwai wani dalili dayasa suke nemana din yana fadin hakan ya mike ya shige ciki ya barmu a falon akaci gaba da hira har dije ta fito tasame mu a wajen.
Sai da akayi magari ba ya fito yana fadin a Junior kanina baku tashi kunyi alwala ba muje jam,i lokacki yayi kada mu rasa jam,i kuyi sauri ina waje ina jiranku.
Yaran suka tashi da sauri sukabi bayanshi zuwa waje inda zasuyi alwala koda suka dawo takwas da rabi ya wuce a lokacin don haka suka zauna cin abincin dare da gamawansu sai kwanciya don sun saba da saurin kwanciya babu hiran dare sai barci.
Washegari bayan mun karyane ya shiga ya shirya yace zai fita ban damu da in tambayesa ba nayi masa adawo lafiya yace amin ya fice daga gidan ya barni da kannena a gidan.
Inna zaune da wata kawart da tazo amsan bashi a wurin inna din matar cikin daga harshe take fadin na fada maki Rashida yau ban barin gidan nan sai kin ban kudina na gaji da yawon hanya hakana.
Sallama tayi ya shigo yana binsu da kallo nan inna ta fara dan kame kame tana fadin kije anjima ki dawo aini nace ki dawo anjima ko saratu.
Allah ya kaimu ta fada a dan hasale tana kokarin mikewa sai yace mama nawane kudin ki don Allah ya fada yana tura hannu a cikjn aljihun wandonshi lokaci guda.
Dubu biyarne ba wasu masu yawa ba amma ta kasa bani kullun tana sani yawon hanya da kashe kudin mashin yi hakkuri mama ga wanan kudin bashin ne wanan kuma dubu gomane kiyi hakkuri dashi ban fito da kudi ba yanzu.
Kai dan albarka wanan bakon arzikin naku ai alherine ga kowa ni Rashida kin sani ba son fitina nakeyi dake ba dama dan jarin nan kadan kema sai in mun sayar muke hada kudin mu karo wani man gyadan .
Ya kara fadin kiyi hakkuri mama don Allah ya wuce dakin dije ya shiga kai tsaye ya jawo kujeran roba ya fito dashi ya zauna.
Nan uwar ta fara dan kame kame a cikin kunya tana fadin mutane kamar jira suke a taba kayansu suciwa mutane mutunci kan abinsu.
Ina kwana ya fada a sanyayye ta amsa mashi da fadin lafiya taci gaba da mita yace Aisha tace kinyi waya kina nemana na tafi sokoto a jiyan kuma na dawo shine take fada min.
Eh dama na kirakane kan muyi magana don kasan yarinyar nan suwaiba ta fito daga gidan mijinta akanka shine ubannanta sukayi min magana da sukaji kazo.
Don a san abinda za ayi tunda yanzu ba budurwa bace ita auren bazawara basai anyi wani shiri ba aure za a daura kawai.
Baiyi magana ba saida ta gama masa bayani ya dago kai yace inna nayi da wanine cewa zan kara aure ko kuma ita suwaiban tace ni Ahmed na taba fadin ina sontane ko nayi hakan da wani.
Kai dan dije dakata nasan dama baka daukeni uwa gareka ba don kana min kallon matsiyaciya kana kunyan ka nunani a matsayin uwarka.
To bari kaji ni yanzu umurni nake baka bawai shara ko ba,asi na kiraka inji daga bakika ba yar yar,uwata nake baka umurnin ka aura banyi alkawarin da kowa zan kara aure a yanzu ba.
Ko matana ta farko duk da nake yaro ninayi shawaran yin auren kuma na aurar da kai ba tare da wani ya saka min ko kwandala ba don haka duk sandana shirya kaina zanyiwa aure na zauna da ita ba wani ba.
Kuka ta saka mashi tana fadin maganganu marasa dadi a gareshi mikewa yayi yana fadin Allah ya gani inna duk wani biyaya da Allah yace aiwa mahaifa ina makishi gwargwadon yadda sharia ya kidaya muna.
Amma baki gani hakan kullun sai abinda zai daga min hankali kike nema yi a gareni inna ji yanzun abinda nazo gidan nan na sama inda kina kama girman ki mama ai wanan matar bata isa a yanzu tace zata kalleki ta fada maki maganan banza ba balle daga murya a gareki kan dubu biyar saidai ace.
Tazo gidan nan nema a wurin ki badai karban bashi ba mena rageku dashi don Allah da kike zubarda mutuncinki haka a cikin mutane yakamata ace kin godewa Allah yanzu saidai mutane suzo wurinki karban taimako a yanzu.
Mukus tayi tabar kukan da takeyi kafin tace to ubana fada min magana tunda yanzu kana ganin kanmu daya dakai wanan yasa raini ya shiga tsakanina dakai har baka daukana uwa tunda ban isa ince kayi abu kayisa ba.
A,a wallahi babu wanan ranan da zaizo insha Allahu da har zan dauki kaina daya dake ko kuma naki jin maganan alherin da zaki dorani a kai aure daine nace ba zan wa zahra kishiya ba a rayuwan zaman mu don zahra bata rageni da komai ba a zaman mu na duniya.
Duk abinda da ake nema wajen mace inna kinsan zahra tana dashi tome zan nema a wurin wata da har na rashi a zahra aida na zama butulun namiji a duniyan nan.
Lokacin Asmau dake labe cikin daki ta kasa hakkuri ta fito don dama bashin itace taje ta ciwo take gudun matar jin muryanshi ya shigo kuma yasa ta labewa don kada ya gane bata bar gidan ba dayace tayi din.
Ganin Asmau ta leko yaba inna kwarin gwiwan fadin rufa min baki sallamame banda farin meke rudin ka a cikin ta yace inna a naki zaton ke nan.
Duk na miji da mutumin kwarai zaiso zahra ta kasance uwar yayanshi tavkuma zama mashi adon gidan shi saboda idab tarbiya ake nema zahra tana dashi ilimi asali natsuwa kyau uwa uba haduwa duk zahra tana dashi kin sani.
Shin inna ba zaki tayani son zahra ba kamar yadda ita yan uwanta suke sona tsakani da Allah inna kowa na zahra yasan baki sonta a gidan nan ban dauka gaskiya bace sai yau din nan da kike son tarwatsa muna zaman lafiya da matata inna ?
Sherin kuma zaka kullamin yanzu don kawai nace ka auri yar uwarka dake mutuwan sonka tun kurciya idan tana sona ni bansonta inna don ko banza Suwaiba ba irin macen da nakeso bane a rayuwana ba.
Don haka kada a kara min wanan zancen don Allah don gaskiya idan an kara rayukane zasu baci sosai a lokacin ya dogo ya kalli Asmau kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya fice daga gidan kai tsaye.
Amma inna lalai yaya ya daukeki tallaka don yaga baki boko ba baki da kudi kuma yasa yake nuna baki isa da sh, , , ,
Shiru tayi tana kallon kofan shigowan shine a tsaye don ya manta bai rufowa dije kofan daya budeba wanda yanzun kayan Aishane a dakin da sauran tarkacen dije.
Ya tuno yasan kuma idan ya barshi a bude banu mai rufo mata shi hakan yasa ya dawo gidan ya mayar da kujeran a dakin ya rufo mata dakin nata.
Shine kuma ya samu kanwar tasa tana magana a kansa yanzu ya tsaya yana sauraren abinda take fadi baiyi magana ba dakin dije ya shiga ya mayar da kujeran ya fito.
Kara kallon Asmau yayi ya fice gidan kai tsaye yau ko na shiga uku Asmau ta fada me zai maki ai ba zaice komai ba tunda yasan ba zan barshi ba.
Saidaya gama abinda ya fita yi ya dawo gida bai jima da shigowa gidan ba akayi masa sallama ana fadin ga masu nama nan sun kawo ya fita .
Ya samesu ya kasa yadda za ayi da naman yasa aka shigo muna da sauran a ciki yake fada min ga namanan ya turawa inna nata ya kuma sa ankai gidan mu amma anyi kulli biyu na mama daban yace aba Tani na ummah ta gyara masu.
Aiko angode wanan dawainiyar baiyi yawa ba kuwa har yajuya zai tafi sai ya juyo don jin abindana fada a lokacin cikin mamakin kalamin nawa yake fadin .
Zahra ni wani dawainiya nayi haka da har kike ganin yayi yawa ga mutanen da suka dauki yarsu suka ban a matsayin abokiyar rayuwa .
Wanda nake alfahari da kasancewa hakan a yanzu zahra duk wanda yace min bakeba nima zance bashi ba kowaye kuwa yayi gangancin fada min hakan a yanzu sai inda karfina ya kare a wurin yakar maishi.
Ke daya aka kawo gidana gashi yau ta sanadin ki mun koma mu hudu gana biyar nan din mu nan ubangiji yana shirin kawo muna in Allah ya yarda.
Lumshe idona nayi ina maijin dadi ga irin maganganunshi gareni da kullun yake nuna min shi ba butulu bane a cikin maza yasan anyi masa an kuma kyautata masa a lokacin da baida shi da ya kamata ace munyi masa.
Inna na gida zaune da yamma su baffa sukayi sallama taji mamakin ganin yan uwan mahaifinsu suku gaba dayansu lokaci guda haka dole tasan wani abune ya kawosu gidan a lokacin.
Shimfida tayi musa take suka gaisa tambayansu tayi ko lafiya babban nasu yace ai tunda kika ganmu balafiya ba don yaron nan Amadine ya samemu gida da wani zance mara dadi akanki da yarki.
Allah ya baki da dan albarka da kowa ke fatan haihuwan irinsa a duniya amma kina son ki halakashi da bakinki don wanan yar taki mara hankali tana zugaki.
To munzone mu fada mata idan mun isa dake ko tayi aure hakana ko kuma ta kwashe kayanta ta koma gidan ubanta tunda baku da hankali daga ke har ita.
Kuka inna ta fara tana fadin maganganu ya kara fadin saiki matsa kiwa kanki baki a kan wanan yar taki don kina takaman kin haifeshi.
Sukai mata kaca kaca don bai boye masu komai ba hankalinta ya tashi jin yace dama saboda ita muke zaune a nan idan ta matsa mashi zai sayar da gidan ya koma wurin mahaifinsa da zama.
Wanan yasa muka samu sauki akan inna tazo har gida ta taso Asmau ta bashi hakkuri itama din kuma taba nata mahaifiyar hakkuri akan ta daina irin halaiyanta.
Allah da ikonsa Abba ya dawo saman kafansa da lafiyansa saidai babu karfin jikin sosai kawai za a ce Abba ya dawo yana sakawa master albarka dashi da yan uwanshi.
Mun wuni a gida tare da ummah don munje taron Abba da dawowa ranan a can gida muka wuni ana nuna muna gata da zalla kauna.
Ina can ne master ya bugo min waya yana sheda min zancen komawa da zaiyi washegari don aikin daya taso masu a lokacin dole zai barmu a nan din ya tafi don shima yasan bazan bishi haka a gagauce ba.
Hakan yasa na dawo gida don tafiyan nasa na hada mashi kaya duk da hakan saida ya gwada cewa mu tafi a tare zaifi masa saukin amma kafin nayi magana Dije ta bashi amsa da haba Amadi .
Ka barsu nan wanan karon ta haihu a gaban iyayyen ta da yan uwa inyaso daga baya sai kazo ka daukesu ku koma zaifi tunda yanzu kaga cikin nata ya tsufa sosai ai zata iya wahala a hanya.
To dije yadda kikace hakan za ayi don nima ba dadewa zanyi a can ba in dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login