Showing 81001 words to 84000 words out of 257873 words

Chapter 28 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

522

ai dai kunga gidan nan beyi kama da wanda mutum yake zaune a cikin sa ba tun da har can ɗakin sa kun duba duk babu alamar yana kwana a gidan nan. Ni tsoro nakeyi koma wani mugun abu ne ya same shi" na ƙarashe cikin sabon kuka.

Yanda Mama Fauziyya ta buɗe baki ze baka tabbacin ta rasa abin faɗa ne, a fusace Anty Labiba tace
"Dan ubanki ai se ki bazama ki binciko in da ya shiga. Ki tashi mu tafi idan kuma baki gaji da kwasar takaicin bane se ki zauna ki taya ta kwana ni dai nayi nan" daga haka ta nufi ƙofa itama Mama Fauziyyar ta miƙe ta bita ganin haka yasa na rufa musu baya ina fashewa da sabon kuka nace
"Ni wlh bazan iya zama ni kaɗai ba gida zan tafi"
"Ai kin san hanta maza tafi amma karki kuskura naga ƙafar ki kusa da motar mu ki jira idan muka tafi se ki biyo bayan mu" cewar Mama Fauziyya. A bakin ƙofa na durƙusa bayan fitar su na ringa rusa kuka baji ba gani, se da baby na ya fara kuka kafin na tashi daga gurin na ɗauke shi daga kan kujerar da yake kwance na zura masa ido ina kallon sa hawayen dake saukar mun suna ɗisa akan fuskar sa. Rungume shi nayi ina cigaba da kukan. Ban ma san me ya kamata nayi ba, an shiga an fita tsakanina da Abba na kawai dan ba abinda za'a gaya mun na yarda wai shi yace a dawo dani gidan nan.

Jin yaƙi yin shiru yasa na miƙe na shiga ƙoƙarin goya shi, motsi naji kamar ana murzawa ƙofa muƙulli kafin kuma aka shiga bugawa, sakko da yaron nayi da sauri na ƙanƙame shi kamar wadda aka zo ƙwace shi, a hankali na nufi ƙofar, ta jikin yar ɓular leƙe na hangi waɗanda ke tsaye, Abubakar ne da Nasir sun ruƙo wani da banga fuskar sa sosai ba saboda kansa yana jingine ne jikin kafaɗar Abubakar ɗin. Ganin waɗanda na sani ne yasa naji hankali na ya kwanta dan haka na buɗe musu ƙofar. Gabana ya yanke ya faɗi ganin wanda suka ruƙo ɗin, Bilal ne. A yanayin da yake yafi kama da wanda yasha daƙyar a hannun yan fashi ko ɓarayin daji. Da sauri na matsa na basu guri suka shigo se lokacin na lura ashe har da Hajja da Anty Amina Yayar sa.

Jikina har rawa yake ina kallon su, Hajja ta fashe da kuka tana cewa
"Wannan masifa da bala'i har ina?"
"Dan Allah Hajja kiyi shiru, kin dai ji abinda likita yace yana buƙatar hutu sosai kar a dame shi da hayaniya ko wasu tambayoyi shiyasa ma nace ku wuce gida kawai amma kuka biyo mu kin zo kuma zaki cika masa kunne da hayaniya" Abubakar da suka kwantar da Bilal ɗin akan kujera ya faɗa, se kuma ya kalli in da nake tsaye kamar me jiran a bani umarni na fice a guje yace
"Anty Halima ƙaraso mana".

"Halima? Au dama tana gidan nan?" Hajja ta faɗa tana waige na. Kamar mara laka na matsa cikin falon, Hajja ta sake fashewa da kuka tace
"Ba shakka, yanzu kina gidan nan kwana har biyu sama ko ƙasa ba'a san inda mijinki yake ba amma baki biyo kadi ba Halima? Ko da yake baki da asara idan ma mutuwa yayi hankalin ki kwance tunda kin aje iri se dai kiyi jiran lissafi kawai"

"Wai dan Allah wane irin abu kikeyi haka Hajja?" Anty Amina ta sake katseta cikin fushi, se ta miƙe ta isko ni tare da karɓan yaron hannuna tana cewa
"Zauna Halima, sannu kinji".
Zaman nayi ina zare ido dan gaba ɗaya kaina ya kulle da abinda yake faruwa. Daga kwancen da Bilal yake ya miƙo mun hannu, na kalli fuskar sa da tayi luhu luhu kusan kamannin sa ma sun canza ban san sanda na isa kusa dashi ba na durƙusa lokaci ɗaya na fashe da kuka.

Sha biyu ta gota sanda Hajja na Nasir suka bar gidan Abubakar da Anty Amina suka zauna zasu kwana tare damu. Abubakar ɗin ne ya taimakawa Bilal yayi wanka bayan ya ɗan warware daga magagin da yake tayi kamar wanda baya cikin hayyacin sa. Shayi kaɗai ya iya sha, a nan falo suka kwana ni kuma muka kwanta a ɗaki da Anty Amina. Kwata kwata na gagara runtsawa, ga tunanin abinda ya samu Bilal dan har sannan babu wanda yace mun komai ga babyn dake ta tsula kuka har ya zarce na kwanaki biyun da mukayi a asibiti, haka muka kwana Anty Amina na jele dashi tsakanin ɗaki da falo idan ta gaji Abubakar ya karɓa Bilal dai yasha bacci saboda magungunan daya sha dan se guraren takwas na safe ma kafin ya farka yayi sallah.

**********
A hanyar komawa Mama Fauziyya take cewa Anty Labiba
"Halima ta bani tausayi Labiba, be kamata ace a yanzu ne Yaya Aminu ze nuna fushin sa ba. A gani na da haƙuri yayi a zauna a gida ko sati biyu ne tayi, idan har aka ja wannan lokacin be zo ba ina ganin komawar ma bata da amfani kawai a kira shi ya bata takardar ta shikenan dama ƙila rabon wannan ɗan ne kuma gashi an haifa".

"Anty Fauziyyah kenan, ni dai bazan tofa komai akan sabgar Halima ba amma lokaci ze yi alƙalanci" Anty Labiba ta bata amsa. Da suka isa gidan ma seda Mama Fauziyyar ta sake yiwa Mama magana akan ta taushi Abba Halima ta dawo gida.
"Duk ma wanda za'a tura ta zauna da ita ba kamar tana nan gabanki ba. Sanda ya kamata ku nuna mata kuskurenta bakuyi ba ba se yanzu da hakan ze iya cutar da ita ko ya cutar da abinda ta haifa ba. Kuskure ai an rigada anyi shi tun farko da aka biyewa son zuciya aka yi auren haƙuri kawai zakuyi ku tayata karɓar ƙaddarar ta" cewar Mama Fauziyyar.

Mama ta nisa tace
"Ban taɓa ganin ɓacin ran Abban su irin na wannan karon ba. Abinda yake ta nanata mun ya kira yaron nan da kansa har sau biyu be amsa ba ya kuma aika masa da saƙo dukda haka be biyo baya ba, kenan da ace mutuwa ma Haliman tayi haka ze wofantar da ita har ayi mata sutura a bunneta babu shi babu wani nasa a gurin kome? Rantsuwa fa yayi akan ba zata zauna ba, duk ƙaunar dake tsakaninsa da Halima ya yanke wannan hukuncin ai dole na ɗaga masa ƙafa idan ya huce nasan da kansa zeyi duk abinda ya kamata. Ni yanzu damuwata ma wanda za'a tura matan. Na kira Gwaggo Habi tunda ita tace in dai tana raye aka aurar da Halima ta haihu zata je mata zaman jego amma karkiji tijarar data mun wai na kira Yaya Salamatun data ɗaure ƙugun ayi auren taje ta zauna mata.

Na yi tunanin ko Yabi ta gidan Alhaji Salahu to daga maganganun da suka ringayi jiya da suka dawo daga asibitin ma kawai na fasa karma taje ta sake samo zancen da za'a yi yawo dashi a dangi, se dai ko Zainab taje ta kama mata ayyukan gida idan yaso tayi masa magana can a dangin sa ya nemo musu me saka ruwa da wankan jinjirin kafin ta iya".

"Oh Allah, yanzu Halima da gatan ta da komai ace ana kame kamen wanda ze mata zaman jego? Allah dai ya wadaran kunnen ƙashi irin na yayan zamani. Shikenan; ki tura mata Zainab ɗin idan yaso ni na ringa zuwa ina mata wankan mu gani daga nan dai zuwa kwana uku shi kuma Abban nasu kiyi ƙoƙari ki lallaɓa shi ya barta ta dawo gida dan Allah. Ni badan bama se nacewa Abban su Sadam ya kira shi ya taushe shi dan gaskiya Yaya Amina aka bar yarinyar nan a gidan can wlh zata lalace ne kawai ga jego ga damuwar miji kar muje ya ɗora mata depression a kawai". Akan haka suka rabu dama Anty Labiba bata ma zauna a ɗakin ba balle ayi tattaunawar da ita. Har cikin ranta tana tausayawa Halima, se dai rashin sanin ciwon kan da Haliman take gwadawa yasa take danne duk wani tausayin ta take so a barta da wayonta tunda tana ganin ze fishsheta.

WASHE GARI

Da wuri Nasir yazo yayiwa Bilal sauran allura guda ɗaya cikin ukun da aka ce za'a yi masa. Anty Amina ce tamun wanka sama sama da ruwan heater shi kuma babyn ta dafa a gas ta masa a wani ɗan baho na saitin kayan robobi na dan ba'a siya masa saitin baho ba. Cikin kayayyakin dana ɗan siya na ɗakko mata riga ta saka masa mai ma se stella da nake shafawa na bata ta shafa masa dan haka nan na rasa ɓoye duk kayan sa da muka taho dasu daga gidan mu. Tana shafa masa man take tambayata bamu siyi man jarirai bane ko yaya da za'a shafa masa stella? Ni dai murmushi kawai nayi na ɗakko mata ledar da yan kayan dana tsinta suke da dubu goman daya bani sanda zeyi tafiya nace mata

"Iya kuɗin daya bani kenan yace nayi siyayya waɗannan ma cikin kuɗin da ake bani a gida nake ragewa ina siyan su".
Sak tayi, bata kuma sake cewa komai ba ta ƙarasa shirya yaron ta fita dashi nima na shiga shirya kaina. Yini guda yan uwan sa nata zuwa jaje, a ya da na fahimci abun dai kamar dai ɓata Bilal yayi se jiya aka ganshi. Wai duk wanda yazo se su ringa tambayar yaushe na haihu? Kamar dai labarin be iske su ba suke nufi har da ita kanta Hajjan bayan tijarar data so ta mun daren jiyan data dawo yau ba kunya ta ɗauki ɗan tana ta wata murna wai jiya duk hankalinta ba'a jikinta yake ba shiyasa bata fahimci komai ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 21*
Ina ɗaki, hayaniyar yan dubiya duk ta cika mun kunne, tun da Anty Amina ta tambaye ni abinda za'a dafa da rana na nuna mata shinkafa da mai wanda su kaɗai suka suka rage mana a gidan, ina ganin Hajja ta shiga kitchen ɗin na fito na barsu. Ta biyo ni ɗaki tana tambaya ta sauran kayan girki nace mata iya abinda muke dashi kenan, zata yi magana Anty Aminan ta jata waje shikenan nayi zamana a ɗakin ban sake fita ba suma kuma babu wadda ta sake leƙa ni. Da yaron yana gurin su ma aka maido mun dashi shikenan naja ƙofa ta na kulle duk da yunwar da nake ji dan da safe shayi kawai nasha su suka cinye sauran abincin jiya dana dawo dashi yanzun ma dana rasa mafita shayin na sake haɗawa na sha da cake, duk da ba wai na ƙoshi bane amma na rage hanya, ina gamawa na tattara komai na mayar cikin wardrobe har ina mamakin kaina wai yau ni ce nake ɓoyon abinci?

Da yamma Mama Fauziyya da Anty Labiba da Anty Mimi se wasu ƙawayen Mama su biyu suka zo tare. Tun da safe da Mama Fauziyyan ta kira ni akan zata zo tayi mana wanka na gaya mata yayar Bilal tana nan se tace zasu shigo da yamma toh.
Zuwan su ne ya fito da ni na tsaya daga bakin ƙofa jin suna gaisawa da yan uwan Bilal. Duk su biyar ɗin naji sun masa sannu, amma babu wacce ta tambayi ba'asin meya same shi suka tsallake suka shiga ɗaki na. Se da muka gaisa na fita na ɗakko musu ruwa, ina shiga kitchen Fadila ta biyo baya na. Ban ko kalli in da take ba na ɗebi ruwan a faranti na fita na barta a tsaye.

Ƙawayen Maman basu jima ba suka tafi bayan kowacce ta ajiye mu. Abin barka. Anty Labiba ce ta tafi rakasu, bayan fitar su Anty Mimi tace
"Me kuma ya samu mijin naki Halima?" Mama Fauziyya dai na ta faman juya yaron kafin ita kuma tace
"Amma dai tun safe ba'a canzawa yaron nan kaya ba ko? Ga rigarsa nan har da stain ɗin manja a jiki".
Ƙasa na yi da kai na kafin na ce
"Nima ban san abin da ya same shi ba, bayan kun tafi jiya suka dawo dashi har yanzu kuma basu ce mun komai ba" na faɗa bayan da Anty Labiba ta dawo ta sake maimaita mun tambayar Anty Mimi. Su ukun suka haɗa baki gurin cewa
"Allah ya rufa asiri" kafin Anty Labiba ta wuce banɗaki ta haɗo ruwan zafi a bahon da aka ma yaron wanka da safe ta fito tana cewa
"Se ki tashi kema kiyi wankan duk da wannan ruwan ɗauraye jiki kawai za kiyi ba wani wankan kirki ba. Bari na kira Mu'azzam idan ze kawo Zainab ɗin su taho da babbar tukunyar nan da murhu, ki dai tsaya kiyi wankan gaske wlh in ba haka na jikin ki zaki lalata".

Se da nayi jira ruwan heater ya ƙara tafasa kafin nan naci tuwon da Mama Fauziyya ta taho dashi. Ina jin yanda suke kallo na amma na ɗauke kai na ci gaba da cin abincin dan yunwa nake ji sosai, kowa dai yasan cikin jego babu yanda za ayi shayi ya riƙe ni tun safe dan da suka dafa shinkafar ko tayi basu mun ba. Anty Mimi da bakin ta be fiya shiru ba ce ta kasa daurewa tace
"Baki ci abincin rana bane Halima?"
"Na ci mana Anty" na bata amsa ina ɗauke kwanon gaba na, kafin kuma wani ya sake cewa komai na fice dan kai kwanon kitchen. Motsin da naji a bayana yasa na juya da sauri naga Hajja ce. Fuska ba yabo ba falla sa tace
"Naga sun zo miki da abinci ko? Se ki ɗebo a bawa mijin ki idan ma mu ba zaki bamu ba". Nayi shiru na rasa abinda zan ce mata. Wato idon su na kana duk abinda ake wucewa dashi. Ganin ta juya ta fita yasa na sauke ajiyar zaciya na bi bayan ta. Tunanin ta yanda zan ɗebo abincin na fito dashi ba tare da sun mun surutu ba na shiga yi.

Cikin sa'a, ina komawa ɗakin na tarar da Anty Labiba na cin sauran tuwon dama malmala ɗaya ne tun da uku ne na ci biyu. Se na wuce sum sum na shiga cire kaya na a raina naji daɗi ta wani gefen amma kuma yanzu ban san ya zamu kaya da Hajja ba. Sanda na fito wanka Anty Mimi ta ce suruka ta na kira na, se da na shirya kafin na fita. Duk jama'ar yan dubiyar sun watse se ita kaɗai a falon Bilal ɗin ma an mayar dashi can falon sa yana tare da Abubakar.

"Wato saboda kin raina ni Halima nayi miki magana kiyi shigewar ki ɗaki ki bar ni ina zaman jiran ki ko?" Ta faɗa fuska cike da fushi. Kafin na bata amsa Anty Labiba ta fito da kwanukan tuwon bata ko kalli in da muke tsaye ba ta shige kitchen; se na yi ƙasa da kai nace
"Wlh mantawa nayi Hajja, se da na fito daga wanka suka ce kina kira na kafin na tuna kuma na tarar sun cinye sauran abincin dama bashi da yawa".

"Dole kice kin manta mana tun da kin raina ni baki ɗauke ni a bakin komai ba; idan uwar da ta haife ki ce ta faɗa miki magana zaki tafi sharafin gaban ki ne ba tare da kin aikata abin da ta umarce ki ba?" Ta faɗa cikin tsananin fushi,
"Kiyi haƙuri" na faɗa murya ta na karyewa. Kamar ma na sake zuga ta ne tace
"Saboda tsabar baki da tausayi mutumin na kwance hajaran majaran bayan kece silar shigar sa halin da yake ciki amma abincin da zaki bashi ya ci kike baƙin ciki a kai; mu da muka zo jinyar sa baki bar mu ba kin haɗa mu da shinkafa da mai se kace wasu mabarata kika shige ɗaki kika bar mu wato kora da hali kike mana ƙarara, to yanzu zamu tafi se ki ƙarata Bilal dai ba zaki canza masa uwa ko dangi ba ba kuna ki isa ki hana wani nasa shigowa cikin gidan nan ba".

"Ikon Allah" na faɗa a zuciya ta dan ban hango dalilin wannan faɗan rashin dalilin nata ba; kuma ta ina na zama silar ciwon Bilal? Kiran da Anty Labiba ta mun daga kitchen ya sa na sake cewa tayi haƙuri na juya na tafi ina ji tana ci gaba da banbamin ta da faɗar maganganu.

"Me za'a girka miki kafin mu wuce?" Anty Labiban ta faɗa bayan dana shiga kitchen ɗin, se kawai na faɗa jikin ta na fashe da kuka. Yanda tayi sak nasan jikin ta ne yayi sanyi kafin ta tattaro ƙarfin hali ta janye ni tana cewa
"Meye haka kuma? Kukan me kike yi?"
"Dan Allah Anty badan hali na ba kiyi haƙuri" na faɗa cikin shassheƙa. Se ta ce
"Da kika mun me Halima?"
"Ni dai kiyi haƙuri dan Allah ki tausayawa rayuwa ta ki taya ni roƙon Abba ko sati biyu ne naje nayi a gida idan na warke se na dawo" na sale faɗa, se tayi tsaki ta ce
"Ke baki da baki ne halan? Ni da Allah ki nuna mun in da kayan girki suke idan kuma bakya buƙata mu tafi magriba ta kawo kai".

"Shinkafa kawai muke da ita se mai kuma kin ga bashi da lafiya balle ya bayar da abin da za'a yi cefane ko kuma ya siyo" na bata amsa cikin kuka. Se ta kama baki tana kallo na tace
"Su yan uwan nasa da suka cika gidan duk cikin su babu wanda yasan hanyar kasuwa ko da zasu siyo cefanen?"
Shiru na mata na ci gaba da kuka na. Duk yanda na ringa roƙon su akan su tafi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login