Showing 27001 words to 30000 words out of 257873 words
jaka na shirya, bana jin ciwon komai ban da kaina da yayi mun nauyi se jiki na da babu ƙwari dan haka a zaune nayi sallolin da Anty Labiban tace sun same ni a kwance. Ina idarwa ta miƙa mun cup data haɗa tea na girgiza mata kai ina cewa
"Bana jin yunwa Anty". Se ta mayar ta ajiye akan drawer ta nemi guri ta zauna tare da ciro wayar ta daga aljihun rigar ta ta shiga dannawa. Kusan minti goma muka yi shiru, so nake yi na tambaye ta ko Bilal ya tafi ne amma yanda ta tsare gida yasa na ji shakkar yi mata magana da dai naji bazan iya jurewa ba se kawai nayi shahada cikin murya ta data ƙara laushi nace
"Anty Bilal ya tafi ne?"
Yanda kasan tana jira na kuwa tayo kai na tana cewa
"Ki kiyaye ni Halima, ni zaki tambaya Bilal ya tafi ko yana nan ajiyar sa kika bani ko yaya akayi?. Badai bakya tausayin kanki ba da kananun shekarun ki zaki jawa kanki ciwo saboda namiji. Se ki zuba ruwa a ƙasa kisha zaki auri Bilal autan maza. Badai namiji kika ɗaukaka har kike neman halaka kanki saboda shi ba Halima? Allah ya bada sa'a" se ta miƙe fuuu tayi waje tana ci gaba da maganganu.
Da kallo na rakata har ta fice ina jin babu daɗi a raina. Na rasa wace irin ƙiyayya Anty Labiba take yiwa Bilal. Ban san me ya tsare mata da bata iya ɓoye tsanar da tayi masa a zahiri ba.
A can waje kuwa cike da damuwa Bilal yake zauna, yana so ya koma cikin ɗakin yaga halin da Halima take ciki amma rashin ganin fuska a gurin Anty Labiba yasa yake zaune a gurin. Da daren jiya Mu'azzam ya kira shi ya sanar masa da Halima bata da lafiya an kwantar da ita a asibiti a yanda yace tana ta kiran sunan sa ne shine Abban su yace a kira shi yazo. Sanda yaje ɗin ya tarar da ita anyi mata allurar bacci a hirar su ya tsinci wani abu a dalilin rashin lafiyar tata. Duk se yaji ya tsani kansa, yasan Halima tana son sa shima kuma yana son ta amma kuma ya rasa yanda ze yi dole ya fito ya gaya mata gaskiya. Be yi zaton zata saka abun haka a ranta har ya kwantar da ita ba se dai da ya ci gaba da jan ta yana ɓoye mata har se an kai gaɓar da gaskiya zata fito da kanta a ganin sa gara ta sani su taru su nemawa kansu mafita.
Ganin kusan minti talatin shiru Anty Labiba bata leƙo ta kira shi ba ya fara tunanin ko bacci Haliman ta koma dan yana da yaƙinin ido biyu ba zata gaza neman sa ba tun da tasan yana gurin, tashi yayi yana ƙarfafawa kansa guiwa akan ko me Anty Labiba zata faɗa se ya koma ɗakin, yana kai hannu ze buɗe ƙofar ta fito, kallo me kama da harara ta masa haɗi da yin tsaki ta raɓa shi ta wuce se yaji ransa ya ɓaci. Ta girme shi kuma ƙanwar mahaifiyar Halima ce amma kuma hakan ba shi yake nufin zata ringa wulaƙanta shi kamar wani wanda yazo mata maula ba. Shi badan Halima ba me ma ze haɗa shi da ita har ta ringa wulaƙanta shi haka?
Fuska babu walwala ya shiga ɗakin, na ɗaga kai da sauri jin an buɗe ƙofa muka haɗa ido ban san sanda na miƙe ina sakin murmushi ba ya nufo ni shima yana murmushi yace
"Kin tayar mun da Hankali Halims, me yasa?"
"Sau ke gani na nayi ƙasa ina wasa da gefen hijabi na ba tare da nace masa komai ba, ganin sa ya bani nutsuwar zuciya ya kuma tabbatar mun yana tare dani ma'ana ya janye waɗan can kalaman marasa daɗi daya faɗa mun jiya wai mu haƙura da juna.
"Ki zauna kar ƙafafun ki su gaji" ya faɗa yana kallo na se na ƙarasa na zauna akan gado har sannan murmushi be bar kan fuskata ba, ya matso da kujera kusa da ni ya zauna yana leƙa fuskata yace
"Ashe haka kike so na ban sani ba Halims?"
Harar wasa na masa ba tare da nace komai ba, ya sake gyara kijerar da yake a kai ya langwaɓar da kai yana kallo na yace
"Ko da nace mu haƙura ƙarya nake yi ni da kaina nasan bazan iya jure rashin ki a tare da ni ba. Tun da kika tafi ni kaina dauriya ce kawai irin ta maza ta sa ba'a kawo ni an kwantar a gadon Asibiti ba mutuwa ce kaɗai zata iya raba ni dake Halims amma muddin ina raye dole zan nemo mafita, ki taya ni da addu'a Allah ya hore mun na fita kunyar ki kafin ranar auren mu albarkacin wannan son da kike mun bazan baki kunya ba".
Bude ƙofar da aka yi ya saka yaja baya daga gare ni muka kalli ƙofar a tare, Abba ne ya shigo tare da Uncle Mudassir Autan su Mamanmu. Cikin jin kunya Bilal ya miƙe daga kujerar da yake zaune yana musu sannu da zuwa, fuskar Abba babu yabo babu fallasa ya nufo in da nake se Uncle Mudassir ne ya amsa masa kafin shima ya matso yana mun murmushi na gaishe su ya shiga tambayar jiki na sannan ya ɗauki folder dake kan bedside ya shiga dubawa dake shima likita ne.
"Dr yace zuwa yamma zasu sallame ki tun da babu wani abu ko akwai in da yake yi miki ciwo ne yanzun?" Abba ya tambaye ni, se na shafa ciki na da naji yayi ƙara alamar ina da buƙatar cin wani abu na girgiza masa kai a hankali nace
"Babu komai Abba na samu sauƙi".
"Allah ya ƙara afuwa, ki huta. Su Goggo Habiba suna hanya ni na hana Mu'azzam ma ya kawo ta tun da safe saboda an ce a barki ki huta yanzun ma ta tayar da rigima ne tun da kuma sallamar ki za'ayi shi yasa nace su zo ɗin kawai" Abba ya sake faɗa. Nayi rau rau nace
"Goggo Habiba kuma? To Mama fa?" Be bani amsa ba ya juya kan Bilal da tun shigowar su yayi shiru kamar ruwa ya cinye shi yace
"Ina ganin zaka iya tafiya ko" se ya kalle ni kafin ya shafa kai haɗi da rusunawa yace
"To Abba, Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne" Abba da Uncle Mudassir suka amsa da amin se ya nufi ƙofa yana waige na.
"Idan ka samu sarari yau ko gobe kazo ina son ganin ka" Abba ya faɗa Bilal na dab da fita, take na karanci razanar da Bilal yayi se kuma ya waske yana murmushi yace
"To Abba idan ma yanzu kake son ganin nawa se na jira ka a waje"
"Ka same ni a filin sukuwa ƙarfe huɗu zuwa biyar na yamma" Abban ya bashi amsa daga nan ya fita bayan ya sake musu sallama zuciyar sa fal zullumin ganin me Abban Halima yake so yayi masa?
Se da akayi sallar magriba muka bar asibiti saboda wata allura da aka yi mun ƙarfe shida. Na lumshe ido na ina ci gaba da sauraron faɗan da Goggo Habi take yi, tun da taje asibitin bakin ta be huta ba har yanzun da muke hanyar komawa gida zagi kalar wanda ta manta ne kawai bata mun ba har tana cewa in da ita ce Labiba bari na zatayi na mutu kawai tun da turbar da na zaɓar wa kaina kenan to saboda Allah ni na ɗorawa kaina son Bilal ake nufi ko me? Allah da kansa ya ce shi yake sanya ƙauna a zukatan mutane, menene laifi na sabo da nayi so domin Allah? Zuciya ce kowa da irin tasa, wani yana ɗaukar abubuwa da sauƙi in da wani yake zafafawa babu kuma wanda za'a ce baya kan daidai.
Naji daɗi kuma ban ji ba da naga mun wuce gidanmu ba gidan Anty Labiba ba. Allah ya gani haushin ta nake ji saboda ita ce silar komai da bata uzzurawa Bilal da tambaya ba ai da komi ba lalace haka ba rashin jin daɗin komawa gida kuma da naji nasan surutun Goggo Habi tsaf ze iya haifar mun da wani sabon ciwon se dai ba ta tata nake ba tun da nasan bata da ikon sakawa ko hanawa a cikin lamarin aure na, kakata ce ta ɓangaren uwa ba uba ba balle naji tsoron zata iya tilasta Abba yayi abin da suke so.
Abin da ya saka jiki na yin sanyi yanda ko kallon banza ban ishi Mama ba balle na arziƙi, haka nan na shige ɗaki na jiki babu ƙwari ina jin babu daɗi. Mama da ko ciwon kai nake yi se ta damu bata samun nutsuwa har se taga na warke ita ce zan kwana a asibiti ba taje ta duba ni ba sannan in dawo gida tayi kamar bata san da wanzuwata ba? Ko da yake ba laifin kowa bane se na Anty Labiba ita take zugata, se kace ita wani ya mata dole a sanda ta kawo nata mijin da ni ban ma gama tantance yaren sa ba har yau, su ba yarabawa ba ba igala ba haka nan kuma ta aure shi suke zaune shekara goma ba wanda yace mata saboda me se ni zata saka a bakin duniya ta cusawa kowa tsanar wanda nake so.
Da daddare gurin ƙarfe sha ɗaya yunwa ta matsa mun dole na katse wayar da muke yi da Bilal na fito neman abin da zan ci. Tun ƙarfe tara muke waya, yau ɗin ya dawo asalin Bilal ɗina me so na da tattalin farin ciki na. Zumuɗin da nake jini nin ban ga yana yi akan auran mu ba se gashi yau ya tashi gaba ɗaya ya rikita ni da tsadaddun kalaman soyayya irin waɗan da kunnuwa suke da muradin sauraro a ko da yaushe. Rabon da muyi hira ta nutsuwa kuma me daɗi irin haka tun ba'a saka ranar auren mu ba. Kamar yanda ya ce mun wani alkhairi ne ya sakko mana ba zato na tsammani yana zaune kawai wani tsohon abokin Baban sa ya kira shi yake cewa ya samu labarin zeyi aure, a taƙaice dai ya saka yayi masa list na duk wani abu daya rage masa cikin harkar auran yace ze ɗauki nauyi zancen da akeyi har ya turo masa kuɗaɗe ya ce a fara aikin kafin sauran su iso. Ya ce mun
"Halims Allah na son mu kasance tare, a sanda na sare nake ganin ba zan iya ba se ya turo mun da agaji ta in da ban yi tsammani ba. Ke alkhairi ce a rayuwa ta ina roƙon Allah ya bani ikon kyautata miki kwatankwacin yanda kika kawo haske cikin rayuwa ta".
Saboda murna har rawa se da nayi duk da ba wai na gama jin ƙwarin jiki na bane ba, na ringa kwararawa ko ma wanene wanda ya kawo mana wannan ɗaukin addu'a. Bamu kashe wayar ba se da naji zuciya ta ta fara tashi dalilin yunwa ga kuma surutun da muke ta yi ba dan Bilal ya so ba muka rabu akan da zarar na ci abincin na yi masa ko flashing ne.
Abba da Mama na tarar zaune a falo, gaba na ya faɗi ganin hawaye akan fuskar Mama Abba kuma yana durƙushe gaban ta da alama haƙuri yake bata, na matsa kusa dasu da sauri ido na na kawo ruwa na fara tambayar me ya faru?
"Babu komai Halima, wai tunanin zakiyi aure ki bar mu ne duk ya fara sanyayar mana jiki shi ne take kuka" Abba ya faɗa kamar me yin magana da yarinya yar shekara biyar ko ƙasa da haka. Fashewa nayi da kuka na zauna gaban Mama nace
"Ni ce ko? Sabo da ni kike kuka?"
"Me yasa zan yi kuka saboda ke Halima? Bana fatan ubangiji ya nuna mun ranar da fushin wani daga cikin ku ze taɓa zuciya ta har yasa in zubar muku da hawaye ina neman tsari da hakan. Hawayen tausayin nake yi bana baƙin ciki ba" Mama ta faɗa se Abba yace
"Haba Amina ban san sands kika zama me nace akan magana guda ɗaya ba, shi ba zaki yarda da ƙaddara ki bar komai a hannun Allah ba?"
Kafin tayi magana nayi saurin kama hannun ta ina kuka nace
"Dama na san saboda ni ne, dan Allah Mama kiyi haƙuri, ki yi mun addu'a ki kuma sakawa al'amari na da Bilal albarka nasan ubangiji baze kunyata ku ba. Addu'ar ku zata kasance hasken da ze kore mana kowanne duhu. Kuma ki dena damuwa Mama yanzun nan Bilal ya kira ni ya gaya mun wani abokin Baban sa ya bashi kuɗi yace ya ƙarasa gini, babu abin da ba ze yi ba da yardar Allah Mama ki kwantar da hankalin ki babu wanda zeyi mana dariya kamar yanda suke sauraro".
Hannu biyu Mama ta ɗaga tace
"Allah na bar amanar Halima a hannun ka. Kada ka bari wauta da makauniyar soyayya su jagoranci al'amuran ta a gidan auren ta"
"Amin, yanzu ki kayi magana Amina. In sha Allahu se mun ce gara da aka yi" Abba ya sake faɗa.
A sanyaye na tura shayin dana haɗo zuciya ta duk babu daɗi. Ban zaci rashin son da Mama take yi wa aure na da Bilal ze saka har ta zubda hawaye ba. Se na ringa jin kamar banyi daidai ba da tun farko naƙi bin ta tata amma kuma ban hango laifi na akan bin son raina da nayi ba. A cikin labarin ta na samu tawa ƙarfin guiwar. A kullum ta kan karanta mana irin rayuwar da sukayi da Abba, wuyar da suka ci tare har zuwa yanzu da daɗi yazo shima suke shan sa tare.
Tun ina ƙarama na tashi da sha'awar irin rayuwar da iyaye na suke gudanar wa ta tsantsar soyayya da tattalin juna har zuwa kanmu yaran da suka haifa.
Mahaifiya ta Amina Sa'id haifaffiyar unguwar Yakasai ce yayin da Abba yake haifaffen Galadanci. Tamkar banbancin dare da rana haka suka sha banban gurin asali, Mahaifin Mama attajiri ne kuma basarake wanda a zamanin sa sunansa yayi amsa kuwwa a ƙwaryar birnin kano da kewaye. Allah ya bashi tarin dukiya wadda ya ƙare rayuwar sa yana hidimtawa iyalansa da al'ummar dake zagaye dashi. Mamana ita ce ya ta huɗu cikin jerin yaran sa bakwai daya haifa da matar sa ta aure guda ɗaya Hajiya Saude. Namiji ne babban su Alhaji Lawan se me bi masa Hajiya Rumana sannan Mama Fauziyya se Amina mamana kenan, Baba Faisal ya rasu shekaru biyar baya, Baba Mudassir se Anty Labiba data kasance autar su.
Abbana ya fito daga babban gida me yawan ahali domin matan mahaifin su huɗu, a jerin yaya shine na goma sha uku a gidan gaba ɗaya a ɗakinsu kuma shine na huɗu kuma namiji tilo. Gidan su gida ne irin na bani babu, Mahaifin su Malam Ibrahim talaka ne domin har ya mutu be bar musu komai ba ban da gidan gandu. Duk da bashi dashi kuɗi amma yayi ƙoƙari sosai akan tarbiyyar yaransa. Ya saka su makarantar addini duk kuma wanda kaga yayi karatun boko a gidan to shi ya saka kansa ba Malam Ibrahim ba. Abbana shine namiji na farko daya fara karatun boko a gidan domin sauran da sun tasa sukayi sauka a makaranta shikenan se su shiga kasuwa, da dama ta fara zuwa se aure su fara tara Iyali wannan yasa jikokin gidan muke da bala'in yawa wasu idan ka kalli shekarun su dana iyayen su se kaga kamar basu suka haife su ire ire na mun shiga layin sa'annin yayan jikoki ne saboda iyayen mu da basu yi aure da wuri ba.
A BUK Abba ya haɗu da Mama, lokacin yana level 2 Business administration ita kuma tana level 1. Daga mutunchi kasancewar sa me ƙoƙarin gaske ya kan koya musu karatukan da suka shige musu duhu a hankali mutunchin nasu ya rikiɗe zuwa soyayya wanda ita Maman ce ta fara nuna sha'awar hakan. Daƙyar Abba ya amince, badan ba tayi masa ba ko kuma baya son ta se dan ganin tazarar dake tsakanin sa da ita. Ya kan ce mata
"Akwai banbanci me girma tsakani na dake Amina. Ni ba sa'an auren ki bane, ƙima ta bata kai ta ko da direban da yake kawo ki makaranta ba ki rufa mun asiri ki barni na kammala karatuna lafiya domin shine madogara ta idan wani abu ya faru na rasa wannan damar ban san ina zan kama ba". Bata sare ba taci gaba da bibiyar sa da kuma ubangiji ya ƙadarta akwai rabon aure a tsakanin su se gashi sun yi har an haife mu a kullum bakin Abba baya gajiyawa da nanata halin karamcin da ahalin Mama suka gwada masa.
"Sun ƙauna ce ni a sanda bani da komai, sun aminta dani suka bani guda daga mafi soyuwar ahalin su idan har ban saka musu ta hanyar faranta ran Amina har bakin raina ba da wanne ido zan tsaya gaban Allah na maida amar da mahaifin ta ya bani?" Abin da yake yawan faɗa kenan. Mama ta manta asalinta da rayuwar jin daɗin da ta taso a ciki ta rungumu mijin ta da sabuwar rayuwar da ta zaɓawa kanta. Sun kwana basu ci ba, wata rana su ci sau ɗaya ko sau biyu an tashe su daga gidajen haya ba adadi amma duk ta jure bata sare ba haka nan dai dai da rana ɗaya bata taɓa tilasta masa karɓan tayin taimakon da yan uwanta suke masa ba kamar yanda yace mata zai nemi halal ya ciyar da ita alfarma ɗaya kawai yake nema a gare ta shine karta raina yana ji jikin sa wata rana ze mayar da ita inuwar data saba da ita gashi kuwa Allah ya amsa bayan wani lokaci.
A sanda Mama take da ciki na Anty Labiba ta dawo gidan mu da zama, tun tana zuwa ta kama mata ayyuka ta tafi har ya zama ta dawo gidan gaba ɗaya bayan an haife ni saboda yanda take so na. Da ita aka sha gwagwarmaya ba kuma ta bar gidan mu har