Showing 177001 words to 180000 words out of 304363 words

Chapter 60 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33349

mana sai naji tace innalillahi auren kufa baiko cika wata takwas ba sosai nace ba a haihuwa hakane wai hakamafa master yace min da nake fada mai zancen haihuwan.
Wallahi akwai rikici har in yar nan ta rayu don ko saidai idan da cikin tashiga gidan dama nace don Allah kibar zancen nan wani iri nake ji a zuciyana tace na bari amma dai akwai magana gaskiya.
Bari na kira ummah naji na fada sai naji da sauri tace min ki rufawa ummah asiri don Allah don baki san dasuwa take ba yanzu tunda haihuwane.
Muka dan taba hira can naji motsinshi ya tashi ya shigo dakin nayi mata sallama ina cewa ka falka ke nan yace wallahi nagajine ga zafi kuma koma na tayar da injin din nan ne yanzu ?
Da darefa idan ka tayar yanzu yace saina nemi kudin wani mai mana a saya nace ai kaji zancen muje falo kawai ka kwanta nayima fifita zaifi.
Da sauri ya juyo yana fadin wa ki rufa min asiri kada anji ki kaini asibiti kuma kice ba lafiya ai gara naje darbejiyan malam Tanimu insha iska zaifi.
Ni kumafa na fada cikin gatse yace shine kuma ai to mu zauna din ta waje amma gaskiya zafi nakeji sosai wallahi aiko da mamaki son yau gaskiya ba zafi yadda kake nufi na bashi amsa mu kafita na dauko center carpet dina na shimfida muna muka zauna a dan barandan mu akwai iska sosai a wurin dake hurowa daga baya ta inda dabbobinsu suke.
Barci ya samu sosai ni kuma ina aikin girkina inayi ina dan dubashi har lokacin da na kusa sauke girkin nawa din duk yana kwance yana barci son sanyin wurin.
Ina mamaki a raina don ban taba ganin shi yana barci ba haka da rana irin wanan ranan don hakane abin yake ban mamaki.
Na fada maku ku kwantar da hankalinku indai wanan aikin ne ba a wuce sati biyu insha Allahu bukata bai biya ba irin hakan.
Tunda har kunce ya fara kiranku alama ya nuna aiki yana kyau ke nan insha Allahu saidai mu jira muga ikon Allah yanzun kam.
Har in bai kiraba yau zai kiraku zuwa gobe da yardan Allah son duk inda yake yanzu shima a matse yake cikin kunci don aiki ya fara aiki a jikinshi sunan Allah aiba wasa bane.
Hakane malam musa ai don shine mukazo yanzu mu fadama abindake gudana jn akwai wani sadakan da za a karayi sai mu bayar ayi muna akai.
Kai ya girgiza masu yana fadin kwandala naku na fada maku banso cikin zancen nan don nima ina son in samu ladan da zaku samu ga wanan niyar don nima alkawari na daukarwa yaron.
Godiya suka kara mai sukayi sallama dashi cike da mamakin shi gashi dai bako a garin amma bai hurda da kowa akace sai makwabtanshi da suke dan gaisawa dasu amma kuma yana da halin kirki.
Ba laifi suma basu zauna ba don suna da dan rufin asirin su daidai gwagwado hakana saboda basu zaunaba akwai sana,anyi ga kuma kiwo da suka dukufa gayi har yanzu dama ba a raba bafilace da kiwo.
Kamar abin almara wayan Alh jauro ya dauki kara yasaka hannu yana laluben wayan ya duba kamal farko da tafito mai a bakinshi shi Allahu akbar kunga dan halas yana kirana yanzu.
Waye suka tambaya yace dangaske wallahi shine ke kirana da sauri dayan yace kaga kada ka nuna mai muna tare don na fahinci baison muji maganan.
Ya dauka suka fara zolayan juna da fadin kai jiya da yaukan naci da fari wanan amini yana tunawa dani yace ko yaushe ai ina tunawa daku ban manta da kuba.
Jiya muna magana wayan ya katse dan gasken ya fada hakane na dauka aikai ka kashe wayan yace saboda me nidana kiraka zan katse yanzu dai munyi maganan kai tsaye kaji damuwana.
Wallahi jauro na fada maka ina cikkn matsala sosai kwanan nan in gajarcema dai wani bakon yanayi ke shiganaga don na kasa fahintar ko wani yarone nake yawan mafalkinshi kwanakin nan sosai.
Don a iya tunanena na tuno sosai ko akwai yaron da muka taba zaluntane muna yara ke neman hakinshi a kaina naso ace kana tare da yan uwa a yanzu ko cikin ku akwai wanda zai iya tuna wani abu na kurciyan mu.
Jam Jam yaro kuma yaro wa muka cuta irin haka da har zai dinga dawo maka yanzu a rayukan ka kaiko dangaske saidai in wani abokin aikin kane nan ?
Abin ya daure min kai sosai jauro naso ace kana kusa dasu bande da Jabbo ko Allah zaisa su tuna wani abin na baya da mukayi.
Aiko ina kusa dasu na tashi amma barin samesy in masu bayani sai na sake kiranka yana fadin haka ya kashe wayan.
To masu karatu ku farga da iri haka ku kula idan zaki wayan siri ki natsu ki fahinci da wanda kike waya idan abin na boyene kisan abin fada don baki san wanda ke kusa da maishi ba a lokacin.
Don hakanne ya kasance ga Alh dan gaske da ace wani abu mai muni ya fada game da sauran da sunji a lokacin sai aka samu ya nuna taimakonsu yake nema gaba daya a lokacin.
Jin hakan yasa su jin tausayin dan uwan nasu don sunsan irin halin da yake ciki a lokacin nan sukai shawara kawai su fada mai gaskiya inda Jabbo yace su bari shi da kansa zai mashi magana idan ya bugo.
Hakan akayi lokacin da suka idar da sallah la,asarne suka samu wuri a natse suka bugawa layinshi ba bata lokaci kamar yana jiran kiran nasu lokacin ya dauka sai yaji muryan Jabbo a layin yana magana.
Suka gaisa akai ya kwana biyu nan yake tambayanshi ko yaji sakonshi wurin jauro yace eh shinema dalilin kiran naka yanzu don ka kara muna bayani da bakinka.
Yadda ya fadawa Alh jauro haka ya karanto masa shima yai shiru yana sauranren shi cikin tausaya masa sosai a fili sai bayan ya gamane yace dashi ina fatan kana saurarena kaji mezan fada maka.
Ni a tunane da kuma abinda muka hango wanan mafalkin naka yana nunine ga danka daka watsar a cikin duniya ko zaka iya tunashi yanzu ?
Idan baka manta ba tunda ka barshi ka dawo mambila ban tsamani ka taba tuna wanan yaron a rayuwanka kuma alhalin kasa dankane na cikin ka.
Cak yaji kamar ana zare mashi numfashi lokaci guda hankalinshi yana kokarin gushewa a jikin shi a haka wayan ya fadi a hannunshi ba tare daya sani ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
6️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,


Daidai lokacin da nazo gittawa ta gefen shi sai gaji nayi ya zabura da karfi kamar wani abu yabi ta saman kanshi yasashi tashi firgice har saida na tsorata daga inda nake nakai kofa na tsaya ina kallonshi
Ya dan kama wajge waige kafin ya mayar da kanshi kasa na dan lokaci can kuma ko ya tuna cewa ina wurin ne sai ya dago ya dan kalleni.
Lafiya dai na tambayeshi ya girgiza min kai tare da fadin ba komai anyi sallah ne nace da dan saura lokaci sai naga ya mike ya shiga daki .
Ruwa ya watsa ya dauro alwala ya fito ya tafi massalacin yayi sallah daga can ya wuce zuwa kasuwa ya karaso sayayyan su ya dawo .
Ina daki don ni nasaba da zaman dakin idan ba wani abu ya fito dani waje ba lokacin ko yaushe zaka sameni a dakina zaune .
Indana gane ya shiga kasuwa ledan da nagani dauke a hannunshi lokacin yasa na fahinci hakan wai ashe tsaraba ya sayo da zamu kaiwa kannena a gida.
Saida ya fara cin abinci yake fadin anjima saiki shirya muje gidan mu gaidasu kafin intafi don in tafi zuwan zai zama maki matsala kuma.
OK yau din zamu tafi ke nan na fada ehmana ko zaki iya hawa mashin din garba zuwa ya tambaya yana kallona don kinga yau din idan mun tafi tare nima sai in samu in masu barka ai.
Hakan nada kyau kuma zanji dadin hakan mashi kuma me zai hanani hawa tunda sunsan ba mota muke dashi ba dama ba kunya a cikon hakan ai.
Nasan ke yanzu baki jin kunyar hakan gaskiya amma ummah ba zataji dadin ganin mu haka ba ai ita ya fada a cikin wani irim murya mara dadi nace baka ko fahinci ummah ba har yanzu gaskiya.
Zahra irin wanan dalilin yasa kikaga ina jajircewa ga karatun nan don mu samu abin rike kammu nan gaba dana iyalin mu masu zuwa don kada ki fito daban a cikin yan uwa.
Ka daina irin wanan tunanen don Allah Allah fa bai manta damu ba master ko yaushe kaga bawa a wani hali yana sane da rayuwanshi ko a hakan mungode ai in anfimu mu kuma munfi wasu ai.
Hakanane wallahi irin wanan halaiyar naki zara ke kara kwantar min da hankalina da ace ni wanine zahra ba abinda zai hana banyi sharia da mahaifina ba don a yanzu shidin wanine a cikin kasan nan.
Wananne rana na farko daya sako min zancen mahaifinshi a hiran mu duk zamana a gidansu dan haka da sauri nace don me zakayi sharia dashi kaiko ?
Don an tabo min inda ke min kaikayi saboda na kasa gane zancen mahaifin nasa gaba daya har nakanyi konkwanto ince waiko dai zancen mutane akansa gaskiyane wani lokaci.
Sai naga ya girgiza kai kaiwa cikin takaici ba tare da yace min komai ba a lokacin yaci gaba da cin abincin shi yana tunane a zuciyarshi lokacin.
Nima dai tunanen nakeyi na cewan da yayi mahaifin nasa wanine yanzu a kasan nan don me ya fita batun danshi mutum kamar Ahmed ace baya tare da mahaifin shi.
Wai a ina matsalan takene nasan dai matsalan ba babba bane don da babbane yadda ake fada Abba ba zai yarda ya aura mashi niba haka duk da naji su mommy na fadin ba haka a banza Abba ya daura min aure da Ahmed din ba ai .
Akwai shige da ficen da wasu bangare sukayi aka fitar mai da hankali don a tozarta ummah dani a idon mutane koma meye nidai nasan ina son mijina sosai.
Muna idar da sallah magariba muka fito cikin shirin mu na daiji yanacewa Dije zai kaini gida mu gaidasu bai fada masu yar uwata ta haihu ba don haka nima naja bakina nayi shiru.
Har zamu fita naji yace yar uwantace ta haihu zamuje barka Dije ke fadin madalla karuwa aka samu ashe to muna masu barka ita kuma inna sai cewa tayi.
Kaji mata masu biyan bashi ba akawo a cinye a juye a masai ba kullun mutum na kiwo ana zama kamar bata kiwo a gida ko dabbobi keci haka ai suna biyan maishi.
Nagane nufin ta sosai amma ban nuna hakan ba don naji Dije tace aikowa yaci bashi da niyar biya yake dauka Allah ya horewa kowa ya biya da hannunshi sai naji ya lalubu hannuna alaman mu tafi.
Mukai masu sai mundawo muka fice daga gidan yana jaye da mashin dinshi da yake shigowa da ita har cikin gida saboda tsaro.
In kuma dare tayi zai jawota zuwa part din mu ya tura cikin kitchen din mu a kulle idan kuma zai tafi school dakin Dije yake ajewa duk saboda tsaro.
Ya tada mashin din na hau yafara tafiya sai naji yace irin wanan halin na inna nadaga cikin abinda yasa nake son barin gidan nan zahra duk abinda ya faru da ita kwanaki bata daddara ba har yanzu.
Wai kwanaki kinsa uwar garke ta taba ita kuma tayi mata irin waibuwan su na dabbobi amma har yanzu baisa inna ta daddaraba ga halin ta ji wanan maganan da take fada yanzu don Allah .
Me uwar garke tayi mata na tambayeshi a gagauce kovya mantane ya shiga labarta min abinda malamin da aka kaishi wurinshi ya fadamasu.
Ai dabba taiwa rashin mutumci wanan uwargarken akuyan namu tunda kinsan in dabbata kosa tana da waibuwa akace shine nan ta rikide ta bata tsoro a dakin tunda bata tausaya mata ba.
Daga bayan mashi nace what da dan karfi sai lokacin yagane katobaran da yafarayi yace ke bafa wai ita din aljanna bace ko wani abu ita din a,a wani lokacine dai sai aljannu su shiga jikinsu su yiwa mutane abinda zai basu tsoro idan sunga ba daidai ba sai su tsorata mutum shi nake nufi.
Ai bansan da cewa tsoro yasa nayi mai wani danka ba a lokacin daga baya inda nake zaune nayi shiru yana magana banma jishi ba son tunanen da makeyi a lokacin.
Zahra fa ya ambata da dan karfi firgigit na amsa mai yace ina hankalin ki yaje kuma ina magana kefa kin faye tsoro wallahi wanan maganan ina abin tsoro a cikin sa kuma ?
Ba zan kara kaiwa dabbobin nan abinci ba ko wani abu ko inda suke ba zan kara kallo ba gaskiya sai naji ya kwashe da dariya yana fadin banda abinki ai kyautatawan da kike masu zaisa su ganeki su san kamshi ki da muryan ki ko wani lokaci.
No a dai bari kawai kaima da kake kyautata masu baisa sun bar mahaifiyarka ba ai balle ni bakuwa a cikin ku dama idan ina gida naga rana yayi nakan kai masu ruwa in zuba masu abinci son naga Dije ke wahala dasu yasa nake hakan.
Don Allah kici gaba duk na sani wallahi su kadai na gada daga kudin mahaifina daya barmin shiyasa kikaga dije na kulla min dasu yanzu kuma gaki kin karbeta zakice kin daina kuma princess ?
Nifa tundaka fadi hakan tsoron su nake ji yanzu kuma gaskiya tunda mutum ba sanin ya masu laifi zaiyi ba kai ina ilimin ki ya shiga kike wanan maganan haka nimafa bawai na yarda da wanan maganan bane kawai dai abinda mutumin ya fada nake fada maki.
Daidai lokacin muka kawo kofan gidan mu ya faka na sauka a hankali muka kwankwasa maigadi ya bude muna kofa muka shiga muna gaisawa dashi.
Duk da yana ganin duhu a lokacin babu abindake fita bakinshi har cikin zuciyar shi sai kalman innalillahi baiyi aune ba yaji hawaye yana zubo mashi a fuskanshi lokaci guda.
Tabbas yasa yana da yaron daya haifa da matarshi ta farko Rashida basulluba yar zamfara da sukai aure na saurayi da budurwa a lokacin da yabar gida a baya can da kurciyarshi.
Ada can baya yana yawan tuna yaron yana kuma da sha,awa ya daukoshi ya dawo kusa dashi ya zaune dashi ya tashi a gabanshi amma sannu a hankali zancen yaron nasa gaba daya yafita a zuciyarshi.
A baya yana tuna yaron amma sai yakanji kiyayyan yaron da uwarshi da tan uwanta ya ziyarci zuciyar shi a irin hakane har yaji kwata kwata yaron ya fita a zuciyashin baki daya.
Shaf ya manta da zancen shi ga baki daya sai gashi lokaci guda a yan watanin nan ya fara mafalkin wanan yaron da baisan kowaye ba sai bai kawo cewa wanan dan nasa bane ruhinshi ke bibiyan shi a yanzu.
Amma yau zancen abokan nasa ya tunasar masa da hakan ko yana raye ko yana mace yanzu Allahu ya alamu don baisan ta inda zai fara nemanshi ba yanzu.
Tunda an yamusa garin a yanzu an maida ita jaha mai cin gashin kansa itama yasan a yanzu ba Gusau din da yasani bane a baya don zasu samu cigaban zamani.
Kai anya kuwa yaron nan yana raye shekara ashirin da takwas amma har yanzu ba wanda ya waiwayi juna da yana raye yasan malam ladan nada wayayyen kai dolene zai nemishi akan yaron don ko lokacin bawai iyayyen Rashidan na ainihi suka bijirewa zuwanshi da itaba nan yan uwan haihuwan iyayyen ne suka kawo wanan matsalan.
Duk da yasan yana son Rashidan a lokacin yadda yake ji a jikinshi don kiran da akaimai gida na asiri ba zai iya dakatar da tafiyan nasa ba a lokacin.
Don kirane na gagauce a duk inda yake a lokacin dole sai ya dawo gida ko babu shiri kamar yadda lokaci guda suka turashi cikin duniya ba wanda yasan inda yake hakama wanan karon aka kirashi ya dawo gida ba shiri.
Idonshi ya runtse a cikin takaici yana maijin zafin faruwan hakan a rayuwanshi why da abubuwa suke zo mashi a hakane cikin rayuwanshi kadai.
Yasan ya dawo gida da niyar komawa ya dauko iyalinshi a lokacin amma sai abubuwa suka faru da yawa bayan dawowan nasa har yakai ya manta da zancensu a zuciyar shi.
Oh lord ya fada a fili tareda furta Astangafurallah Allah na tuba ka yafemin kada ka kamani da wanan babban laifin dana aikata a rayuwana.
Yasani iyayyen Rashida da yan uwanta ba wasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login