Showing 18001 words to 21000 words out of 257873 words
baze yi tasiri ba.
"Yanzu haka nan da wace hujja zamu ce zamu hana shi aurenta? Go be fa suka ce zasu zo saka rana naga da ƙorafin ki ya tsaya wasa ba aure zeyi ba yanzu kuma ya yunƙuro se ki zo da wata magana daban Amina ban fa san ki da haka ba na kuma san ba kowa yake zugeki ba illah Labiba kuma zan kirata. Ita dai tunda Halima taƙi ƙanin Alhaji Saleh shikenan ta tsangwami zancen auren ta Bilal" Abban ya faɗa. Seta girgiza kai tace
"Babu ruwan Labiba wlh, kuma ko da taƙi al'amarin tana da hujjoji da ababen dubawa ne ai kuma son da takewa Halima yasa har take adawa da abinda take ganin ze iya zaka matsala a rayuwarta dan dai ka sani ko ni da na haifi Halima dan dai soyayyar uwa da abin cikin ta daban ce amma bazan ce nafi Labiba ƙaunar Halima a zahiri ba" Mama ta faɗa. Se yayi murmushi yace
"Bana in kari da ƙaunar dake tsakanin Labiba da Halima wani haɗi ne daga ubangiji wannan na kuma san duk abinda zatayi akanta zatayi ne don ganin rayuwarta ta in ganta. Ƙaramar uwa da yarta, ai babu me shiga tsakaninsu dan idan aka juyo ta wani fannin muna nan za ta iya baki kunya kuma ta juya tabi bayan yarta. Ni dai abin da zan ci gaba da faɗa miki shine ki ci gaba da yi mata addu'a kawai in sha Allahu e mun ce gara da akayi ba kuma zamuyi nadamar wannan tarayyar ba" da maganganun daya danneta kenan harta sakko tabi ta tasa taci gaba da addu'ar da dama kullum cikinta take.
A daren ta kira Anty Labiba ta gaya mata zancen zuwa sa ranar a take kuma tace a cireta ciki bata cike da iskancin Bilal da Halima. Tun dai taji ta gani ai shikenan mai Allah ya tabbatar da alkhairi. Dariya kawai Maman tayi ta kira Yayarta Hajiya Rumana kawai tace zata yiwa Matar Yayansu Lawan Anty Laure magana tun da taga ta fara harkar snacks na biki, duk da ba'a gidan zasu zo saka ranar ba amma zatayi abin tukuici akai can gidan Baba Salahun.
Washe gari lahadi ƙarfe huɗu na rana Kawunnan Bilal biyu da Aminin mahaifinsa ɗaya suka je saka ranar auren mu gidan Baba Salahu. Kusan a kowanne ɓangare ana al'ada, wasu su kan yi tsohuwar da aka saba akai akwati da kayan sa rana. Wanda suka zamanantar da abun kuma kuɗi suke badawa waɗan su kuma a sanda aka kai kuɗin aure ake haɗawa da na sa ranar ko kuma a haɗo kayan tare da lefe to su dai su Bilal bamu san wanne zasuyi a ciki ba, dama sanda akayi tambaya basu bada komai ba Abba yace baya buƙatar wani kuɗin na gani ina so ko na aure yanzun ma haka nan suka zo da saka rana shekara ɗaya se dai Baba Salahu yayi tsallen albarka yace basu san zance ba.
Watanni shida shine abin da suka yanke zasu aurar da yar su, bayan duk dogon zaman jiran sa da aka sha har idan suna ganin hakan ya musu gajarta to fa suyi haƙuri kawai domin a cikin dangi akwai wanda dama suka ci burin haɗa ta dashi. Aminin mahaifin Bilal ne yace ba za'a yi haka kuma tabbas kam iya lokaci an basu domin be manta ba an tafi shekara ta uku kenan da sukayi tambayar auren kuma shi kansa be san ranar har ta shekara suka shiryo ba da tun kan su zo dama ze gaya musu yayi yawa musamman dama ga bikin ƙanwar Bilal ɗin da za'a yi duk lissafin sa tare zasu haɗe. Haka dai aka rabu, duk sauƙin kai da rashin ɗaukar duniya da zafi irin na Baba Salahun bayan sun tafi se da ya kira Abba yayi masa mitar mutanen fa ko goro basu zo dashi ba balle wani abu na al'ada. Abban yace babu komai.
Irin murnar dana shiga bayan da na samu labarin a watanni shida masu zuwa zan zama mallakin Bilal ba me faɗuwa bace. Har party na haɗa, cikin sa'a washe garin ranar tayi daidai da ranar zagayowar haihuwata dama dan haka na roƙi Mama da muke hi hi yanzu akan zanje gidan Anty Labiba. Bata hanani ba, dama na gayawa Hansa'u da su Baby zamu je gidan zoo ranar birthday na Baby na bawa kuɗi ta yi mana kayan taɓawa na siyi cake da a jiki aka rubuta mun Happy engagement Mrs Bilal to be ban sanar ma Bilal ɗin bama se da na samu na bar gida haka ko suka je shi da abokanansa biyu muka sha hotuna muka ci snacks muka yanka cake bamu ji ma ba na wuce gidan Anty Labiba dan kar zance ya tashi tace ban je ba. Na dai sha zagi a gunta amma ban damu ba, tace kayan gado yan goron dutse zasu mun duk tarin da Mama takeyi a saboda aure na ba zata bari ta ɓarna tar da kuɗin ta ba har kayan kitchen da take siya da wanda itama ta siya mun Amirah zasu ajiyewa nace duk naji.
Shikenan rayuwa ta dawo mun sabuwa, soyayya da shaƙuwar mu da Bilal se abin da ya sake gaba. Na samu ƙatuwar takadda na zana calender ta wata shida kullum da safe na tashi zan soke ranar ki nake yi tamkar na janyo lokaci ni dai buri na da fata na kawai na zama matar Bilal.
Wata Juma'a sati biyu kenan da yin sa ranar mu watanni biyar da sati biyu kuma a cikin kwanakin da suka rage ma aurena da Bilal kamar ko yaushe munyi waya yace mun ze zo gurin ƙarfe biyu kuma se ya kirani yace na faɗawa Mama idan ya zo ɗin zamu ɗan je wata unguwa. Na ringa juya maganar, ba sabon abu bane fitar mu taren amma tun bayan da akayi sa ranar mu Mama ta zaunar dani tana mun faɗa da wasu maganganu in rage rawar kai karna kuskura ganin an saka mana rana da Bilal na ɗauki halin da bani dashi a da. Ko zuwa yayi yanzu se tace mu zauna a falonta muyi hira ko a compound a maimakon falon Abba da muka saba zama kamar kuma kaɗan take jira dani abu ƙarami zanyi ta fara mun faɗa shi yasa duk na rasa ta yanda zan ce mata zamu fita tare.
Ina tsaka da tunanin Amirah dake gidan Anty Labiba taje hutu tayi sallama, naji daɗin zuwan nata sosai, tare suke da Inaya da Amir wai Babansu Amir ɗin ne ya kawo su. Seda na fita na gaishe shi yana ta tsokanata wai amarya bayan ya tafi na cewa Mama zanje gidansu Hansa'u in karɓo atamfar ankon Baby an kawo mana tana can daga nan zamu kai ɗinki. Da Inayah muka tafi Amirah tace ba zata raka ni ba, seda nawa Bilal text na gaya masa ina gidansu Hansa'u cikin sa'a bata nan wai ta tafi wankin kai bayan tare mukayi zamuje shine bata kira ni ba. Zama nayi muka ɗan yi hira da Ummansu kafin muka tafi bayan da Bilal ya kirani akan yazo.
Page ɗaya ya rage free, ina fatan kin aika 800 ɗin ki kuɗin karatu 💃🏼💃🏼💃🏼
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk*
[5/18, 13:07] Buhainat: KURA A RUMBU
(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)
LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)
WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)
Whatsapp
07061838488
Arewabooks
@Maryamfarouk01
Wattpad
@MaryamahMrsAm
TikTok
@Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels
Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba. Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, ki ji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi
KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun
1840175439
Access bank
Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama.
Page 6
Duk nazarin na ban hango abin da take ganin na rashin dai dai ba. Rashin yi mun kyauta ne aibun sa ko kuwa rashin kammala ginin da be yi ba da kuma zancen lefe? A cikin ukun sune abin da nake ganin Anty Labiban take emphasizing se dai ni a ganin ta wannan ai ba komai bane ba. Bilal nake so ba abun hannunsa ba. Iya kar ƙoƙari yana yi gurin ganin ya kammala in da ze ajiye ni kuma ba a ɗaura auren nan an ga be yi mun lefe ba balle su ce wani abu. Ni duk wani lefe da wasu bidi'o'i basa gabana duk da dai ba zan ce bana so ba amma tunda nasan wanda zan aura bashi da ƙarfin yi shi yasa ban sawa raina ba sanin kuma masu shirya mun a gida ba yin al'amarin suke yi ba shi yasa kwata kwata ban sa a ka ba. Ko ankon yammata na kamu dana fitar saboda naji Mama da Aminyarta Hajiya Rakiya suna maganar ne shiyasa har na saka ran Maman za tayi taro.
Ban cewa Anty Labiba komai ba itama kuma ganin na ci gaba da sabgogina ba tare da na ce mata komai ba yasa ta fahimci amsar ke nan ina kan bakana ba gudu ba ja da baya. Allah ya gani tayi bakin ƙoƙarinta gurin haska mun tun da kuma na runtse ido abin da ya rage kawai su bini da addu'a ne, Allah ya saɓa tunanin su akan Bilal ɗin. Shikenan ta aje komai ta shiga yi mun gyara irin wanda ya dace da budurwa kuma yar gata kama ta.
Biki nata matsowa, tun da na koma gidan Anty Labiba sau ɗaya Bilal yazo a waje kuma muka tsaya yace sauri yake yi be zauna ba tun ranar kuma se dai muyi waya. Idan na masa ƙorafi yace aikin gini ne da sauran shirye shirye suke hana shi zuwa har ya rage saura kwana ashirin da biyar ranar Hansa'u tazo ta sakani gaba akan dole na kira Bilal ya basu kuɗin sallamar yammata ko kuma ita ta kira shi da kanta. Kira biyu na masa be amsa ba se ya mun text akan suna seminar ne ze kira ni. Se na mayarasa da text ɗin akan Hansa'u ce take so za suyi magana ina jiran sa. Har aka yi sallar isha'i muna zaman jiran kiran sa ko ya zo amma shiru daga ƙarshe ta tafi bayan da mukayi faɗa dan tace yana sane yaƙi zuwa ni kuma na kafe akan be gama abin da yake yi bane. Ko minti biyar bata yi da tafiya ba kuwa se gashi ya kira ni. Se da na gayawa Anty Labiba kafin na fita, ya ringa kallo na yana yaba kyan da nayi.
"Amarya kin sha ƙamshi. Kin ga yanda walwalinki yake haske ido kuwa Halims menene sirrin?" Murmushi kawai nayi na wuce ciki ya bi bayana ya na cigaba da zugani. Se da na aje masa ruwa da lemo yana ta bin duk motsi na da ido kamar ze cinye ni ɗanya, har na zauna ya kalle ni yana shafa cikin sa yace
"Yanzu fa muka gama ko gida ban je ba na taho dan nasan kina jira na". Se da na kalle shi sama da ƙasa, ƙananan kaya ne a jikinsa baƙin wandon da army green ɗin riga short sleeve. Sumar kan sa ta ɗan taru haka gashin fuskar sa da alama ya kwana biyu be yi aski ba ga ƙamshin turaren sa ya baibaye ko ina ni dai be yi mun kala da wanda ya wuni a gurin aiki ba. Cikin gida na wuce dan na fahimci maganar tasa yunwa yake ji. Se da yaci ya ƙoshi ina kallon sa ya sha ruwa kafin ya washe baki yace
"Kin san Allah, ni fa idan bake kika bani abinci ba sam se dai kawai naci amma bana ƙoshi". Nayi murmushi kawai se ya sake cewa
"To Hansa'un? Babbar Aminiyar mu Allah dai yasa ba tayi fushi ba"
"Ai ta tafi gida ma" na bashi amsa a gajarce, se ya fito da ido yace
"Haba dai? Ai na ɗauka ta dawo nan da zama itama har se an gama biki shi yasa ko da naga nayi magriba ban gama ba ban damu ba tun da kuna tare".
"Ka ji ka da wata magana fa, bikin saura kwana 25 shi ne zata dawo nan da zama tun yanzu?" Na bashi amsa ina kallon sa se yace
"Au haka fa, kin san saboda zumuɗi gani nake kamar sati biyu ne ya rage"
"Ban ga alama ba" na bashi amsa kai tsaye se yayi shiru yana kallo na. Haɗe fuska nayi na ci gaba da cewa
"Dama zuwa tayi akan maganar shirin biki da abun da za muyi na yammata shi ne tace na kira mata kai ka sallame su".
"Hajiya Hansa'u kenan iyayen rigima, wace sallamar yammata kuma se kace wasu yara ko yammatan ƙauye?" ya faɗa yana wata dariya me kama da ta rainin hankali. Se kawai na tsaya ina kallon sa jin abin da yace wai kamar yara ko yammatan ƙauye, me yake nufi kenan?
"Kin yi shiru kina kallo na" ya faɗa yana kawo hannunsa fuskata na goce nace
"Ban fahimci abin da kake cewa bane, a ƙauye ne ake bada sallamar ƙawaye?"
"Ni dai gaskiya rabon da naji an bayar da wani kuɗin yammata tun san da Abdulhadi yayi aure da muka je can garin ƙawayen amaryar nan suka sa mu gaba wai se mun basu kuɗin party" ya faɗa. Se kawai nayi shiru ina jin sa yana ta zuga zance shi kaɗai ni kuma ina danna wayata. Sallamar Anty Labiba ce ta katse shi. Ya zamo daga kan kujera kamar gaske ya shiga gaishe ta ta amsa fuska ba yabo ba fallasa kafin ta fara magana
"Dama na tambaye ta zancen gida dan muna so mu ga guri saboda musan awon labule da sauran abubuwan da zamu mata se take cewa bata sani ba, ga lokaci yana ta matsowa bama so a shiga hidimar biki bamu sallami gidan amarya ba".
Kamar in toshewa Anty Labiba baki haka na ringa ji sanda take maganar, na kalli Bilal yana ta mutsu mutsu kamar wani mara gaskiya se naga kamar harda zufa yake yi duk kuwa da garin babu zafi. Anty Labiba tayi shiru tana kallon sa bayan ta gama magana tana jiran jin amsar sa amma be ce komai ba se satar kallo na da yake yi ni kuma na sadda kaina ƙasa se ta miƙe ta kalle ni tace
"Duk yanda kuka yi ina jiran ki" ta fice ta bamu guri. Gani nayi yanayin fuskar sa ya canza, zuciya ta ta tsinke amma na dake na saurara naji ze ce wani abu dangane da maganar data masa amma naji shiru se ma kallon agogo da yayi ya ɗauki muƙullin sa daya ajiye kan center table ya kalle ni yace
"Dare ya fara yi Halims bari nazo na wuce ko?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Mamaki yasa kawai na bishi da kallo na kasa cewa komai. Yayi murmushi yace
"Babu rakiya? Ko baki gaji da kallo na bane na zauna?" Cikin ɗari ɗari nace
"Baka ce komai ba akan abin da Anty Labiba ta faɗa". Murmushi ya sake yi mun yace
"Na ji mana Halims, cewa tayi ai duk yanda mukayi ki gaya mata. Na zata duk abin da ake ciki kin sani me yasa baki gaya musu ba da har zaki bari yanzu ta titsiye ni? Me kike nu fi kenan Halima? So kike a ga gazawa ta ko me? To yanzu ai se hankalin ki ya kwanta tun da kin tozarta ni" ya faɗa sautin sa a ƙasa se dai yanayin kalaman da kuma yanda ya kira ni da Halima kai tsaye mai makon Halims yasa na fahimci ransa a ɓace yake.
"Yanzu kuma me nayi? Wace irin magana kake yi haka dan Allah meye abin tozarci a nan?" Na faɗa ina marmar da ido, gaba yayi yana cewa "Na gaji sosai bacci kawai nake so nayi zamuyi magana daga baya kawai"
Yanda kasan ya ɗaure mun baki haka na tashi na masa rakiya zuwa ƙofar falon ya tafi, ɗaki na wuce na kwanta bayan na kwashe kayan da yayi amfani dasu. Anty Labiba bata ce mun komai ba kamar yanda ni ma ban ce mata ba, haka Hansa'u data ki rani da safe kan ya mukayi nace zan kira ta shikenan bata sake tada maganar ba tun ranar kuma Bilal be zo ba a waya ma sau ɗaya ze kira ni da safe ko da yamma da mun gaisa ze kashe ko da na ɗakko magana ze bani uzurin yana abu shi kenan se washe gari kuma ze sake kira. A haka muka shafe kwana goma, idan ka ganni baka buƙatar a ce maka bani da nutsuwa saboda yanda jiki na ya nuna. Dama ba wani auki ne dani ba, ba tsahon kirki kuma bani da kiɓa, ɗan gyaran da Anty Labiba take mun da kunun alkama da madarar da dake ɗura mun suka sa na fara kumari yanzu kuma bani cikin nutsuwa ko abincin ma se naji yunwa na neman kayar dani nake ci ita kuma ta saka mun ido bata ce mun yi bata ce mun bari. Randa aka kwana takwas da zuwan Bilal ne ma da ta ganni na zauna na zubawa guri ɗaya ido ina tunani shine har ta mun magana tace
"A banza zaki kashe kanki Halima mu zaki yiwa asara tun da dai gashi ƙiri ƙiri ya nuna miki baya yi idan kina da hankali ya kamata ki cire shi daga ranki. Dama yau nake niyyar in tambaye ki in gayawa Mama yanda akayi saboda kar su cigaba da shirin biki a banza ko kuwa dai in kama kaina kar in shiga abin da babu ruwana?"
Se na kalleta a birkice nace
"Me zaki gaya mata kuma Anty?"
"In gaya mata na tambaye shi zancen gida tun da ya tafi be sake dawowa ba mana ita ai me hankali ce idan taji haka zata fahimci in da zancen ya dosa, dama dai na gaya mata ta dakata da duk wani shiri dangin Abbanki ne dai suke ta shirin su dan ma dai dama bikin ba na ki ke kaɗai bace abin haushin baze musu yawa ba" ta bani amsa. Se kawai na fashe da kuka, ta saki baki tana kallona