Showing 195001 words to 198000 words out of 257873 words
nan a bakin wani Nasir ba zata mana da daɗi ba" Bilal ya faɗa da ƙyar dan yana jin jiki. Nasir ya guntse dariyar sa ya cigaba da tuƙi yana satar kallonsa.
"Wlh sai na nuna masa shi ƙaramin mahaukaci ne, sai ya san ya dakeni" Bilal ɗin ya sake faɗa shi dai Nasir bai ce komai ba har suka isa gidan ya shigar masa da mota ya rakashi ciki ya tambaye shi ko akwai abinda yake buƙata ya ce babu daga nan ya masa sallama ya wuce gida akan zai dawo da safe ya duba shi.
Kwana yayi yana saƙa da warwara akan matakin daya kamata ya ɗauka akan Halima domin duk ita ta shirya komai, yayi ƙwafa ya ɗauki wayarsa ya kunna. Message ɗin Zulaiha ya shigo dama kuma saboda itan ya kashe wayar suna fitowa daga gidansu dan karta dame shi da kira yana gurin Haliman bai ko karanta ba ya lalubo number Halima ya aika mata da saƙo akan karma ta ɗauka ta ci galaba akansa kuma zai karɓi yaransa, maganar yaran ya san ita kaɗai ta isa ta sake zargo masa wuyanta dan ya san ƙulafucinta akan yaran ba zata taɓa yarda a raba su ba.
Yana gama turawa ya latse wayar zai sake kashewa sai ga kiran Zulaiha ya shigo, ya amsa, cikin asalin muryar da ya santa da ita mai laushi cike da kunya da kuma nutsuwa ta masa sallama.
Ya saki ajiyar zuciya, abinda yake akanta ya motsa masa sai ya gyara kwanciya yana cije baki saboda yanda duk jikinsa yayi tsami a hakan ma dan ya gargasa da ruwan zafi sannan ya shafa Aboniki kuma ya sha pain relief.
Ta gaishe shi abinda rabon da ta masa tun randa aka ɗaura musu aure.
"Ashe ɗazu kazo Yaya Bilal" ta faɗa. Ya buɗe ido da mamaki kafin ya ce
"Bangane ba? Ba kina gidan ba sanda muka zo?"
"Yanzu Umma take gaya mun da duk abinda Kawu ya muku, dan Allah kayi haƙuri, na rasa mai muka tsarewa Kawu a duniya da kwata kwata baya ƙaunar mu kullum bashi da wani buri illah na ya tozarta mu mu da mahaifiyarmu" ta sakw faɗa cikin shirin yin kuka. Da sauri ya tare ta da cewa
"Me aka ce yayi mana? Ni ai babu wani na rashin jin daɗi daya faru amanarku kawai ya bamu ya ce baya son kawo ƙara duk abinda ya faru muyi hukunci da kanmu in dai ba abun yayi girma bane"
"Kawai ba zaka faɗi gaskiya bane amma Umma ta gaya mun ya ci muku mutunchi sosai" ta faɗa tana sakin kuka. Duk sai ya diririce ya ringa mata rantsuwa akan shi wlh ba abinda Kawu ya musu idan ma yayi toh hankalinsa baya gurin bai fahimta ba.
"Shikenan toh tunda ka ce haka, ya Anty Halima? Ya su Al'amin kwana biyu ko motsinsu bana ji" Zulaihan ta sake faɗa bayan ya gama lallaɓa ta tayi shiru. Ya sauke numfashi ya ce
"Yau suna can gidansu sun je yini zanje na ɗakko su kuma kaina ya fara ciwo shine kawai na ce su kwana acan" ya lafta mata ƙarya. Tayi wani miskilin murmushi ta ce
"Allah sarki, Anty Halima dai akwai haƙuri gaskiya ko sau ɗaya banji kace tayi rigima irin yanda mata sukeyi idan za'a musu kishiya ba, ko dai bata sani bane?"
"Waya gaya miki? Tayi abunta mana kawai dai ba da yawa yanda mata sukeyi ba; kin san na faɗa matata ta dabance ita" ya bata amsa. Ya ji sauyi a muryarta ta ce
"Allah sarki mu da ba na daban ba"
"Ke kuwa ai kece asalin ta daban ma" ya faɗa ta ce
"Hmm" kawai.
"Amma ɗazu kika ce bakya nan muka zo bayan kuma na ganki har magana munyi?" Ya canza akalar maganar, sai ta ce
"Wlh kwana biyu na rasa mai yake damuna. Tun bayan da aka ɗaura mana aure ni dai sai in ringa ganin abubuwa suna faruwa kamar mafarki nakeyi. Umma ta ce kamar wai iskokai ne suke taɓa ni wani lokacin sai na canza nayi ta abubuwa kuma daga baya idan na dawo hayyacina ba zan tuna mai ya faru ba" ta faɗa. Bilal yayi shiru yana juya maganganun a ransa kafin ya ce
"Amma dama kina da matsalar jinnu ne tsayin lokacin nan ban taɓa sani ba?"
"Wlh nima ban sani ba amma Umma ta ce wai ƙila na gado ne itama haka suka mata sanda aka mata aure amma tana tarewa shikenan suka barta dan ko magani ba'a nema mata ba Kakarsu tace idan aa mata magani za'a gayyato mata wasu ne dan su waɗannan ɗin da kansu zasu tafi ko ba'a musu komai ba toh shine yanzu da Anty Habiba har ta ce muje Ɗanfodiyo Umman ta ce a dakata dai zuwa in tare idan basu rabu da ni ba sai muje"
"Da aljanun zaki tare kenan?" Ya faɗa kamar a tsorace. Tayi dariya ta ce
"Bafa a jikina suke ba kawai shafata suke yi"
"Duk ɗaya ai, kin san yanda kike birkicewa kwana biyun nan kuwa? Harfa zagina kikeyi"
"Subhanallah zagi?" Ta faɗa cikin rawar murya, jin zata saka masa kuka yayi saurin cewa
"Wasa nakeyi amma dagaske dai in zai yuwu gara a fara neman maganin tun yanzu dan gaskiya bana jin daɗin yanda kike canzawa har na fara tunanin ko dama dai haka halinki yake ɓoye mun kikayi?"
"Yanzu tsahon shekarun da muka ɗauka Yaya Bilal har akwai wani hali nawa da zai ɓoyu ace baka sanshi ba?" Ta faɗa cikin kuka. Yayi tsaki ya ce
"Kin san ba abinda na tsana kamar kukanki kuma ni ba cewa nayi kin ɓoye mun wani abu ba cewa nayi na fara zato amma yanzu da kika faɗa mun sanadi kinga ai na fahimta ko?"
"Toh yanzu wai yaushe za'a je ganin gida in ji su Anty Habiba?" Ta tambaya bayan da ya gama lallaɓata tayi shiru, ya ce
"Idan suna da lokaci ko jibi sai a zo"
"Har jibi? Yau fa litinin, saura kwana biyar fa tariyar ya kamata ace zuwa yanzu ma an yi jere kaga fa gobe za'a fara jeren Nuratu ita tub wancan satin aka ga gida" ta faɗa cikin shagwaɓa. Ya ɗan yi shiru, nan gidan ya so ya bata amma yanzu Halima ta wa kanta ya fasa kaita sabon gidan nan ɗin zata dawo bayan ya gama koya mata hankali. Numfashi ya sauke ya ce
"Goben toh sai suzo, ke ma ki shirya idan naji dama dama gobe ko da daddare zanzo na ɗauke ki muje ki gaida Hajja" daga haka sukayi sallama bayan tace Allah ya nuna musu goben.
Washe gari da wuri dukda yanda yake jin jikinsa ba daɗi haka ya lallaɓa yaje gidan Hajja dan ya gaya mata zancen zuwan yan jeren Zulaiha.
"Tazo ta haɗe kayayyakinta ne ko a ina zaka sakata?" Tana nufin Halima. Ya ce
"Ai ba gida ɗaya zan haɗa su ba, akwai gidan da Hafiz ya bani aro kafin muga yanda hali zai yi" ya mata ƙarya. Ta taɓe baki ta ce
"Ai shikenan"
"Yanzu me zan bayar na abinci da sauran abubuwan da za'a yi? In Allah ya kaimu ranar Asabar zata tare". Banza ta masa har kuma ya gama surutunsa bata sake ce masa komai ba dama kuma tunda ya shiga ya lura a fushi take ya zata kuma maganar jiyan ta wuce ai tunda kafin ya tafi harta koma tsohon saitinta bai sani ba yanzun kuma fushin me takeyi.
Gida ya koma, kamar ya kira Anty Amina sai kuma ya fasa daya tuna ita ba Hajja bace abinda ya aikata ba zai taɓa gogewa a idonta nan kusa balle ta sake sauraron sa ba. Ƙarshe Anty Habiba ya kira, bai yi mamaki ba da yaji bata masa zancen abinda ya faru ba da alama Hajjan bata gaya musu ba kuma ya godewa Allah domin ko da suke ciki ɗaya ya san muddin maganar ta wuce Anty Amina toh kamar duk jama'ar gari sun ji ne.
Da dare ya lallaɓa yaje ya ɗakko Zulaiha, yan uwan nata basu je ganin gidan ba ranar sai da ya je ya ɗauketa a hanyar dawowar su daga gidan Hajja wacce tunda suka gaisa ta shige ɗaki bata sake fitowa ba sallama ma Zulaihan ce ta leƙa ta ce mata zasu tafi tace a gaida gida haka Fadila sai da Bilal ya mata tsawa kafin ta gaisheta Abubakar kuwa ko kallon arziƙi bai musu ba daga ita har Bilal ɗin suna shiga ma ya fice daga gidan ya barsu.
Jin tayi shiru tunda suka fito ya saka ya ce mata
"Masu zuwa kafi ashe basu je ba"
Ta muskuta ta ce
"Basu je ba wlh matsala aka samu"
"Wace irin matsala kuma?" Ya tambaya, tayi rau da ido ta ce
"Sai sa aka je ɗebo kaya gurin kafinta wai tsabar mutumin nan bashida mutunchi ya ce wai wasu kaya kuma za'a ɗauka? Tariyar ma dai ina ga da wuya idan zata yuwu a wannan satin sai dai a sake saka lokaci"
Cikin rashin fahimtar zancen nata ya ce
"Ban gane me kike nufi ba?"
Sai da ta ja hanci kafin ta ce
"Wai fa kuɗin da aka bashi miliyan uku na kayan gadonmu da kujera mu biyu duka ya haɗa yayi aikin Nuratu da su, ni dama tunda na ga kayan na cew Anty Habiba sun fi ƙarfin na kuɗin da aka ce ayi tace ba haka ba, sai da aka je ɗakko nawa wai ai shi da duka kuɗin yayi amfani yayi wancan kayan bai fahimci na mutum biyu ake nufi ba" cikin kuka ta cigaba da cewa
Ni tun farko dama abinda nayi gudu kenan na ce kawai na haƙura da lefe kayi mun kayan ɗaki kamar na san wannan matsalar zata faru".
Shiru yayi yana juya maganar a ransa. Ta yaya za'a yi a bawa mutum aiki na mutum biyu ya ce ya ɗauka na mutum ɗaya aka ce? Ba su suka zaɓi abinda suke so akayi lissafi suka biya kuɗi ba?
Kukan da takeyi ne ya fara rikita masa Lissafi dan haka ya ce mata
"Ke komai sai ki fara kuka, yanzu toh ya akayi? Wace matsaya aka samu akan kayan?"
"Wace matsaya kuwa? Dama ai an kwashe na Nuratun tun wancan satin toh aka ce za'a mayar masa ya bayar da guda biyun wai ba zai karɓa ba tunda zaɓar design ɗin akayi yayi su ba wai a ajiye suke dama aka ɗauka ba. Har ma an kai gidan nata yanzu sai Umma ta ce nayi haƙuri abinda aka samu na gudummawa idan Nuratun ta tare sai a haɗa ayi mun wasu"
"Wannan ai ba magana bace, kenan ke ba zaki tare ba ko kuma zaki tare babu kaya ne?" Ya faɗa a ɗan fusace. Ta sake fashewa da kuka ta ce
"Toh ya kake so nayi? Ka san dai ba zance aa ba dan ko nawa ne zan iya ɗauka na bayar saboda asirin yar uwata ya rufu. Kana kallo wanda zata auran ɗan manyan mutanene masu kuɗi idan aka kaita babu kaya ai abin gori zai zamar mata".
Kallonta ya ringayi jin abinda ta ce, wato shi da yake ɗan talakawa shi yasa zata tare masa babu kayan ɗaki ko kuma a ɗaga tariyar har sai randa suka samu kuɗi kenan ko me take nufi? Kamar ta shiga zuciyarsa tayi saurin cewa
"Karka fassara maganata da wata ma'ana naji kayi shiru, na san kai ni kake so ka kuma sha faɗar ko da tabarma aka kawoni gidanka baka da matsala dukda hakan ma ba zata faru ba. Shi kuwa Faruk har tausayin Nurati nakeji dan wlh ni dai banji a jikina tayi dacen miji ba"
" Ya zaki ce haka? Ni dai ganin da na masa banga wani aibu a tareda shi ba yana da nutsuwa sannan yana son ta" cewar Bilal, ta ce
"Hmmmm" irin ba zaka gane ɗin nan ba kafin suka sake yin shiru har suka isa gida.
Maganar Ummansu ta sake masa yanda Haliman ta gaya masa
"Abinda ya sa har nake faɗa maka saboda kai an rigada an zama ɗaya dukkanmu masu taruwa mu rufawa juna asiri ne dan ba yau aka fara ba" cewar Umman, yayi shiru kafin ya ce
"Babu damuwa Umma ba za'a ɗaga tariyar ba, dama akwai kayan da na ce miki na bayar da kuɗi a yi sanda ta ce kayan ɗaki take so ba lefe ba, zan masa magana idan ba'a siyar ba tunda dama basu maido mun da kuɗi na ba sai a karɓa idan ma an siyar sai a samo wasu tunda suna da kayan a zube a gurin".
Umman ta ringa zuba masa godiya harda hawaye haka Zulaihan data rakashi duk sai tausayin su ya rufe shi, ya san basu da shi, shi ba dan Umman ta ce a basu kuɗin lefen ba dama niyya yayi ya mata kayan ɗaki kuma ba zai barta haka ba zai mata ko akwati biyu ce ta kayan sakawa. Ya ɗan jima dan mota suka shiga murnar kayan ɗaki tuni ta manta da cewar da tayi ba zata sake yin wani abu dan ta faranta masa rai ba sai ta tare, shima kuma da yake kwana biyu bai samu ba ba Halima babu Jalilah ya biye mata dukda ba wani nisa sukayi ba ta shige gida shima ya wuce.
Tun daga bakin get mamakin mai ya faru a gidan ya kamashi saboda ganin kwalaye da ledoji harda kofuna da robobin take away dana Rufaida duk an watsar dasu a ƙofar gidan. Ya sauka ya buɗe get nan ya tarar da tsakar gidan ma kaca kaca da wasu tarkacen a ajiye, komawa yayi ya kashe motar dan ba zai iya shiga da ita a yanda gurin yake ba ba shiga yana mamakin meya faru? Ko ɓarayi ne suka shiga? Amma kuma da wahala ace ɓarayi su shiga gidan bayan layin a kulle yake da get kuma masu gadin basa matsawa ko ina.
Ta window kitchen ya hango saman drawers ɗin ta dake cike da kwalayen flask da sauran kayan amfanin da bata buɗe ba babu komai a gurin, gabansa ya faɗi, da sauri ya tura ƙofar falon ya buɗe ido yana kallon gurin da ke nan fili fetal kuma an share tas babu ko tabarma a ciki. Sai lokacin ya lura ai dama bai hango labule ba tun daga waje.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 50*
Turus yayi yana bin falon da kallo zuciyarsa tana ƙara gudu, shiga yayi ciki da kyau har sannan yana ƙoƙarin gane abinda yake faruwa. Ƙofar ɗakin Halima ya tura, nan ya tarar da gurin shima tamkar falon babu ko tsinke anyi shara da alama ma har mopping akayi. Sakin ƙofar yayi ya matsa ya buɗe ta ɗayan ɗakin da yake mazaunin nasa; a nan ne ya tarar da kaya zube a ƙasa wanda kallo ɗaya ya musu ya fahimci nasa ne.
Ɓacin rai haɗi da baƙin ciki suka kamashi lokaci ɗaya, fita yayi daga nan ya wuce part ɗin sa da sauri domin zuwa yanzu ya fahimci su Halima ne sukayi gidan tsirara. Ta window nan ɗin ma ya hango filin gurin sai tsirarun kayan da suke mallakinsa na falon kamar DSTV decoder sai wani teburi da sai bayan tafiyarta ya kawo shi gidan ya ɗora computer akai dan yana shirye shiryen fara Forex trading da zarar ya haɗa kan kuɗaɗen shagunan Jalilah daya siyar.
Bai shiga ɗakin ba dan ya tabbatar yanda yaga falon an masa tik haka zai tarar da cikin ma saboda dai komai da yake gidan ya sani mallakinta idan aka cire kayan sakawarsa sai yan tsirarun abubuwan da ba za'a rasa ba. Tunga ya ja yana saƙa da warwara a ransa, bai taɓa zaton zasu kwashe kaya ba domin ya san basu rabu da Halima ba, Halimar daya sani ba zata iya rabuwa dashi haka salin alin ba tilas ta dawo masa ko kwashe kayan ma ya sani ba zai wuce wannan yar abu ta kazan ƙanwar Babar tata bace Labiba dan dai ko Mama yana da yaƙinin ba zata ce azo a kwashe kaya daga yin saki jiya ba.
Guri ya samu cikin tarkacen da suka watso tsakar gidan ya zauna saboda kansa da ya ji ya sara masa, shi da ya gama lissafi akan kawai Zulaiha zata tare a nan gidan shiyasa ko da suka kawo zancen babu kayan ɗaki bai musa ba idan ya so daga baya a hankali sai ya shiryawa Halima can gidan idan ta tashi komowa ta tare a can ɗin shine suka masa akuya suka rusa masa lissafi.
Ko me ya tuna kuma ya miƙe da sauri kamar wanda aka zabura ya fita. A ƙofar gidansa ya tsaya yana ƙwalawa Iliyas, ɗaya daga cikin masu gadin bakin layin kira yanda kasan duniya ce zata tashi. Ilyas ɗin ya taso da sauri jin kiran kamar ba na lafiya ba, ya ɗan rusuna ya ce
"Lafiya Alhaji?"
"Wace lafiya? Kuna ina ɓarayi suka hauro mun gida suka kwashe kaya suka fita da su?" Bilal ɗin ya faɗa cikin kiɗimar ƙarya, Ilyas ya kalle shi ba yabo ba fallasa ya ce
"Ɓarayi kuma?"
"Eh, ko da yake ba ma zai yuwu ace ɓarayi bane sai dai idan da ku aka haɗa baki, wato kunga matar gidan bata nan shine kuka daidaici na fita kuka shiga kuka kwashe mun kayan gida ko? Toh wlh kotu ce zata rabani da ku, sai kun gwammace kiɗa da karatu zaku san kun jangwalowa kanku tsiya" Bilal ɗin ya faɗa yana zaro waya a aljihu.
Basiru, ɗaya mai gadin da hargagin Bilal ya saka ya taso ya ce masa
"Ji mana Alaji, karka kuskura ka sake ce mana ɓarayi idan ba haka ba zaka sha mamaki wlh. Dan muna aiki a nan ba yana nufin bamu da ƙima ko daraja ba da kowa zai taka mu yanda yake so, da kuma zaka zo kanawa mutane haukar ƙarya, waye bai san ka saki matar gidan ba?
Ta zo ta kwashe kayanta, kawai ka