Showing 138001 words to 141000 words out of 257873 words

Chapter 47 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

480

stroke da tayi sannan ta shiga doguwar suma. Shi dai Abba daya gama sauraronsa saida ya kwashi kusan minti goma a zaune kafin ya iya buɗe baki yayi magana tsabar yanda ya shiga shock, suna raye a duniya wace irin damuwa ce haka Halima take da ita da har take barazana ga rayuwarta amma basu sani ba?

Dr ne ya ringa kwantar masa da hankalin ganin yanda jikin sa yayi laƙwas ya kasa cewa komai sai ajiyar numfashi kawai yakeyi. Haka nan ya shanye maganar a cikin sa duk yanda Mama ta ringa nacin ya faɗa mata yanda sukayi da likitan amma yace mata babu komai, ta kaɗa ta raya tayi kukan duk a banza yaƙi faɗa mata domin ya san damuwar da take ciki a yanzu kaɗan ce akan ya sanar mata da ainihin halin da Haliman take ciki.

Buɗe ƙofar da akayi ya sake ya dawo daga dogon tunanin daya tafi, Alh Saleh mijin Anty Labiba ya tsaya daga bakin ƙofar yana cewa
"Dan Allah Alhaji kazo kayi mata magana ko kai zata saurareka" sai ya miƙe yana cewa
"Wacece"
"Labiba mana, gata nan wai gidansu Mijin Halima zata tafi" ya bashi amsa jin haka ya saka Abba ya fita da sauri dan dama tunda ya dawo ya tarar da rigimar Anty Labiba taje har can gidan Bilal bata same shi ba ranar da aka kai Haliman asibiti taji ba'asin me yayi mata shine yanzun ma ta tada bala'i kamar zata hau iskokai Mama da Mama Fauziyya na riƙeta tana fizgewa wai gidansu Bilal zata tafi idan ma bata same shi ba sai ta saka an ɗaure Hajja ai dole ya fito duk ma inda ya shiga ya musu bayanin abinda yayiwa Halima.

Tsawa Abba ya daka mata ganin yanda ake riƙeta tana fizgewa duk ta tara mutane sun tsaya suna kallonsu, ta fashe da kuka tace
"Na rantse da girman Allah bai isa ya kasheta yaci banza ba har in wani abu ya samu Halima wlh sai na ɗaukar mata fansa akansa". Cikin faɗa Abba yace

"Bana son shashanci Labiba da girman ki zaki ringa abu kamar wata ƙaramar yarinya shikenan Allah ba zai jarabci bawa da lalura ba sai wani ya zama sila? Kada na sake ji, ku tashi ma ku wuce gida kawai tunda hayaniya zaki tayarwa da mutane". Haka ya tattarasu duka da sauran yan dubiyar da suka zo dukda babu wanda ake bari yana ganinta bayan su amma dangi kamar masu jira ana cewa bata da lafiya suke ta tururuwar zuwa dubiya, gashi dai babu wanda ya san takamaiman abinda yake damunta haka nan duk wanda yazo ya tafi zai haɗa nasa kalar labarin da ciwon da zai ɗora mata, amma dai maganar data fi ƙarfi ta kuma fi shahara a gari ita ce Guba ta ci saboda Bilal zai ƙara aure kamar yanda wacce ta fara kai labari Galadanci can gidan kakannita tace daga majiya mai ƙarfi ta samo bayanin gurin ɗaya daga cikin ƙannen Bilal.

BILAL

Bayan daya sauke su kai tsaye gidan Hajja ya nufa, tuƙi kawai yake amma bashi da nutsuwa a tattare dashi. Tsakanin sa Allah tun waccen ranar da Halima ta bankaɗo sirrinsa yake jinsa tamkar tsirara yake yawo, kamar kowa ma yasan abinda yake aikatawa a ɓoye. Koda da yake nuna tamkar komai ba komai bane kawai yana yi ne saboda ya ceci kansa amma shi kaɗai yasan kalar kunya da nadamar da yake ciki a yanzu. Tsautsayi da ƙaddara ya saka koda ya lura ya bar wayarsa a gida bai koma ya ɗakko ba saboda yasan Halima bata da ɗabi'ar bibiyar masa waya ko lokacin da baya saka password babu ruwanta da wayar sa balle yanzu daya kulleta ya kuma san babu ta yanda za'ayi ta iya buɗewa koda ace ma tayi niyyar hakan.

A tsakar gida ya tarar dasu Fadila tsaye da akwatinta tana ganin sa tace
"Yawwa gashi nan ma yazo ai" Hajja tace
"Kai kuwa ina ka jefa wayarka tun asuba nake kira baka amsa ba ko ka manta sammako zatayi? Shiyasa fa tuntuni nace ka bata kuɗin motar ta a hannu saboda irin haka yanzu da ƙyar idan zata samu motar farko sai tayi jira wata ta cika".

Cikin falo ya shige ba tareda ya amsa ta ba ya zauna kan kujera haɗi da dafe kansa da hannu biyu, Hajja ta shiga tana cewa
"Au ina magana shine zaka shige ɗaki ko ka amsa ni?"

"Ai tafiyar tata ba zata yuwu ba ma Hajja" ya faɗa yana gyara zama, sai ta zauna itama tana cewa
"Saboda me?"
"Mun ɗan samu matsala ne da Halima ta tafi gida, kinga kuma idan ta tafi ai ba zai yuwu ki zauna ke kaɗai ba tunda har yanzu jikin ki da saura" ya bata amsa. Sai kuwa ta zabura tace

"Kaji yar abu ta kazan uba au saboda zanzo gidan shine tayi yaji?"

"Bafa dalilin zuwanki bane" yayi saurin katseta, Fadila tayi tsugul tace
"Wlh saboda haka ne dama ai na gaya miki wlh da wahala ta yarda ki zauna a gidan nan dan ji take kamar na ubanta bata so kowa ya shiga sai ita da danginta".

"Ke, waya sako bakinki ko sa'anninki ne suke magana?" Ya faɗa yana ballawa Fadilan harara, Hajja ta taso masa itama tana cewa
"Ko ba'a sako da ita ba ai gaskiya ta faɗa, to kuwa bata isa ta hanani zuwa gidan ka ba billahilazi tunda haka ta zaɓa to kuwa ta tafi kenan sai ka tafa mata resit ka bita dashi kaga sai tayi zama mai lasisi kai kuma ka samu sarari ka auro mutuniyar kirki da suka gaji arziƙi ka saka ina dama duk ita ta kanainaye komai da anyi magana kace Halima to yanzu ta tafi Kuma in dai da yarda ne kar ta sake dawowa cikin gidanka ya isa kuma haka a canza sheƙa".

Shiru yayi kansa a ƙasa, ya za'ayi Hajja tace ya saki Halima? Sannan kuma tayaya zai gaya mata shi fa ko aure zaiyi ba Jalila zai aura ba ko dan bata san ainihin alaƙar dake tsakaninsa a Jalila bane?

Miƙewa yayi a a sanyaye yana cewa
"Idan ta huce dai na san zata dawo"
"Ta dawo ina? Ai wlh kaji ma na rantse ta tafi kenan. Ba dai dama ni na dage sai ka aureta ba na ɗauka dangin arziƙi ne ashe duk shigo shigo ba zurfi suka mana, tunda kuwa yanzu ta saka ƙafarta ta tafi to kuwa ba zata dawo ba kama cireta maza daga ranka ka tattara hankalinka kan wannan yarinya Jalila ayi maza ayi komai ita kuma can su ƙarata Allah sauki tsiya lafiya".

Da wata sabuwar damuwar ya fito daga gidan Hajja, can gefen hanya ya gangare ya kashe mota ya kife kansa jikin sitiyari ya tafi tunanin haɗuwar sa da Jalila.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 35*

Amirah ta ɗaga Sharifa data saka kuka daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu.
"Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya, Suraj ya ajiye kayan yana cewa
"Tareda Babansu suke" ya juya ya fita sai Amirah tace
"Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace
"Toh lafiya dai?"
"Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko saurarona ma batayi ba" Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana kallon Al'amin daya haye kan kujera ya kwanta alamar baccin sa zai cigaba, sai ta juya kitchen ba tareda tace komai ba amma zuciyarta cike da saƙe saƙe.

Kan gado na faɗa bayan dana shiga ɗakin dafe da ƙirjina da nake ji tamkar an ɗaure ni da igiya, daƙyar nake fuzgar numfashi, na ringa juyi a kan gado ni kaɗai tsayin lokaci kafin ubangiji ya kawo mun rangwamen abinda nakeji ta hanyar rabani da numfashina na wani lokaci.

A waya Mama ta kira Abba, tambayar sa tayi ko Bilal yace masa wani abu ne tunda ance tare muka zo sai ya ce mata
"Bai tsaya ba yana sauke musu kayan su ya juya ko gaisawa bamuyi ba"
"Ikon Allah, to mai ya faru?" Ta sake tambaya cikin jimami. Daga can yace
"Ni kam ina zan sani ne Amina? Ba gata nan a cikin gidan ki tambayeta mana", jin kamar ya fara fusata ua saka tace
"Toh shikenan sai ka dawo" ba tareda ya bata amsa ba ya katse wayar dan ransa y sosu matuƙa da ko in kulan da Bilal ya musu. Sosai yaji ba daɗi sanda Alhaji Bala da suke tsaye yace masa
"Wannan ba Mijin Halima bane naga yaja mota bai ko tsaya ya gaida mu ba? Koda yake yanda ta shige itama kamar dai akwai matsala dan na lura bata ma ga tsayuwarmu ba, amma shi ai idan ɗan arziƙi ne yaci ko matsala suka samu ya tsaya nan ya maka bayani ba yaja mota ya tafi ba".
Wannan maganar ta dame shi har ta saka ya fasa komawa cikin gidan da yayi niyya ya sallami Alhaji Balan kawai ya wuce inda zashi ya a tafe kuma yana tunanin dalilin zuwan Halima da sassafen nan.

Sai gurin ƙarfe tara Mama tace Amirah ta shiga ta kirawo Halima ta karya lokacin har tayiwa su Al'amin wanka sun ƙoshi sun shiga sabgogin su, ihun da Amirah ta fasa bayan shigar ta ɗakin ya saka Maman tashi da sauri tamkar zata hantsila ta shiga ɗakin, gabanta ya yanke ya faɗi ganin Amirah tsugunne kan Halima tana girgiza ta haditda kiran sunanta amma ko gezau bata motsa ba, cikin tashin hankali ta isa gaban gadon ta ɗagota jikinta ta shiga jijjigata da ƙarfi amma bata koyi alamar zata farka ba.

"Ta mutu innalillahi mun shiga uku Yaya Halima ta mutu" Amirah ta faɗa hannu biyu akai cikin matsanancin kuka Mama dake rungume da Halima ta ɗaga mata hannu tana cewa
"Bata mutu ba fita ki kira Mu'azzam, kiyi sauri dan Allah yazo mu kaita asibiti" ta ƙarasa tana ƙoƙarin buɗe idanun Haliman. Da gudu Amirah ta nufi ƙofa sai kuma ta juyo cikin kuka tace
"Kin manta ya tafi makaranta tun ɗazu yana da exam yau?"

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Amirah ki fita kowa kika gani ki kira mu kaita Asibiti" Mama ta faɗa tana fashewa da kuka itama. Tareda Samari biyu Amirah ta dawo wanda a waje ta taresu sun taho a mota su suka ɗauki Haliman suka fito da ita daga Mama har Amiran babu wanda ya tsaya neman koda Takalmi suka biyo su Zainab na kuka riƙe da Sharifa haka Al'amin dukda ba wai sanin mai yake faruwa yayi ba kawai ganin sunayi ya saka shima ya kama. Suna ƙoƙarin sakata a motarsu Suraj ya iso ƙofar gidan dan dama tare suka fita da Abba ya kaishi Airport zai tafi Lagos, motar sa Mama tace su sakata suka shiga ita da Amirah ya ja motar da gudun gaske suka nufi asibiti.

Bayan tsayin lokacin dana ɗauka tsakanin mutuwa da rayuwa na farka, na buɗe idanuwana da naji tamkar an manne mun su da super glue daƙyar na iya buɗe su na kalli in da nake saidai ban fahimci komai ba hakan ya saka na sake mayar da idanuwan nawa na kulle ina jin sautuka sama sama kamar daga can nesa. Mama dake zaune kan kujerar dake kusa dani ta miƙe da sauri saboda ƙafata dana motsa, ta kira sunana, dukda ba wai na fahimci mai ta faɗa ba sautin da naji ya saka na sake buɗe idona na sauke akan fuskarta. Ta kama hannuna hawaye na ziraro mata tace

"Kin farka Halima?" A hankali tamkar mai koyon magana na kira sunanta a rarrabe "Ma..ma" haɗi da matsa hannunta data riƙe nawa dashi. Cikin kuka mai haɗe da dariya ta amsa da
"Na'am Halima kin farka? Alhamdulillah". Ji nayi maganganunta suna hau mun kai sai na sake mayar da idona na rufe tayi azamar kamo fuskata tana cewa
"Ki tashi dan Allah kada ki sake komawa Halima dan Allah ki buɗe idonki ko hankalina zai kwanta" ta ƙarasa cikin kuka. Na sake buɗe idona na kalleta, tabbas naga ƙauna mai tsanani haɗi da tausayi cikin ƙwayar idanunta dake tsiyayar da hawaye, kalaman Bilal da ya ce "Da uwarki nayi zina" suka dirar mun tamkar saukar mashi take wani abu ya taso ya sake tokare mun maƙogaro, ban iya yin abinda ta buƙata ba na sake mayar da idanuna ruf na rufe su sai ta saki hannuna ta nufi ƙofa kusan da gudu ta fice daga ɗakin ba jimawa suka dawo tareda likita da Nurses biyu. Sai da ya gama dubani kafin ya kalleta cikin kalaman kwantar da hankali yace

"Kiyi haƙuri Hajiya na faɗa miki jikinta yana da buƙatar hutu sosai zata farka idan lokacin hakan yayi in sha Allahu ki daina damuwa zata samu lafiya da yardar Allah"

"Likita ta farka fa, ta buɗe idonta har magana tayi mun kafin ta sake komawa dan Allah likita kayi wani abun yarinya ta ta farka kaifa kace mun awanni kaɗan amma gashi kwana biyu kenan bata farka ba". Kwana biyun data ambata ya saka na sake buɗe idona na kalle su, hannu biyu ta ɗaga tana cewa
"Alhamdulillah, ka gani ko idonta biyu". Ganin tana ƙoƙarin ɗago ni ya saka ya dakatar da ita, a hankali ya kira sunana na kalle shi yace

"Kina jina Halima?" Nayi shiru badan bana jin sa ba sai dan bansan ta yanda zan amsa masa ba. Bakina yayi mun nauyi tamkar an ɗaure mun harshe. Cikin taushi ya sake kiran sunana da maimaita tambaya ina jinsa amma na kasa amsawa. Mama ta fashe da kuka tana cewa

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Dr mai ya samu yarinyata dan Allah kayi mun bayani ni Musulma ce koma menene zanyi haƙuri na karɓi ƙaddarar data samemu".

"Dan Allah Hajiya ki nutsu, idan ba zaki iya shiru ba kuma ki fita waje. An gaya miki babu abinda ya sameta kawai tana buƙatar lokaci ne babu yanda za'ayi mutum ya tashi daga dogon suma irin haka kiyi tsammanin nan take tunanin sa zai dawo tamkar yanda yake a da sannan wannan hayaniyar da kukan da kikeyi shima kina ƙara mata wata damuwar ne cikin wadda take" ɗaya ɗaga cikin Nurses ɗin ta faɗa a hasale, sai ta juya cikin kuka ta nufi ƙofa na bita da kallo ina so in tsayar da ita amma kuma banida ikon yin hakan.

Wata yar fitila likitan ya kunna ya shiga haska idanuwana bayan ya gama ya zaro biro daga aljihun rigarsa yace
"Idan kina jina ina so ki ringa bin biron nan da idonki duk inda nayi dashi kinji?" Na lumshe idona kafin na buɗe nayi abinda ya ce. Ya mayar da biron aljihu yana cewa

"Yawwa Halima, yanzu ki motsa ƙafar ki na gani" nayi yanda yace sannan ya kama hannuna yace in matsa hannun sa nan ma nayi sannan ya sakeni, cewa yayi na tashi na zauna. Nayi jimm dan kwata kwata banajin alamar ƙashi ko tsoka a jikina ji nake tamkar a iska nace, sai da ya sake maimaitawa kafin na yunƙura a hankali naja jikina Nurse tayi saurin saka mun pillow a bayana na jingina ina mayar da numfashi tamkar wadda tayi tseren gudu. Hamdala yayi kafin ya karɓi folder dake hannun Nurse yayi rubutu ya bata yace taje pharmacy ta karɓo abinda ya rubuta sannan idan ta fita ta turo masa Mama.

Tare suka shigo da Abba, Mu'azzam, Anty Labiba da Mijinta sai Mama Fauziyya. Gaba ɗayan su kallo ɗaya zaka musu ka karanci hashin hankalin da suke ciki, Abba ya matso ya dafa kaina nayi karfin halin tattaro kalmomi na haɗa na kira sunansa, "Abba" ya amsa yana shafa kaina
"Na'am Halimana kin tashi?" Sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya kuka ya kwace mun Abba ya rungume ni yana cewa

"Kuka kuma Halima menene? Kiyi shiru dan Allah kinga halin da kike ciki babu abinda zai faru ki dena kuka kinji?"

"Ina ganin kuyi haƙuri ku koma waje ƙila ganinku ne ya dawo mata da wani abun kuma a yanayin da take ciki yanzu bama son duk wani abu da zai sosa mata rai balle ya sake ƙara mata wata damuwar" likita ya faɗa. Duka suka fita banda Abba dake rungume dani idanuwansa sunyi jajir tamkar shima zai yi kukan yana ta bubbuga bayana da cewa nayi shiru, Nurse ɗin da Dr ya aika ta dawo da allurai da da drip ya karɓa ya fara haɗawa, zai zare ruwan dake hannuna Abba ya dakatar dashi yace

"Dan Allah kada ka saka mata abinda zai sake mayar da ita wannan baccin"
"Amma Alhaji saboda lafiyarta ne" cewar Dr, sai Abba ya girgiza masa kai yace
"Na sani amma ka ɗanyi haƙuri ku bamu guri zanyi magana da ita". Tsayawa yayi kamar ba zai fita ba kafin ya juya, Nurse ɗin da ta yiwa Mama magana ɗazun ta buɗe baki zata sake magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa su fita.

Sai sa suka rufo ƙofar kafin Abba ya ɗago kaina daga kafaɗar sa yace
"Kukan ya isa haka Halima kiyi shiru kinji"
"Tsoro nakeji Abba" na faɗa daƙyar kafin na kama hannunsa na ɗora saitin zuciyata da nakejin ciwo tamkar an hura mun wuta nace
"Zuciyata zafi takeyi Abba mutuwa zanyi"

"Ba zaki mutu ba Halima har sai lokacin da ubangiji ya rubuta faruwar hakan, duk wani tsanani a rayuwa yana tareda sauƙi kiyita nanata Hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarki in sha Allahu zaki samu salama kinji?"
Kai na ɗaga masa alamar naji take kuma na kama na shiga nanata Hasbunallahu a hankali a hankali na fara jin abinda ya tokare mun maƙoshi yana zagwanyewa, zafin da zuciyata take mun ma ya fara raguwa inayi Abba ma na biyawa a fili sannu sannu har bacci ya ɗauke ni. Ajiyar zuciya ya sauke ganin nayi bacci, sai da ya ɗauke ƙwallar data zubo masa kafin ya gyara mun kwanciya akan gadon ya lulluɓa mun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login