Showing 123001 words to 126000 words out of 257873 words
Accident? A garin yaya? Ina suka je?
Bani da mai bani wannan amsar sai kawai na saka wayar a ajihun rigar dake jiki na na ɗauki Sharifa muka fita. Sai da na je get na tuna ban ɗauki kuɗin da zan hau mota ba na sake komawa na ɗauka. Daƙyar na samu abun hawa duk wanda na tare sai ya ce ba can ya yi ba, a hanya nayi ta sake gwada kiran Bilal amma wayar taƙi shiga. Yanda na ji muryar sa na san da alama yanayin babu daɗi a raina na ringa addu'ar koma menene Allah ya taƙaita wahala.
Hanani shiga securities sukayi duk yanda na roƙe su daga ƙarshe na koma gefe na cigaba da kiran Bilal har sannan kuma wayar taƙi shiga. Ga gajiya ga yunwa dake damuna ga sauron bala'i a gurin haka nan na tsaya a bakin ƙofa ina addu'ar Allah ya fito da shi ko wani da na sani ko zan samu su bar ni na shiga. Har ƙarfe tara muna tsaye kafin mai gadin yaga dama ya bari muka shiga. Ido na shiga warewa ina laluben ta inda zan hango su Hajjan amma ban dace ba. Wata Nurse na tambaya tace bata gane wa nake nufi ba, haka na ringa bi gado gado a can ciki na same su.
Hajja na kwace kanta da hannunta ɗaya naɗe da bandeji sai ledar jini da aka saka mata amma idon ta biyu. Ajiyar zuciya na sauke dan har ga Allah ban zaci haka zan ganta ba, irin yanda na ji muryar Bilal na ɗauka zanzo na tarar da ita a halin rai da mutuwa ne. Muna haɗa ido ta ɗauke kai gefe, na kalli sauran Anty Amina, Yaya Saude sai Fadila da Hadiza yar ƙanwar Hajja. Anty Amina ce kaɗai ta amsa sallamar da na yi musu, na jingina da gadon dan har jiri nake ji saboda yunwa da gajiya kafin na shiga gaishe su da tambayar mai jiki.
"Tun bayan magriba nake a waje maigadin ya hanamu shigowa ina ta kiran wayar sa kuma tun ina hanya bata shiga" na faɗa. Ina rufe baki Fadila tayi tsaki ta ce
"Ƙaryar banza"
"Ke Fadila meye haka?" Anty Aminan ta tsawatar mata. Murmushi kawai na yi kaina a ƙasa, kusan minti biyar duk munyi shiru sai ga Bilal da Hafiz sun ƙaraso gurin. A mutunce muka gaisa Bilal kuwa muna haɗa ido ya mun kallon da na fassara da harara. Hafiz ya karɓi Sharifa dake bacci a hannu na yana tambayar ina Dady na ce masa yana can gidan mu.
"Jikin nata ai da sauƙi ba kamar yanda na yi tunani ba" ya faɗa, a raina na ce
"Munyi biyu". Bilal ya ce
"Da sauƙi kam amma baka ga a yanda muka kawota asibitin bane Allah ya taimaka ta samu kulawa da wuri ne kawai amma da an ja wani lokaci irin jinin da ta zubar da ba wannan maganar akeyi ba".
"Toh Allah ya ƙara kiyaye gaba Allah kuma ya sa ya zame mata kaffara" cewar Hafiz gaba ɗaya muka amsa da "Amin".
Fita suka sakeyi da Bilal, na gyara tsayuwa ta dan ƙiris ya rage na faɗi babu kuma wanda ya mun tayin gurin zama a cikin su bayan wani lokaci suka sake dawowa. Sallama yayi musu bayan ya aje musu kuɗin da ban san ko nawa bane ba. Hajja ta ringa saka masa albarka haka su Yaya Saude kamar maroƙa sai faman zabga masa godiya suke. Ina lura da Anty Amina dake ta faman cika tana batsewa bani da tabbacin mai aka mata da alama kuma kamar bata ji daɗin rawar jikin da suke ta yi ba.
Sharifa ya miƙo mun ya na cewa Bilal
"Ba yanzu zaku wuce gida ba? Dare fa ya fara ga gurin da sauro kada a ɗibar ma Sharifa malaria". Naji daɗi har raina da Bilal ɗin ya ce tafiya zamuyi Fadila da Hadiza ma suka ce tafiyar zasuyi muka fita gaba ɗaya ya rage Anty Amina da Yaya Saude wadda zata kwana da Hajjan. A hanya Hadiza ta sauka Bilal ya tare mata Adaidaita da zau ƙarasa da ita muka wuce tare da Fadila ban so kwanan da ta ce zata yi a gidan mu ba. Har gida ya sauke mu, a hanya ya cewa Bilal
"Ya dai kamata fa ka samu mota ko ƙarama ce saboda irin haka" shi kuma yayi dariya ya ce
"Tukunna dai ai har yanzu ban isa riƙe mota ba, yanda rayuwa ta ƙara tsada mota ai sai irin ku dai manya mu dai barmu mu cigaba da hawa Adaidaita sahun da muka fi ganewa". Hafiz ɗin ya yi dariya ya ce
"Gara ma kace baka da ra'ayin siyan mota zan fi yarda idan kuma haka ne ai ita Madam na san ba zata ƙi ba sai ka siya mata ko dan saboda hidimar yara ko kema kin fi ganewa hawa Adaidaita sahun?" Ya jefo mun tambayar, murmushi kawai nayi na ce
Hawa Adaidaita ai sai dole gara dai ya taimaka ya siya mana motar mu huta"
"To ka dai ji abinda Madam ta faɗa" Cewar Hafiz ɗin. Zancen motar suka cigaba dayi har muka isa. Ua zaro kuɗi daga aljihun sa ya sakawa Sharifa a hannu sanda zamu sauka nayi masa godiya muka wuce.
Muna ƙoƙarin shiga falo Fadila ta ce mun
"Yanzu ko kunya bakya ji da auren ki a gaban mijin ki kike washe baki kina magana da wani namijin daban? To tun wuri idan ma zaki shiga hankalinki ki shiga dan Yaya Hafiz da iri na ya dace" ta faɗa tana wani watsa hannu da juya ido.
Kallonta nayi cike da mamakin kalamanta na ce
"Da alama kinyi hauka ko Fadila? Ban gane na washe baki ina masa dariya ba? kin san me kike cewa?"
"Tsaki ta yi ta shige ciki kamar gidan ta. Na bita da kallo kafin na bi bayan ta zuciya ta na tafarfasa na ce
"A zaton ki kowa shashasha ce irin? Ko zamanin yammatanci na ban banzatar da kaina nayi alaƙar banza da maza ba balle yanzu da nake da aure kuma wai da abokin miji na. Kije ke da Allah ƙazafin da kika mun" na nufi ɗaki dai dai lokacin Bilal ya shigo, tana ganin sa ta shiga matsar hawayen ƙarya tana cewa
"Ni kike cewa karuwa Halima?"
"Da Allah malama dakata duk naji abinda kowaccen ku ta faɗa, ki shiga hankalin ki ba kowanne iskanci zan ɗauka ba yanzu" ya faɗa yana nuna ta da yatsa. Murmushi na saki raina fes da yanda karo na farko ya tsaya mun na kalleta na ce
"Ba a koda yaushe ƙarya da munafunci suke cin nasara ba nan gaba kin san me zaki faɗa" na wuce ɗaki Bilal ya biyo baya na.
"Saboda ba mahaifiyar ki bace a Asibitin shiyasa sai da kika ga dama sannan kika je ko? Ai da kinyi zamanki kawai ma baki je ba dan banga amfanin da zuwan naki ya yi ba" ya faɗa take murmushi kan fuskata ya gimtse. A hankali na ce
"Wace irin magana kakeyi haka Bilal? Wlh kana kashe waya na tafi, na fi awa guda a waje kafin security ya barni na shiga kai kuma nayi ta kiran wayarka tun ina hanya amma bata shiga ba.."
"Dalla malama rufe mun baki maƙaryaciya kawai" ya dakatar da ni cikin tsawa. Wani sanyi na ji tun daga kaina har ƙafafu na, na bishi da ido ganin ya nufi kan gado ina da na zube kuɗin da Hafiz ya bawa Sharifa ya kwashe su ya fita daga ɗakin. A hankali na sulale a ƙasan in da nake tsaye saboda yanda ƙafafu na sukayi matuƙar sanyi. Har ta fara kai mu ga zagi kenan? Kullum gaba abun yake yi a maimakon ya yi baya.
Daƙyar na ƙarfafi jiki na na canzawa Sharifa diaper na fita na dama mata abinci Fadila na kwance kan kujera tana waya na wuce kitchen na haɗo abinci na koma ɗaki, duk yanda nake jin yunwa haka ma kwanta wani irin abu nake ji da ban san yanda zan misalta shi ba. Da asuba ina jiyo shi yana sharar tsakar gida, sai da gari yayi haske kafin na fito ina takawa a hankali saboda yanda yunwa ta gama rarake mun ciki. Sai da na fara haɗa baƙin shayi na sha yan hanji na suka warware kafin na shiga fere doyar da na gani a kitchen ɗin. Ban san ya yake so ayi da ita ba dafawa za'ayi ko soyawa ko fate?
Na gama na kwashe ɓawon kafin na fita daga kitchen ɗin da niyyar zuwa na tambaye shi yanda za'ayi da doyar sai gashi ya shigo muka ci karo a bakin ƙofa. Matsa masa nayi ya shiga, ya aje ledar ya matsa gaban sink in da na ajiye robar da doyar take ciki ni dai ina tsaye ina kallon sa kafin murya kamar wanda aka cusawa tsumma a baki ya ce
"Ki rabata biyu tayi yawa idan ya so kiyi mata fate da sauran da daddare. Murmushi na yi ma ce
"Soyawa za'a yi yanzu?"
"Ke baki san abinda ya kamata kiyi ba?" Ya hayayyaƙo mun, sai na wuce in da ya ajiye leda ina cewa
"Har yaushe na fara yanke hukunci akan abinda ka kawo cikin gidan nan? Ai sai yanda kace ayi. Soyawa za'ayi da ƙwai ko sauce za'ayi mata?"
"Ki soya ki dama kunun gyaɗa ga gasara nan a ciki" ya faɗa. Kamar na ce masa gyaɗar bata da yawa ta kuma ta Al'amin ce amma dai nayi shiru kawai na ɗauki tukunya na rage doyar kamar yanda ya ce yana tsaye. Tare suka fita da Fadila bayan na gama haɗa abin karyawar. Na fashe da kuka ina kallon doya ƙwara ukun da suka bar mun a matsayin rabona. Ganin ina kukan ya saka Sharifa ma ta saka kuka dole na rarrashi kaina dan tayi shiru.
Kafin a sha biyu na kammala abincin rana na zuba na asibiti a zatona zai dawo ya ɗauka ko zai turo amma har aka fara shiga masallaci bai dawo ba na kira wayar sa har sau biyu kuma bai amsa ba sai kawai na shirya na tafi. Gidan Mama na fara biyawa na ajiye Sharifa, dama shinkafa da wake da mai da yaji na dafa ganin sun gama abincin rana na canza fulasai na zuba miya a maimaikon Mai na haɗa komai. Mama ce ta ce na jira Abba ya dawo daga masallaci sai muje tare da ita ta duba Hajjan, sai uku da wani abu Abban ya dawo sannan muka tafi. Muna shiga asibitin zuciyata ta fara bugawa, na san da wahala idan Bilal bai yi fushi ba ko da yake dole ma yayi fushi har ƙarfe uku da wani abu amma ba'a kawo musu abincin rana.
Ina ga ganin Mama ya saka kai tsaye aka bar mu muka shiga sai dai kuma ban gansu a gadon jiyan ba. Wata Nurse da jiyan naga ta zo ta duba jinin da aka saka mata na tambaya tace sun koma Retainer ship. Ba yabo babu fallasa suka karɓe mu, ganin kwanukan abinci yasa hankali na ya kwanta tunda dai basu zauna da yunwa ba. Mama bata jima ba ta musu sallama ta tafi bayan ta ajiye wa Hajja dubu ashirin kuɗin dubiya. Har ga Allah banji daɗin yanda ko a fuska basu nuna jin daɗi ba balle su gode mata. Tare muka fita na rakata mota muka ci karo da Anty Amina wadda da alama itama zuwan ta kenan suka gaisa muka wuce.
"Amma dai ki dawo da wuri saboda waccen rigimammiyar da kika baro karta ishe mu da kukan ta na rashin dalili" Mama ta faɗa bayan da ta shiga mota. Ina tsaye har suka tafi kafin na koma. A ɗakin na tarar da Bilal na tabbatar kuma ya gammu tare da Mama tunda yanzu ya dawo amma bai tsaya ya gaishe ta ba ya wuce ciki abunsa. Na samu gefe na zauna dan ɗakin yana da girma akwai kuma wadatar gurin zama, bai ce mun ƙala ba nima ban ce masa ba suna ta hirar su har da Hajjan kace gidan biki ne na wai Asibiti ba. Sai da aka kira La'asar ya fita, nima fita nayi na tafi in da naga an shimfiɗa kafet nayi sallah ta acan. Ina gurin a zaune na hango Bilal yana tahowa da wasu mata biyu a bayan sa sai Namiji da kaya riƙi riƙi.
Da farko ban zata tare suke da matan ba tunda mutane nata shige da fice a gurin sai da naga sun shiga gurin da ɗakuna suke. Mayar da hankali nayi kan wayata da nake dubawa amma haka kawai zuciyata ta ringa kaɗaita mun son sanin su waye baƙin. Ɗaya da facemask a fuskarta dan haka ban gane ta ba wacce fuskarta take a buɗe kuma ban santa ba. Ƙoƙarin cire tunanin su nayi a raina amma na kasa, dole na tashi na koma ɗakin ina tafe zuciyata na bugun da ban san dalilin sa ba.
Ina tura ƙofar ido na ya sauka cikin n mai facemask ɗin. Gaba na ya yanke ya faɗi nayi saurin yin a'uziyya a zuciya ta. Ta zubo mun idanuwan ta masu girma haka nima na ringa kallonta dukda yanda kallon nata yake sake assasa gudun zuciya ta. Farace tas farin gaske kuma ba na bleaching ba, tana da kyau wanda ko mai hassadar mutum ba zai ƙarya ta hakan ba a shekaru kuma zata iya haura talatin dukda jikinta bai nuna shekarun ba amma aka ce ido ba mudu ba amma ya san ƙima.
A hankali nayi sallama dukkan yan ɗakin suka zubo mun ido sai lokacin ita kuma ta ɗauke nata idon daga kallo na. Na wuce gurin da na tashi na zauna ba tareda na kalli kowa a cikin su ba. Muryar Hajja na ji tana cewa
"Halima baki ga baƙi a ɗakin bane?" Sai lokacin na ɗaga kai muka sake haɗa ido da ita ta sakar mun murmushin da ya sake faɗar mun da gaba kafin cikin muryar ta da naji kamar na taɓa jin ta a wani guri ta ce
"Halima ce?"
"Ita ce" Bilal dake tsaye kusa da ƙafafun Hajja ya faɗa yana kallo na. Na mayar da kaina ƙasa kafin na ce
"Ina wunin ku?"
Ban san sanda ta taso ba ƙamshin turaren da na ji dab da hanci na ya saka na ɗago kai ta kuma sakar mun murmushi haɗi da miƙo mun hannun ta ta sigar musabaha tana cewa
"Sannu Maman Al'amin". Murmushi na ƙirƙira na miƙa mata hannun, hannuna na da laushi amma sai na jishi tamkar na namiji a cikin nata. Ta dafa ni ta ce
"Ina yara na?"
Maimakon na bata amsa sai na kalli Bilal da ya zubo mana ido fuskar sa ɗauke da yanayin da na kasa fassarawa.
"Ki dawo ki zauna mana JALILA ku da kuka sha hanya zaki tsaya surutu kuma" Hajja ta faɗa, sai na ɗaga kai da sauri na kalleta bugun zuciya ta yana ƙaruwa. JALILA na ji ta ambata, JALILA abokiyar aikin Bilal ta can Headquarter su ko kuwa wata daban?
Dama haka JALILAR take budurwa ce ba matar aure ba yanda nake tunani?
Haka kawai na ji zufa na tsatstsafomun dukda a ɗazu sanyin Ac har takura mun yayi shine ma dalilin da ya saka na tafi waje nayi sallah. Ta sake sakar mun murmushi kafin ta koma in da ta taso tana kallon Bilal ta ce
"Yau naga Maman Al'amin". Murmushin yaƙe yayi ya ce
"Ai kuwa dai yau kinga Halima"
"Babu wanda zai ce ta haifi su Al'amin tafi kama da yayar su" ta sake faɗa tana yar dariyar da ta saka na ji kamar numfashi na zai tsaya. A hankali na miƙe ba tare da na kalli kowa ba na nufi ƙofa na ci sa'a kuma har na fita babu wanda ya dakatar da ni.
Na zauna kan bencin da ke ƙofar ɗakin haɗi da dafe ƙirji na da hannu biyu ina sauke numfashi. Ina nan zaune suka fito gaba ɗayan su da suke cikin ɗakin banda Anty Amina ina jiyo muryar Hajja ma musu Allah ya tsare hanya babu wanda ya lura da ni a cikin su suka wuce. Tashi na yi na bi bayan su, na tsaya daga can gefe ina hango su jikin wata mota, gaba wacce suka zo taren ta shiga ita da Bilal suka shiga ba, ji na ringayi kamar mafarki ne ba wai gaske abin yake faruwa ba. Na shiga laluba jiki na ina neman wayata dan na kira shi na tabbatar da gaske shi ne suka shiga bayan mota da wata Mace ba ni ba ko kuma dai idanuwa ne kawai suke hasashen gaibu?
Banji waya ta a tareda ni ba na tuna sanda na koma ɗakin a gefe na na ajiye ta ba cikin aljihu ba dan haka na koma da sauri ina waigen motar da ta tashi har sun fice daga harabar gurin ajiye motocin. Yanda kasan anyi ruwan sama an ɗauke haka sukayi shiru ina shiga ɗakin, ni ba ta su nakeyi dan ko sunyi maganar ba bana zaton zan fahimci abinda suke cewa. Na ɗauki waya ta na fita ina jiyo yanda Fadila da Hadiza suka sheƙe da dariya kamar wasu taɓaɓɓu harda tafawa. Ina kiran layin sa aka ce mun a kashe yake ba tareda na koma nayi musu sallama ba kawai na fice daga Asibitin na wuce gida.
I wanted to summarize it in one or 2 chapters but i was overruled
Nagode da masoya na haƙiƙa waɗanda ko sunyi fushi basu manta tunanin su, waɗanda suke yiwa Marubuci kallon Mutum ba wai Bawa da suka siya da kuɗi ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 08142548705* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 32*
*Barkanmu da Sallah yan uwa* 🙏🏽
Sai da na fita kofar asibitin kafin na tsaya ina raba ido, ina zan nufa ne ma? Gida zan tafi ko kuwa gari zan shiga cigiyar inda