Showing 132001 words to 135000 words out of 257873 words

Chapter 45 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

483

muryarsa tana cikin sautikan da bana fatan sauraronsu a kusa dani, muryoyin da nayi matuƙar ƙoƙarin koresu daga kaina suka shiga dawo mun, voice ɗin ƙarshe dana saurara wanda ba zan iya maimaita kalmomin da suke ciki na suka shiga dawomun sai na saka hannu biyu na toshe kunnuwana ina jujjuya kaina da nake jin tamkar zai tarwatse saboda azabar ciwon da yakeyi mun daidai lokacin kuma ya shigo ɗakin ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallona kafin ya ce

"Lafiyarki kuwa Halima?"
Ban amsa ba illah cusa kaina da nayi tsakanin cinyoyina dan bana son ganin sa, ina jinsa ya nufoni yana sake nanata
"Mai ya faru? Wani gurin ne yake miki ciwo ko kanki ne?" Ya faɗa yana tsugunnawa a gabana. Daƙyar na ɗaga kai na kalle shi na ce
"Ka tashi ka fita kai ka dame ni kaine bana son gani ko sauraron muryarka a kusa da ni".

"Kanki ƙalau kuwa Halims yau ni kike faɗin baki son gani na naki son jin muryata ko dai gamo kikayi da Aljanu?" Ya faɗa yana ƙoƙarin kama fuskata. Cikin zafin nama na fizge take kuma na ɗaga hannu na sauke masa mari a kuncinsa kafin na miƙe tsaye cikin kuka da hargagi nace
"La fitar mun daga ɗaki Bilal ka fita idan ba haka zan maka abinda har duniya ta naɗe na zaka manta da ni ba".

Ya miƙe tsaye cikin tsananin mamakin abinda na aikata masa yana dafe da gurin da na mare shin yayi taku biyu yaja baya yana kallona amma ya kasa cewa komai. Hargagina ya farkar da Sharifa ta ƙwala ihu sai ya nufeta nayi saurin bangaje shi na ɗauke ta ina cewa

"Koda wasa kada ka kuskura ƙaramin hannunka ya taɓa mun ya, iya zunubin daka ɗiba ya ƙare a kanka Allah ya isa tsakani na da kai Bilal kuma wlh har idan mugun halinka ya shafi yayana bazan taɓa ƙyale ka ba" na ƙarasa ina kaiwa ƙasa dan gaba ɗaya jikina babu sauran kuzari. Har ya buɗe baki zai sake mun magana idon sa ya sauke akan wayar sa dake ajiye a ƙasa dan haka ya tsugunna ya ɗakko, ina kallonsa ya buɗe, a cikin chat ɗin nasu na barta kan wani video da ta turo masa ina kallo ya runtse idonsa haɗi da dunƙule hannun sa kamar zai kai naushi kafin ya saci kallona.

Nayi murmushin takaici na ce
"Kaji kunya Bilal wlh kaji kunya. Mumini a fuska ashe a zuciya tantirin ɗan is...."
"Ya ishe ki Halima kada ki kurkura ki furta abinda yake kan harshen ki idan ba haka ba sai kinyi nadama wlh, kar kiga kin mareni na rabu dake na ɗauka bakya cikin hayyacin ki ne amma yanzu tunda na lura kina sane kada kiyi gigin kawo mun wani hauka dan zanyi maganinki ne" ya dakatar dani cikin tsawa sai dai duk maganar da yayi bai bari mun haɗa ido ba yayi ta ne yana kallon wani guri daban.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 34*

Kwanaki biyu da suka biyo baya nayi su ne cikin taimakon ubangiji domin a kowacce daƙiƙa ji nakeyi tamkar numfashi na zai iya yankewa. Babu abinda yake shiga cikina banda ruwa da paracetamol da nake ta banka saboda azababben ciwon da kaina kama, ikon Allah kaɗai yake riƙe dani akan ƙafafuna hatta yaran ma game game kawai nake musu duk abinda hannu ya kai nake haɗawa na basu su ci.

Nayi kuka har hawayena sun ƙafe ya zama sai na zuci nakeyi, a duk sanda na tuna abinda naji kuma na gani dangane da Bilal sai inji na tsani kaina. Ban san ta inda na gaza ba, ba yabon kai ba na sani ko a cikin mata samun irina mai kula da tsaftar jikinta ciki da waje sai an tona. A koda yaushe na kanyi ƙoƙarin na kasance a yanda idonsa ba zai taɓa ganin wani abu da bazai so ba a tareda ni. Bana wasa da kyaran jikina a duk sanda na samu kuɗi kafin nayi komai sai na ware wanda zan siyi duk abubuwan da nake buƙata na amfanin kaina kuma saboda shi. Ina ɗaukar last kwabo na na siya abun daɗi naci saboda jikina ya samar da ni'imar da zata gamsar dashi, ban taɓa damuwa da rashin yi biyamun buƙatu na yau da kullum da yakeyi ba ni dai burina a kullum nayi abunda zan faranta masa amma ace ya rasa abinda zai saka mun da shi sai wannan?

Wai tun yaushe ma yake aikata hakan ba tareda na sani ba? Tun kafin muyi aure dama haka yake ko kuwa daga baya ne ya fara? Bani da mai bani amsa amma abinda nafi ƙarfafawa shine bayan aurenmu ko ma in ce bayan na haihu tunda shine lokacin daya fara zaryar zuwa Abuja da sunan aiki ashe abinda yake kai shi kenan. Na tuna lokacin da na tafi gida wankan Al'amin sanda yazo ganinmu bai ko nuna ɗoki ko alamar yayi kewata ba har naji haushi a lokacin ashe dalili kenan. Tun bayan sannan dama ya koma part ɗin sa gaba ɗaya da kwana kuma daga lokacin ya auri chat koda yaushe ya zauna wayarsa na hannu yana danne danne ashe dalilin kenan.

Babban abinda ya sake bani mamaki dashi ta yanda tunda ya fita daga ɗakina wancen daren tsayin kwana biyun bai sake tako ko da kan barander ta ba balle ya shigo yayi mun magana ko yayi mun wani bayani da zai kare kansa balle har ya rarrasheni ko ya nuna nadama akan abinda ya aikata ɗin. Ko da yake ni kaina bansan zaman me nakeyi a cikin gidan ba domin a yanda bake jin zuciyata bai kamata ace na ƙara kwana a ƙarƙashin inuwa ɗaya da shi ba amma kuma na rasa ƙwarin guiwar yin hakan. Allah ya sani ina Son Bilal irin Son da zuwa yanzu na yarda jarabawa ce a tattare dani a kusa ko a nesa kuma bana fatan wani abu da zai rabani dashi amma a yanzu ban san me nakeji akan sa ba.

Da azahar ina kwance a tsakiyar falo ina juyi saboda azabar ciwon da cikina ya tasar mun da nasan yana da alaƙa da horon yunwar da nake yiwa kaina. Al'amin dana aika ya kirawo mun Maman Yusuf suka shigo tare, tana ganina ta ƙaraso da sauri tana salati haɗi da cewa
"Na shiga uku mai ya sameki Halima?" Da hannu na nuna mata cikina, ta ɗago ni zaune sai ta sake ɗaukar salatin daya fi na farko tace

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un kin ganki kuwa Halima? Kwananki nawa a kwance? Ina shi Baban nasu da ya barki haka sai kin mutu sannan zai kira iyayenki ya basu gawa ko me?"

Jin ta tsaya kwakwazo ya saka na kamo hannunta daƙyar na ɗora akan cikina da muryata da bata fita nace
"Cikina mutuwa zanyi". Sai ta miƙe jik na rawa tana cewa
"Ba zaki mutu ba in sha Allahu bari na kira Sadi mu tafi asibiti" ta fita kusan da gudu, ni dai ba zan ga sanda ta dawo ba haka dishi dishi naji sanda aka kwasheni aka fita dani daga lokacin ban sake sanin komai ba sai farkawa nayi na ganni a gadon asibiti Bilal na zaune a gefena. Mayar da ido na nayi na runtse bayan dana fahimci a inda nake, ya miƙe tsaye haɗi da kamo hannuna yana cewa

"Kin tashi Halima?" Ban amsa ba sai janye hannun da nayi daga nasa na yunƙura na gyara kwanciya ta ta hanyar bashi baya, ina jin sa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya fita daga ɗakin ba'a daɗe ba suka dawo tareda likita. Likitan ne ya kira sunana dan haka na gyara kwanciya ta ba tareda na amsa ba ya sake maimaitawa yana cewa

"Halima bakya ji nane?"
"Ina jinka" na bashi amsa cikin muryar da bata fita sosai. Yace
"Masha Allah sannu kinji, ina ne yake miki ciwo yanzu?" Sai na girgiza masa kai alamar babu. Matsowa yayi ya saka abun awon bugun zuciya a ƙirji na kafin ya cire ya ɗauki abun auna Bp ya saka mun a hannu sai da ya gama sannan ya kalli Bilal yace

"Jinin ya sauka sosai yanda ya kamata bata cikin kowanne haɗari yanzu". Bansan sanda na saki tsaki ba jin Bilal ɗin yana cewa
"Alhamdulillah har hankalina ya kwanta" duk su biyun suka kalleni ni ko dama basu nake kallo ba, likitan ya sake cewa

"Bari naje idan ruwan ya ƙare sai kayiwa Nurse magana tazo ta cire mata ina ganin za'a sallame ku ma ba sai ta kwana ba tunda jikin yayi sauƙi, ni zan shiga wata theater yanzu idan mun gama zan sake zagayowa sai kayi mata bayani kuma" ya faɗa yana dafa kafaɗar Bilal ɗin. Bayan fitar Dr ya koma ya zauna kan kujerar daya tashi cikin lafazin da a baya nake so yake kuma jefani cikin shauƙi da begen sa ya ce
"Faɗuwar da kikayi ɗazu kafin muzo Asibiti kika fara bleeding, toh bayan mun iso da suka gwada suka ce kina da ciki kusan wata uku" sai yayi shiru. Na gyara kwanciya ta na zuba masa ido ina so naji ƙarshen maganar tasa, wai ina da ciki, a yaushe nake da cikin har kusan wata uku amma ban sani ba? Jin yayi shiru ya sunkuyar da kai yasa nayi ƙarfin halin cewa

"Sai me ya faru daga nan toh?" Ya kamo hannun na fizge haɗi da jefa masa wani kallo sai ya matsa ya ce
"Dr yace a yanayin da kike barin cikin zai iya zame miki matsala shine na saka hannu aka ƙarasa fitar dashi dan dama ya rigada ya lalace". Ban san sanda na yi dariyar da kana ji zaka san ta zallar takaici da baƙin ciki bace na ce

"Ai dama na saba rainon cikin cikin ƙunci da rashin lafiya ko ka manta? Gara dai ka faɗa mun gaskiya baka buƙatar cikin shiyasa kace a cire shi kuma hakan da kayi ba laifi bane domin ko ba'a cire yanzu ba nima idan na sani ba zan barshi ba dan ba zan sake yarda na haɗa zuri'a da Maƙaryaciya, Maha'inci kuma Mazinaci mara tsoron Allah irinka ba" na ƙarasa ina kallon cikin idon sa. Take idanunsa suka canza launi, ya nuna kansa da yatsa ya ce

"Ni kike jifa da kalmar Zina Halima?"
"Karya nayi ba halinka bane?" Na faɗa ina kallon sa tar babu alamar tsoro ko nadamar hakan, sai ya miƙe tsaye, da fari na ɗauka zai rufeni da duka ne ko kuma ya mareni amma sai naga yaja da baya yana huci kamar wanda kunama ta harba, hakan ya bani damar cigaba da cewa

"Ban taɓa zaton haka kake ba Bilal, ka ci amanar So da yarda. Bilal mai nayi maka a rayuwa da ka zaɓi saka halaccin da na maka ta wannan hanyar? Laifi ne da na So ka na ce sai kai? Laifi ne da na fifita farincikin ka a kan na kowa? Dame na rage ka? Ta ina na gaza daka zaɓi zubar da ƙimarka da mutunchin ka haɗi da barin ubangijin ka ta hanyar aikata abinda yayi hani da? Bilal Zina da aurenka?.... "

"Wlh kika sake cewa tak Halima sai nayi miki abinda baki taɓa zato ba" ya katseni cikin hargagin da saida yayan hanjina suka juya. Ya nufoni idanunsa jajir har wani jirkicewa sukayi ya nunani ya ce
"Ki iya bakinki ki kuma san abinda kike furtawa idan ba haka ba" ya kaɗa yatsunsa biyu akan fuskata. Na haɗe yawu daƙyar saboda har ga Allah na tsorata da yanayin sa, ban kuma sake cewa komai ba kawai na maida kaina gefe hawaye suka shiga ziraro mun. Wannan shine a dake ka kuma a hanaka kuka, wannan naɗe tabarmar kunyar da yakeyi cikin hauka kuma ya sake tabbatar mun da cewar duk abinda na gani gaskiya ne. To ta yaya ma zai ƙaryata bayan da idona da kuma kunnuwana na ga shaida kuma a wayar sa ba wai wani ne ya faɗa mun ba?

Sai bayan sallar Isha'i likitan ya bamu sallama, dana sakko daga gadon zuciyata ta raya mun in fita na tari Adaidaita na tafi gidan mu sai lokacin na tuna banga yara na ba. Ina tsaye bakin ƙofar reception ya taho bayan yayi settling bill ya tsaya ba tareda ya kalleni ba yace "muje mana"
"Ina yarana?" Na tambaye shi yayi gaba yana cewa

"Suna gidan Alhaji Sani" (Gidan Maman Yusuf) shine dalilin daya saka na bishi na kwanta a bayan motar ganin ya nufi wata hanyar daban ba wadda zata kaimu gida ba kamar nayi masa magana sai kuma nayi shiru kawai. Can wani gurin siyar da kayan ciye ciye mukaje, ya fita ya barni ya ɗan jima saboda layi kafin ya dawo yana shigowa motar naji ƙamshin gashi ko Kaza ko Nama ga wata ledar da nake zaton Fura ce ko Yoghurt ya aje su a sit ɗin gaba ya tayar da motar. Ko kusan burgeni banji yayi ba, a lokacin Allah Allah kawai nake mu isa gida naga yarana daga nan na zauna nayiwa kaina karatun abinda zai fishsheni.

Ɗaki na wuce kai tsaye na faɗa wanka dan shi nafi buƙata a lokacin, ina wankan ina kukan daya rigada ya zame mun aboki a kwana biyun. Dana fito na jiyo surutai a falo dan haka na zura Hijab na fita na tarar da Maman Yusuf ce da Anty Amina kishiyarta sai Al'amin da su Kursum da Alina suke guje guje. Sannu suka shiga jera mun, na samu guri na zauna ina ɗan murmushi. Maman Yusuf ta ce

"Sannu Halima kinga ki har kin ɗan marmaro fuskarki ta ciki ba kamar ɗazu ba" ni dai nayi murmushi ba tareda nace komai ba sai ta sake cewa

"Ina fita muka ci karo da Baban nasu ai nasan ba lallai kin san ma ya aka fita dake ba dan naga kamar suma kikayi" sai tayi ƙasa da murya kafin ta ce
"Ya kuwa kira yan gidanku naga kun dawo ku kaɗai?"

Murmushi nayi nace
"Eh sunje asibitin" ta gyara zama ta ce
"Toh, ɗazun ne naga da nace ya kira iyayenki ya gaya musu kinga yanda ya hayayyaƙo mun kamar zai rufeni da duka nace toh ko shima irin mazan nan ne da basa son faɗa idan wani abu ya faru a gidan su?"

"Yo rashin lafiya kuma menene abun ɓoyewa ai kamata yayi ma ace iyayen su za'a fara kira a gaya musu idan abu yazo da ƙarar kwana ai dole a kirasu ace an mutu ai" Anty Amina ta faɗa suka jigaba da jajanta mun kafin shigowar Bilal ta saka suka miƙe Maman Yusuf na cewa
"Ko dai mu tafi da Sharifa a ƙarasa yayen kawai?" Nayi yar dariya tace
"Ai bama ta da damuwa naga taci abincin ta sosai suka sha wasa tayi bacci ko sau ɗaya batayi kuka ba". Har get na raka su ina musu godiya, a kitchen na hango shi yana ƙoƙarin ɗumama kaza a microwave na wuce ɗaki na kimtsa kaina, bana jin yunwa ko dan ruwan da aka saka mun ne dan haka nayi sallolin da suke kaina bayan na idar na haye gado na kwanta. Bilal ya sake shigowa ɗakin a karo na uku dan sau biyu yana shiga sanda ina sallah, ya kwantar da Sharifa da tayi bacci akan gado kafin ya tsaya a kaina yana kiran sunana.

Ban amsa ba haka nan ban motsa ba, ya miƙa hannu ya taɓa ƙafata na buɗe ido da sauri na kalle shi yayi gajeran tsaki ya ce
"Da idonki biyu dan wulaƙanci kina ji na kenan kika yi shiru" ban tanka masa ba ya sake cewa

"Ki taso kici abinci ki sha maganinki". Sai lokacin na tashi zaune na kalle shi nace
"Har yaushe ka fara damuwa dani ko lafiya Bilal?"
"Halima kada ki tunzura ni, ina duk iya ƙoƙarin da zanyi naga na biki a hankali amma naga alama magana kike so ki jani da ita. Rashin kunya da zagina da kika yi basu isheki ba so kike ki ƙara wani" ya faɗa yana harɗe hannayen sa a ƙirji. Sai na tashi zaune da kyau na sauke ƙafafu ƙasa na fuskance shi na ce

"Ƙwarai magana nake so muyi". Ya zuba mun idanunsa da suka canza launi kafin ya ja stool ɗin gaban mudubi ya zauna ya ce
"Ina sauraronki".

"Ka dubi Allah ka faɗa mun gaskiya Bilal dame na rageka a zamantakewarmu?" Na faɗa bayan shirun kusan minti biyu da nayi ina ƙoƙarin kamo ta inda zan fara magana, yayi tsaki ya ce
"Idan kina da magana mai muhimmanci kiyi"
"Wannan ita tafi komai muhimmanci a gurina domin ina so na san cikin zunubin ka ina da kaso ko babu" nima na katse shi, sai ya kalleni kafin ya ɗauke kai gefe ba tareda yace komai ba. Kukan da ban so zuwan sa a lokacin ba ya ƙwace mun dukda haka na ce

"Mai ya baka sha'awa a matan bariki Bilal? Mai ka taɓa nema nayi maka banyi ba daka gwammace ka fita ka nema a waje?"

"Kina ji ko Halima kowanne mutum da kika gani a rayuwa yana da kuskuren sa kuma da za'a ce kowa a tona nasa da ba lallai a samu sauran wanda za'a ringa yiwa kallon mutumin kirki ba a duniyar nan, idan da kina da tunani bai kamata ki bari abinda kika gani ya dameki har ki nemi ki hallaka kanki a banza da damuwa ba, kuma duk maganganun da kike faɗa kawai ina miki uzuri ne kuma ko da kike wannan surutun baki da qata shaida akan abinda kike zargin na aikata. Abinda kika gani kawai normal abu ne tsakanin Saurayi da budurwa amma gaba ɗaya kin wani mayar dashi kamar wacce kika kamani turmi da taɓarya da ita, idan ba ban yafe miki ba sai Allah ya bi mun kadin ƙazafin da kike mun domin baki da hujja" ya faɗa ba tareda ya kalleni ba.

Ni ko tunda ya fara magana hawayen da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login