Showing 249001 words to 252000 words out of 257873 words

Chapter 84 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

526

basuji zuwansu bama oho?

Anty Amina na matse ido tacewa Zulaiha bari taje,
"Ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai zaizo da sauƙi bari naje muga yanda za'ayi" cewar Anty Amina Zulaiha dake kuka ta ɗaga mata kai. Anty Amina na fita itama Zulaihan ta canza kaya ta bar gidan cikin tashin hankali, dukda rana ce amma mutane sun cika bakin layin anata mayar da magana kowa da kalar nasa narration ɗin dukda babu wanda ya san mai ya faru.

Bayan fitar Anty Amina a hanya ta kira mijinta ta gaya masa abinda yake faruwa ya tambayeta station ɗin da suka tafi tace bata sani ba amma ya kira Abubakar daga nan ta wuce gidan Baba Sani dan tace ba zata iya kiran Alhaji Aminu ko Yaya Alhaji ba kamar yanda Abubakar yace ta san ma da wahala Alhaji Aminu ya saurareta har gara Yaya Alhajin dukda shima ranar daya je duba Hajja tana kwancen haka ta ringa zaginsa tace wai dashi aka haɗa baki aka cuci Fadila ya san ba mutumin kirki bane amma ya bari ya aureta.

Duk irin ƙoƙarin da su Nasir da Mijin Anty Amina sukayi akan a basu belin Bilal abu bai yuwu ba kamar yanda suka ce gobe za'a turashi kotu dan haka su nemi lauyan da zai tsaya masa kawai.

Cike da damuwa Zulaiha ta kalle Alhaji Mudan, tsohon saurayinta ne kuma babban mutum ne mai faɗa aji. Gurinsa ta tafi ta roƙe shi akan ya shiga maganar ya fito da Bilal; kai tsaye ya kira CP kuwa yace ya bashi lokaci zai bincika ya kira shi sai bayan Magriba Alhaji Mudan ɗin ya kirata yake gaya mata sai dai tayi haƙuri for babu dama amma sunce gobe za'a kai shi kotu zai ga duk abinda zai yuwu a kotun kada ta tayar da hankalinta.

"Abinda kuka kasa ganewa kenan ku tsallakemu ku auri yaran da yawanci banda ɓacin rai da damuwa babu abinda kuke tsinta a auren nasu. Duk yanda akw ciki you keep me update, dukda zanyi tafiya goben amma idan kin kira layina baki samu ba ki kira Bashir duk abinda ake buƙata zai yi" Alhaji Mudan ɗin ya faɗa mata tayi masa godiya kafin ta kashe wayar tana sharw hawaye.

Ummansu da ta gama jin komai tayi tsaki tace
"Aikin banza aikin wofi, haka kawai kika nace sai shi ba yanda banyi dake ba tunda mun rigada mun gama cin moriyar ganga mu yar da fata mu huta kika ce ke ba haka ba yanzu tun ba'aje ko ina ba gashi nan, na ma rasa wane munafukin ne ya kawo zancen unguwar nan ɗazu kina fita Usainar Hadi ta shigo wai daga gidan Larai take taji ana zancen an kama mijinki wai ashe ɗan damfara ne. Tunda zance yaje gidan Larai kuma ai duk Kano ta ɗauka dama cike take da baƙin cikin Allah ya rufa mun asiri kun tashi lokaci guda."

Zulaiha dake jan hanci tace
"Amma Umma duk duniya dai kin san ba zan taɓa samun mijin da zai so ni saboda Allah ba kamar Bilal. Kina kallo duk abinda ya faru amma ya karɓeni a hakan muna zaune sau ɗaya bai taɓa nuna rashin amincewa ko zargina ba kina zaton da ace ba shi na aura ba da yanzu ban dawo gidan nan ba?"

"Yawon kika cigaba dayi ko me?" Umman ta tambayeta tana dafe ƙirji, tana goge fuska da hijabi ba tareda ta bata amsa ba ta shige ɗaki. Da shirin wanka ta fito, ta shige banɗaki ana idar da sallar Isha'i ta cewa Umman zataje ta kaiwa Bilal abinci.

"Au ke abinci ma kike shirin tafiya kai masa? Toh bari kiji, bafa zata saɓuba wlh. Tunda akai auren nan ɗan abinda yake kawowa da yanzu ya daina. Rabon daya ajiye mana buhun shinkafa a gidan nan tun watan aurenku, haka kuɗi yanzu ko ya ya zo dubu biyar ce ko goma Allah na tuba mai zasu mun?
Ni ba haka na zata ba dan haka an yi akan gaɓa mun samu mafaka sakin ki kawai zai yi can ya ƙarata ki nemi mijin gaske ki aura."

"Idan kika ga na rabu da Bilal Umma to kice shi ya sakeni ko ya ce baya buƙatar cigaba da zama dani. Ina son Mijina, abinda ya sameshi kuma ba zai sa in daina son sa ba dan ya karɓe ni da abinda ya fi nasa muni bai gujeni ba dan haka sai inda ƙarfi na ya ƙare amma ba zan taɓa bari ya tozarta ba" tana gama faɗar haka ta fice daga gidan.

Take away mai kyau tayi masa sannan na siya masa tabarma irin mai soso a ciki da pillow harda net kafin ta wuce station ɗin. Ta tarar da Abubakar da Nasir a can da kuma Lawyer da aka ɗaukar masa mai suna Barr Sajid, yini ɗaya kacal amma sai ka ɗauka har an kaishi gidan yari ne duk ya fita a hayyacinsa musamman da Cell ɗin da aka sakashi sai a hankali, da dabaru irin nata da kuma kuɗaɗen hannunta ta saka aka canza masa cell mai ɗan dama-dama. Har after ten suna gurinsa ta ringa kwantar masa da hankali kafin suka tafi tareda su Abubakar zasu sauketa a gida.

Washe gari ƙarfe sha ɗaya aka fara shari'ar Bilal, babu jeka ka dawo ya amsa laifinsa dukda Lawyer a jiya ya faɗa masa idan an je kotu ya musa zargin da ake yi masa, a lokacin da za'a bayar kafin a sake zama zaiyi duk mai yuwuwa ya wanke shi amma daya kwanta cikin dare ya aksa bacci sai tunani daga ƙarshe ya yankewa kansa shawarar karɓar ƙaddara a yanda tazo masa kawai.

Sati biyu Alƙali ya bayar, kotu ta watse duk kuma yanda lauyansa ya shiga ya fita nan ma Beli bai samu ba aka kai shi kurkuku kafin zagayowar ranar da za'a sake zama.

Yana kallon Jalilah dake tareda Ahlan tana masa murmushi irin na bakaga komai ba ma tukunna a lokacin da aka fito dashi za'a sakashi a motar gidan Kurkukun. Haka ya sauke kansa ƙasa ya kasa kallon yan uwansa da duk suka halarci zaman kotun Hajja Anty Habiba ne kaɗai basu zo ba ita tana can tareda Hajjan. Takanas wata maƙwafciyarsu taje da daddare daƙyar ma aka barta ta shiga ashe labarin kama Bilal taje kai mata. Yanda maganar ta baza gari lokaci ɗaya abun mamaki, lungu da saƙo dangi kowa labari ya isar masa yanda kasan an yi yekuwa.

Haka aka wuce dashi Prison tun kuma daga isarsu ya fahimci ashe jiya a Aljanna ya kwana, yana ganin bai taɓa riskar dare mai muni irin na jiya ba yana isa Kurkukun ya fahimci Alƙiyamarsa ta tsaya, lokacin fara girbar abinda ya shuka tun a duniya ya zo. Haka ya canza kaya ya rungumi sabuwar rayuwar da Son zuciya da kwaɗayi suka jefashi a ciki.

Dare ya tsala, yana kwance kan dandaryar ƙasa, tun yana kore sauro da wasu ƙwaruka da suke binsa da bai ko tantance waɗanne iri bane ƙarshe ya haƙura ya zubawa taurarin da sukayiwa sama ado idanuwa tamkar mai ƙirgasu amma a zahiri yayi nisa cikin tunanin rayuwa ne.
Ya amince duk abinda ya faru shi ya jawa kansa, kwaɗaiyi da son zuciyarsa ya kawo shi wannan matsayin. Ya ringa tariyo rayuwarsa tun daga sanda ya fara sanin kansa, shi ɗin ya taso da burika da dama. Tabbas Hajja tayi ƙoƙari akansu, ko da sun rasa mahaifinsu tun suna da ƙananan shekaru amma bata barsu sunyi kukan maraici ba. Iya ƙarfinta ta sama musu abinda wasu masu uban a raye ma basu samu kamarsa ba, musamman shi daya kasance na daban ko a cikin sauran tana sonsa kuma bata ɓoye hakan ko a cikin yanda take tafiyar da lamuransu.

Ko da bai samu kuɗi yanda yake fata ba amma ubangiji ya rufa masa asiri domin yana samun abinda zaiyi buƙatun yau da kullum ba tareda ya nemi taimakon wani ba. Sai dai ido da hange-hange da kuma burika suka saka ya raina ni'imar da Allah yayi masa, hakan ya saka ya zama kullum yana cikin neman hanyar da zai samu kuɗi amma fa daga kwance ba tareda ya sha wahala ba domin kamar yanda yake cewa su Nasir a sanda suke yawo cikin ruwa da rana suna fafutuka ya kan ce shi ba kalar wahala bane ruwan jin daɗi aka masa dan haka yana zaune arziƙi zai tarar dashi ba sai ya fita ya nema kamar yanda sukeyi ba.

Cikin sa'oinsa da suka gama karatu tare shi ya fara samun aikinyi, sannan ubangiji ya hore masa macen da ya sani samun kamarta a wannan zamanin sai dace. Bata dubi abinda yake dashi ba, bata taɓa damuwa da mai zai bata ba, ta san yana dashi amma ta ɗauke kai ta wadatu da abinda take dashi sannan bata taɓa yin ƙyashin bashi abinta ba. Ta shanye baƙin ciki, ta ɓoye damuwa, ta jure tozarci da wulaƙanci amma daga ƙarshe ya biyewa shaiɗan ya barta.

Tabbas, yanzu da bulalar nutsuwa ta sameshi ya fahimci kura-kuren daya tafka a zamantakewatarsa da Halima ya kuma yarda da cewar da mutane da yawa sukeyi haƙƙinta sai ya bibiyeshi.
Duk abinda ya samu ta silarta ya rasashi, waɗanda sukayi saura ma ya sani yana dab da rasa su uwa uba ya rasa mutunchi da ƙimarsa.

Ya ringa tafka kuskure a koda yaushe yana raya cewa nan da lokaci kaɗan zai daina, zai gyara kura-kurensa sai dai a duk sanda ya yi yunƙurin dainawar sai zuciya ta sake angizashi ta sake kwaɗaita masa wani abun ya sake ƙudurce idan ya same shi zai tuba a haka yayi ta zurmawa har aka kawo wannan lokacin daya faɗa cikin rijiya mai gaba dubu. Bai fahimci talala ubangiji ya ringa masa ba sai yanzu daya kama shi dumu-dumu.

A haka ma kuma ya godewa Allah domin ya masa gata da bai barshi ya mutu a kan ɓarna ba, yana addu'a da fatan abinda ya faru ya zame masa ishara da sauran masu hali irin nasa.

A haka ya shafe sati biyu a kurkuku cikin yanayin da shi kaɗai zai iya fasaltawa. Sai ya kwana ya yini bai saka komai a cikinsa ba dan hatta da ruwan gurin baya iya sha. Shopping sosai Zulaiha tayi masa harda miya da soyayyen nama ta kai masa amma yana shiga ciki wasu suka ƙwace bai kuma iya yin ko tari ba domin fuskokinsu kaɗai daya kalla ya san babu abinda suke jin tsoro, zasu iya yi masa komai tunda dama ba barin gidan zasuyi ba da yawansu ɗaurin rai da rai aka yi musu. Haka ya shafe kwanakin cikin wahala da ciwo, ga zazzaɓi ga damuwa da tashin hankali kafin cikar lokacin idan ka ganshi sai ka ɗauka shekara goma yayi ba wai sati biyu ba.

Yayi baƙiƙƙirin, tunda yaje sau uku yayi wanka shima ba soso ba sabulu haka kayan jikinsa sai da wani da suke cell ɗaya ya taimaka ya wanke masa. Abu ne ya haɗu da mai son jiki wanda bai saba da wahala ba shiyasa abin ya masa yawa, yan uwansa babu wanda bai zubar da hawaye ba lokacin da aka kawoshi za'a shiga dashi kotun.

Hajja data dage sai an je da ita haka ta kware baki ta fashe da kuka tana cewa
"Sai kace wanda yayi kisan kai kalli yanda suka mayar mun dashi?"

"Koma menene shi ya janyowa kan sa ai Hajja, kuma babu wanda ya masa komai, Abubakar ya ce baya cin abinci baya wanka ai dole ki ga ya zama haka. Kawai kici gaba da addu'a Allah yasa shari'ar ta zo a yanda muke fata kawai" Anty Ladidi ta faɗa mata.

Sai da akayi Shari'a biyu kafin aka zo tasu, bayan maganganu daga kowanne ɓangare, Lawyer Alhaji Lawan ya tabbatarwa da kotu an mayarwa da Client ɗinsa kuɗaɗen daya bayar na siyan gida ciff ba tareda ko naira biyar tayi ciwon kai ba. Shima lawyer Jalilah ya faɗi an mayar musu da wani kaso na daga jumullar kuɗin kayan da aka ɗiba, kuma client ɗinsa ta amince da roƙon da yan uwan wanda ake ƙara sukayi na cewa za'a ringa biyanta kuɗin a hankali har a warware. Abinda yayi saura tsakaninsa da kotu ne domin jin matsayin laifukan daya aikata a matakin dokar ƙasa.

Alƙali Yakubu Bechi daya gama sauraron jawabi daga bakin lawyoyi yayi rubuce rubuce kafin ya fara karanto hukunci kamar haka.
"Bayan sauraron kowanne ɓangare, an gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da cewa Bilal Saleh ya fasa store da Jalilah Muhammad ta ajiye kaya in da ya ɗebi kayan da kuɗinsu ya kai kimanin naira miliyan talatin (₦30,000,000)."

A firgice Bilal ya ɗaga kai ya kalli inda Jalilah take zaune, ta kuwa sakar masa murmushi harda kashe masa ido ɗaya. A ina ya ɗebi kayan miliyan talatin? Amma ya zaiyi? Bai isa ya musa ba ko na miliyan dubu tace ya ɗiba haka nan zai amsa tunda shi ya jawa kansa.

Mayar da kai yayi ya cigaba da sauraron Alƙali dake cewa
"An samu shaidar hoto mai motsi daga CCTV camera da kuma shaidu na gani da ido wanda suka ga lokacin da aka fita da kayan.
Haka kuma, an tabbatar da cewa ka damfari Alhaji Lawan Isiyaku in da ka siyar masa da gidan da Jalilah Muhammad ta baka kake kula mata dashi bayan ka gabatar da bogi, ka karɓi naira miliyan hamsin da biyar (₦55,000,000)".

Alƙali Yakubu yaja fasali kafin ya ci gaba da cewa
"Duk da haka, kotu ta lura da wasu abubuwa masu muhimmanci:
Ka amsa laifinka tun farko ba tare da wasa da hankalin kotu ba. Sannan kotu ta samu tabbaci da shaidar mayarwa da Alhaji Lawan kuɗinsa da kuma wani ɓangare na kuɗin kayan Jalilah Muhammad bayan kotu ta fara sauraren shari’ar.

Sannan, a zamanka a kurkuku ka nuna cikakkiyar nadama da bayyanannen yunkurin gyara ta hanyar ayyukanka waɗanda ma'aikata suke lura da shi.
Wannan kotu ba ta tsaya kan hukunci ba kawai, tana kuma la'akari da gyara da dama haɗi da niyyar shiriyar wanda ya aikata laifi. Saboda haka, kotu ta yanke hukunci kamar haka:

1-A kan laifin fasa store da sata, kotu ta yanke maka hukuncin shekara biyar (5) a gidan gyaran hali, amma za a dakatar da aiwatar da hukuncin zuwa nan gaba idan aka sake samunka da aikata wani laifin (suspended sentence) a tsawon shekara biyu.

2-A kan laifin damfara, kotu ta yanke maka hukuncin shekara bakwai (7), sai dai saboda ka mayar da kuɗin da kuma nadamar da ka nuna, kotu ta sauya hukuncin zuwa shekara uku (3) ko kuma tarar naira miliyan goma a matsayin diyya ga wanda aka damfara, sannan da aikin taimakon al'umma (community service) na tsayin shekara ɗaya a ƙarƙashin kulawar hukumar gyaran hali. Sannan ba zaka tsaya takarar siyasa ko samun wani promotion na aiki ba a tsakanin shekaru biyar masu zuwa.

3-Zaka biya gomnati tarar naira miliyan 5 diyya ga gwamnati a matsayin horo da kuma darasi akan laifukan daka aikata. Karya ɗaya daga cikin Sharuɗa ko saɓawa doka yana nufin kotu zata dawo da cikakken hukunci haɗi da ƙari a kai.Ina fatan hakan ya zame maka darasi a rayuwarka da sauran masu aikata laifuka irin naka." Daga haka ya buga guduma wacce take nuna tabbatuwar kammala hukunci.

Bilal dake jingine da katakon box ɗin da yake ciki ya ɗago idanuwansa cike da hawaye, tsananin nauyi da kunyar da yakeji ta saka ya kasa ɗaga ido ya kalli ɓangaren da masu sauraron Shari'a suke. Yana jin nauyin idanuwa akansa amma bashi da ƙarfin guiwar da zai iya haɗa ido da kowa a yanzu. A hankali ya zame a gurin, ya fashe da kukan da bai shirya yin sa ba.
Bai san inda aka shiga aka fita har aka nema masa yanci, sau ɗaya lawyer da aka ɗaukar masa yaje gurinsa a prison shima basu wani yi magana mai tsayi ba ƙorafi yayi masa akan amsa laifinsa da yayi a kotu bayan ya tsara masa duk abinda zai faɗa idan anje.

Abubakar da Nasir ne a duk sanda sukaje suke bashi tabbacin ya kwantar da hankalinsa Insha Allahu komai zai dai-daita. Koma dai mai akayi ya godewa Allah ya kuma godewa ɗanuwansa da Amininsa Nasir da basu dubi halinsa sun wofantar dashi ba.

Kamar an ce ya sake ɗaga kansa karaf suka haɗa ido da Halima dake zaune a row ɗin dake kusa da ƙofa. Ji yayi gabansa ya faɗi, tayi masa wani irin kwarjini, kallon da takeyi masa daya fassara na baƙin ciki da jin kunyar abinda ya aikata. Kasa daina kallonta yayi kamar yanda itama take kallonsa kafin ta miƙe a hankali ta fice daga ɗakin kotun wani wanda bai san ko wanene ba da sai lokacin ya lura dashi ya bi bayanta riƙe da jakarta data bari akan table.

Sam bai ji maganar da ɗansandan dake kusa dashi yakeyi masa ba sai da Barr Sajid ya ƙaraso gurin yana murmushi da yi masa barka. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yana amsawa dukda hankalinsa gaba ɗaya yana kan Halima da tunaninsa ya tafi akan sanin wanene wancan daya bi bayanta?

A wajen kotun bayan murna da jaje daga yan uwa, Hajja dake riƙe da hannunsa kamar wani zai ƙwaceshi ta kalli Barr Sajid da yace zasu tafi da Bilal ɗin a ƙarasa cike takardu. Kamar zata fashe da wani kukan tace
"Ɗannan ba an sallame shi ba?"
"An sallame shi Hajiya, amma dole sai munje anyi cike-ciken takardu tukunna. Ganin harda Abubakar suka tafi ya saka hankalinta ya ɗan kwanta suka wuce gida tareda su Anty Amina da sauran yan uwa da suka halarci zaman kotun.

Dab da magriba su Bilal suka isa gidan Hajja a motar Nasir shi da Nasir ɗin sai Abubakar. Yanda yake jin jikinsa tamkar wanda aka haƙo daga rami ya so ace kai tsaye gida suka fara kai shi yayi wanka tukunna ko Asibiti ma dan shi kaɗai ya san abinda yake ji amma dai yayi shiru har suka isa gidan Hajjan. Nasir ya musu sallama da addu'ar Allah ya ƙara kiyayewa. Abubakar na kallon Bilal ya ce

"Yaya Nasir yayi maka ƙoƙari, duk tarin abokananka shi kaɗai ya tsaya da jikinsa da aljihunsa har Allah ya ƙwatoka. Ka gode masa kuma kada kayi wasa da abotarku dan shi ɗin mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login